← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 152

Sashe 142

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan nan Dr Paredes ya sake dawowa ward d'in zai shiga ya dubata su Annie duk suna zaune har sunyi waya da y'an uwa sun sanar an samu k'aruwa ta b'angaren Nuraz,Hajiya dai ta kasa daurewa tana kallon Dr Paredes dake niyyar shigewa room d'in da tsadadden speech d'inta tace "Dr ko dai mu hak'ura mu koma gida? Ganin mai jegon bazai yuwu ba?" Murmushi ya sakar mata ya shafa kai yace "I'm sorry Aunty yanzun za ku gansu" Hajiya tace "Aah to ai maganar gaskiya ce,ace tun d'azun muna zaune a nan,an ce ta haihu munyi waya da dangi amma shiru har yanzun bamu ganta ba bare abunda ta haifa" shi dai Dr Paredes tuni yayi knocking ya shige ciki ya bar Hajiya tana mita su Kalthom sai dariya suke yi mata,yana shiga ciki da murmushi a saman fuskarsa ya kalli yadda masoyan suke cikin farin ciki,baby'n a hannun Nuraz yana jijjigata,Dr ya gama dubata da ya tabbatar komai lafiya yace daga yanzun zuwa nan da y'an wasu mintuna zai yi discharged nasu,Nuraz yayi masa godiya,suka yi musabaha ya mik'a mata baby'n bcus lokacin da Dr Paredes yayi knocking bata wani sha sosai ba shi yace ta bari sai ya fita,ta karb'eta shi kuma ya biyo bayan Dr Paredes,fuskarsa ya a d'aure cikin takunsa mai tattare da nutsuwa ya fito,da Hajiya suka fara yana fitowa tace "Kai dai Noor kana wani abu da bai dace ba" saurin kallonta yayi yana sake had'e rai as if he doesn't know how to laugh yace "me nayi ni kuma?" Ta zabga masa harara tace "idan ba iya shege ba tunda ka zo ka wuce mu a nan,da kaje kaga jikin nasu ai sai ka fito ka sanar da mu halin da ake ciki,amma ka shiga ka zaune kusan awanni biyu kenan" tab'e baki yayi ya wuce yana fad'in "yanzun ai gashi za ku gansu,na yi zaton wani abu ma za kice na yi daga zuwa na" yana fad'a ya wuce zai koma duk suka bishi da kallo su Annie dai sai dariya suke yiwa Hajiya,tana ganin zai shiga shi kad'ai tayi maza ta rik'osa tace "ai sai ku wuce muje mu gansu ko kuwa dai gadi aka kawo mu yi nan d'in?" Bai tanka maganar da take yi ba ya bari suka fara wucewa then ya biyo bayansu,Hajiya ce kan gaba suna shigowa ta fara magana "fisabilillahi ace tun d'azun yarinyar nan ta haihu amma sai yanzu ake barinmu mu gansu,yo Allah na tuba ni na d'auka ma baza'a bari mu shigo ba ai" Nusrah dai da ta kalleshi sau d'aya taga yana had'e rai tayi murmushi,Annie dake shigowa ta kalli Nusrah tace "sannu baby ansha fama ko?" Shyly Nusrah ta sunkuyar da kai tana yi mata barka da zuwa,Lolly ta shafa gefen fuskarta tace "sannu daughter! Allah ya k'ara lafiya" ta amsa a hankali da ameen,Hajiya aka fara bawa baby tana kallonta tayi murmushi tace "ikon Allah Maryam kalli nan ki fad'a min da waye take kama uwar ko uban?" Annie ta kalli baby tana murmusawa tace "Hajiya gane kamannin yaro a yau kuma?" Hajiya ta b'ata rai tace "Is it unrecognizable?" Annie tayi sauri tace "ana ganewa amma ni kam yanzun ba lallai na gane abunda kike son cewa ba" Hajiya tace "yo kamannin ubanta mana,ni ba don mace bace wannan ai sai nace Noor ne yana jariri,sak fa shi kamar an tsaga kara haka fuskarta yake" Annie tayi murmushi kawai bata sake cewa komai ba,basu d'auki wasu awanni masu nisa ba aka sallame su daga hospital d'in,suka tattaro suka yo mansion kowa sai murna yake ana d'aukan baby,ana dawowa gida Hajiya tace ai sai Nusrah ta wuce su tafi apartment d'inta a can za tayi jegon,Nuraz ya kalleta ya kalli Nusrah dake dariya,fuskarsa a had'e babu kunya yace "ina za ki kai min mata?" Hajiya tace "wanka za'ayi mata na gaskiya,yo muma duk da yake y'an da ne ba don munyi wankan ba ai da baza a ganmu da kyanmu har wannan lokacin ba" bata gama fad'a ba yace "babu inda za taje wani wanka,shi Dr cewa yayi lallai sai anyi wankan?" Hajiya ta bud'e ido tana kallonsa tace "O'ohhh Allah ya kawo mu wani irin zamani na rashin kunya,yanzu Noor wankan da za'ayi mata ne baka so? Gata ne fa za ayi muku?" Ya tab'e baki yace "ni dai na ce bana so,idan kuma lallai sai anyi to bismillah amma ku d'auki baby'n ku barmin mata na" yana fad'an haka ya wuce bai sake cewa komai ba,Hajiya ta bishi da ido ta rasa abun fad'a,Lolly,Bareerah da Annie sai dariya suke saboda yadda Hajiya tayi kamar wata statue ta bi Nuraz d'in da kallo,can ta tab'e baki tace "yo a baka matar taka mana sai me,ni dai Allah ya so uwata ta yi min wanka na gaskiya mai inganci,don ka ce baka so a yiwa matarka waye ya rasa?" Dariya su Kalthom suka sa,Afaf dake kusa da Hajiya kasancewarta d'alibar likitanci tace "Hajiya ba lallai ne sai anyi wankan ba fa,da yawa ma yanzun sun fi son haka,tunda akwai magani sannan mutum zai yi amfani da towel ya gasa jikinsa,ganyen ne dai kawai ba'a amfani da shi,amma ana yin wankan" Hajiya ta tab'e baki tace "ina fa wanka a nan,mu dai munyi wanka yarinya,ku yanzu me kuka iya banda shegen k'arya" suna ta dariya su dai suka wuce cikin apartment d'insu,abun mamakin kuma tunda ya fito yace baya so a kaisu ko wane gida,duka family d'in sai suka goya masa baya suka bar masa matarsa a nan d'in because a yanzun sun riga sun tarbiyyantar da zuciyarsa abunda yake so shi suka rik'e a matsayin maudu'i,dai² da second d'aya basa so yace ga abunda yake so a canja da wani,sun san irin illar da suka yiwa rayuwarsa a bayan even though suna da tabbacin ba zai yi wani abu na ba dai² ba yanzun,but suna yi masa haka ne ba domin su sangartar da rayuwarsa ba,sai don su ba shi dukkan kulawa/gata that they could not gave him at that time.

*2 days later...*
Chapter 142 · 0% Book details