← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 152

Sashe 37

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Da wayar a kunnensa tunda suka had'a ido da ita ya kasa ci gaba da magana,suka wuce ta gabansa,,har suka tsaya bakin apartment d'insu jikinta bai daina kyarma ba,Nusrah ta rik'ota suka wuce ciki bayan ta sallami mai cab d'in,suka shiga cikin parlor'n tana rik'e da ita,tana ganin Annie da sauri ta saki Nusrah ta fad'a jikinta tana fashewa da kuka mai tsanani,hankalin Annie a tashe ta kalli Nusrah ta kalleta ta rik'o ta da sauri za tayi magana aka danna doorbell,Annie ta kalli Nusrah ta juya ta kalli entrance tace "Daughter duba ki gani waye.!?"
        Ta gyad'a kai a hankali ta wuce jikinta a sanyaye idanunta suna tara kwalla,Annie ta sake rik'o ta sosai a hankali tace "Wai mene ne yake faruwa.!? Ki sanar da ni abunda ya tada miki hankali,wani abu ya faru da kuka fita.!? Na san lafiya k'alau kuka fita,yanzun kuma kin dawo min kina kuka,wani ne ya yi miki wani abu a can d'in.!?"
      Kuka take sosai hawaye wani na bin wani duka ta kasa magana,Nusrah tayi saurin bud'e entrance,bata tsaya duba waye ba ta dawo ta zauna a k'asa tana kallonta,Annie ta waiwayo kanta cikin damuwa tace "Daughter fad'a min mene ne ya faru da kuka fita"
   Ta gyad'a kai a hankali ta fad'awa Annie komai da ta sani,Annie ta kalli Lolly bata gane kan zancen ba tace "Yanzun ba za kiyi shiru ki fad'a min abunda ya tada miki hankali ba.!?"

    Tana sheshshek'ar kuka bata yarda ta d'ago ba tace "Big Siater.. I saw him with my aye..!"

   Annie ta zaro ido tace "Shi wa.!?"

    Dai² lokacin yana shigowa cikin parlor'n ta furta *"RAFEEK..!"*

       Wani irin mummunan tashin hankali ne ya ziyarci Annie,bakinta a bud'e da mugun mamaki ta maimaita "Rafeek.!? Kika gani.!?"

       Ta gyad'a kai tana ci gaba da kuka,tsaki Annie tayi mai rai da lafiya,cikin hayaniya tace "Shi ne dan kin ganshi kika tashi hankalinki haka,ya san kina yine.!?"

   Ta girgiza kai,still Annie ta sake jan tsaki tace "shirme kawai.! To ko ganin ki yayi ina ruwanki da shi.!?"

     Ta d'ago idanunta da suka fara canjawa tace "Amma Adda ya ganmu fa shima,ni dai ina jin tsoro.!"

     "Da ya ganku sai aka yi yaya kenan.!? Ko kuma ya nuna miki ya damu da ke ne.!?"

      Tace "A'ah.!"

    Annie ta tab'e baki tace "Tunda ya nuna bai san da zaman mu ba ke mene ne naki na damuwa.!? Koma mene ne ya faru a baya,k'addara ta had'a mu da shi,ya kamata zuwa yanzun ki cire komai a ranki kiyi rayuwarki kamar kowa,ubangiji ya tsara faruwar komai,saboda haka bana so kina sa minor things a ranki,ko dan gudun komawa cikin mawuyacin halin da kika fad'a a shekarun  da suka gabata.."
      Tayi ajiyar zuciya a hankali tana goge hawayenta,ta kalli Nusrah data takure a guri guda idanunta sunyi rau² tana shirin yin kuka ta zuba mata ido,Annie ta juya kad'an tana kallon abunda take kallo,taga idanunta akan Nusrah,tana kallonta taga yadda tayi da fuskarta tayi ajiyar zuciya had'e da tsaki tace "Kema kukan za kiyi min ne madam.!?"
     Tayi saurin kallon Annie tana girgiza kai a hankali,Annie ta harareta tace "Ki yi min kuka yanzun na had'a ku duka nayi maganin ku.."
     Ta k'arasa maganar tana harararsu,Nusrah tayi ajiyar zuciya kawai bata ce komai ba,sai lokacin ta tuna anyi knocking ta bud'e,a hankali ta waiwaya,suka yi ido biyu da shi tsaye yake a guri d'aya,alamun dake kan fuskarsa suka tabbatar mata ya gama jin komai da suka tattauna,da sauri Nusrah ta mik'e tsaye.....

