← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 152

Sashe 135

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna shigowa ward they see Bareerah coming out of the room da Annie take da alama kamar akwai wanda take nema,but har suka k'araso bata gansu ba sai da Nusrah tace "Bareerah Aunty! Who are u looking for?" Quickly ta waiwayo tana sakin murmushi tayi sauri ta matso inda suke za ta karb'i basket a hannun Nuraz tace "wollahi Abbah na fito nema,yanzun yayi waya yace suna hanya tare da bak'i,ashe basu k'araso ba" Nusrah tace "Ohh! Maybe yanzun su shigo" bata gama magana ba,Bareerah ta hango shigowarsu with about 10+ people,ta bud'e ido da sauri tace "ga su suna shigowa ma" Nusrah tace "Ohk let's wait them to come in,my hand starts to held" Nuraz kam tuni yayi gaba,Bareerah tayi dariya jin abunda Nusrah tace,tace "ke dai babyn Annie duk kin zama raguwa,anya bamu kusa samun baby ba?" Nusrah tayi murmushi shyly tace "Kai Aunty i have nothing fa" daga haka tayi gaba k'asan zuciyarta tana addu'ar Allah sa abunda Bareerah ta fad'a ya zama gaske,surely da ta kasance cikin infinite joy,haka kawai sai ta tsinci kanta da shafa cikinta a fili tayi furucin "I wish maganarkin nan ya tabbata,i know Hayat would be more than happy,dama ya fi ni damuwa da maganar cikin",tura k'ofar tayi tana sakin murmushi da sauri kuma ta mak'ale a tsaye tana kallon Annie dake jingine da bed tana feeding baby,wani k'ara tayi like a rattle da d'an gudu ta k'arasa ciki tana ihun murna,Annie ta bita da kallo tana sakin murmushi,Lolly da su Hajiya began to laugh at her for being so young,placing the basket dake hannunta towards the bed ta nufi gadon,kusa da Annie sosai taje ta zauna ta fara lek'en fuskar baby'n,sai kuma ta tab'e baki ganin ba baby girl d'in bace da fad'in "Annie! I like that baby girl" Hajiya tayi murmushi tace "sai ki yi k'ok'ari ki haifo mana" turo baki tayi tace "tou ni Hajiya y'ar k'arama da ni sai na haihu yanzu?" Hajiya glanced at her tace "kuji min ja'ira idan banda Allah bai nufa ba,ai yanzun da kin haihu ma ko kin kusa" turo baki ta sake yi tana k'unk'uni duka suka saka mata dariya,Annie tayi murmushi tana cire breast d'in a bakin baby'n tace "Don't worry baby u will not have to give birth until kin k'ara girma" ta washe baki tana dariya Nuraz da hankalinsa ke kan phone kamar bai ya jinsu ya furta "Uhn! Sai dai idan ba kya gidan ko?" duka suka kallesa,jin d'akin yayi shiru da sauri ya d'ago,yaga shi suke kallo,sai ya sauke kansa yana sakin murmushi dai² lokacin da su Abbah suke shigowa,he is at the forefront sai Baba da wasu mutane mata da maza kyawawa dasu,dukansu da suke cikin d'akin suka bisu da kallon rashin sani but no one showed it clearly until their sallama were answered,fuskar Abbah a sake yake fad'in "Bismillah ku k'araso ku zauna ga guri" dukansu dai gwanin burgewa daga mazan har matan kana kallonsu za ka tabbatar akwai jin dad'i tare da su,and idan batun naira ma ake yi itama ba bak'on su bane,bayan sun zauna and greeting each other in a friendly manner,Nuraz da ya tashi ya basu waje suka zauna ya kalli Nusrah kad'an fuskarsa a had'e ganin wani cikin samarin da suka shigo ya kura mata ido sai kallonta yake,fuskarsa babu walwala ya furta "Annie bari na lek'a office na dawo amma ba jimawa ma zanyi ba" Annie ta kad'a kai tayi masa addu'ah fuskarta a sake,har ya juya ya fara tafiya yace "Roohii! Zo muje office mu dawo" ta d'ago a shagwab'e babu kunya za tace ya barta ita dai yaje ya dawo Bareerah tayi mata ido,sai ta mik'e a hankali tana turo baki tana cewa "Hajiya mun tafi sai mun dawo" Hajiya ta raka Nusrah da ido tace "Oh! Ji min gulma,ni wannan sakaliyar matar tasa wai nan wani sabon iyayi zata ma mutane harda tura baki ita dole ba ta son zuwa ne ko me?" Lolly tana dariya tace "Kai Hajiya tou kiyi musu addu'ah,kina gani ma daga ke sai Annie kad'ai suka iya yiwa sallama" Hajiya ta tab'e baki tace "Tou Allah dawo daku lafiya,idan sun bada sallama kuma sai ku tarar da mu can gidan" Nusrah tana dariya ta d'agawa Lolly hannu tace "Bye Aunty" ta k'arasa fita a room d'in da sauri,a tsaye ta gansa yana jiranta fuskarsa cif babu fara'a,yana ganin ta tsaya rike da k'ofar bata rufe ba ya rik'o hannunta da sauri ya k'arasa rufewa,Nusrah dai ta bisa da kallon mamaki because ita dai ta san lafiya k'alau suka fito daga gida,yanzun