← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 152

Sashe 18

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har aka shekara guda da watanni da haihuwarka babu wanda yasan duniyar da Rafeek ya shiga,wayoyinsa idan an kira ba'a samu,anbi sahunsa k'asar ana tunanin ko wani abu ya same shi ba'a same shi ba sai labarin tafiyarsa birnin Washington aka tsinto,ran Alhaji zakar ya sake b'aci,a lokacin daya fahimci nufin Rafeek ya yanke hukuncin babu ruwansa da shi daga nan har zuwa ranar da zai dawo,,a wannan d'an tsakani da aka samu na haihuwarka al'amura suka yi ta faruwa,nima nawa gefen Allah ya karb'i rayuwar mai gidana,hatsari ya runtsa da su a hanyarsu ta zuwa lagos,,Hauwa da kai har lokacin kuna gidan kakanninka,duk da a farkon dawowa ta gida naso ku dawo gurina mu zauna tare a gidanmu tun bayan dana gama iddah,but yadda Alhaji zakar da iyalinsa suka tsaya kan al'amuran ku da kunya irin ta bafulatani yasa sai na kasa fitowa na fad'i abunda ke raina,haka nayi ta zuba ido kullum a gurina kake wuni,har Hauwa suka fara k'ok'arin yin exam zuwanta bai dai²ta ba sai Maimunatu kad'ai take zuwa wasu lokutan saboda damuwar da take ciki ya fara affecting tunaninta,,a wata ranar Talata da rana bayan sun dawo daga hospital suna zaune a parlor Maimunatu na bawa Hajiya labarin matsalar da doctor yace zata iya samunta nan gaba kad'an idan bata ragewa kanta damuwa ba,Hajiya tana mata nasihar ta maida komai ba komai ba,suka tsinkayi sallama daga bakin entrance,shiru duka suka d'auka Maimunatu na kallon Hajiya cikin tsananin mamaki tace
"Hajiya kamar muryar Yah Rafeek ko.?"
Kallonta Hajiya tayi tana had'e rai tace "ban sani ba,sai dai ki duba ki gani"
Hauwa ta shiga rud'ani da tunanin anya shi d'in ne da gaske tunda gaba d'aya lokaci ya tafi da tunanin baza ta sake ganinsa ba,Maimunatu ta daure ta amsa sallamar,tun kafin taje ta duba a bashi izinin shigowa ya bayyana,yana sanye cikin shiga ta alfarma d'an gayu da shi ya had'e cikin wani d'anyen suit mai matuk'ar tsada daya fito daga company'n armani,duk wanda ya kalleshi dole ya sake dan yadda ya dawo tun daga kan tsarin outfit da gyaran kansa sak bature,gaba d'ayansu kallonsa suke yi da wani irin mamakin dama yana raye a cikin duniyar,fuskarsa babu wanda ya kasa shaida ta tunda shi d'in ba bak'o bane bare ace sun kasa tantance shi,ya tsaya gaban Hajiya yana niyyar durk'usawa ya sake tabbatar msusu lallai Rafeek d'in ne da gaske,to amma yanayin sauyawar da yayi da irin tufafin da ke jikinsa yasa suke ta binsa da kallo,shi kam tunda ya shigo babu wanda ya kalla a cikinsu Maimunatu fuskarsa nan a d'aure kamar wanda yayi gamo da mutuwa,kansa a k'asa ya tunda ya durk'usa ya magana,yanayin yadda yayi shi zai tabbatarwa da duk wani mai ido lallai ya aikata gagarumin laifin da yake son neman yafiya,but kamar wanda ya rasa baki haka yayi ta zama da sunkuyayyen kai ya kasa d'agowa bare ya fuskance ta,Hajiya da duk wanda yake cikin parlor'n gaba d'aya sai kallonsa suke babu wanda ya iya magana har bayan wani lokaci sannan Hajiya tana jinjina kai tace
"Rafeek.! Idonka kenan ko.? Anya kana son gamawa da duniyar nan lafiya,kana buk'atar albarka kuwa.!?"
Ya sake sunkuyar da kai kamar zai tsaga k'asa ya shige cikin dauriya muryarsa na wani irin karkarwa yace
"Ki garfaceni Hajiya ta,wollahi ba'a son raina na aikata haka ba,,kiyi hak'uri ki yafe.."

