Sashe 68
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
In the morning at about 7:00am ya fice daga gidan,ba shi ya dawo ba sai can misalin 10am,Nusrah dake zaune a parlor tana fama da assignment taji alamun shigowar sa,ta d'ago ta bishi da idanunta,kallo d'aya ta yiwa fuskarsa ta gane he wasn't in the mood,as he did not speak haka nan itama bata kula shi ba har ya wuce,ko me ya tuna kuma taga ya dawo da baya,tana ganin ya juyo ta d'auke kai,ya kalleta kamar zai yi magana again ya fasa ya juya yayi shigewarsa,girgiza kai tayi ta maida hankali kan abunda take yi,zuciyarta ta sanar da ita "Kije yanzun kafin ya sake fita" da sauri ta tashi and left behind tana jin zuciyarta tana yi mata babu dad'i,knocking ta fara yi tana tsaye taji shiru ta sake yin knocking,Nuraz dake tsaye ya had'e rai yace "Who's there.!?" Nusrah ta gyad'a kai tana danne b'acin ranta tace "Ni ce" shiru yayi bai sake magana ba,har ta yi kamar za ta koma taji ba zata iya tafiya ba ta tura k'ofar ta shiga,a bakin bed ta hangosa tsaye ya rik'e waist kamar mai tunani,ta mayar da k'ofar ta rufe,da sauri ya waiwayo jin an shigo ya tsare ta da idanunsa,ta tsaya daga inda take bata k'araso ba,tana sauke idanunta daga kansa saboda kallon da yake mata if she kept looking at him to know that za'a samu matsala,he was silent and waited for her to speak but for about five minutes she could not say anything,he turned slowly and continued to look at what was in front of him,ajiyar zuciya tayi and then ta fara k'ok'arin yin magana "I want talk to u" bai juya ba yace "Ok!" Ta kalle shi as he turned his back ta daure tace "But u turned away from me,how can i speak.!?" Yace "Ina sauraren fad'i abunda kike son cewa" kasa daurewa tayi a hankali ta fara tahowa har ya rage nisan da yake tsakaninsu ba shi da yawa sannan ta dakata,muryar ta tana rawa tace "I don't know what's going on cikin kwanakin duk ka canja min daga yadda kake,idan laifi nayi maka ya kamata ace ka sanar da ni saboda b'oyewar babu amfanin da zai mana,and a nawa tunanin yanzun mun wuce matakin da za mu b'oyewa juna wani abun,ni ban san mene ne nayi maka da zafi ba,i just kept quiet and waited for u to tell me,but sai na ga this was not the solution,,why are u always angry with me.?" Juyowa yayi ya ci gaba da kallonta har lokacin hannayensa suna saman waist d'insa,sai daya gama k'are mata kallo sannan ya tab'e baki kamar ba zai ce komai ba and then simply yace "Babu abunda kika yi" tayi saurin kallonsa bakinta har hard'ewa yake tace "If there is nothing me yasa za kana share ni,ko gaishe ka nayi sai ka ga dama kake amsa min,baka tab'a tunanin ina jin ciwon abun da kake yi min ba.!? I am a being like everyone who knows happiness and rivalry,idan ba laifi nayi maka ba me yasa da can baka tab'a min haka ba sai yanzun.!?" Idanunsa ya lumshe ya bud'e yace "Na fad'a miki babu komai!" A tsiwace tace "Wollahi akwai,bcos matuk'ar babu k'ira na tabbatar babu abunda zai ci gawayi,just come out and tell me idan ma ra'ayi ka canja akaina,ba sai ka ba ni wahala ba kawai ka fito ka fad'a min" Kasak'e yayi yana kallonta fuskarsa da tsantsar mamakin dama ta iya fad'a haka? Yadda taga ya tsare ta da ido tayi blinking idanunta tace "Baka ce komai ba" Yayi ajiyar zuciya yace "What do u want me to say.!?" Tana had'e rai tace "Say's everything",yayi tak'aitaccen ajiyar zuciya yace "I think na fad'a miki babu komai ko.!?" She quickly interrupted him "I can't believe there's nothing" yace "Ok.! K'arya nayi kenan.!?" Kuka tasa masa,yayi saurin matsowa kusa da ita a rikice yana fad'in "Look ni ban ce kiyi min kuka ba,daga tambaya kawai sai kisa min kuka" cikin kuka tace "To ni ya kake so nayi da rayuwata? Shi kenan ko wane lokaci ba ni da kwanciyar hankali,da wanne zanji dan Allah,da damuwar data dame ni ko kuma da naka.!? Idan na tambaya kace babu komai na yi shiru ina tunanin za ka fad'a min abunda yake faruwa nan ma babu mafita,kawai ni ka fito ka fad'a min abunda nayi maka" sumar kansa ya shafa a hankali yace "Ok na ji zauna muyi maganar tunda haka kike so" da kyar ta yarda ta zauna a saman study table d'insa shima bayan ya ci bak'ar wahala wajen lallab'ata,ya zauna saman resting chair yana kallonta,ta d'ago tana goge hawaye suka had'a ido da shi,ta sake tsuke baki kamar idan yayi wani maganar zata sake saka masa kuka,k'asa² yace "what do u want me to tell u right now.!?" Bata yarda ta kalleshi ba tace "Everything" yace "Akan me zan fad'a miki komai.??" Tayi shiru bata ce komai ba,shima shirun yayi mata sai data sake kallonsa and then he began to tell her about his plans for their trip to Nigeria,but ya b'oye mata da yawa daga cikin k'udurin sa na yin hakan,tayi ajiyar zuciya bayan ta gama ji tace "To amma shine sai ka dunga share ni akan wannan abun?" Yayi mata murmushi yace "Bana so a cikin ku duka wani yace ba zai je ba" tace "To kuma ai baka fad'a mun ce ba za mu je ba" yace "Ehh! Babu mamaki yanzun da nayi haka kuyi saurin amincewa" tayi ajiyar zuciya kad'an,daga nan kuma sai ta sakko saboda ta ji dalilin nasa,sun d'anyi hira sosai cikin raha da nuna kulawa sannan ta fita,tana tafiya yayi ajiyar zuciya ya fara shirin sake fita bcos zuwa next week yake shirya musu barin k'asar.