← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 152

Sashe 114

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

    Yinin ranar tunda Nusrah ta sauka basu samu sun zauna ba,da dare ma bata fito ba tana d'aki kan waya suna hira da Nuraz,duka tun da tazo bayan sakkowar da tayi da ta farka a bacci bata sake fitowa ba,and a gobe suke sa rai za su nufi Gombe,washe gari da safe bayan ta kammala shiryawa tana zaune bayan sun yi breakfast suna zaune around 8:00am kasancewar driver yaje kai motar a sake dubata,Abba ya fito cikin manyan kaya milk colour d'in shadda da taji aiki babbar riga da ta ciki,Nusrah looked at him and smiled yace "Baby dariyar me kike yi?" She smiled again tace "Abbah ganinka nayi like a new groom" He smiled and said nothing as his driver came in,yace "Alhaji an gama" Abbah yace "To yanzun sai tafiya ko?" He replied respectfully,Abbah ya kalli Nusrah yace "well,baby if u are done can we go?" Tayi masa murmushi tace "na gama Abbah" ya kad'a kai yace "Well let's go then" babu musu ta tashi Binitta dake tsaye ta biyo bayansu tana yi musu sallama,Abbah ya wuce gaba while Nusrah suka taho tare da Binitta,har bakin mota ta rakata suna zuwa driver yasa kayansu a booth,suka shiga back seat,driver ya tada mota Binitta tana d'aga musu hannu,luf Nusrah tayi tana karanto addu'o'i from wanda idan mutum ya dai²ta a cikin abun hawa har zuwa na tafiya,ana bud'e get motarsu ta fara tafiya a hankali,lokacin da suka dai²ta a bisan titi driver ya d'age glasses sama here suka fara gudu.

