← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 152

Sashe 58

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

    Tsayin lokaci ta d'auka shiru tana tunanin mene ne hakan yake nufi.? Ta tambayi kanta ya fi a k'irga amma ta kasa ganewa,da taga za ta b'atawa kanta lokaci wajen tunani da son bincikar abunda ba ganewa za tayi ba ta tab'e baki tace "ko me haka yake nufi oho.!" Next page ta bud'e taci gaba "Had'uwar mu ya kasance wani babban k'addara ne daga Allah.!" Nutsuwa ta sake yi sosai tana karantawa har ta kai k'arshen page,though bai fito ya bayyana ko da waye suka had'u ba zuciyarta ta gama finding mata mace ce yake magana akai,ta sake tab'e baki felt like she was keeping,but she found herself unable to keep up,ci gaba tayi da bibiyar rubutun yadda yake zayyana irin yadda yake ji game da ita a ransa ya sake tabbatar mata zarginta akan lallai mace ce and ba wai yana nufin mahaifiyarsa ba,wani page data bud'e taga hotuna sun zubo a hankali tabi su da kallo kafin ta fara bi tana tsintowa,kasancewar a kife suka zube sai bata samu damar gane ko waye a jiki ba,ta d'ago su tana fad'in "Ohh.! Allah ya kamaka" she turned the images confidently tana murmushi,her eyes wide open kamar za su fad'o k'asa with signs of fear,fuskarta tana sake bayyana tsananin mamaki a fili ta furta "Where did he get those pictures.!?" Tana rike da su sai juya su take tana k'are musu kallo da tunani,duk inda tunaninta da hangen nesanta suka kai sai data bincika but the situation was beyond her knowledge,she was quietly thinking lokaci guda her mind began to remember ranar da suka je gidansu tare bayan sun taho a hanya sun tsaya a wani photo studio har yace ayi mata passport,ta sake kallon pictures d'in a fili ta tambayi kanta "To ai passport aka yi min ranar,,where did he got these.!?" Zuciyarta tace "idan baki manta ba kayan da suke jikinki a lokacin sune wad'annan ai" tana jinjina lamarin har ranta tace "kenan a ranar aka d'auke ni ban sani ba ko yaushe ne hakan ya faru.!?" Murmushi tayi kad'an tace "Ikon Allah" a saman page d'in idanunta suka sauka inda ya rubuta "I had hidden my love for her ba tare da tunanin abunda zai faru da rayuwata ba,continuously hoping to have the power to express my love for the first time,ita ce kad'ai nake ji a cikin jini na,,but i don't know why all the time i tried to express my love i couldn't tell her that few words.! Abunda ban sani ba ashe abunda zai faru da rayuwata kenan,,,na b'ata tsayin lokaci ina ci gaba da kasancewa b'oyayyen masoyin da ba'a san da zamansa ba and mara amfani..!" Next page ta sake bud'ewa "The day i was about to express my love for her,i just came back ina zumud'i bcos my mind was telling me that i was going to be the lucky,but lokacin dana ganta tsaye da wani,naji zuciyata ta yi rauni.. I felt like my heart were explode,na bawa kaina laifi and na tuhumi kaina why i hadn't said it before,that *I love her.!?"* Ido Nusrah ta zaro tana fad'in "Then who is she.!?" Ta fad'a tana saurin bud'e d'ayan page d'in like ance mata idan ta duba gaba za tayi finding out amsarta.
     "Ke ce.!" Taji an fad'a as his voice crossed her ear's,murmushi tayi tace "Ni kuma.!? How did i become his love.!?" Sai da tayi maganar sannan kuma tayi saurin d'ago kanta because she made sure that the speaker was near her and hakan da yake fatuwa was not a dream or a thoughts,tana d'agowa karaf idanunta suka sauka a kansa,yana tsaye daga bakin k'ofa his hands were pouring into his trouser pocket,wani irin yawu ta had'iya cikin in'ina da kame-kame irin na mara gaskiya,ba tare data furta komai ba tayi saurin rufewa ta ajiye,ya lumshe idanunsa