← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 152

Sashe 31

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta girgiza kai alamun A'a,Annie ta takurata akan lallai ya kamata ta daure ko sau d'aya ta ganta,ba dan ta so ba sai dan nacin da Annie ta gwada,tana hararar ta ta amsa,Annie ta d'auki wayarta dake ajiye bisa cinyarta ta shiga kiran Bareerah through video call,Bareerah na yin connecting tayi sallama,Annie ta amsa taga tana kitchen tace "Yawwa Bareerah,ina Nusrah take.!?"

Bareerah tace "taught tana bedroom a kwance"

Annie tace "ok.! Ki kai mata waya za muyi magana" tace "toh",Annie na kallonta ta fito ta wuce bedroom d'in sannan ta kalli screen d'in tace "Ga ta zan bata wayar"
Annie ta gyad'a mata kai,dukan su suna jin lokacin da Bareerah tace "Nusrah anshi waya Annie tana son magana dake",a hankali ta tashi ta zauna tana sakin ajiyar zuciya,alamun tayi kuka sosai da suka fita,ta karb'a ta d'an kalli screen d'in taga Annie zaune a parlon gidansu,sallama tayi tana sauke idanunta k'asa,Annie ta amsa tace "daughter d'ago ki kalle ni" a hankali ta d'aga idanunta da suka kumbura,Annie tace "Stay still,ina son nuna miki wani abu ne yanzun kin ji ko.!?"
Ta gyad'a kai,a hankali Annie tace "Wannan wace ce d'inki.!?" Ta fad'a tana juya cameran saitin Hamshak'iyar Hajiyar,Nusrah na ganinta gabanta ya fad'i,ta daure tace "She's my mommy" Annie ta jinjina kai ta juyo fuskan cameran kanta tace "Kin tabbatar.!?" Ta amsa tana share siraran hawayen da suka zubo mata,Annie tace "Good! Shi kenan ajiye waya,za muyi magana idan mun dawo" ta amsa da "toh" a sanyaye tayi musu addu'ar dawowa lafiya,Annie ta amsa sannan tayi disconnecting kiran,ta d'ago tana kallon Hajiyar tace "Ina fatan kin ganta kuma kin shaida ta.!?"

Cikin kame² Hajiyar tace "Kamar yaya na gane ta.!? Taught na fad'a muku bamu da wata yarinya a gidan nan.!?"
Nuraz ya mik'e tsaye yana tura d'ayar wayarsa a aljihun trouser d'insa,duka suka kalleshi,ya sake d'aure fuskarsa yace "Hajiya for sure wannan yarinyar a gidan nan take,so ki daina pretending kina denying ba nan take ba" ta d'ago ranta a b'ace tace "K'arya zan maka kenan.!?"
Ya dage shoulders yace "Ban fad'a ba,amma dai na tabbatar kusan hakan kike shirin yi,y'ar mijinki ce itan ke kuma bakya sonta a gidan nan ko..?"
Ranta a mugun b'ace ta gimtse fuska tace "Kada ka fad'an bak'ar magana" yace "Babu bak'ar magana,amma na tabbatar kema kin san hakan ne" ta kautar da kanta gefe tayi k'wafa,Annie ta kalleshi tace "habibiiy! Ka yi shiru" ya sauke kansa k'asa bai sake magana ba,Annie ta kalleta tace "Shi kenan Hajiya tunda kince ba y'arku bace,mu zamu koma" bata kalli inda suke ba tace "Okay.!"
Daga haka bata sake magana ba har Annie tayi mata sallama,da suka fito babu wanda yayi magana suka kamo hanyar dawowa gida,suna tafe cikin mota shiru kowa da tunanin dake ransa,Nuraz yayi saurin kallon Annie yace "Annie.! this woman ko is a devil"
Ta gyad'a kai tace "agreed",yace "didn't u understand something.!?",tace "like what.!?" Yace "she lies twice fa,first lokacin da kika sanar mata sunan yarinyar ta shiga mamaki,and then ta tambaya wani abu ya same ta.!? Kinga kenan ta santa ko.!?" Annie ta gyad'a masa kai,yace "secondly tace su yarinyar su ta b'ace har sun yi jana'izarta,,if u compares both statements of her,u will proved that she lied to us"
Annie ta sake jinjina kai tace "na fahimci haka,shi yasa ma na taso muka taho,cos idan muka takura ta dawo bamu san mene ne zaiyi going through ba kuma,,so yanzun na riga na yanke shawaran kawai zata ci gaba da zama tare da mu,zuwa nan da d'an wani lokaci,kafin mu sake tuntub'ar su muji."
Ya jinjina kai alamun hakan yayi,har suka k'araso gida maganar da suke ta tattaunawa kenan akai. Bayan sun huta Annie ta kira Nusrah tayi mata bayanin komai,Nusrah tayi kuka sosai sannan ta yiwa Annie godiya,tun daga ranar take ta zaune a gidan,tun bata saki jiki sosai ba,har ya zama ta saba da su sosai,zamanta a gidan yasa tayi gaining some peace of mind,ta sake yin y'ar k'iba tayi fresh da ita,a kullum idan ta tashi za ta taya Bareerah su yi aikin gidan tare,though she knew idan Annie ta ganta tana hanawa amma ta dage sosai wajen ganin ta kyautata musu itama,and har lokacin ba wani sosai take zama ayi hira da ita ba,tafi dai ta shiga d'aki ta kwanta tana tunani,sai idan Annie ta shigo ta ganta tayi mata fad'an ta ragewa kanta yawan tunani sannan zata fita parlor ta zauna ko ta kunna TV.
A gefen mahaifiyarsa kuwa zuwa yanzun jiki Alhamdulillah! Ko dai da yake har yanzun bata magana sosai sai kad'an² suma words ne da basu wuce a lissafa,kuma still tana kan magani,sai ya yanke shawaran kawai idan zai tafi U.K zai tafi da ita can,yana ganin can suna da na'urori masu kyau kulawar da zata samu da canjin gurin zama,yanayin sauyawar iska zai sake taimakawa jikinta sosai.

