Sashe 125
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Tun misalin k'arfe 8:00pm cikin arean headington ya fara yin shiru,yayin da duk wani da yake da niyyar zuwa dinner d'in a lokacin ya kasance a cikin babban d'akin taron da aka tanada domin gabatar da dinner d'in,yadda aka k'awata gurin jami'an tsaro an yi multiplying wanda suke cikin mansion d'insu,banda security cameras dake duk wani lungu na gurin,haske kuwa a ko ina tamkar rana,jama'a sai shiga da fita suke,fararen fata da bak'ak'e,manyan mutane masu fad'a aji cikin birnin London da wajenta,abokan aikin Rafeek da wanda suke business tamkar taron dan su aka yi shi,lokacin da motar su Nusrah ta samu k'arasowa wajen wani irin escort da aka shirya musu abun sai ya bada mamaki,yadda al'amarin yake sai yasa ayi tunanin wasu jinin Queen Elizabeth ta k'asar ne za su bayyana saboda yadda ake ba su girma da muhimmanci,motocin suna yin parking daga cikin wani RR (Rolls-Royce) dake tsakiya silver aka bud'e side d'aya,Nuraz ya fara fitowa sanye da wasu irin outfit masu kala da jinsin Indians,farin skinny trouser da royal blue d'in riga mai double breasted,tsayinta har guiwarsa,anyi mata wani irin ado,daga k'asan side d'aya yayi kamar paralyse,ta gaba da bayansu security ke dafe musu,cikin takun nutsuwa ya zagaya inda take bai bari kowa ya rab'eta ba ya bud'e mata,ta ziro k'afarta dake cikin farin high hill d'in takalminta mai kama da glass,tun bata kammala dai²ta k'afarta akan k'asa ba ya mik'a mata hannunsa fuskarsa d'auke da wani irin murmushin da ke expressing his beauty,kulawa,love gami da nutsuwarsa duka ya dunk'ule ya mallaka su gareta alone,cikin salon fayyacewa ya d'an risina,itan ma tana yi masa kyakykyawan murmushi a yangance ta saka hannunta cikin nasa,kuzo ku yi kallon yadda fararen fata suke rigegeniya suna kallonsu da d'aukansu a photo saboda burgewa,cikin wannan dandazon na hangi *'DAN MACE FAN'S* suna rigegeniyar capturing picture,a hankali cikin nutsuwa da yanga ta fara d'agowa idanunta a cikin nasa,tana mik'ewa rigarta tayi wani irin bud'ewa ta sauka a saman k'asa like turkey tail,quickly turawan da za su yi musu rakiya suka k'araso duk y'an mata ne sunyi shiga cikin gowns pink colour wasu cikinsu suka rik'e rigar nata,shi kam gogan d'an tallafe waist d'inta yayi k'asa² yayi mata magana,tayi dariya tana d'aga idanunta ta hangi friends d'inta (Sarah Ali,Veronica,da Maria),cike da farin cikin ganinsu ta d'aga musu hannu passionately tana yi musu murmushi,juyawar da tayi ya bawa Nuraz damar sake tallafe waist d'inta da duka hannayensa ya bata peck a cheeks kunya yasa ta d'an nok'e a jikinsa,here hasken flashes ya fara aiki a kansu,ya saketa ya rik'o hannunta then suka fara tafiya a hankali ana binsu da wedding perfumes kamar ranar ne ake bikin aurensu,tunda suka iso banda sautin piano da guitars da different violin's babu abunda yake tashi,suka fara ratsawa suna wucewa,hasken flashes yaci gaba da bibiyarsu har suka haura saman stage da aka tanadi wajen zamansu,time d'in duka mutane suka fara zaunawa y'an uwa da suke wajen gwanin burgewa fuskokinsu d'auke da farin ciki,kowa cikin ado babba da yaro,isowar uban taron da gimbiyar sa guri ya sake d'aukan kyau,haka suka dinga ratsowa cikin shiga na alfarma Rafeek yana gabatar da Lolly wajen friends d'insa turawa da matansu,Lolly cikin tsantsar