😨😨   #Who's he.!?

#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 19.
#Aᴄᴄɪᴅᴇɴᴛᴀʟʟʏ

*Wai me yasa wasu mutanen duk inda mutum ya kai da hak'uri sai sun k'ure sa.!? a lokacin da mutum yake musu mutunci da kauda kansa daga k'ananun abubuwa,sai sun sa dole yayi magana,idan kun san za ku dunga aikamin da k'ananun maganganu ta inbox ku daina karantawa dan Allah,ni bance dole ku bini ba,wad'anda suka ga zasu iya su karanta,amma wai yau har ta kai ana fad'a min idan na san littafina na kud'i ne na fad'a,wanda da zance na mai da shi na kud'in ba lallai masu fad'amin maganar su kasance cikin masu siyan ba,dan kawai banyi update a lokacin da na saba yi ba,idan haka ne me yasa tun farko ban rubuta muku details na inda zaku biya ba.!? Ku burin ku a turo muku novel ku karanta a lokacin da kuke so baku damu da sanin mai turowar yana lafiya ko A'a ba,yana da uzuri ko basa da su.. Wannan ba rayuwa bace,duk mutumin da yake girmamaka ya kamata kaima ka mutunta sa,ko ba komai yana sa ka farin ciki ta hanyar aikinsa.. Maganar gaskiya ban ji dad'i ba kuma kun yi disappointing d'ina,Allah ya sani ban cika son yin magana ba sosai,amma dole ta sa ni yi,za kuga duk comments d'inku babu wanda na amsa,raina ya b'aci gaskiya da abunda ya faru jiya.. Amma a kiyaye gaba,idan yau mune gobe fa ba mu bane.*

*Fatima & Ummu Hummaira ina godiya sosai,ubangiji ya bar k'auna.. Anaa ahabbakum-thiir.*😍
💕

Saurin wucewa tayi ta nufi hanyar bedroom,ransa a matuk'ar b'ace yake kallonsu duka ba tare da ya ce komai ba ya wuce hanyar bedroom d'insa,Annie ta juya jin tafiya ko sallama bai yi musu ba ta ganshi yana wucewa and ba shi da niyyar ya kula su,ta girgiza kai tace "Mr Man.! Come here.."
Har ya kusa da entrance ya tsaya,sai daya d'auki lokaci kafin ya waiwayo a hankali yana sake had'e rai ya dawo inda suke,ya zauna kad'an saman armchair ba tare da yayi magana ba,Annie ta kalleshi sosai tana had'e rai tace "Me aka yi maka ne kake cunkushe mana fuska..!?"
Yayi saurin d'agowa suka had'a ido da Nusrah data fito tayi saurin kawar da kanta ta wuce,yana sake had'e rai yace "Nothing" a can k'arshen mak'oshi,Annie ta kalleshi sosai tace "Really.!?"
Ya d'ago kad'an yana marairaicewa yace "Annie babu komai,kawai fa stress ne" ta tab'e baki tace "Na ji,,amma ai baka yi sallama ba da zaka shigo"
Ya sake d'agowa yana kallon mahaifiyarsa yaga ta kwantar da bayanta idanunta a lumshe ya kalli Annie da wani irin yanayi a fuskarsa k'asa² yayi sallama,sannan yace "Annie what wrong.!?"
Ta kalleshi sosai tace "Uhn.! Nima dai ban san mene ne yake damunta ba,amma koma mene ne na san baya rasa nasaba da mahaifin.."

