← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 152

Sashe 57

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     3:00pm Nusrah came home from school yau d'in ma bata tsaya jiran su Sarah ba saboda kanta da yake mata ciwo a hankali take tafiya like she didn't want to har ta tsare cab ta fad'a masa inda zai kaita,yace ta shiga ta bud'e ta zura k'afarta tana jin kanta yana sake yi mata wani irin ciwo kad'an²,kamar wacce aka bawa umarnin d'agowa dai² lokacin ta daga idanunta da suke lumshewa su kad'ai,can daga d'an nesa da su kad'an ta hango shi tsaye ya jingina da motarsa hannayensa zube cikin aljihun trouser d'insa da alama sister d'insa dake skul d'in ya zo d'auka,tana kallonsa suka had'a ido yayi mata murmushi,da sauri ta shige mota had'e da rufewa,ya bita da kallo a hankali har suka wuce ta gabansa,tana ganin sanda ya juyo ya bi motar da kallo ta mirror,tayi ajiyar zuciya mai nauyi a hankali ta sake lumshe idanunta,har suka shigo arean bata bud'e idonta ba tana ta tunani sai da taji sun tsaya,a hankali ta bud'e lumsassun idanunta ta fita bayan ta sallami mai cab ta wuce tana sauke k'ananun ajiyar zuciya,ta tsaya a bakin entrance bayan tayi knocking ta jingina bayanta a jikin building,Bareerah tazo ta bud'e mata k'ofa ta shige,direct bedroom ta fara nufa tayi tunanin Annie tana ciki,ta tsaya shiru ta yi tunanin ko tana bathroom tunda data shigo bata ji alamun su ba and ta san basa zuwa ko ina,wajen mintuna goma tana jira taga bata fito ba a hankali ta cire kayanta tayi knocking k'ofar,jin shiru ya sake tabbatar mata bata nan,ta tura k'ofar a hankali tana lek'awa kamar mai jin tsoro,ajiyar zuciya ta sake yi sannan ta shige,ruwan wanka ta had'a mai d'umi da ta san za taji dad'in sa,tun tana wanka take jiyo wayarta tana ring bata wani damu ba ta ci gaba saboda ta san kiran ba lallai ya zama wani mai muhimmanci ba,tana gama wankan ta d'auro alwala sannan ta fito,simple gown ta d'auko mai mad'auri ta zauna tayi shafe² tasa kayanta tasa kajol da man leb'e tana gamawa ta d'auki wayarta dai² lokacin da wani kiran ya shigo,a hankali take bin number da kallo kamar kada ta d'auka amma haka ta daure duk da ta so gane number but ciwon da kanta yake mata yasa ta hak'ura ta d'auki kiran tasa wayar a kunnenta,muryar Aatif ta jiyo a wayan yana fad'in "Babu fad'a mene ne ya kawo gaba madam.!?" Ta runtse idonta ta fesar da wani iska so hard,confidently tace "What is the benefit of that call.!?" Yayi murmushi yace "Haba mana ko dai munce mun hak'ura da juna ai ma dunga gaisawa ko.!?" Kai tsaye tace "I don't want" yace "why.!?" Tayi siririn tsaki ta katse wayar,sake kira yayi tayi banza da wayar har yayi ya gaji,taja tsaki tana jin yadda nerves d'in kanta da k'irjinta suke bugawa hurriedly,ta bud'e jakarta medicines d'inta da take tare da su ko wane lokaci ta fito ta zube ta d'auki wannan ta d'auki wancan haka tayi ta b'allesu tana had'iya,tana gamawa ta mik'e slowly ta fita without returning them to where she take,Bareerah soon arrives and seeing the remedies spilling onto the bed ta tattara tayi keeping a cikin drawer,data fito jin shiru a ko ina ta kasa zama,duk inda take tunanin Annie za ta shiga sai da ta duba haka Lolly ma but bata ji alamar suna gidan ba,ta dawo parlor ta zauna jigum like an orphan,alert da wayarta tayi ya bata damar d'aga kanta a hankali taga messenge ne ya shigo,bata iya dubawa ba ta kwanta kad'an tana lumshe idanunta tana motsa bakinta,ranar har dare bata ji su ba sai duk ta rasa me yake mata dad'i,sai can dare after 8pm aka yi knocking door da sauri ta tashi tana addu'ar Allah yasa su ne,tana bud'e door ta ga Annie tsaye bata san lokacin data rungume ta ba tana sakin ajiyar zuciya,Annie tayi murmushi ta shafa kanta,ya kalle su kad'an ya wuce ciki yana mamakin halayyarta,direct bedroom d'insa ya wuce ita kuma suka shigo tare da Annie,a parlor suka zauna tayi mata sannu da dawowa,Annie tace "Sannu daughter ya skul.!?" Tace "Alhamdulillah Annie na dad'e sosai da dawowa ban ganku ba" tayi murmushi tace "Mun je wani unguwa ne and bamu dawo da wuri ba,ina fatan babu matsala ko.!?" Tayi murmushi tace "Babu Annie" Annie ta girgiza kai tace "haka ake so.." Since ta dawo daga skul ta fahimci akwai abunda yake faruwa a gidan saboda yadda mutanen cikinsa suka koma wasu iri,da daren ma dai da yake sun saba had'uwa a parlor taga daga ita sai Annie da Bareerah,haka tayi ta kallon k'ofar d'akin Lolly da nasa but shiru sun k'i fitowa kuma duka ranar ma bata sa Lollyn a idanunta ba tun da suka gaisa da safe kafin ta fita,zuciyarta duk sai tayi mata wani iri ko cikakken awa d'aya Annie bata yi da dawowa ba tayi mata sallama ta koma bedroom, though ba bacci take ji ba amma zaman shirun da basu saba yi ba yau sai taji daban,data shiga bedroom gefen window ta tsaya tana duba balcony taga ko yana can tunda mafi yawan lokaci idan baya son hirar da suke a parlor can yake zuwa,da bata ga alamun sa ba nan d'inma ta koma saman bed ta kwanta ranar gaba d'aya haka gidan ya kasance kamar gidan makoki.

