← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 152

Sashe 141

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

In less than an hour asibitin ya fara cika da y'an uwa,Annie da su Bareerah,Maimunatu da Mommy matar baffanta Mr Sajid duk sun zo,Nuraz kam duk bayan mintuna yake kiran waya yana tambayarsu,idan akace bata haihu ba har yanzun sai yayi shiru yana tunanin anya zai biyewa su Hajiya ya zauna wani meeting? Abu tun ana batun minutes aka tafi hour but shiru kake ji,da yayi waya da su a time d'in ana asr prayer suke cewa ai har yanzun bata haihu ba,but Dr paredes yace da su nan da 6pm za ta iya haihuwa a ko wane lokaci,suna k'ara kwantar masa da hankali,bayan few minutes yana kwance cikin d'akin katafaren hotel da ya sauka yaji sam ba zai iya zama ba,and he couldn't seem to calm down at all idan bai je gareta ba,a taken yasa Clark to book them flight su koma UK,su ma company da ya zo gani kasar ya kira ya basu hak'uri and inform them there is an urgent excuse that has brought them home,but su saka wani lokacin daban in Allah ya amince shi kuma zai dawo,suka nuna masa babu komai tunda zaman da ya rage suyi dama biyu ne,k'arasa zama ne ba za'ayi da shi ba,duk abunda yake akwai idan an zauna kawai za'a turo masa duk ma abunda aka yanke,yayi musu godiya suka wuce airport,daga France tafiyar 32 minutes suka yi ya kawo su UK but all Nuraz seems to have spent almost a year in the airplane,suna sauka da suka shiga motocin da suka zo d'aukar su,daga airport kai tsaye ya bada umarnin a wuce Nuffield health,su Annie duka sai ganinsa suka yi kamar wanda aka cillo daga wani duniyar,Hajiya kowa yayi jigum suka bisa da kallon mamaki,ya d'auke kai ganin irin kallon da Lolly take masa suka gaisa da su Hajiya,bai wani jima da shigowa ba suna cikin gaisawa da su Afaf sai ga Dr Paredes ya fito,he looked at Nuraz with a smile da mamaki sosai a fuskarsa na ganinsa a lokacin suka yi shaking hands,Dr Paredes cikin tsokana yace "Dama zuwanka ma'am take jira kenan?" Nuraz smiled at not understanding what Dr Paredes meant,shima Dr Paredes d'in ganin bai fahimci abunda yake magana akai ba,yace "congratulations Dr psycho,ur wife has just given birth,and u've got a baby girl" fuskar Nuraz ta fad'ad'a da murmushi yana kallon Dr Paredes yace "zan iya ganinta yanzun?" Dr Paredes yace "me zai hana?" Su Annie duk suna jin ance ta haihu kowa ya fara murna da hankulansu duk a tashe yake because Dr Paredes told them that if she passed the time they must give her a CS,tare suka shiga da Dr Paredes suka bar su Annie suna kiran waya suna fad'an haihuwar,suna shigowa he began to point out where she was,aka kawo masa kyakykyawar baby girl d'insu a nad'e cikin tsadadden pink baby towel mai matuk'ar laushi,ya karb'e y'arsa duk da ba ta baby'n yake yi ba ta madam d'insa yake first,ya zauna gefen bed kad'an rik'e da baby'n yana kallon yadda take sauke numfashi a hankali,yayi murmushi ya shafa fuskar Nusrah da fad'in "Hello! Mr's Noor" idanunta ta motsa kad'an tana shak'ar k'amshinsa tayi maza ta waresu a kansa,tattausan murmushin da yake yi itama shi tayi masa,sai kuma ta fara k'ok'arin tashi ta zauna,yayi sauri ya d'an dafe ta yana kad'a mata kai,ta lumshe ido ta bud'e tana kallonsa muryarta a k'asa² tace "Sannu da dawowa" bai amsa ba sai kallon da yake mata yana sakin murmushinsa mai kyau,ta ji bai yi magana ba ta d'aga kai ta kalleshi a hankali ta taso daga kwanciyar and lean against him tana lek'en fuskar baby'n,murmushi ya kufce mata ta kalleshi sosai tana gyara ma baby'n fuskarta da towel ya rufe,tace "Hayat baby girl ce?" Yayi murmushi ya kad'a mata kai,farin cikinta ya kasa b'oyewa saboda tana son baby girl tace "woah! I love the baby girl so much" yace "Nima haka fa,kinga addu'ar mu ya amsu ko?" Ta kad'a masa kai da sauri tace "yeah! Allah raya mana" yace "ameen" shiru suka yi na wani d'an lokaci ya d'ago baby'n kad'an ya kai bakinsa dai² kunnenta,addu'o'i ya fara yi mata then yayi mata khud'ubah,yana gamawa ya kalli Nusrah wacce banda murmushi babu abunda