Sashe 29
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dai² yana fitowa Annie da Bareerah suna k'arasowa gurin cikin sauri,kwance take a k'asa ta mimmik'e idanunta sun k'afe baka ganin bakin ciki sai zallar farin,ga wani irin gurnani da take kamar dabbar jeji,suka yi tsaye kanta duk sun kasa tab'ata bare su iya d'aukarta su fita da ita,Annie tayi k'arfin hali tace
"Habibiiy.! Ina ganin ya kamata mu tafi da ita gurin malamin nan yanzun"
Ya kalli Annie fuskarsa da damuwa yace "Annie yanzu.!?"
Tace "Ehh yanzu mana,maza taimaka ka kaita mota"
Ya kalleta ya kalli Annie yace "Ni kuma.!?"
Tayi saurin d'agowa ta kalleshi tace "Kai d'in mana,ba kaine namiji ba,kuma dai ai ka san ka fimu k'wari ko.!?"
Ya sake kallon yadda take yi ya d'ago ya kalli Annie yana marairaicewa yace "please Annie ku dai kamata ku kaita"
Ta b'ata rai ta hararesa tana barin gurin tace "idan ba zaka yi ba ka barta nan idan na fito sai ka goya min ita a bayana"
Yana jin tace haka ya san magana ta fad'a masa,babu shiri ya koma cikin room d'insa da sauri ya d'auko car keys ya fito,Annie ta dawo tana sanye da hijab,ya sunkuya ya d'auketa suka fita Annie tana bada Bareerah sak'o ta kula da gidan da Hauwa dake d'aki though ta san har su dawo ba lallai ta farka ba,suma in sha Allah za su dawo yanzun babu jimawa,ta amsa tana biye da su har ta rakasu bakin mota,ya bud'e back seat ya kwantar da ita,Annie da shi suka shiga front seat yaja mota suka fita,suna tafiya Annie taga bai tambayeta inda zasu ba,ta juya tana kallonsa tace "Dama ka san gurin ne.!?"
Ya d'an kallota kad'an ta cikin mirror ya ci gaba da driven yace "Ehh!" Mota tayi remaining silence baka jin komai sai sautin groaning d'inta,har suka shiga unguwar Yakasai babu wanda ya sake yin magana,yana ta bin kwatancen,suka tsaya a bakin line ya gyara parking,da yake gidan malamin babu nisa daga inda suka tsaya,suka fita ya d'auketa har suka k'araso k'ofar gidan malamin,sun d'an tarar da mutane zaune a k'atuwar rumfar gidan,suka tsaya kad'an yana rik'e da ita har lokacin,suna ta jira har mutane suka ragu,aka yi musu iso gurinsa suka shiga,ya kallesu yana musu barka da zuwa ya nunawa Nuraz gefe yace ya ajiye ta,suka gaisa da shi cikin mutunci,bai tambayesu abunda yake tafe da su ba ko dan ganin yanayin da take ciki ma kad'ai yasa shi fahimtar inda matsalar take,ya kalleta yayi murmushi kad'an ya kalli Annie yace "tana da tsarki.!?"
Annie tace masa "Ehh.!" Yace "Alwala fa.!?"
Annie tace "A'ah.!"
Ya kalleta yace "Ku shiga da ita cikin gida ayi mata alwala"
Annie ta amsa tana kallon Nuraz "D'auke ta muje.!"
Babu musu ya d'auke ta suka shiga cikin gidan,aka basu ruwa a buta yana rik'e da ita a jikinsa Annie tayi mata alwala,sannan suka dawo gurin Malam,har lokacin bata daina wannan gurnanin ba,Malam yace "Ajiyeta ta kalli gabas" ya sauketa daga jikinsa ta kalli gabas,malam yasa aka kira masa d'ansa guda d'aya yace "zauna ka rik'e min manyan yatsunta na k'afa" ya rik'e su da kyau kamar yadda malam yace,Nuraz da Annie suna gefe suna kallon ikon Allah,Malam ya rik'o forehead d'inta ya fara karanto ta'awizi yayi basmala after then ya fara karanto ayatur-ruk'yah,wani irin gigitaccen k'ara tayi ta runtse idonta hawaye suka fara bin fuskarta,Nuraz yaji gabansa yana ta fad'uwa,tunda tayi ihun yaji yana neman rasa nutsuwarsa,Annie dake gefensa ta dunga shafa kansa da jikinsa har ya d'an samu k'awrin guiwar ci gaba da zama amma duk a tsorace yake,malamin bai saurara da karatu ba har sanda Aljanun dake jikinta suka ce za su yi magana,yana ta karatu sai daya tabbatar ya galabaitar da su sannan ya dakata suka yi magana da su,duk abunda ya faru sai da suka bashi labarin suma ba laifinsu bane turo su aka yi su shiga jikinta
Yace "wane ne ya aiko ku.!?"