Bai k'arasa ba ta dakatar da shi cikin fad'a² "Rafeek baka da bakin da zaka nemi yafiyata,tun da wuri kuma muna shaidar juna maza ka tashi ka fice min a gida kafin na sab'a maka."
Saurin rik'o k'afafunta yayi,Hajiya ta lumshe idanu ta bud'e tana d'an janye k'afafunta,ya sake rik'owa sosai muryarsa na ci gaba da rawa yace
"Dan Allah Hajiya ta ki gafarce ni,wollahi na tuba."

"Baka ga komai ba Rafeek,me zai kaika saurin neman yafiya.? Mu laifin me ma kayi mana da zaka nemi gafarar mu,mu da muka yi laifi mu yafi kamata mu nemi yafiyarka saboda mun yanke hukunci ba tare da tunanin abunda gaba zata haifar ba,da ace tun farko mun tsaya munyi tunani da haka duk bata faru ba,amma tunda kai muka yiwa ba dai² ba kayi hak'uri ka gafarce mu,in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba."
Tana kaiwa nan ta sauko daga saman kujera tayi tsugune akan k'afafunta tana kallonsa tace "Muna fata zaka yafe mana laifukan da muka yi maka,muna sane da wanda ma bama sane."
Wani irin kunya ce ta dabaibayeshi ya kasa kwakwkwaran motsi a gurin bare yayi magana,Hajiya cikin fusata ta banka masa harara tace
"Da kai nake isashshe uban mutane,,idan ma banda rashin kunya irin taka Rafeek har kana da idon da zaka kallemu.? Bayan tarin kunyar daka samu ji yanzun ka d'auko jiki mu yafe maka.. Idan munce mun yafe sai kuma ayi yaya.?"
Shiru yayi bai yi magana ba,Hajiya taci gaba da fad'a son ranta ta inda ta shiga ba tanan take fita ba,Hauwa tunda ya shigo take jin gabanta na fad'uwa ta kalle su duka a hankali ta sunkuya ta d'auke y'an kayanta ta bar parlor'n,Hajiya ta bita da kallon tausayi bayan ta dawo da kanta kan Rafeek da yayi wani irin kicin² tace
"Sai ka wuce ai kaga yaron,ka kuma tabbatar ka bata hakur'in abubuwan da suka faru a bayan,yanzun kam kayi kad'an kace yaron nan ba jikinka bane.."
A karon farko ya d'ago yana kallon Hajiya data had'e girar sama dana k'asa yace
"Hajiya ni kuma me zai had'a ni da yaro.!?"

