← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 152

Sashe 128

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

About a month da mutuwar auren Hajiya Karima but to that point nothing has changed cikin rayuwarsu,da daren ranar suna zaune suna hira cikin parlor at about 12:30pm,ita da Hajiya Mariya suna sake tsara yadda za su koma rayuwar Abbah,so saboda dare gari duka was silent at that moment,and hirar nasu ma duka k'asa² suke yinsa,sai suka ji kamar k'arar fad'owar abu cikin gidan,Hajiya Karima ta waiwaya ta kalli Gwaggonta Hajiya Mariya tana fad'in "Hajiya kamar abu ya fad'o ko?" Hajiya Mariya ta girgiza kai tana tab'e baki cikin izza tace "Nima kamar na so jin hakan,amma bari na duba na gani" tana yin maganar ta dafa ta mik'e ta nufi hanyar k'ofa,kamar wacce aka hankad'o ta dawo da baya tim kake ji ta fad'i k'asa,Hajiya Karima da komai ya faru kan idonta ta zaro ido tana dafe baki,da sauri ta tashi za ta nufo ta,suka ji an buga tsawa daga bakin k'ofar da fad'in "Nemi guri ki zauna kafin na fasa miki kai!" A firgice su duka suka d'aga kai suka kalli inda suka jiyo maganar,manyan zaratan samari ne su biyar suke shigowa,kowanne fuskarsa sanye da bak'in face mask,banda k'wayar idanu da zagayen baki there's nothing da ake gani a fuskokinsu,mutum biyu ciki suna rik'e da guns k'irar ak74,while ogan sun dake gaba yana rik'e da wani shegen pistol black one k'irar TAURUS 9MM,sai biyu dake rik'e da WASR-2,idanun Hajiya suka k'ara girma cikinta ya bada sautin "K'uuuu!" A ranta fad'i take "shi kenan,ta faru ta k'are!" Wanda shi ne a kan gaban ya d'aga kai yana k'arewa parlor d'in kallo,then he turned to look at Hajiya Mariya da ta kafeshi da idanu,yana zare jajayen idanunsa da wani irin fasashshen murya yace "Ke! Me kike kallo ne?" Tayi saurin girgiza kai ganin yana saita ta da bindiga and narrowed her eyes,yadda duk suka yi tsumu² ita da Hajiya Karima sauran suka fashe da wani irin mahaukaciyar dariya banda shi,yana ci gaba da muzurai ya juya ya kalli Hajiya Karima da take k'ifi² da idanu yace "Munji labari akwai k'udi a gidan nan,so we do not want to waste any time here aje a fito mana da su" Hajiya Mariya dai bata iya sake d'agowa ba bare tayi magana,sai Hajiya Karima itama d'in cikin rawar baki,jikinta ko ina kyarma yake and was swearing profusely babu kud'i,ya kalleta a fusace "Kada ki rainawa kanki hankali Hajiya maza kije ki fito da su ko yanzun mu harbeku har lahira" jikinta yana b'ari tace "Billahillaziiy laa ilaaha illaa huwaa ba-mu da kud'i,sai dai ko kayan kud'in!" Har ya turb'une fuska jin ta ce akwai kayan kud'i da sauri ya kalli yaransa yace "Maza aje a bincika,kada a b'ata lokaci" suka amsa suna tisa k'eyarta zuwa ciki,duk wasu sark'ok'in da suka mallaka ta dalilin Abbah da y'an canjin kud'i da suka yi saura cikin gidan basu yarda sun bari ba,sai da suka raba su da komai,duk da hakan basu barsu haka nan ba sai da suka turmushe su har ita tsohuwar najadun (Hajiya Mariya) sannan suka fita suka barsu da warning d'in idan suka yi musu ihu bayan fitarsu duk sai sun kashe su,bakin kowacce a b'ame hawaye masu k'una na irin wulak'ancin da suka fuskanta suna kwaranya daga idanunsu,a haka daren ya wuce suna nan zaune inda suka barsu,har garin Allah ya gama wayewa ba tare da sun samu damar runtsawa ba ko wani ciki ya danni zuciyarsa ya baiwa d'an uwansa hak'uri.