A week after ya gama shirin tafiya training d'insa,,Nusrah na zaune a parlor ya fito sanye cikin shigarsa ta yau da kullum yana sanye cikin V-neck double breasted waistcoat red wine da suke colour d'aya da trouser d'insa,sai bak'ar long sleeve,da bak'in cover shoe na maza,hannunsa d'aure da agogon Omax black leather,sumar kansa ta sha gyara tayi luf² sai baza k'amshi yake,har ya fito bai kula da mutum a gurin ba,sai daya ratso cikin parlor'n sannan ya ganta kwance saman armchair tayi shiru tana tunani,kamar zai wuce kuma ya fasa,ya k'araso inda take yayi making snap a dai² fuskarta,suddenly sound d'in da suka yi releasing yasa ta firgita da sauri ta dawo duniyarta,ya kalleta kad'an yace "Tunanin me kike yi ne.!?"
A daburce ta girgiza kai tana b'oye idanunta,ya tab'e baki kad'an yace "Ok! Bring ur hijab and come with me.!"
Ta d'ago da sauri ta kalleshi,yayi saurin wucewa ya barta yana tafiya yana fad'in "don't keep me waiting"
Har ya fita bata iya motsawa ba,tana ta tunanin inda za suje,ita dai ta san magana ba had'a su take ba,daga gaisuwa shi kenan,a kullum kuma abunda yake raba su kenan,,yana zaune cikin motar ya sako k'afarsa d'aya waje yana wasa da ita,ya kira Annie,tana d'auka yayi sallama then yace "Annie.! we'll just go out and get back right now",tace "kai da waye.!?",yayi jim yana tunani kafin yayi k'arfin hali yace "with her" ta gane wa yake nufi,sai tace "okay! May God keep the way and return u safely" ya amsa "ameen,thank u Annie",suka ajiye wayar a tare,shiru² yana jira har ya fidda rai zata fito,a hankali ya gyara zama yana shirin rufe k'ofar ya hangota tana fitowa,k'arasa abunda yayi niyya yayi,yana ta kallonta har ta k'araso,ya bud'e mata gefensa ta shigo ta rufe,a hankali ya fara driven d'insu har suka fita daga gidan,yana hawa kan titi ya fara gudu,tayi ajiyar zuciya ta saci kallonsa ta gefe,ta ji gabanta yana fad'uwa a hankali ta dafe k'irjinta tana addu'ah,har suka tsaya bakin get d'in gidan yayi horn aka bud'e musu suka wuce,ita dai har sannan bata yarda ta dago ba sai da yayi parking ya fita a hankali taji yace "come down" ta d'ago a hankali zata bud'e ta fita taga gidansu suka zo,a tsorace ta waiwayo tana kallonsa yana daga waje yana kallonta,ta dunga girgiza kai tace "let's go home,i don't want to come here.!"

