← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 152

Sashe 2

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Annie..! Am scared..!"

Tsawa tayi masa tace "Fita nace.. Kada ka damu maza ka wuce,ni nace ai zan zo yanzun na same ka.."
Kansa dake a k'asa ya kasa kallonta tun d'azun ya d'ago ya saci kallon fuskarta,,suna yin ido hud'u ta sake karkace hanya ta nufo shi gaba d'ayan ta,kamar yadda ta nufo shi haka ya juya ya kama hanyar ficewa,sai dai ko k'ofa bai kai ga isa ba,irin mugun tsalle data doko ya ganta tsaye a gabansa,yadda tayi acting kamar a movie sai yasa shi yin still yana ta kallonta tsoro k'arara a fuskarsa,,still cike da k'arfin hali Annie tayi saurin rik'e ta tana janta baya da nufin ta mayar kan gadon,a fusace ta d'ago tana fizgewa jin an rik'eta an hanata sakat,bisa tsautsayi ko data waiwayo tana fizge jikinta ganin Annie rik'e da ita ta kasa kwacewa yasa ta hankad'ata da dukkan k'arfinta,da jikin gini ta fara buguwa kafin ta silale tayi k'asa,sautin buguwarta da k'arar da tayi a lokaci guda na azaba suka sa Nuraz da har ya fita a d'akin babu shiri ya sake dawowa a d'imauce yana kiran Annie,k'ara ya fasa lokacin daya hangota kwance cikin jini,cikin tsananin tashin hankalin da bai tab'a tsintar kansa a ciki ba ya nufi inda take yashe ya d'ago kanta ya rungume,jin bata motsi a hargitsen ya fara jijjigata yana kiranta hankalisa a mugun tashe yake fad'in
"Annie..! Ki rufamin asiri ki tashi,,dan Allah kada kiyi min haka..! Idan kika tafi kika barni yaya kike so nayi..?? Ki tashi Annie kada ki tafi..!"
A wannan lokaci ko da nuraz yake kan sambatun kiranta,Annie kam bata san yana yi ba,bcos tuni tayi nisan kiwo,,juyawa ya shiga yi da tashin hankali yana dube²,haka nan duk sai yaji ya rasa mene ne yake nema,kuma ya rasa abunda ya kamata ya fara yi wanda zai dawo masa da Anniensa cikin lafiyarta,gashi shi kad'ai ne a gurin ya san da wahala ya iya d'aukarta,saboda yadda take rusheshiya tafi k'arfin ya d'auke ta shi kad'ai,,yana zaune rungume da kanta da jini yake ci gaba da zuba yana jijjigata yana kuka,ta zagayo ta bayansa without ya sani,ji yayi kawai an shak'e shi ta baya,da hannayenta biyu ta shiga hajijiya da shi cikin k'arajin maganarta da ba komai ake ganewa ba take maimaita fad'in
"I told u bana so,,bana so².. Me yasa..?? Sai nayi ajalinku.. Ni ce ajalin ku.. Kuma nima sai nayi nawa ajalin.. Sai na kashe ku,na kashe kaina,,dukanmu baza mu rayu ba.. Sai mun mutu dukan mu.. Sai mun mutu,,mutuwa za muyi.!!"

