← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 152

Sashe 25

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Kai tsaye hanyar d'akin kwananmu na nufa,ina tafiya ina sake tunanin halin da na bar y'ar uwata,na kusa da k'ofar d'aki na jiyo muryar Baba yana daka min tsawa
       "Kece.! Maryam ina za ki shiga.!?" Na juya a tsorace na kalleshi jikina sai b'ari yake nace "Baba d'aki zan shiga."
Ya kalle ni sosai yace "Wane d'akin.!?" Nayi shiru na sunkuyar da kaina a k'asa,ya girgiza kai "Ko da wasa kada ki kuskura ki shiga ciki,idan baki jiba kina iya gwadawa,zan nuna miki ni ne na haifeki.."
   Nayi shiru ban d'ago ba,zuciyata ta cika da tsoron shi kenan mai afkuwa ta faru,ina nan tsaye Baba ya kalli babban yayanmu "Abdullahi.!" Ya amsa,yace "Maza shiga d'akin can duk abunda kasan na ta ne ka watso min su nan" yayi masa nuni da tsakar gida,ya sake amsawa ya wuce,ina tsaye ina kallon y'an gidanmu gaba d'aya duk wad'anda suke gida suna nan idan aka cire mata na sama da ni da suke gidan aurensu,mutum goma sha uku suna tsaye suna kallon abunda yake faruwa,haka matar Baban namu itama tana tsaye,har Yayanmu ya gama watsar min da kayana ban iya nayi kwakwaran motsi ba,na sunkuya na tattara kayana ina jin zuciyata kamar za ta fashe da tsananin bak'in ciki,ina gamawa Baba ya fito daga d'akinsa ya kallesu duka ya girgiza kai,muryarsa cike da tsoratarwa "Wannan ita ce makomar duk wanda ya ji ba zai iya yi min biyayya ba,a matsayina na mahaifinku ni kad'ai ne gatan ku,shin ina iyayenki suke.!? Duk da suka watsar da ku akwai wanda uwarsa ta tab'a zuwa da sunan ta zo duba shi.!? Ni nake wahala da ku,bai zama dole ku bini ba.!?"
   Babu wanda ya iya amsawa,yace "Idan kunji ba zaku iya ba,kuna da zab'in ku tafi kuyi rayuwarku yadda kuka so,,sai dai ku sani daga ranar da muka rabu mun rabu kenan,har abada zan kasance a matsayin ba mahaifinku ba.. Sauran shawara ta rage ga mai hankali."
   Jikin kowa yayi sanyi,Baba ya juyo gare ni ya kalle ni "Maryam! Tun da har kin kasance bakya jin magana,ga hanya nan na baki kina da damar kiyi duk abunda kika ga yayi miki kyau,kamar yadda na jima ina tunatar da ke,duk ranar da Allah yasa na ji labarin kin je gurin y'ar uwarki za mu rabu,amma sai baki ji magana ta ba,,shi kenan tunda kin zab'e ta,ki je Allah ya bamu alkhairi.. Dan na cire ku a cikin zuri'ata ba wani abu ne da zai d'aga min hankali ba,Allah ya so ina da wasu y'ay'an.. Ba zan yi bak'in ciki ba,kuma dai Allah ya gani na tsaya akan tarbiyyar ku har na aurar da ku,tsakanin ni da ku idan akwai wanda ya zalunci wani ubangiji ya saka masa.."
    Yana fad'a ya wuce d'akinsa yana barwa Yayanmu sak'on "idan ta fita ka rufe min k'ofar gidana.." Duk y'an gidanmu sun yi cirko² kamar zakarun k'auye kowa si bina yake da kallo,nayi godiya ga Allah da irin k'addarar daya zab'a mana,sannan na d'auki jakar kayana nayi sallama da y'an gidanmu,dan na san ba lallai ne ko a hanya mu sake gamuwa ba..