kuma ta ga mood d'insa was changed,suka fara tafiya yana rike da ita a jikinsa,suna fita daga room d'in already Hajiya ta ga abunda ya faru ta furta "Magulmata biyu" Baba yace "A'a dai Hajiya kada ki tab'a min mata a kan idona" hajiya tace "Mata!? Wannan d'in?" Baba yace "K'warai kuwa baki ganta kyakykyawar gaske ba? Wannan da kike gani ko cikin jinsin aljanu ba za'a samu kamarta ba" gaba d'aya aka yi dariya,Hajiya ta tab'e baki tace "haba dai yo ko ni tsohuwa ma ai nafi wannan kyau" Annie dake k'ok'arin bawa Bareerah baby tace "A'a fa Hajiya ni dai kawai na gane kishi kike yi da babyna ta kwace mijin" Hajiya ta kyab'e baki tace "wane mutum,ko ta kwace ma zai dawo ne,aro na bata",bayan an tab'a barkwanci sosai Baba yayi sallama duka suka amsa,in a serious tone yace "Alhamdulillah alaa kulli halin" sai ya kalli Abbah yace yayi addu'ah,bayan Abbah ya gama kwararo addu'o'i,Baba ya waiwaya ya kalli Annie yace "MARYAMU!" Annie ta d'ago da sauri ta kalleshi,taga yana yi mata murmushi,bata san na mene ne ba kawai sai ta mayar masa,Babah yana ci gaba da kallonta yace "Kin san wad'annan bayin Allah'n?" Ya nuna mata su duka,haka Annie tayi ta kallon fuskokinsu but ta fi kallon mutum uku daga cikin matan y'an dattijai da suke zaune kusa da Hajiyar su Rafeek,kai ta kad'a a hankali bayan ta gama kare musu kallo bata gane abunda Baba yake nufi ba ta furta "A'a Baba ban gane su ba" su duka suka yi mata murmushi,a hankali Baba yace "Tou kema baki sansu ba ina kuma ga HAUWA'U?" Annie ta sake k'ura musu ido tana kallo da tunanin inda ta san wani fuskar mai kama da nasu,within thirty seconds ta bud'e ido sosai ta furta "Na tuna!" Baba ya kalleta yana murmushi yace "me za ki iya tunawa game da su?" Hawayen da suka kawo idanunta suna saukowa ta furta "Su ne da gaske Baba?" Lolly tayi saurin kallonsu ta kalli Annie tace "Annie! Su d'in su waye?" Sautin kukan Annie ya fara fitowa tana kallonsu har lokacin tace "K'annen Innarmu" a rikice Lolly tayi saurin mik'ewa tana yi musu wani irin kallo,da sauri kuma sai ta koma kusa da y'ar uwarta ta dafa kafad'arta da fad'in "Da gaske su ne wad'annan?" Annie ta kad'a mata kai tace "of course su ne! Su d'in jinin mahaifiyarmu ne,ga kamanninsu nan na gani" Baba ya jinjina kai yana kallon Annie da har lokacin take share hawaye yace "K'warai da gaske y'an uwan mahaifiyarku ne,amma na yi matuk'ar mamaki da kika iya gane su" Annie ta kalli yadda Lolly take had'e rai ta juya ta kalli Baba kafin tayi magana d'aya cikin dattijan uku ta furta "Ku gafarce mu watsar da ku da muka yi,muma ba'a son ranmu bane,lokacin da ya kamata ace mun kasance masu tsananin hak'uri ko don ganin mahaifiyarku ba ta raye sai duka muka biye dokin zuciya,lallai mun aikata kuskure mai girma a rayuwarmu,da mun yi hak'uri mun duba zumunci da bamu yi muku abunda muka yi ba,amma kuyi hak'uri haka Allah ya k'addara tun farko,shi yasa aka samu wad'annan sab'anin suka shigo tsakani" Annie ta gyad'a kai tana share hawaye tace "Babu komai mun yafe muku,ko da ma can da ace baku zo ba muna da niyyar zuwa mu neme ku" Matar tayi murmushi tace "Allah sarki ai Yaya ya sanar da mu" Annie tayi saurin kallon Baba tace "Baba dama kana zuwa amma baka tab'a kaimu wajensu ba?" Baba ya girgiza kai yace "Ban je ba,su suka zo har gida kusan shekara guda kenan" Annie tana jinjina maganar da Baba ya fad'a a hankali tayi murmushi,Baba yaga Lolly tak'i magana fuskarta babu walwala yace "Hauwa'u!" Lolly ta d'ago kai tana kallon Baba idanunta taf hawaye yace "kuyi hak'uri kinji,in sha Allah aka sallami y'ar uwarki zanyi muku bayanin komai" Lolly dai bata ce komai ba sai share hawaye da tayi,nasiha sosai Baba yayi musu haka Hajiya ma tayi musu,da yake duk Annie dama tafi sauk'in kai yanzun sai gashi tana ta fara'a Baba ya nuna musu k'annen Innarsu su uku yace "wannan ta farko itace Khadijah,ita take biyewa Innar ku,sai Asiya ga ta a tsakiya duk gidan su Innar ku itace auta,ita kuma wannan" ya nuna wacce Lolly ta tashi daga kusa da ita yace "Sa'adat tsakaninsu da Innar ku bayan Khadijah akwai maza biyu sun rasu da jimawa" sai mazajen su da suka zo tare da samari uku Junayd,Kazim da Abduljalal da k'aramin yaro d'aya da bai wuce 9yrs ba Khaleel,suka sake yi musu bayin kansu,kafin wani lokaci duk sai ga su sun sake ana ta hira da su kamar dama sun san su.
Chapter 135 · 0% Book details