Bata k'arasa ba yayi wata irin zabura ya mik'e tsaye yana toshe kunnensa,Annie ta kalleshi za tayi magana taga yanayinsa ya sake sauyawa idanunsa har sun koma wasu iri,a fusace kafin ta yi magana tuni ya bar mata wajen.
"Habibiiy.!" Annie tayi calling him out,not looking back and standing where he was ta sake kiransa,still bai motsa ba daga yadda yake ya jiyo tace "Came back let's talk.!" kasa juyowa yayi yana tsaye a gurin har ta maimaita yafi a k'irga,da yaji bazai iya jurewa ba cewa yayi "I'm sorry Annie,but bana tunanin yanzun zan iya jurewa muyi wannan maganar" ta jinjina kai a hankali cikin damuwa,da ta fahimci yanayin da yake ciki da sauri tace "Ok..!"
Yana jin tace haka ya wuce da sauri,yana shiga waistcoat d'in ya fara unbuttoning,kamar ta yi masa laifi ya cire ya cilla saman resting chair yana sauke wasu irin ajiyar zuciya,waist d'insa ya rik'e da hannaye biyu yana furzar da wani irin zazzafar iska,after some minutes ya gyad'a kai yayi licking lips tunawa da kalmar da Annie ta kusa fad'a,angrily ya zare stocking d'in and began to unbuttoning long sleeve dake jikinsa,wani irin zafi yake ji tun daga cikin b'argonsa,sai daya tabbatar ya rage kayan jikinsa ya zauna daga shi sai nickers a saman bed yana hargitsa curly hair d'insa,ya d'auki lokaci a haka yana tunani then ya kwantar da bayansa a saman bed d'in ya lumshe idanunsa,jin zuciyarsa yake ta yi masa wani iri saboda b'acin rai,jikinsa banda hucin zafi da shivering babu abunda yake,hannunsa ya d'ora saman forehead d'insa ya dafe "Me yasa za ki gansa yanzun.!?" Ya furta a k'asan mak'oshi a zafage ,bud'e k'ofa akayi a hankali,bai tashi ba har ta k'araso cikin d'akin,yanayin da ta gansa a ciki yasa tayi saurin juya masa baya,a rikice tace "Wai ka zzz.. Zo..!"
Tana fad'a bata jira ya amsa ba ta fara tafiya za ta fita,bai tashi ba har lokacin idanunsa a lumshe yaji alamun ta bud'e k'ofa za ta fita ya d'ago a hankali yana fad'in "come over here" ta tsaya cak a inda take bata juya ba,ya tashi ya zauna sosai ya maida hannayensa baya ya dafe su a saman bed,chest d'insa ya d'ago yana kallon yadda take kame²,yaja siririn tsaki yace "Ba dake nake ba,kika juya min baya.!?"
Ta kasa juyowa ta kalleshi,ya mik'e a hankali ya fara tafiya yana rangaji kamar ya sha wani abu,har ya tsaya a bayanta bata sani ba sai da yayi magana,ta juyo a razane ta ganshi tsaye daf da ita,tayi saurin rufe idonta,za tayi magana ya rigata "Bakya ji ko.!?"

Ta girgiza masa kai,yace "Mene ne ya hanaki yin magana.!?"

Ta fara in'ina,a masife yace "Speak well.. I don't want any of ur in'ina" a tsorace tace "To kasa riga."
Sai lokacin ya kalli jikinsa daga shi sai nickers,yayi tsaki ya juya mata baya da sauri yace "Who's calling me.!?" Da sauri idanunta a k'asa tace "Annie.!" Ya tab'e baki yace "Jeki gani nan zuwa" ta fita da sauri ko tsayawa taji abunda zai sake cewa bata yi ba,yana jin ta rufe masa k'ofar yayi maza ya fad'a bathroom,wanka ya fara yi ya d'auro alwalar maghreb,yana fitowa ya gyara sumar kansa ya shafe jikinsa da mayukansa,sannan yasa long sleeve ya kawo wani wool men sleeveless sweater mai V-neck saboda yanayin sanyi ya d'ora a sama ya kamo hanyar fitowa.

***
Chapter 37 · 0% Book details