Suka amsa masa "Shugabanmu ne ya aiko mu.!"
Yayi murmushi yace "K'arya kuke.. Za ku fad'a min gaskiya ko saina k'one ku.!?"
Suka yi shiru basu ce komai ba,ya sake maimaitawa nan ma shiru,ya kalli d'ansa dake rik'e da k'afafunta yace "Rik'e sosai mu ci gaba" yana fad'a yaci gaba da karatu,tana ta kuka da iface² bai dakata ba sai daya sake galaibatar dasu,sannan ya maimaita tambayar wane ne ya aiko su.!? Babu gardama ko taurin kai suka ce "Shugabanmu ne."
Yace "me tayi masa zai aiko ku shiga jikinta.!?"
Aljanin dake magana a jikintan yace "Ba shi ta yiwa ba."
Malam yace "Wane ne to.!?"
Yace "Matar Babanta ce"
Malam yayi murmushi yace "Kada kuyi min k'arya,kun san zan k'ona ku ko.!?"
Aljanin yace "Ba karya muke yi ba,itace tasa shi yayi mata aiki,shi ne ya aiko mu muka shiga jikinta"
Yace "Saboda me.!?"
Aljanin yace "saboda soyayyar da mahaifinta yake mata ta yi yawa.."
Malam ya jinjina kai yace "A matsayin me aka aiko ku kuyi a jikinta.!?"
"Suka ce "Mu haukatar da ita ta fita ta bar gida.."
Malam ya sake jinjina kai yace "Ku kuma sai kuka shiga jikinta ko.?"
Suka yi Shiru basu amsa ba,yace "da ku ake amfani ana cutar bayin Allah,bayan kuma bayinsa ne kuma zaku je zaku tarar da shi,shin bakwa tsoron had'uwa da shi ne.!?"
Suka ce "Muna ji.!"
Yace "K'arya kuke yi,da kuna jin tsoronsa da wani abun baku yi shi ba,,yanzun zaku fita daga jikin baiwar Allah ko kuma kuna so mu ci gaba da fafatawa ni da ku.!?"
Suka yi shiru basu amsa ba,ya sake maimaitawa nan ma shiru,Malam ya jinjina kai yana kallon su Annie yace "Baza su tafi ta dad'in rai ba,dole sai na k'ona su"
Yana fad'a ya ci gaba da karatu,ihu taci gaba da yi,can da suka ji azaba suka amsa "Zzzzzzzz... Zzz... Za mu fita..! Kayi hahaha.. Hahak'uri.. Zzz zza mu tafi.."
Malam ya dakata yace "zaku fita.!?"
Suka ce "Ehh.! Za mu fita"
Yace "maza ku fita,ta ina za ku tafi.!?"
A gaggauce suka ce "Ta k'afa"
Ya girgiza kai yace "Ban amince ba"
Suka ce "ta baki" nan ma yace "A'ah.! ku dai zab'i wani gurin"
Suka ce "To to ta hanci"
Ya jinjina kai yace "Toh.! Kuyi min alk'awari idan kun tafi ba zaku sake dawowa jikinta ba"
Suka yi shiru basu amsa ba,yace "ko na ci gaba da karatu ne.!?" Suka ce "A'ah.! Za mu tafi."
Yace "Toh kuyi al-k'awarin ba zaku sake dawowa jikinta ba"
Suka ce "mun yi.."
Yace "idan kuka sake kuka dawo,aka sake kawomin ku nan zan k'ona ku,kun amince.!?"
Suka amsa sun amince,yace "to ku yi bankwana sannan ku yi gaggawar fita" haka suka yi yadda yace ta shiga jera atishawa,daga cikin gida malam yasa aka kawo masa wuta a kasko,ana kawowa ya dunga banka mata turaruka da ruwan addu'ah,ba'a jima ba ta shiga ware idanunta Malam yana kallonta yace "Yaya sunan ki.!?"