     Ba tare da na samu tausaya daga mahaifina ba,duk da kasancewarsa shi ne wanda yayi silar zuwa na duniya,y'an gidanmu ma kuma tun da Baba yace na bar masa gidansa babu wanda yayi ko da tari bare su iya bashi hak'uri ya barni na kwana zuwa da safe,,a cikin wannan daren na sake barin unguwar duk da kasancewata y'a mace na kama hanyar Sardauna crescent,na sauka a k'ofar gidan around 12am har da mintuna na bawa mai napep kud'insa na bud'e get na shiga na kulle,na k'araso bakin entrance nayi knocking,still tak'i zuwa ta bud'e,,na yi magana nayi bagging d'inta amma bata yi niyyar zuwa ta bud'e ba,na yi shimfid'a na zauna ina tunanin rayuwa a haka muka ga wayewar gari,da safe ma still na koma nayi magana amma bata kula ba bare ta bud'e,na tafi orphanage da ta fad'a min zata kaika da niyyar na karb'o ka,zuciyata da tunanin hakan zai sa idan Allah ya taimake ni ta ganka ta yarda abunda na fad'a mata gaskiya ne,,na sha wahala sosai a wannan yinin ranar kafin hukumar gidan marayun su yarda su bani kai,muka dawo gida na koma ta can baya wajen window da nufin yi mata magana ina rik'e da kai kana bacci,har lokacin tana zaune inda na barta,nayi ta rok'onta har dare shiru,na hak'ura nace "shi kenan za mu jira duk tsayin lokaci,muna nan tare dake ba zamu barki ba,kinga yaronki ma na karb'o miki shi.."
   Daga haka ban sake magana ba na koma inda nayi shimfid'a na zauna ina ci gaba da tunani,ban san me ya faruba dana barta a d'aki ba,bayan wani lokaci tazo ta bud'e k'ofar tana lek'owa,na d'aga kaina muka kalli juna da ita,jikina a sanyaye nayi murmushi nace "kin gani ko,bamu tafi ba muna nan muna ta jira mu zo gurinki."
   Bata yi murmushi ba sai gesturing fuskarta da take yawan yi kamar wacce ke jin wani abu na mata yawo a jiki,kusan mintuna uku muna kallon-kallo ta koma ta bar k'ofar a bud'e,na tattara y'an kayana na bita a baya ina rik'e da kai a hannu d'aya d'ayan muka kayanmu,,,zuwa na gidan na iske abubuwa da dama,wasu masu dad'i wasu kishiyarsa sai dai mafi yawa daga ciki sune marasa dad'in,rashin lafiyar Hauwa ba k'aramin gigita min tunani yaso yi ba,a wannan hali rashin fahimta daya shafi tunaninta,muka yi ta yawon zuwa hospital,daga karshe muka samu wani likita ya bani shawaran mu gwada zuwa psychiatry,saboda duk binciken da likitoci suka yi sun tabbatar kwakwalwarta ce ta fara tab'uwa,tun daga ranar da likitan nan ya fad'a min hakan bamu sake komawa ko wane irin hospital ba sai psychiatry,munyi yawo akan neman lafiyarta har ban san adadi ba,a nan Kano munje² har ban san adadin yawon mu ba,muka shafe tsayin shekaru biyar muna yawo tsakanin *DAWANAU* da gida,sai dai kullum muna nan tsaye guri guda tana dai under medication ne,naga lamari babu ci gaba na tattaro ta muka dawo gida,sati uku da fitowarta daga dawanau muka nufi birnin ikko (lagos),can d'inma dai yawon muka yi ta fama da shi,ita sun rik'eta a asylum mu kuma muka kama haya,a can ne saboda kasancewar baka gama primary ba na samu damar mayar da kai shool,har ka gama makarantar primary ka tafi secondary muna zaune a can,bamu da kowa a garin ni nake kaika makaranta ni nake d'auko ka,idan na dawo na ji da aikin gida da zuwa duba ta,har zuwa lokacin da kayi wayo kana iya zuwa da kanka ka dawo,,a takaice dai muka sake shafe tsayin shekaru sha biyu a Lagos gurin neman magani ba tare da samun nasara ba,,nasarar da zan iya cewa mun samu a wannan fannin duk abunda yake faruwa da ita bata duka,but idan abun ya haura mata za kaga tana yi kamar zata fita aguje tana surutai,bayan wannan babu wani abu makamancinsa sai dai ko shirun data koma yi daga baya,idan ka yi o magana baza ta amsa ba,haka ma surutai ta daina yi,,daga lagos al'amari yak'i a lokacin ka kammala secondary school muka sake dawowa Kano,dawowarmu babu jimawa idan baka manta ba shi ne farkon lokacin dana nema maka admission a U.K a jami'ar Oxford,after then na sake neman kasuwancin da zai rik'e mu na fara saboda dukiya idan ba'a juya ta tabbas wata rana dole ta k'are,bare mu da muka d'auki shekaru muna yawo,,mun shekara uku ina yawon kasuwanci komai dana san ana amfanin yau da kullum ina siyarwa,Alhamdulillah ubangiji shi ne komai,ya sawa mutane son kayan da muke kasuwancin su,Allah cikin ikonsa ya sake dafa mana kasuwanci ya karb'u,a da mu muke siyarwa cikin k'ank'anin lokaci ya juya al'amarin ya zama mun koma wholesaling sai dai mu shigo da kaya mu raba su ga retail's,Alhamdullah ba zan gaji da fad'a ba a tsakanin shekaru bakwai da dawowarmu kasuwancin mu ya tsaya da k'afafunsa mun samu wadata fiye da baya,Alhamdulillah alaa kulli halin,ba mu da wani damuwa daya wuce lafiyar mahaifiyarka,kullum rayuwarmu cikin haske take but a kullum na kasance mai addu'ar hasken da zai tunkaromu nan gaba ya kasance mafi girma daga cikin hasken da muka samu a baya... Wannan shi ne tak'aicce cikin labarin rayuwar mu..!"