       Nusrah sighs as she sends her text to Nuraz tana sanar masa sun tafi,tana turawa ta kashe network d'in wayar had'e da turawa a handbag,she slowly turned ta kalli Abbah and smiles,kafin tayi magana Abbah yace "Labarin ki kike son tuna min ko?" Ta kad'a kai,yace "ban manta ba nima" she smiled again,Abbah ya gyara babbar rigarsa ta gefe d'aya yace "Hajiya Karima! As u heard about her since then asalin sani na da ita she was coming to plaza tana kawo abinci" Nusrah tace "dama Abbah a nan ka santa?" Yace "Yeah! u know i'm not really going to plaza until weekend,so lokacin da na fara ganinta was on the weekend,ranar wani Saturday da yamma na bar gida na nufi plaza a lokacin it was exactly three months of ur mother's death,zuwan mu ke da wuya za mu shiga cikin plaza ita kuma za ta shiga da packages a hanunta,cikin mamaki kasancewar ban tab'a sanin akwai masu kawo abinci ba,and a lokacin banyi tunanin abinci ta kawo ba,nasa driver ya tsaya nace yayi min magana da ita,driver ya sauke glasses yace "Hajiya ana magana" ta waiwayo ta kalleshi tace "Waye yake magana?" Glasses d'in side nasa ya sauke na kalleta nace "Sannu ko?" Ta amsa tana kallona da mamaki,nace "Me kika shigo yi nan?" Wani irin kallo tayi min bud'ar bakinta tace "ban gane me nazo yi ba? Kayan sana'a na kawo mana,or do u think i might steal here?" Kalamanta sun ba ni mamaki but ba hayaniya nake so muyi da ita ba,na kad'a kai nacewa driver muje,muka wuce muka barta a nan,mun shigo ciki here we found more than half of the shopkeepers sitting on the floor kan tabarmin da aka shimfid'a suka yi sallah,muka gaisa da su kamar ko wane lokaci suna yi min barka da zuwa,Karima ta k'araso cikin mamakin yadda taga ana girmama ni ta bada abinci ga wad'anda suka yi order,na duba abunda ya kaini na fito na ji suna magana da wani matashi da take tambayarsa shin wane ne wannan mutumin da taga ana girmamawa? Here Farouk ya shaida mata cewa "Ai shi ne mai wannan plaza d'in,dukanmu nan a k'ark'ashinsa muke" Karima cikin mamaki tace "Tabbb' d'i jan,babbar magana!" Matashin da suke magana ganin ta yi shiru and to then furucin da tayi yace "Lafiya dai ko Hajiya?" Bud'e bakin da za tayi tace "Wollahi Farouk ba lafiya ba" yace "Me ya faru Hajiya?" Tace "Yanzun nan muka had'u da shi zan shigo ya tambayeni ina zanje? Na gwab'a masa magana" ya kad'a kai yace "Babbar magana,Allah yasa kada ki jawowa kanki matsala,even though na san Alhaji ba shi da matsala,but ya kamata kije ki bashi hak'uri gaskiya,tunda kinga mu duka a k'asansa muke,babu dad'i ace sannadiyyar mu wani abu mara dad'i ya faru da shi" tace "Dan Allah ta ina kake ganin zanje na ba shi hak'uri? Nima kaina na ji ban kyauta ba yanzun,kuma ko ba wannan ba kada yace na daina kawo abinci nan,ka ga dai wannan sana'ar fiye da rabin ku ne customers d'inmu" yace "Gaskiya ne ya kamata kiyi hakan,but ba ki da matsala duk lokacin da kika shirya zan raka ki in Allah ya yarda,sai dai gaskiya ba kullum yake zuwa ba,sai weekend wani lokacin ma sau d'aya yake shigowa a weekend" Karima replied with a certainty koma yaushe ne za ta kasance cikin shiri,what happened after that time as they had arranged with Farouk to come and apologize Allah shi ne masani,because i didn't know her heart,da wani week d'in ya zagayo ina zaune office a plaza kasancewar ranar daga wajen d'aurin aure na wuce na isa da wuri,ya akayi² ban sani ba,ina zaune aka yi sallama na amsa na bada izinin shigowa,Farouk ya shigo muka gaisa,har zuciyata na manta wancan abu da ya faru,da naga Farouk ya tsaya na kalleshi da tambayar "Lafiya dai ko Malam Farouk!" Yace "Ehh lafiya k'alau Alhaji,sai dai akwai wata y'ar matsala ne" nace "toh ina saurarenka" yace "Dama Alhaji akwai wata mata ce da take kawo mana abinci,wancan week d'in da ya wuce mun yi magana da ita ta fad'a min kun d'an samu sab'ani har ta fad'a maka magana,to shi ne tace tana so ta baka hak'uri kasancewar daga baya ta ji bata kyauta ba" nace "To Farouk banda abunka,ai wannan ba abune da za'a damu akansa ba,na tabbatar da ta san ko ni waye ba za ta yi min abunda tayi ba,but ka fad'a mata na hak'ura kuma na gode" Farouk yace "Ai Alhaji tare muke da ita,dama cewa tayi na nema mata izinin zuwa kuyi magana" Allah ya sani ba don son raina na amince nace Farouk yace ta shigo ba,yana fita ya sanar da ita ta shigo tana sunkuyar da kai shyly,muka gaisa ta ba ni hak'uri ta yi min gaisuwar Momman ki,i was very surprised but i didn't asked her where she knew an yi min rasuwa na sallameta ta tafi,tun daga wannan ranar ya kasance duk weekend ta mayar da plaza gurin zuwanta,wani lokacin har mamaki al'amuranta a cikin plaza suke ba ni,lokacin da na fara fahimtar inda manufarta yake,na yi k'ok'arin nuna mata tayi hak'uri because at this time i was not ready to get married,but i was committed to helping her whenever buk'atar hakan ya taso,but she didn't seem to care,ita dai kawai buk'atarta na aureta,nace "Ta yi hak'uri ta nemi miji ni kuma in Allah ya amince zan yi mata komai na kayan d'aki" ranta ya b'aci ta tashi ta kalleni bud'ar bakinta tace "Wollahi Alhaji duk yadda zan yi sai na yi ka aure ni" nace "Allah shi yake k'addara faruwar komai,duk abunda za kiyi ba zan hana ki ba,but aure tsakaninmu babu shi" ta kalleni tayi k'wafa tace "Well,let's see it",daga haka she didn't say anything ta fice daga office,tun daga ranar ban sake ganinta ba sai da aka d'auki tsayin wata guda,ranar ta shigo plaza cikin ado ta shigo office,i can't remember what really happened after this time,abunda kawai na sani shi ne lokacin da ta shigo bata yi sallama ba,na d'ago zanyi magana jin an shigo muna had'a ido na tsinci kaina in a state of kasa furta abunda nayi niyya,daga nan naji duk duniya ita kad'ai nake da burin aura,naje Gombe na sanarwa Malam yak'i amincewa,da na dawo bayan mun yi magana da Karima because lokacin ba na iya b'oye mata komai na sirrina tace "Ai ba dole sai ya amince ba,za mu iya zuwa a d'aura mana aure" na amince da shawararta daga nan muka sami limamin unguwarsu ya d'aura mana aure,,,wannan shi ne abunda ya faru a tak'aitace,abunda ya faru bayan haka tabbas ba na cikin nutsuwar da zan iya ganewa,but ki yi hak'uri da duk halin da kika shiga a dalilina,haka Allah ya k'addara and bayan nan komai ya zama tarihi tunda ga shi Allah ya sauya miki da mafi alkhairi.. "
Chapter 114 · 0% Book details