yake kan fuskarta tana jikinsa a mak'ale tace "wane suna kasa mata?" Yayi murmushi yace "wane suna kike so?" Ta d'ago kai a hankali tana kallon idanunsa da sauri tace "Ni dai sunan Annie nake so" yace "Maryam kenan,sai kuma ana kiranta da wane sunan?" ta d'aga kai alamar tunani da sauri tace "Sai muna ce mata *MAYSAM"*,yayi murmushin sa mai kyau yace "Yeah! That's what i want" a tare suka yi dariya Nusrah tace "Ya akayi komai nace kaima haka?" Yace "ya baza ayi haka ba tunda mun kasance abu d'aya?" Dariya tayi tana kallon baby'nsu dake yamutsa fuska looks like tana son yin kuka,ya kalleta yana jira yaji me za tace,ganin yadda tayi kamar statue sai ya kalli inda take kallo,a hankali ya d'ago baby'n ya sumbaci baby pink lips d'inta yace "tou madam a ji damu kafin mu fara rigima,i know kukan yunwa ne zai zo yanzun" he didn't finish ta fara kuka Nusrah ta zuba mata ido tana kallo,sai da ya sake magana sannan ta karb'eta,tana gyara ma baby'n kwanciya a kan thigh's d'inta ya sauke mata zip k'asa,and helping her ta cire breast d'inta da suka yi wani irin cikowa,they made a bismillah together ta dangwala teat d'in a bakin baby,as soon as ta kama kamar za ta ci babu,tana fara jan milk Nusrah tayi k'ara ta cire da sauri tana runtse idanu,baby Maysam itama jin an mata dangwalili tana ta wuru²n neman abincinta ta bud'e murya iya k'arfinta ta fara kuka,da sauri Nuraz yace "what happened?" Duk ya rud'e ganin daga uwar har y'ar kowa da abunda yake damunsa,idanuta a rufe tace "wollahi ba zan iya ba ni dai" yace "mene ne baza ki iya ba?" Kamar za tayi kuka tace "shayarwar mana" ya zaro ido yace "ban gane ba" tayi saurin bud'e idanunta da hawaye suka cika tace "ka ji zafi kuwa da ta kama?" Kamar zai fashe da dariya saboda yadda tayi sai ya daure yana kad'a mata kai yace "How do i feel? Daurewa za kiyi ki bata haka ta sha,idan ba haka ba kuka za ta ci gaba da yi" tayi rau² da idanu tace "ni dai gaskiya a samu wani dabaran amma" yace "but what?" Tace "ba zan iya ba fa" yayi murmushi yace "alright! Ya kike so ayi yanzun?" Ta kalleshi tana turo baki tace "a samu mai raino ni dai" dariya ta bashi yace "mai raino fa kika ce? So what is the benefit here kina son baby ba za ki iya kulawa da ita ba?" Tace "tou ai haihuwa daban wannan daban" yace "A'a madam duka abu d'aya ne,idan suna da bambanci me yasa Allah (S.W.T) ya ambacesu da cewar rainon ciki da shayarwa watanni 30?" Shiru tayi tana kallonsa,a hankali ya rik'o breast d'in zai sa a bakin baby tayi sauri ta kalleshi za tayi magana yace "hold it madam,kina kallo kuka take yi ba?" Tace "it's paining me wollahi" yace "daurewa za kiyi ta sha a haka,zai daina daga baya" ta fara kumbura fuska za tayi magana yace "alright! Idan baza ki bari tasha ba ni zan sha mata" tana ji yace haka bata san lokacin da ta gwalo ido ba,tace "what?" Ya kifta mata ido d'aya yace "Yeah! Ai kin ji ni" kallon k'asan ido tayi masa mai kama da harara,tana tura baki a shagwab'e tace "Itama da ta kama na ji zafi bare kai?" Yayi murmushi yana kallon k'irjinta da suke cike yace "Kin san idan na kama kuwa ba zan bari ba sai na shanye duka" dariya ta fashe da shi tace "ni dai kawo ta tou na gwada,amma Allah da zafi dan baka ji ba kamar ana zuba min wuta" yace "ta ina zanji tunda ba ni ne ke ba?" Ya k'arasa maganar yana mik'a mata ita lokacin duk ta tura hannunta a baki tana tsotsa yace "kin gani ko saboda yunwa har ta fara tsotsan hannu,please Roohii kada ki mata horon yunwa,ba na son wannan tsotsan hannun,idan ya kasance sai yunwa yaci karfinta zaki feeding d'inta zai zama jiki a wajenta and ba a nan problem d'in yake ba sai ta fara girma,lokacin abun zai dame mu muyi kokarin hanata ita kuma baza ta iya bari ba because ya zama d'abi'ar ta" kad'a masa kai tayi saboda yadda yake maganar cikin sanyayyun kalamai tace "in Allah ya yarda zanyi k'ok'arin ganin ban barta da yunwa ba Hayat" ya kad'a kai yana sakin murmushi yace "thank u,Allah ya baki ikon kulawa da mu" tace "ameen" tana dariya because ta kamo tasharsa.
Chapter 141 · 0% Book details