← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 152

Sashe 111

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*****
      On the other hand lokacin da Nuraz ya bar mahaifan nasa,cikin wani irin farin cikin da bai tab'a tsintar kansa a ciki ba ya shigo bedroom d'in,here ya tarar da Nusrah zaune a saman armchair ta mik'e k'afafu daga ita sai towel whose height was not above her knees,da sauri ya k'araso ya rungume ta,tayi murmushi tana k'ank'ame shi so tightly,sun d'auki lokaci a haka kafin ya saketa ya dawo next to her ya kwanta and placing his head over her thighs and playing with his finger,ta lumshe ido tana jin tsigar jikinta tana yi mata wani iri,idanunsa a rufe yana sakin murmushi yace "Rooh!" Taja numfashi very hardly kafin ta amsa "Na'am" yana yin murmushi yace "Kyakykyawan labari na kawo miki" murmushi tayi tace "every time i get good news from u,thank u so much Hayat" yace "Kina so na fad'a miki?" Ta gyad'a kai da sauri cikin d'oki,yace "Labarin guda biyu ne,which is ur favorite?" Quickly tace "Duka ina so" yayi murmushi yace "Sai dai na fad'a miki d'aya" ta b'ata rai tace "Ka fad'a min duka pleaseee!" Idanunsa ya bud'e fuskarsa ta kasa b'oye farin cikin da yake ciki,yace "Well labari na farko,za kije Nigeria" quickly ta kalleshi bakinta ya kasa rufuwa saboda mamaki,yace "the second one is.!" Kafin ya fad'a tace "What are we going to do there?" Ya d'ago kansa yana kallon fuskarta,yadda tayi alamun like she didn't want yasa shi cewa "Ke kad'ai za ki tafi" ta zaro ido gabanta yana bugawa tace "Ni kad'aifa kace?" Yayi nodding mata kansa yana lumshe ido,tace "Uhn!" Quickly ya bud'e idonsa yace "Ba za ki je bane?" Ta gyad'a kai da sauri,yace "why not?" Tace "I just don't want" yayi shiru yana kallon mood d'inta daya canja,tashi yayi ya zauna yana fuskantarta yace "look into my eyes Rooh!" Girgiza masa kai tayi zai yi magana tace "I've no where to go" muryarta kamar za ta yi kuka,yayi shiru ya zuba mata ido,a hankali ya rik'o chin d'inta but tak'i yarda su had'a ido,yayi ajiyar zuciya a hankali yace "shi kenan yanzu haka kike so na fad'awa Dad? Or do u want me to tell him kince ba za kije kiran da Abba'n yake miki ba?" Tayi saurin d'ago idonta tace "Abbah? Wane Abba'n?" Ya d'aga mata gira cikin sigar tambaya yace "Abbah nawa kika sani?" Tayi shiru kamar mai tunani can tace "Ai nima ban gane wanne kake nufi ba" yayi ajiyar zuciya yace "Abbanmu nake nufi" ta yi shiru tana kallonsa,yace "Ina tunanin kamar za kuje Gombe idan kin isa Nigeria" here she began to understand where his words intend to go,quickly tace "To kuma ni kad'ai zan tafi?" Yana nodding mata kai yace "Haka nake tunani" tace "why don't u go?" Yayi saurin katseta "u know ina da aiki ko?" Tayi jim a hankali tace "Kwana nawa zan yi to?" Ya d'aga shoulders yace "Ban tambaya ba" tayi shiru tana kallonsa can da aka jima tace "Allah ya kaimu lokacin" ya kalleta kad'an yace "Oh! Yanzun kuma za kije?" Ta gyad'a kai a hankali tace "Ba dan ina so zan jeba" yace "Me yasa haka?" Tace "Da can ina son zuwa,but yanzun ne gaskiya ba na so" yace "Ko a kira Abbah ace ya tafi shi kad'ai?" Tayi saurin d'aga masa kai,ya tsaya kallonta cike da mamaki yace "what happened to u?" Tana kallonsa tace  "nothing" ya girgiza kai yace "I don't think so" ta zuba masa ido kamar bata sanshi ba,ya kalleta yace "Za ki fad'a min abunda yake damunki ko a'a??" Tace "Ni fa babu komai" yace "Ban yarda ba" tayi shiru tana kallonsa,yace "Lokacin da kike da lafiya ke da kanki kike cewa kina son zuwa,me yasa yanzun kika canja?" Ta bud'e baki za tayi magana,yace "Idan Allah ya amince jibi za ki tafi,ko yanzun ma saboda dare yayi ne,da a gobe za ki tafi" kuka ta fashe masa da shi tana fad'in "Ni Allah ba na son zuwa" yayi still yana kallonta da mamakinta,sai da tayi mai isarta ta bari sannan yace "Tunda ba za kije ba,sai ki kira Abba'n da kanki ki sanar masa",bata kula shi ba sai da ta gama share hawayen then ta d'auki wayarta da tun bayan shigowarsa ta ajiye,ya wuce arean closet ya barta a nan cike da takaici,after ya rage kayan jikinsa yana fitowa ya jiyo tana magana a waya,he didn't say anything ya wuce zai shige bathroom dai² lokacin