Yana kallonta yace "Why don't u.!?"

Tana girgiza masa kai a tsorace hawaye na bin fuskarta tace "Please.! Let go back",ya girgiza kai yace "come down" tana girgiza kai tace "I won't" tsawa ya daka mata yana had'e rai yace "U will",jikinta na b'ari taci gaba da hawaye,ya zagaya inda take ya bud'e mata,cikin bada umarni yace "come out",a hankali ta sako k'afafunta waje but ta kasa tashi,ya kalleta bai yi magana ba yaga tak'i fitowa,hannunsa yasa ya d'agota,tayi saurin kallonsa ganin sunyi daf da juna,da sauri ya saketa ganin irin kallon da take masa ya fara tafiya,har suka tsaya bakin entrance d'in bai juyo ba,yayi knocking sannan suka tsaya jira a bud'e musu,Binitta tazo ta bud'e musu k'ofa,d'an kallonta yayi kad'an yace "hope they are here.!?" Tace "Sure sir" ya jinjina kai ya wuce cikin parlor'n,Binitta na tsaye bakin door d'in taga Nusrah ta shigo,a d'an tsorace ta kalleta tace "Is that really u.!?"

Nusrah ta gyad'a mata kai a hankali,Nuraz ya waiwayo ya kalli Binitta bai zauna ba yace "do you know her.!?" Tace "Sure sir"

Yace "Where.?" Ta bashi amsa "in this house.!" Yace "Since when.!?",ta kalli Nusrah ta kalle shi kafin tace "it was long ago",ya jinjina kai yace "who is she.!?" Tace "She's a daughter of our leader",ya sake tambayarta haka ne.!? Tace masa "sure" k'wafa yayi yaci gaba da tafiya Nusrah ta biyo shi a sad'ad'e kamar ba gidan su ba,ya samu guri ya zauna,amma ita ta kasa zama,ya d'ago ya kalleta yaga she's totally not compatible ya daure yace "sit" yana nuna mata kusa da shi,a hankali ta daure ta zauna,suna ta zaune suna jira kasancewar Binitta ta kira Hajiyar ta fad'a mata akwai bak'i a parlor'n k'asa,kuma ta san da zuwansu,har kusan half of hour sannan ta sakko sanye da shirin bacci bcos to 9pm a lokacin,tana tafiya tana binsu da kallo har ta k'araso cikin parlor'n,yauma bai gaisheta ba ya d'ago kansa a hankali ya kalleta eye to eye yace "hope u recognize me.!?"

Tayi gesturing tace "No.! But i wanted to witness ur face",yayi wani b'oyayyen murmushi a sauk'ak'e yace "we came here with my mom" ta d'ago ta kalleshi sosai kafin ta sake d'aure fuskarta tamau tace "What brought u here.!? what have u come to do.!?"

Alama yayi mata da hannu irin ta kwantar da hankalinta d'innan,ta banka masa harara tana jira taji yace wani abu,a hankali yayi mata nuni da Nusrah wacce ta sunkuyar da kai k'asa yace "Ina fata kin gane wannan.!?"

Ta yi saurin kallon kusa da shi,Nusrah ta d'ago a hankali tana hawaye,Hajiyar ta zaro ido kad'an,but sai ta dake tace "So what idan nace ban gane ba.!?"

Ya sake yin murmushi yace "Nothing" tana kallonsa tace "Me kuka zo yi ne.!?"

Ya mik'e tsaye yana tura hannunsa d'aya a cikin aljihu d'ayan kuma ya cusa fingers d'insa cikin gashinsa ya hargitsa kad'an yana lumshe idanunsa yace "Gaggawar me kike yi.!? Ai zamu fad'a miki abunda muka zo yi.!?"
Chapter 31 · 0% Book details