*BACK TO STORY...*

     Dogon ajiyar numfashi suka yi a tare Nuraz ya kalli Annie a hankali idanunsa sunyi ja hawaye suna zuba yasa handkey yayi whipping d'insu yace "Annie me yasa bayan rasuwar mijinki baki yi wani auren ba!?"
   Murmushi tayi wanda iya kacinsa saman lips tace "Habibiiy.! Shin ta yaya ne ni da nake da patient zanyi wani aure,sannan kai kuma na kai ka ina.!? Kada ka manta ba ko wane namiji ne yake son rik'on d'an da ba nasa ba.. Besides ma ko da ace zanyi aure a wannan lokacin ko wane ne yazo da niyyar aurena ba zai tab'a yarda da aure ni ba."

    Yace "Me yasa to Annie.!?" Tace "Ka manta a baya na fad'a maka korata babanmu yayi kamar yadda ya yiwa Hauwa.!? Saboda haka ka ga babu namijin da zai yarda ya auri wacce take *KORARRIYA*,bcos zai ta zargin me tayi haka mai muni iyayenta suka rabu da ita.!? Ka ga kenan rayuwar aurenta kawai dai zai kasance ne ta yi auren amma baza su tab'a samun nutsuwar zuciya ba,,sannan a duk ranar da aka samu sab'ani zai iya goranta mata,hakan kuma zai iya kaisu ga rabuwa.."
      Gyad'a kai yayi yace "Na fahimci uzurinki Annie.."
     D'an murmushin yak'e tayi ta goge fuskarta,a hankali tana kallonsa cikin salon son ta canja hiran ganin ya yi shiru yana tunani tace "Yaushe zaka koma ne.!?"

    Ya d'ago kansa da sauri dake k'asa yana tunanin irin hukuncin da zai yiwa mutane biyu da suka canja tarihin mahaifiyarsa yace "Ina kenan Annie.!?"

     Tace "School nake tambayar ka.!"

   Ajiyar zuciya yayi yace "Maybe sai wani satin."
     Tayi saurin kallonsa tana had'e rai tace "Kai bana son shashanci,da karatun yazo k'arshe saura baifi one month ba shi ne zaka fara delaying wajen komawa,,thought cewa kayi k'arshen satin nan zaka tafi.!?"

      Ya gyad'a kai yana marairaicewa "please Annie ki bari na zauna sai wani satin.?"
Chapter 25 · 0% Book details