     In the morning bayan tashinta daga bacci before 8am ta gama shiryawa though she had no lectures sai tayi zamanta a bedroom,kamar wasa ta d'auki wayarta,network take k'ok'arin bud'ewa da niyyar shiga yanar gizo-gizo,alamar da ta gani yasa ta tuna jiya an turo mata message,kamar ba za ta duba ba ta bud'e a hankali idanunta suke bin content d'in bata k'arasa karantawa ba idanunta suka fara zubo da hawaye wayar ta sub'uce ta fad'i jikinta sai rawa yake,sai da ta gama kukan sannan ta mik'e a hankali ta d'auki wayar ta fita,direct tana fitowa ganin babu kowa a parlor bata jira ba tayi knocking door d'insa,shiru² tana jiran taji ya yi magana,ta gaji da tsaiwa ga maganar sai ci mata rai yake,tayi kamar za ta koma sai ta tuna abunda yake jikin text d'in ta fasa,daga k'arshe dai taji baza ta iya tsayawa ba ta bud'e ta shiga,since she had entered the room the fragrance of his scent's da turarukan d'aki da aka yi amfani da su suka kaiwa hancinta ziyara suka sa ta lumshe idanunta ta bud'e ta ci gaba da shiga,ta tsaya a tsakiyar d'akin kafin ta dakata ta ci gaba da bin ko ina da kallo,komai a tsaftace yake a zaune bisa muhallinsa,ganin baya nan yasa taji jikinta yayi sanyi,matsawa tayi jikin glass curtain wall ta janye labulayen gurin hasken rana daya fara d'agowa sosai ya sake haskaka d'akin taja numfashi data hango balcony babu alamu mutum,slowly her brain began to count the date's,harshenta ta d'an datse had'e da runtse idanunta tunawa da ba a weekend ake ba,tasa hannunta ta bugo k'eyarta tana fad'in "Shirme kawai,since today's u don't have lectures sai kika yi tunanin everyone is unemployed.!?" Bata jima sosai ba taje ta gyara labulayen data bud'e,ta juyo da niyyar fita idanunta suka hango mata wani had'ad'd'en diary,ta zuba idonta a gurin tana kallo ko babu komai ta ji ya burgeta kuma yayi matukar yi mata kyau,a hankali taje inda yake ta d'auka tana kallonsa da juya shi a hannunta har ta yi niyyar mayarwa ta ajiye taji ba za ta iya tafiya bata ga abunda yake rubuce a ciki ba,fasa ajiyewa tayi ta nemi guri ta zauna daga bakin bed d'insa,carefully ta warware threads d'in da aka d'aure sannan tayi unzipping diary d'in,blank ta tarar da first page ta tab'e baki a hankali sannan ta bud'e next,shi kansa second page d'in babu wani dogon rubutu wasu few words ne kad'ai a jiki,yadda aka yi rubutun da calligraphy ya so cakar da ita,bcos ba kowa yake iya yinsa ba yasa dole idan ba nutsuwa mutum yayi ba sai su bashi wahala,she kept her eyes wide open tayi gesturing face,she wanted to know what was written but she had suffered a lot before she could say the words clearly *"THE SECRET OF MY LIFE"* A beautiful smile released da ta gano abunda aka rubuta ta gyad'a kai tace "Ummhhum.! Lallai ma,dan kada a karanta shi ne aka rubuta da calligraphy.!? To sai na karanta..!" Next page ta sake bud'e and then she slowly re-spelled it out *"NURAAZ BIN HAUWA.!"* ajiyar zuciya tayi sannan taci gaba da bin content d'in dake k'asa tana sake bud'e shafukan gaba tana ci gaba da bi a hankali,duk wani labarin rayuwarsa shi ne a rubuce including the one he didn't tell her,wani abun idan ta gani sai taji ta kasa daurewa sai ta tsaya ta yi kuka idan ta dakata ta bud'e shafin data tsaya,next page bayan ya gama rubuta tarihin rayuwarsa abunda ya rubuta shi ne "Everyone can take risks but achieve goals it's just for a talented.." wani abun mamakin daya sake d'aure mata kai shi ne abunda ta gani rubuce data bud'e page d'in dake gaba "I found her.!" This is what has been written and there is no further information that allow anyone to understand what did that means.....

       #Hhh! Da alamun an zo gurin da asirin sa zai tonu 💃 let's go 🏃 to see the secret he always hidden.....

#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 28.
#Hɪꜱ ᴛʀᴜᴛʜ
Chapter 57 · 0% Book details