ya bud'e slowly ya fara takowa to where she was,a tsorace ta d'aga kai ta kalleshi yadda fuskarsa take babu wadataccen annuri yasa taji y'ay'an cikinta suna kad'awa,sai da yazo daf da inda take sannan ya zauna daga gefen bed d'in yana kallonta,as she silently bowed her head to the ground ya bashi dariya sai dai ya gimtse yak'i yi and instead of ya tambayeta daya zauna sai yayi mata shiru,a tsorace ta daga kai ta sake kallonsa,so take tayi magana amma ta kasa saboda yadda ya tsare ta da idanunsa,can dai da taga no way out ta daure tace "I'm sorry.!" Ya sake gimtse fuska yace "Me yasa kika tab'a min abu.!?" Kai tsaye tana runtse idanunta tace "I'm so sorry ba da gangan nayi ba" ya girgiza kai yace "how long have u been here.!?" Tace "D'azu ne babu jimawa" ya gyad'a kai yace "What did u come in for.? Ko dama kina zuwa ki yi min bincike idan bana gida.!?" Tayi saurin girgiza kai tace "A'a!" Yace "Uhhuumm! Tell me" tace "Ban tab'a shigowa ba sai yau" yace "Really.!?" Tayi saurin girgiza masa kai tana kallonsa,idanunsa ya lumshe yace "Uhmmm.! What did u see in it.!?" Tace "Nothing" yayi saurin bud'e idanunsa yace "Really.!?" As he spoke ita kanta bata san yaushe ta saki murmushi ba,he adjusted his position zuwa yanayin kwanciya yace "Since u don't see anything karanta min from the beginning!" Saurin zaro ido tayi tace "What.!?" One eye brow ya d'aga mata ba tare da yayi magana ba,pages d'in data wuce ta tafi haskowa ta juyo ta kalle shi tace "There are many fa.!" Yace "What.!?" Tace "Pages d'in" tsayawa kallonta yayi yace "Ohh! Ashe kin karanta kenan.?" ta gyad'a masa kai,yace "Well,,have u finished ur research Miss.Researcher.!?" Ta sunkuyar da kai saboda kunya ta kasa amsawa,yayi shiru yana kallonta da tunanin ya bari ta ga abunda yake ciki ko dai ya fad'a mata da kansa.!? Zuciyarsa tace "Kawai tunda ka samu dama ka fad'a da bakinka zai fi ma'ana,idan ta karanta babu tabbas ya burgeta" ajiyar zuciya yayi nan ya tsinci kansa da fad'in "U know what.!?" Tayi saurin kallonsa tana girgiza masa kai,sai yayi shiru ya kasa magana,yayin da wani sashi na zuciyarsa kuma yana fad'a masa ya kyaleta kawai tunda bata gani ba,jin yadda yayi shiru yasa ta d'ago kanta suna had'a ido tayi saurin d'auke nata ta mike tsaye zumbur as she continued playing with her middle finger tana kame²,ajiyar zuciya yayi yace "Where do u think to go.!?" Tana in'ina tace "Am! Dama ina son tafiya ne" ya gyad'a kai yace "Baki isa ba yarinya" ta marairaice fuska kamar za tayi kuka tace "Amma ai na baka hak'uri" yace "Ina ruwana da hakur'in da kika bayar.!?" Ta juya tana kallon k'ofa yace "Get seated,babu inda za kije sai kin karanta min abunda kika gani" tayi shiru ta sunkuyar da kai,ya kalleta ta gefen ido ya d'auko diary d'in yana juya shi a hannunsa yace  "Ko dai na ara miki ne.!?" Tayi shiru bata ce komai ba,ya tab'e baki yace "Shi kenan tunda ba kya so za ki iya tafiya" tayi saurin katse shi "Ina so mana" yace "Really!?" Ta gyad'a masa kai,yace "Ok let me think" tayi shiru kamar zatace "Wane irin tunani.!?" Sai kuma ta fasa jikinta babu wadataccen kuzari ta juya ta fara tafiya,har taje bakin k'ofa bai ce mata komai ba ita kuma tana jin jikinta yana bata kallonta yake yi,sai da yaga tana shirin fita ya dage ya furta *"I LOVE U.."* Kamar wacce aka dasa haka taji duk jijiyoyin jikinta sun tsaya she quickly turned to him,itan shima yake kallo a yadda ta ga irin kallom da yake mata babu tantama shi yayi maganar,continuously looking at him zuciyarta cike da tsoron abunda ta jiyo,yana kallonta babu shakka ko tunanin wani abu a ransa ya maimaita fad'ar *"I love u.!"*
Chapter 58 · 0% Book details