da take cewa "Abbah ni gaskiya ba zan bika ba" yayi saurin juyowa yana kallonta,ransa b'ace ya dawo ya karb'e wayar,tana kallonsa tace "Give me my phone please,zan fad'a masa yaje shi kad'ai ba na son zuwa" ya had'e rai yace "Wai me yasa kike son lallai sai kin b'ata min rai?" Tace "I'm sorry,but i just don't want to go" yace "for what purpose?" Tace "Haka kawai" ya girgiza kai yace "Ba zan yarda da wannan amsar ba" tace "Allah ni dai haka kawai naji ba na son zuwa" sosai yake mamaki saboda wasu lokacin ita da kanta take fad'a masa tana son zuwa taga dangin Abba'n kasancewar tun kafin mahaifiyarta ta rasu rabonta da zuwa,yace "Ok na ji wannan,amma kin san bai dace ki fad'awa Abbah haka ba ko? Me kike so ayi tunani? Kin fi so ace ni na hanaki zuwa?" Ta girgiza kai,ya dawo gefenta ya zauna yana sassauta murya yace "Idan kikace ba za ki ba,kowa zai yi tunanin ni na hanaki,please ko da ace ba kya so ki yi hak'uri kije kinji?" Tayi shiru tana kallonsa,yace "will u?" ta girgiza kai a hankali alamar a'a,ya girgiza kai shima yace "Kada muyi haka da ke" tace "Ni gaskiya ba na so" yace "u will" tace "A'aahh!" Yace "Ehh!" Tace "well,why don't u go?" Yace "Na fad'a miki ina da aiki ai" tace "Nima ai ina zuwa skul" yayi murmushi ya wuce zai shiga bathroom,ta bishi da kallo kafin tace "Ok! Saboda kana fushi shi ne za ka tafi ka barni?" Ya juyo da sauri yana kallonta,ta had'e rai kamar ba ita ce tayi maganar ba,yace "Me kika yi min da zan yi fushi?" Tace "na sani ko dan na ce ba zan je ba shi ne kake fushi" ya girgiza kai cikin takaici yace "Kawai kuma saboda kince ba za kije ba sai nayi fushi?" Tayi shiru tana turo baki gaba,yace "C'mon ban yi fushi ba" ta kalleshi kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa,ya girgiza kai bai ce mata komai ba har ta k'araso,a toilet bai wani tsaya biye ta son kansa ba,suka yi wanka suka fito,after sun yi shirin bacci suna kwance yaja numfashi a hankali yana kallon shadow d'inta,muryarsa a low tone yace "Kinji me na fad'a miki?" Ta girgiza kai tace "A'a" yace "Jibi za ki tafi" tana b'ata rai tace "Toh" daga haka she didn't say anything sai matsawa da tayi ta rabu da jikinsa,he just look at her shadow,though a cikin duhu ne ya san yanzu tana nan kamar za ta fashe,yayi murmushi ya sake matso da ita jikinsa,ta fara ture shi tana son k'wacewa,ya rik'eta tightly yace "Me kike yi haka? A haka za mu yi sallama?" Ta fashe da kuka tana cewa "Ni wollahi ba na son zuwa,kawai dan an fi k'arfina ne,but Allah ya sani har zuciyata ba na son zuwa" saurin kunna bedside lamp yayi,yana kallon yadda take kuka yace "Shi kenan tunda ba kya so ki zauna,amma duk wanda ya tambaya zan sanar masa ban isa dake ba" tana kuka take fad'in "Ni bance haka ba,tunda ka ce naje zan tafi but ba don ina so zan je ba" ya tab'e baki ya kashe lamp shade d'in yana fad'in "Ke kika sani kuma" tana jinsa ya kwanta bata yi magana ba ta matso jikinsa,ya d'ago da sauri yace "What else?" Tace "I'm sorry" yace "No kada ki damu,i'm not angry" tace "To ai na ce zanje" ya tab'e baki yace "A'a ki barshi kawai ba sai kin je ba tunda ba kya so,kada mu takura miki" a jikinsa ta kwanta hannunta sun k'i tsayawa guri d'aya tace "Ai dama ni banyi maka musu ba,kawai dai na fad'i abunda yake raina ne" ya gyad'a kai bai ce komai ba,tace "will u?" Yace "Ke za'a bawa hak'uri ba ni ba" tayi shiru bata sake cewa komai ba sai ta tura hannunta cikin rigarsa tana lalubensa,da sauri ya rik'e mata hannu yace "Kin ga please ki bari nayi bacci,da safe ina da tarin aikin da zanyi a hospital" harararsa tayi tana tab'e baki,duka suka yi shiru da taji haushi ta cire hannunta daga cikin rigarsa,da aka jima ta sake mayarwa ta ci gaba da wasa da kwantaccen gashin dake wajen,da taji bai hanata ba ta yi tunanin ko yayi bacci,a hankali ta kai hannunta saman fuskarsa tana tab'awa,ya rufe idanunsa and said nothing,saman lips d'insa ta kai yatsanta tana shafawa like tana sa masa lipstick,ya share lamuranta yak'i yarda ya nuna mata idonsa biyu,da ta gaji da kanta ta bari sanadiyyar baccin da ya d'auke ta,yana jin numfashinta ya canja yanayin fita yayi ajiyar zuciya ya gyara mata kwanciya.
Chapter 111 · 0% Book details