***
A matuk'ar firgice ya bud'e idanunsa dake rufe sakamakon mummunan mafarkin da yayi,cikin abunda bai wuce mintuna goma da komawarsa bacci ba,gumi duk ya wanke shi daga shi har white sleeveless singlet dake jikinsa,water bottle dake saman couch ya fara bud'ewa ya tsiyayawa a cup dake gefen bed d'in kad'an ya sha,a hankali ya shiga sauke ajiyar zuciya tamkar wanda ya sha tsere yana sake jan wahalallen numfashi da ajiyewa kafin ya fara motsa bakinsa slowly
"A'uzhubikalimatillahit'tamaat min sharri maa khalak'.. Laa ilaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn.. Laa ilaaha illallaahul'azheemul'haleem,laa ilaaha illallaahu rabbul'arshil-azheem,laa ilaaha illallaahu rabbus-samaawaati,wa-rabbul-ardhi,wa-rabbul-arshil-kareem kareem."
Ya d'auki tsayin lokaci yana maimaitawa kafin a hankali ya lumshe idanunsa ya bud'e yana juya su,bayan d'an lokaci ya rik'e gefen lip d'insa da hak'oransa cikin salon zurfafa tunani akan abubuwan da suke faruwa da shi a cikin bacci,,kimanin lokaci mai tsayi ya d'auka cikin halin jimami then kamar wanda aka tursasa yayi k'ok'arin janye bedspread da k'afafunsa ke ciki ya ajiye su cikin adjustable velcro slides slippers mai d'auke da tambarin Puma kalar fari,,yadda jikinsa yayi sanyi da abunda ya gani yana tashi tsaye yaji kamar ya rasa komai,hatta da kuzarin jikinsa duk sai ji yake yana kokarin gazawa,gefen bed d'in ya dafa da duka hannayensa slowly ya koma ya sake zama yana lumshe kyawawan idanunsa na tsayin lokaci,,muryar Annie ya jiyo dake ta tsaye tun d'azun akansa da sauri ya bud'e idanunsa
"NURAZ..! Habibiiy.!! Har yanzun baka tashi ba ne.!?"
Ta tambaya lokacin da take sake matsowa inda yake,a hankali ya d'ago yana kallon fuskar Anniensa da babu jimawa cikin mafarkinsa ya ganta cikin mugun yanayi,haka nan ya k'ura mata idanu,har ta k'araso bai sani ba sai data tab'a shi
"HABIBIIY..! Me ya same ka haka jikinka a jik'e.? Wasan ruwa kayi ne ko me..??"
Tana tambaya tana tattab'a jikinsa,shiru yayi baiyi magana ba,a hankali Annie ta rik'o shi tana kallonsa,tana shirin sake yin magana taji temperature d'in jikinsa ya sauya zuwa fitar da hucin zafi,da sauri ta sauke idanunta tana watsa masa kallon tuhuma
"Mene ne ya faru habibiiy.?? Wani guri na maka ciwo ne.? Ka sanar dani abunda yake faruwa.!"
Still yayi yana kallon ta ba tare da yayi magana ba,kome ya tuna da sauri ya mik'e ya kama hanyar barin gurin a niyyarsa ya shige bathroom,but sai Annie tayi saurin rik'o hannunsa
"Zo Habibiiy ka sanar min damuwarka.. Me ya same ka jikinka yayi zafi haka..!?"
Girgiza mata kai kawai yayi,a hankali ya zame hannunsa ya shige bathroom without yace da ita wani abu game da tambayar da tayi masa.....

*#HAPPY NEW YEAR.*🎉

#Comment first
#Vote &
#Share pls.
#Real Smasher.
#Jan/1st.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                  *'DAN MACE..*
             (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

*YABON GWANI...*

Hassan Atk
Hussain Atk
Itz B.Y Ebraheem
Hayat Baba Zubair
Ku d'in ku ne gwanaye na,kuma abun alfahari na,idan har ina da mutanen daya kamata ace na ambata,a wannan dan tak'aitaccen rubutun nawa,tabbas ku ne farko,,bisa d'awainiya da kuke da litattafaina a social media,bani da bakin da zanyi muku godiya,sai dai har kullum ina yi muku fatan rabb ya saka muku da mafificin alkhairinsa ameen.