farin ciki take ratsawa cikin manyan matan tana sake yiwa Allah godiya bisa ni'imomin da yayi a gareta,lamarin sun dai sosai ya bada mamaki ga wanda basu yi musu kyakykyawan sani ba,security a bayansu duk inda suka tsaya sai suma sun tsaya,lokacin da taron ya fara nisa har anje gurin da za'a gabatar da kyaututtuka,iyayen sun suka fara tashi suka tunkari inda suke zaune fuskokinsu suna bayyana tsantsar farin cikinsu,kafin su zo inda suke Nuraz ya fara tashi sannan Nusrah suna k'arasowa kusa da su mutane aka fara baza idanu kowa yana son ganin wane irin gift ne zai fito daga garesu,Clark dake bayan Boss ya k'araso gaba hannunsa rik'e da wani jaka,cikin girmamawa da nuna muhimmancinsa garesu ya ciro k'aramin had'ad'd'en akwatin dake ciki ya bud'e,kyakykyawan silver lapel pin mai d'auke da tambarin butterfly sai kyalli yake ya bayyana tsakiyarsa da wasu irin k'ananun stone's farare sai d'aukan ido suke yi,Rafeek yasa hannu ya d'auka fuskarsa tana sake fad'ad'a da murmushi,ya tako gaban Nuraz d'in yana yi masa murmushi mai cike da so irin na tsakanin d'a da mahaifi ya mak'ale masa a left hand side na jikin rigar san,Nuraz ya kalli lapel pin da ya saka masa yayi murmushi kasancewar sai wane da d'an wane ke sawa ya furta "Thanks Dad!" Rafeek yayi murmushi yana lumshe masa ido silently cikin harshen hausa ya furta "it's my pleasure dear son,idan bamu yi muku ba,duka duniyar nan waye ya dace mu yiwa?" Da sauri Nuraz d'in ya rungume shi yana sakin murmushi yake maimaita fad'in "Thank u Dad once again" Nusrah,Lolly da Annie da duka wanda suka san abunda ya faru a bayan da suke wajen fuskokinsu suka fad'ad'a da fara'a,rana na farko a tarihin rayuwarsa da ya rungume mahaifin nasa shima yayi hugging nasa back,lokaci na farko da duka suka cika burin dake ransu since long ago,sun d'auki lokaci a hakan kafin Nuraz ya d'ago kansa zuciyarsa cike da wani irin farin cikin da ba zai iya misaltawa ba,yadda yake jinsa a time d'in sai yake ji kamar duk duniyar ya fi kowa sa'a,ya matsa kusa da Lolly dake k'ok'arin rike hawayen da suke son ziraro mata ya rungumeta,sun d'auki lokaci sosai kafin ya saketa yana d'ago kansa daga jikinta,Clark ya sake fito da wani akwatin zai bud'e Rafeek ya mik'a hannu cikin k'warewa da iya amfani da harshen nasara yayi umarnin ya bashi,because shi da kansa yake son bud'ewa because muhimmancin da yake bata ya wuce yasa wani hadiminsa ya kusance ta,yana daga side d'inta yayi mata rad'a ta kalleshi tana lumshe masa idanu,yayi mata sanyayyan murmushi then ya bud'e kyakykyawan akwatin,akan had'ad'd'en siraran silver chains masu three piece idonta ya sauka,wanda aka yiwa ado da wasu irin white stones na diamond,tana kallonsa da mamakinsa ta kai hannunta ta d'auka,cikin ruhinta tana sake yiwa Allah godiya har ta iso kusa da Nusrah ta mak'ala mata a wuyanta,ta d'auki na hannun da bai kai wancan tsayi ba za ta saka mata a hannu Nuraz ya matso jikinta yana b'ata fuska yace "Mom kin gama na ki fa" ta kalleshi tana harararsa,ya shagwab'e fuska yana kallon Rafeek yace "Dad kace ta bari haka" Rafeek yayi murmushi yana kallonta yace "Madam kina jin abunda Yarona ya fad'a?" bata ce komai bata ci gaba da abunda tayi niyyar aiwatarwa,da sauri ganin ta saka mata na hannun za ta d'auki na k'arshe ya rik'e hannunta yana yin k'asa da idonsa yace "Please Mom!" Yadda yayi yasa