Ta juya ta kalle shi ta kalli su Annie dake zaune da manyan idanunta,cikin muryarta mai sanyi tace "Ina ne nan.!? Waye ya kawo ni nan.!? Ina Abbanah yake.!?"
Malam ya sake kallonsu yayi murmushi yace "Alhamdulillah.! Alaa kulli halin.. Yanzun kam ta dawo"
Ta sake yin y'an dube² tace "Ina Binitta take.!?"
Aka rasa wanda zai bata amsa,sai Malam da yace "yarinya mene ne sunanki.!?"
Ta fashe da kuka a hankali tace "NUSRAH.!"
Malam ya kalli su Annie dake gefe cike da al'ajabi yace "Alhamdulillah.!"
Annie da Nuraz suka masa sannu da godiya,yayi murmushi ya had'a musu magungunan da za tayi amfani dasu da zasu sake taimaka mata,Annie tayi masa alkhairi sosai saboda ya fad'a musu ba'a biyansa sai dai mutum ya bada sadaka da abunda yayi niyya,suka sake yi masa godiya sannan Annie ta rik'o hannunta tace "Tashi mu tafi gida daughter.!"
Ta d'ago ta kalli Annie tana share hawaye sannan ta mik'e a hankali jikinta a sanyaye suka yiwa Malamin sallama suka fito,a mota suka tarar da shi zaune yayi shiru yana tunani suka shiga suka zauna,Annie ta kalleshi kad'an taga fuskarsa da damuwa tace "Sannu habibiiy.!"
Yayi ajiyar zuciya ya d'aga kansa ya kallo Nusrah dake baya zaune ta jingina kanta da seat tana hawaye,a hankali ya dunga driven cikin mutuwar jiki har suka k'araso gida,malam buba dake bakin get yayi musu barka da dawowa,suka k'arasa ciki yayi parking,Annie ta fito ta bud'e mata k'ofa,ta fito a hankali tana kallon gidan,ta rik'e hannunta suka wuce ciki,Nuraz ya biyo su da ledar magungunanta,a parlor ya tarar da su Annie tana amsa gaisuwar Bareerah,ya bawa Annie ledar yana sake kallonta har lokacin bata daina ajiyar zuciya ba,Annie tana masa sannu ya amsa ya wuce bedroom d'insa.
Annie ta juyo ta kalleta a hankali tace "daughter muje kiyi wanka kiyi break.!"
Ta d'ago a hankali ta kalli Annie hawaye yana sakko mata tace "Mama dan Allah ina ne nan.!? Ban san ku ba.!"
Annie tayi ajiyar zuciya tace "Muje ciki zan fad'a miki" ta mik'e a hankali tana rik'e kanta da take jin yana mata ciwo suka nufi bedroom d'in Annie,ta had'a mata ruwa tayi wanka,sannan ta fito mata da wasu kayan tasa,ta kawo mata breakfast taci sannan Annie tace ta kwanta ta huta idan ta tashi za su yi maganar,,ta amsa jikinta yayi sanyi,bata jima sosai da kwanciya ba bacci ya d'auke ta. Har bayan asr prayer bata farka ba,sai da Annie taga lokacin sallah yayi nisa sannan tazo ta tasheta tace tayi sallah,ta amsa sannan ta wuce bathroom ta d'auro alwala ta dawo ta tada sallah,bayan ta idar Annie tace taje taci abinci yana dining,ta girgiza kai a hankali tace "Na k'oshi" Annie ta kalleta tace "A'ah daughter rabonki da abinci fa tun na safe" ta kalli Annie tace "Bana jin yunwa" Annie ta takurata da kyar taje parlor taci,bayan ta gama ta zauna shiru tana tunanin me tazo yi gidan nan.? Annie ta kirata suka koma bedroom,ta zaunar da ita bayan ta nutsu tayi mata bayanin duk abunda ya faru da dalilin zuwanta gidan,ta dunga kuka bayan taji labarin abunda ya faru da ita Annie ta rarrasheta har sai da tayi shiru,sake kwantar mata da hankali Annie tayi,ta mata alk'awarin zuwa gobe idan ta huta sai suje gidansu,,a tsorace ta kalli Annie tana girgiza kai tace "A'ah.!" Annie tace "me yasa.!?"