They've spent the whole day there in this situation babu wacce ta motsa daga gurin bare tayi tunanin sanya wani abu wa cikinta,da dare Hajiya Amina mak'ociyarsu taji shirun yayi yawa ta lek'o,bayan ta jima tana knocking ba'a bud'e ba,har ta tafi ta sake dawowa tare da mijinta,suna tsaye bakin get d'in gidan shiru ya kalleta yace "Anya gidan nan akwai mutane cikinsa kuwa Hajjo?" She was silent and thought for a moment tace "Gaskiya ina kyautata zaton suna nan,da ba sa nan Hajiya Karima za ta fad'a min,ko baza su jima ba idan sun fita tana k'ok'arin sanar da ni" ya jinjina kai yace "well maybe something happened shi yasa muka ji su shiru har yanzun!?" Yayi emphasising maganar,Hajiya Amina tayi jim kafin cikin sarewa tace "Komai ma zai iya kasancewa,fatan dai Allah yasa lafiya" yace "Ameen!" Suka ci gaba da jira,atleast sai da suka spending an hour da wasu minutes suna knocking ko za'a bud'e but shiru,haka layukan wayoyinsu sai kira suke yi suma d'in amsa d'aya suke samu a rufe duka wayoyin suke,da suka ga babu mafita nan suka kama hanyar komawa,sai dai sun ajiye shawaran zuwa gobe idan basu samu wani gamsashen bayani akan lamarin su Hajiya Karima d'in ba za suje gidan mai unguwa,idan yaso ko bude gidan ne sai ayi a duba.

Wasa² daga awa d'aya,biyu abu har wani daren,suna zaune kowacce da damuwar dake damun ranta,bayan tsayin awanni suna nan zaune kamar ginannun duwatsu,Hajiya Mariya tayi wani irin jan zuciyar da ya bata damar d'aga hannu ta goge hawayen da suka sauko saman fuskarta,in a kind of calm tone da wannan dasashshiyar muryar tan,bata yarda sun had'a ido da Hajiya Karima ba ta fara magana "Kuka ba zai tab'a zama mafita ba,ya kamata mu tashi tsaye mu san abun yi kafin lokaci ya k'ure mana!" Furucinta ya bawa Hajiya Karima damar dawowa daga duniyar rud'anin abunda ya faru da su,tana yin ajiyar zuciya and to blink her swollen red eyes,muryarta ba ta fita sosai har gara ta Hajiya Mariya tace "Yanzun Hajiya mene ne kike ganin za mu iya yi?" Hajiya Mariya tace "Komawa cikin rayuwar Alhaji Abubakar shi ne abunda ya dace,ko da babu aure dole muyi masa rik'on da babu abunda zai sa ya kufce daga gare mu!" Hajiya Karima was silent and listened to her speeches,while k'asan zuciyarta yake cike with different emotions,jin ta yi shiru Hajiya Mariya tace "Kina sauraren abunda nake fad'a Karima?" Hajiya Karima ta d'ago ta zuba mata idanu ba tare da ta yi magana ba,Hajiya Mariya ta ci gaba da yi mata khud'uba bisa busa da zugar shaid'an. A wannan daren duk wani mafitar da suke nema,sai da suka tabbatar sun nemo,sannan suka kwantar da hak'ark'arinsu,ba wai dan baccin yana musu dad'i ba,but solution to their problems da suka finding ya basu nutsuwa.