Pᴀɢᴇ 2.
#Eɴᴛʀᴇᴀᴛʏ

      Tun daya shige bathroom d'in yake tsaye k'ark'ashin shower,hannayensa dafe a jikin wall guda na katafaren toilet d'in da yaji kayan more rayuwa ya sake zurfafa tunani akan abunda mafarkin nasa yake nufi,a iya shekarunsa tabbas yasan bai kai matakin da za'a ce ya iya d'aukar irin wad'annan damuwar bane,to amma yaya ne zaiyi tunda k'addararsa tun farko a haka tazo.? Shi dai ya sani kuma har zuciyarsa ya tabbatar bawai yana damuwa da halin da yake ciki bane,abunda kawai yake damunsa a yanzun shi ne yana tsananin buk'atar son ya gane ma'anar yawan mugayen mafarkan da yake,,bakinsa ya bud'e kad'an yaja numfashi ya fesar,a fili ya tambayi kansa
    "Shin mene ne hakan yake nufi..??"
   Ya sake sunkuyar da kansa k'asa deeply thinking about his dreamt,ya b'ata lokacin da bai san adadi ba a k'asan shower ruwa yana ci gaba da sauka a saman kyakykyawan sumar kansa daya sha wani masifaffen undercut with long side swept,duk da yake yanzun ne yake kan tasowa amma sosai gyaran kan yayi masa kyau,but zuciyarsa tana cikin zullumi da damuwa wannan dalilin ya sake taimakawa wajen boy'ewar sirrintaccen kyaun da Allah yayi masa.
   "Tsayin wane lokaci zaka d'auka kana irin wannan mafarkan..?? Ya kamata ka bibiyi asalinkan idan har hakan zaisa ka samu nutsuwa,,lokaci yayi daya kamata ace ka gogewa mutane shakkunsu akan kasancewarka *MARA ASALI..!"*
    Zuciyarsa ke yi masa khud'ba da bashi shawara,a hankali ya d'an dakata da tunani,can daga wani gefen na zuciyarsa yake jin tana sake sanar masa
    "Ya kamata kayi wani abu wajen gano asalinka,idan ba haka ba..!"
    Sai yaji shiru kamar d'aukewar ruwan sama,,tambayar kansa yayi yace "If not.. What..!?"
     Kamar mai jira yayi tambayar zuciyarsa ta bashi amsa da "Har duniya ta tashi zaka tabbata ne a matsayin *MARA ASALI.!* Tare da ci gaba da amsa sunan *'DAN MACE..!"*
   Saitin zuciyarsa yayi saurin dannewa da hannunsa d'aya yana girgiza kai cikin wani matsanancin tashin hankali daya tsinci kansa sakamakon tunane² da yake fama da su ya furta
   "No..!! Bazai tab'a yiwuwa ba..! Sai na tambaye ki,,kuma bazan fasa tambaya ba,duk tsayin *ZAMANI* zan jira na sani,,sai na sani..! Wollahi sai na bibiyi asalina,sai na san *WANE NE ASALIN MAHAIFI NA.!"*
    Ya k'arashe maganar cikin wani irin murya mai amo dake tattare da damuwa,Annie dake tsaka da gyara d'akin tana karkad'e saman bed d'in daya tashi ta jiyo sautin maganarsa daga bathroom,tayi saurin ajiye spread d'in hannunta ta matsa jikin k'ofar toilet tana tambaya
   "Habibiiy.! Me yake faruwa..??" Shiru yayi bai yi magana ba,hakan yasa ta sake fad'in
     "Yi maza ka bud'e k'ofa habibiiy..!"
    Tana naganar tana kwankwasawa da iya k'arfinta,still taji shiru bai amsata ba sai taci gaba da kiransa,jin maganarta yasa a firgice ya juya ya kalli k'ofar,cos bai san a fili yayi maganar ba
   "Yanzun mene ne zan fad'awa Annie ta yarda da ni..?"
    Ya tambayi kansa yana k'urawa k'ofar idanu kamar mai neman amsar a jikin door d'in
    "Yalla habibiiy open the door..!"
   Annie ta sake fad'a tana bubbugawa,jikinsa duk yayi wani irin sanyi a hankali ya janyo towel ya d'aura a waist d'insa sannan ya nufo k'ofar yana b'ata fuska,har lokacin Annie bata daina dukan k'ofar ba tana ci gaba da kiran sunansa
     "Please habibiiy open it for me.."
    Bud'e k'ofar yayi ya tsaya a tsakiyar hanya hannayensa d'age a sama ya dafe both side na hanyar wucewa,bayan ya sake had'e rai wanda yayi masifar k'ara masa kwarjini yana kallon Annie data tsare shi da idanu tana masa kallon tuhuma yace
     "Annie..! What's happen..?"
    Kallon rashin fahimta ta bishi da shi kafin ta kamo hannunsa tana ja da fad'in
      "Wuce muje..!"

      "Annie stop..! Kin kira ni,and u know ban gama abunda nake yi ba..just leave me na k'arasa zan zo.."
   Wani kallon k'asan ido Annie tayi masa tace
   "Na fara wasa da kai ko..?? Zaka wuce muje ko sai na b'ata maka.?"
Chapter 2 · 0% Book details