Yatsunta ta ware tana zaginsa tace "Zaka tashi kaje ko sai na sab'ar maka,kuji min futsararren yaro,to dan ubanka idan baka sani ba abunda kowa yake hangowa a fuskar yaron nake son ka gani da idanunka,,kuma bari ma kaji na sake fad'a maka kamar yadda kowa ya gani ya tabbatar yaron nan jininka ne yake gudu a jikinsa,kaf fad'in duniyar nan banga wanda za'a kira da ubansa bayan kai ba,tashi ka wuce ka bani guri,idan kak'i kuma salin alin maza wuce ka bar min gida.."
Ta karasa maganar tana nuna masa hanya,girgiza kai yayi cikin bayyanannen b'acin rai zai yi magana ta sake tarar numfashinsa
"Ka wuce nace ka gansu,ni ban b'ukaci jin komai daga bakinka ba.!"
Bisa dole ya tashi yabi bayan Hauwa cikin bin umarnin mahaifiyarsa,shi kam ba don plans d'insa na son raba Hauwa da gidan daya k'ullo da baya so yayi ruining d'insa da baiga abunda zaisa yaje ba,wannan shi ne dalilin da yayi masa jagoranci zuwa d'akin Hajiya inda yake tsammanin nan ta shiga,a saman bed d'in mahaifiyar tasa ya hango ta zaune ta zubawa guri d'aya ido ko k'iftawa bata yi,kana gefenta a kwance kana bacci cikin kwanciyar hankali,da ganinta kasan tana cikin tsananin damuwa but bata san wane ne ya kamata ta fito ta fad'awa ba,har ya k'araci kallonta bata sani ba,sai daya shigo cikin room d'in kafin ta farga ta san wane ne a kusa da ita,saurin mik'ewa tayi tsaye tana ja da baya like taga abun cutarwa kusa da ita,kad'an ya kalleta ya d'auke kansa a kanta,yaci gaba da takawa har ya k'arasa inda take tsaye kamar wacce ke jiran ace kyat ta zura a guje,ta ci gaba da matsawa tana saita entrance da zai kaita waje,still ya sake tab'e baki ba tare daya sake kallonta ba ya fara magana
"Me yasa kike da tsananin taurin kai ne.!? Bayan duk maganganun da muka yi dake a bayan,nayi tsammanin zuwa yanzun da kika tabbatarwa kanki nan d'in ba gidan mahaifinki bane zanzo na iske kin koma naku gidan... But sai naga ashe baki yi zuciya ba kina nan still.!"
A karon farko ta d'ago ta kalleshi bata ce masa komai ba ta d'auke kanta daga gare shi,harararta yayi yana tab'e baki
"Hakan yayi miki kyau,but kamar yadda kika ga na dawo a yanzun ina so ki sawa ranki lokacin barinki gidan nan ne yayi,cos ni banga amfanin zaman ki a k'ark'ashin inuwar mahaifana ba,ko muna da wata alak'a ne kuma bayan waccan ta baya.!?"
Sake d'aga kai tayi ta kalleshi suka had'a ido yana jifanta da mugun kallo,juyawa tayi tana kallon baby'nta da yake motsawa alamun yana son tashi,dakatawa shima Rafeek yayi da zancen da yake har sai da yaga yaron bai tashi ba sannan ya juya zai fice daga d'akin muryar Hauwa ta dakatar da shi
"Duk abunda kace naji but har yanzun maganar kawai kake yi babu evidence,,idan dan kana ganin bazan iya barin muku gida bane kake tunani ina so ka cire wannan a ranka,in sha Allah zan tafi cos ba'a binne kurwata a nan ba bare kace na zaune muku a gida.."
Wani irin juyowa yayi yana murmushi da gefen bakinsa ya tako ya dawo gabanta
"Kika ce mene ne.!? Ba'a binne ruhinki ba.? Idan ba shi d'in aka rufe a gidan mu ba zaman mene ne kika ci gaba da yi daga lokacin dana furta cewa na yanke alak'ar dake tsakanin mu.!? Why don't u leave us.!?"
Ya k'arashe yana zare ido da d'agawar sauti,murmushi tayi mai ciwo
"Wannan kuma ba ruwanka bane,zama na ko tafiyata duk basu shafi mutum ba.."

"Sun shafe ni,,cos nan gidan mu ne kuma gidan mahaifina na asali,me zai sa ke baza ki gwada komawa naki asalin ba.!?"

Kallonsa ta sake yi ya d'aga mata gira d'aya "Yeah I mean it.! Ki gwada mana.."
Sauke kai tayi k'asa bata ce komai ba sai dai taji k'irjinta ya fara zafi,Rafeek cikin wani irin murya yace
"I knew baza ki tab'a iyawa ba,wannan gidan naku dai mai kama da village's graveyard babu yadda za'ayi na yarda zaki iya komawa cikinsa.."
Yayi mata murmushi yana shafa sumar kansa,a d'an fusace ta kalleshi
"Kada ka sake ko da wasa ka zagarmin asali na,,gidan mu it's for us ni da y'an uwana da shi muke alfahari,haka kuma naku it's urs,so kowa ya zauna iya matsayinsa,ni bance ka zagarmin asali ba,kuma naga ai nan d'in da kake magana bani na zaunar da kaina ba.."

"Wane ne ya zaunar dake idan ba son duniya ba.? Gidanku a yanzun baza ki iya rayuwa cikinsa ba,saboda kinga duniya kin shiga inda yafi naku,me zai sa ki koma can ko ba haka bane.!?"
Chapter 18 · 0% Book details