Washe gari tun da asubah bayan an fito masjeed,suna kwance suna ramuwar baccin da basu samu yi ba,hayaniyar dake tashi kofar gidan ya farkar da Hajiya Mariya,cikin tsananin mamaki ta bud'e idanunta ta saka slippers ta kama hanyar fitowa daga bedroom d'inta,a hanya suka had'u da Hajiya Karima tana fitowa parlor,Hajiya Karima tana murza ido take tambaya "Hajiya me yake faruwa cikin unguwar nan nake jin hayaniya?" Hajiya Mariya tayi shiru tana bud'e k'ofar parlor,kafin ta fita ta waiwaya ta kalli Hajiya Karima "Kamar ma a k'ofar get nake jin hayaniyar" Hajiya Karima ta kad'a mata kai,kafin ta yi magana aka diro cikin gidan,da gudu har suna bige juna suka shige cikin parlor kowacce na neman wajen b'oyewa,matashin da ya diro ciki bai kula da su ba ya bud'e get,mutanen dake waje suka fara shigowa,mijin Hajiya Amina ne kan gaba da mai unguwa,sai sauran mutane y'an son d'orar da labari,Hajiya Mariya jin hayaniyar ta k'i tsagaitawa ta d'aga kanta a hankali daga bayan armchair da ta b'uya,ko ina jikinta sai kyarma yake ta sad'ad'a ta lek'a window,taron jama'ar da ta gano ya bata damar yin ajiyar zuciya and then ta fito daga mab'oyarta tana kiran Karima,Hajiya Karima ta lek'o daga bayan armchair as if ana cewa kyat za ta fita a guje duk ta had'a gumi,Hajiya Mariya tace "zo ki gane min nan" a sad'ad'e cikin tsoro Hajiya Karima ta fara tahowa inda Gwaggon nata take rik'e da curtains na window ta d'an lek'a,sai da tayi ajiyar zuciya sannan ta kalli Hajiya Mariya tace "Ina tunanin Hajiya Amina ta neme mu bata samu labari ba!" Hajiya Karima ta kad'a kai bata yi magana ba taji ana k'ok'arin b'alle k'ofar parlor da sauri taje ta fara k'ok'arin bud'ewa,daga can wajen lokacin ko da suke kan k'ok'arin bud'ewa jin daga ciki ana bud'ewa abun yayi mugun basu mamaki,but they keep an eye out for what is about to happen,Hajiya Mariya tana bud'e k'ofa idanun jama'a yayi yuuu! Kansu,duk hayaniyar da ake yi lokaci d'aya duka sai aka yi shiru kamar ruwa ya cinye wajen,mijin Hajiya Amina yayi saurin matsowa cikin hard'ewar baki yana kallonsu da jefo musu tambaya "Hajiya! Kuna lafiya? Babu abunda ya faru da ku?" Hajiya Mariya tayi murmushin yak'e ta girgiza masa kai "Babu komai,lafiyar mu k'alau" a rud'e ya furta "Amma Hajiya ina kuka shiga haka babu sanarwa,Hajjo ta tayar da hankali sai an duba ku?" Kafin ya rufe bakinsa her brain had already calculated what to say,tana kallon sauran jama'ar da suka yi shiru suna saurarensu tace "Ehhh! Gaskiya bamu kyauta ba,sai dai yaya za mu yi,tafiya ta same mu da sassafe,sai muka ga bai kyautu a irin wannan lokacin mu kwankwasa muku k'ofa ba kuna bacci" saurin tarar numfashinta yayi "Amma Hajiya ko da sak'on waya kuka tura ai za mu san abun da yake faruwa" shiru ta d'anyi cikin kame-kamen abunda za ta fad'a,da sauri ta furta "To sai dai muce kuyi hak'uri,wayoyin babu chaji muka fita da su,sannan bamu dawo da wuri ba sai wajen 2:00am,kaga dai wannan lokacin shima bai dace mu kwankwasa muku gida ba" duka jama'ar gurin were pleased with her statement,it was there suka fara fashewa,masu Allah ya tsare suna yi,wanda suka zo d'aukan labari suka fita suna jin haushi. Bayan tafiyar mutanen Hajiya Karima tayi bayyanannen ajiyar zuciya tana fad'in "Waii Hajiya! Allah ya so ba ni kad'ai nake zama gidan nan ba,yau ai da ban san me zan fad'a ba idan mutanen nan suka tambayeni" Hajiya Mariya tayi makirin murmushi as she passes zuwa cikin parlor da wani takun tafiya irin nasu da suka san ta kan duniya,tun daga hakan basu yarda sun bari anji kan yadda al'amarin ya faru ba,a cewarsu za ayi musu dariya.
Chapter 128 · 0% Book details