su duka yi masa dariya,a hankali sai ta janye hannunta tana cewa "shi kenan na bari" yayi murmushi yana kallonta da fad'in "Yeah! Thanks" ya d'auka cikin wani irin salon bayar da kulawa idanunsa cikin nata ya sauke guiwarsa d'aya k'asa mutum uku daga cikin y'an matan da suka rik'e mata riga d'azun suka k'araso had'e da janye rigar na ta,kyakykyawar farar k'afarta dake cikin takalminta ta bayyana,sai da ya fara shafa k'afar nata cike da shauk'i kafin ya zagaya da sark'ar ya d'aura mata,cikin wani irin yanayin karb'ar sak'onsa ta kulle idanunta had'e da yin ajiyar zuciya,har lokacin yana durk'ushe gabanta ya d'ago kansa yana rik'o hannunta ya furta "Will u forever be mine?" Nusrah dake tsayen da kulallen ido ta bud'e idanunta da sauri ta sauke a kansa jikinta ya yi sanyi,jin abunda yake fad'a yasa ta kad'a masa kai a hankali hawaye suna taruwa a idonta,yayi murmushi yace "Ki kasance tare da ni,na yi alk'awari a duk inda kike zan kasance mai kare duk wani martabarki,zan sa ki farin ciki,zan ba ki dukkanin kulawa da lokaci na.. Will u..?" Nusrah dake tsayen banda kad'a kai babu abunda take kamar wani k'adangare ga kukan da yake son k'wace mata tana rufe baki,da sauri tayi k'asa ta rungume shi tana k'arasa fashewa da kuka,cikin kuka take fad'in "Thank u! Thank u!! Thank u!!!" Gaba d'aya mutanen gurin babu wanda basu burge ba sai tashin tafi kad'ai suka ji,yana rik'e da ita banda murmushin da yake yi mata babu komai a saman fuskarsa,ya d'agota da kyar yana goge mata hawaye,tayi ajiyar zuciya har lokacin suna durk'ushe a k'asan tana kallonsa tace "Tun kafin yanzun ka kasance garkuwa a gareni,ka so ni da dukkan zuciyarka,ka ba ni kulawa since baka san wace ce ni ba,a k'arshen kuma ka mallaka min arms d'inka suka kasance min inda nake jingina na samu nutsuwa,ka hana min yin kuka a duk lokacin da naji damuwa,idan ban kasance tare da kai ba da wane ne zan rayu na samu wannan nutsuwar?" Musayar kalamai da suka yi tsakaninsu yasa zuciyoyin duk wasu masoya sinking a wani irin yanayin shauk'i,Yallab'ai Rafeek da suke tsaye har lokacin abun ya matuk'ar k'ayatar da shi,banda murmushin da yake saki na tsantsar farin ciki babu komai a saman fuskarsa,yayi k'asa da kansa saitin kunnen Lolly yace "Uhmn! Yaron nan ya iya soyayya ashe?" Tayi dariya tana kallonsa tace "Kada ka manta kai ne mahaifinsa,duk abunda zai yi ina ganin kamar ba zai yi kamar na ka ba" yayi dariya yana d'aga mata gira yace "A'a fa,ni ban iya soyayyar turawa ba,shi kuma kinga ya iya" tayi murmushi tana rik'e arm d'insa tace "Duk abunda za ka fad'a ba zan yarda ba,saboda ni kai na sani,duk wani soyayya da namiji zai gwadawa matarsa,bana ganin ya kai ka bare ya wuce ka" ya lumshe idonsa yana murmusawa yace "Na ki mijin kad'ai kika sani" tace "Kuma shi kad'ai nake gani a idanuna always",bayan d'an lokaci da aka d'auka tsakanin iyayen da yaran ana gwadawa juna soyayya,suna rik'e dajuna suka sauka zuwa gurin zamansu,suma su Nuraz d'in suka koma mazaunin su,daga nan Hajiya kaka tsohuwa mai ran k'arfe ta zo itama tayi musu addu'ar tsayin rai da zuri'ah ta gari,ta basu kyautar ta itama,bayanta sai Annie da Abbah,sai Maimunatu da mijinta,daga su kuma sai sauran abokan arziki,ciki har da Mr Muhammad Sajid da iyalinsa wanda dukansu suka samu damar halartar taron,a raina nace (da yake wannan taron manyan mutane ne duk sun zo,zumunci dai ne babu su a gurin sun watsar da shi,Mom ta hana yaran ma suyi) haka taron ya ci gaba da tafiya,bayan an gama bada kyautuka a nan aka ci aka sha,tsayin lokaci ana gudanar da bikin sai da dare ya fara nisa mutane suka fara yi musu sallama suna tafiya,su kam daga nan ahalin sun (Mr and Mr's Rafeek,Mr and Mr's Abubakar Kumo,Mr and Mr's Noor,Hajiya,Maimunatu da mijinta da yaransu,and Mr Muhammad Sajid da family d'insa da friends d'inta su Veronica) duka mansion suka nufa akayi musu rakiya zuwa sabon apartment d'insu,as their cars parked a cikin mansion a bakin apartment d'insun da ba shi da maraba da na iyayen nasu,bayan duk an yi musu fatan alkhairi,daga nan bakin entrance kowa ya dakata wanda za su tafi suka fara harama,kasancewar wad'anda basu ga gidan ba sai daga baya za su zo su gani,family d'ayan da suka yi remaining suna tsaye gefen security door,bayan sunyi sallama da su Nuraz yana rik'e hannunta suka matsa bakin entrance,na'ura tana gama recognizing faces and mentioning their names k'ofa ta fara bud'ewa,a hankali suna kallon juna,fuskokinsu da murmushi suka d'aga k'afafunsu na dama suna yin addu'ah tare then suka sauke su cikin apartment d'in,sanyayyan k'amshi mai tattare da sanyin ni'ima da ya ratsa jikinsu yasa suka yi ajiyar zuciya tare,door d'in yana gama rufewa duhun da ya gauraye duka gurin da sauri Nusrah ta rik'e arm d'insa,yayi murmushi ya tallafe waist d'inta da hannunsa d'aya,zai yi magana red dim light ya sauka a kansu tare da wasu irin red balloons masu zubi da hearts,suka d'aga kai tare suna kallo sai kuma suka yi dariya,ta sauke kanta jikinsa tana yin ajiyar zuciya,a hankali suka fara tafiya hasken yana bibiyarsu,komai na cikin apartment d'in sai kamshin sabunta yake yi,tsarin ginin da komansa irin na apartment d'in irin na apartment d'in su Lolly ne,colours kad'ai ya bambanta,yana rik'e da ita a jikinsa suka wuce side d'in da bedroom suke,bedroom na farko da suka fara tararwa,komai na ciki fari ne duk da babu wadataccen haske sai bedside lamp dake kunne,opposite da shi kuma purple,wannan ya tabbatar musu white d'in shi ne nasa saboda shi duka rayuwarsa best colur d'insa kenan da ya gwada yana so the most,ita kuma purple d'in saboda purple da pink kusan mata suka fi amfani da su,ya lumshe idanunsa yana jin wani k'aunar mahaifin nasa tana sake bijiro masa from no where,Nusrah da ta kula da yanayin da yake ciki ta matsa a hankali ta kwanta a jikinsa,yasa hannunsa ya zagayeta da su,sun d'auki lokaci a gurin,duka ya rasa abunda ya kamata yayi kafin suka shiga cikin bedroom d'insan,shi kansa d'akin abun kallo ne bare aje kan decoration da aka yi masa da red rose's,suna shiga kasancewar duk sun gaji ya fara zaunar da ita a saman chair,ganin ya juya zai barta tayi saurin rik'e masa hannu,ya juyo ya kalleta har a time d'in ya kasa magana,ta matso jikinsa a hankali ta fara cire masa lapel pin d'in dake gefe,sannan ta fara unbuttoning masa rigar dake jikinsa,yayi ajiyar zuciya yana kallonta har ta gama taje ta d'auko musu bathrobe ta dawo,ya taimaka mata ta cire rigar dake jikinta,a wannan daren tamkar mutumin da ya rasa baki haka Nuraz ya koma mata zuciyarsa kad'ai ke aiki itama duka ta gama narkewa,bayan sun yi wanka sun fito a nan suka yi sallar nafila,suna idarwa suka nufi gadon baccinsu,aka sake bud'e sabon babin soyayya.