← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 152

Sashe 22

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Yace "babu komai y'ata,,yanzun ina muka nufa.!?"
      Jim tayi cike da rashin sanin abunda zata ce can ta d'auki envelope d'in da takardun da Rafeek ya bata suke ciki ta zaro takardun,a hankali take ta bin content d'in,kafin ta d'ago tana sauke ajiyar zuciya tace masa "Sardauna crescent",har bakin get d'in gidan ya sauke ta,yanayin unguwar shiru ta sauka bakin get d'in tana kallon gidan da tunanin inda zata samu wanda zai taimaka mata ta shiga da kayansu,a hankali ta juya ta kalli dattijon da yake sauke musu kayan jikinta duk yayi sanyi tace "dan Allah baba ko zaka taimaka min mu shigar da su.!?"
      Yayi murmushi yace "toh y'ata bari na gwada" suna ta d'iban kayan tare har suka shiga da su bakin entrance d'in parlor,suna gamawa bata tsaya tambayarsa kud'in da zata bashi ba ta bud'e envelope d'in ta ciro 5k ta bashi,ya kalli kud'in ya kalleta yace "y'ata ai kud'in sunyi yawa,tafiyar duka baifi ki bada seven hundred ba"

    Tayi d'an murmushin yak'e tace "ni na baka Baba,kada ka damu"

     Yayi mata godiya saboda fitowarsa kenan daga gida ya d'auko ta,itama tayi masa godiyar taimakon da yayi mata sannan ya tafi,ta shiga gidan ta duba taga komai akwai a gidan,well furnished home items masu tsada da kyau,ta yiwa Allah godiya sannan ta shiga parlor tsakiyar kujerun ta tsaya tana kallon kayan,duk da alamunsu ya nuna basu jima ba sosai ta d'an sake karkad'e k'uran dake kai ta kwantar da baby'nta sannan ta koma ta dunga shigo da kayan dake waje,gida ne madaidaici mai matuk'ar kyau da yaji interlocking sai varenda da entrance d'in ainihin gidan yake shi kuma an malale sh da tile's masu haske har ciki,da yake ba damuwarta kenan ba bata b'atawa kanta lokaci gurin gano kyaun gidan ba,bayan ta gama ta wuce bedrooms d'in ta duba kafin ta fara aikin tsaftacewa,har akayi azhar bata gama ayyukan ba,ta dai tsaya ta yi sallah sannan taci gaba,kafin sallar asr gidan yayi fes sai k'amshi yake saboda turaren data sa a electric bonner,ta koma tayi sallah sannan tayi wanka,tazo ta duba taga ko ya tashi taga har lokacin bai tashi ba,ta zauna ta zubawa d'anta d'aya tilo da ya zama ahalinta a kaf duniyar ido cike da so da tausayin halin da k'addara ta jefo su,a hankali hawaye suka sauko mata,bata yi k'ok'arin gogewa ba haka tayi ta kuka tana tunani har tsayin lokacin da taji zuciyarta da kanta sunyi mata wani irin nauyi,idanunta duk sun sake haurawa sun canja launi,saboda yawan kukan da take yi a duk rana yasa ko ita ta manta rabon da idanunta suyi haske,wajen maghreb ta fara jin yunwa a hankali ta sauka daga saman kujeran da take kwance ta nufi kitchen,store ta bud'e tun zuwanta data shiga ta gyara kitchen d'in taga akwai komai a ciki,ta daure da dafa couscous fari ta d'an sa masa mai saboda kada ya had'e,madara ta fasa na ruwa a bowl data d'auko,ta d'iba yadda take jin zata iya ci ta d'an sa masa gishiri kad'an sannan ta sa sugar dai² yadda take so ta fito daga kitchen d'in ta rufe k'ofar,ta dawo parlor dai² lokacin ta iske little Nuraz zaune yana murza ido yaro d'an watanni sha hud'u,har ta k'araso inda yake k'ok'arin zamewa daga saman armchair tana kallonsa,saman couch ta d'ora bowl d'in couscous d'inta kafin ta juyo inda yake ya fara tab'e fuska zai yi kuka,ta fara k'ok'arin d'aukansa da damuwa a fuskarta,dariya yayi mata ganin ta d'auke shi,a hankali ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya kamar wanda yayi kuka da yawa,dashi ta koma kitcken ta d'auko abu ta rufe bowl d'in,sannan ta kaishi bedroom ta d'ora saman bed,ta shiga bathroom ta had'o ruwa mai d'umi cikin baby tube,kayan jikinsa ta fara cirewa,sannan ta cire masa Pampers ta sashi cikin ruwan,dariya ya kyalkyale da ita saboda yana son yaji an barshi cikin ruwa kamar haka yayi ta wasa da shi yana dariya abun na yi masa dad'i,jinsa cikin ruwan ya fara wasa da ruwan yana watsi da shi,bata ce masa komai ta d'auko baby bath basket da kayan mayukansa suke ciki,ta fito da sponge d'insa da baby shampoo,still sai wasa yake da ruwan yana ta dariya yana magana amma bata ganewa,ta yi masa wanka ta nad'e shi a towel sannan ta shirya shi cikin kayansa masu sauk'in nauyi ta d'auko shi suka dawo parlor,ta zauna a kasa saman rug ta d'orashi kan cinyarta,hannunsa ya fara turawa cikin rigarta tana kallonsa ta cire hannun tana had'e rai saboda duk tana jin babu dad'i,ya sake mayarwa ta cire,yana shirin sake mayarwa ta rik'e hannunsa tana masa kallon k'asan ido,kuka ya fara mata yana kai mata duka da d'ayan hannun cikin gwaranci saboda ba sosai ake gane me yake cewa ba yana mata magana,tausayinsa ya kamata tayi saurin fito masa da nonon ta bashi,ya kama yana sha yana ajiyar zuciya duk da ba wani sosai yayi kukan ba,a hankali ta zuba masa ido tana kallonsa hawaye suka gangaro mata,tayi saurin d'auke kanta gefe,a hankali tayi kukanta mara sauti yana gama sha ta mayar ta d'auko bowl d'in data rufe ta fara sha tana bashi,bata wani sha da yawa ba taji ya fita a kanta taci gaba da bashi,shima bai sha sosai ba ya kautar da kansa gefe,data sake bashi ya girgiza mata kai alamun ya k'oshi,ya mika mata hannu yana k'ok'arin karb'ar spoon d'in a hannunta,sake masa tayi a hankali taga ya karkata spoon d'in ya deb'o ba mai yawa ba yana k'ok'arin kai mata bakinta,k'ura masa ido tayi tana kallo,shi kuma sai magana yake mata yana so ta bud'e bakinta ya bata,bata san lokacin data fashe da kuka mai k'arfi,ta rungume shi tana jin babu dad'i,,ta dakata da kukan ta barshi a nan parlor taje kitchen ta wanke kayan ta dawo ta d'auke shi ta wuce d'aki bayan ta kashe electronics,tunda ta shiga d'akin dashi ta sauya masa kaya itama ta canja zuwa nighty ta zauna shiru tana tunani,bai yi bacci ba har wajen eleven,da yayi bacci ma nan ya barta ita kam bata samu ta runtsa ba saboda tsoron dare da kad'aici daya cika mata zuciya,har wajen asubah bata iya yin bacci ba sai da gari ya waye,lokacin bacci ya fara fizgarta Nuraz ya tashi,nan ya dasa rigima,yana ta laluben abincinsa,da kyar ta daure tayi feeding d'insa ta shirya shi ta d'an kwanta lamo tana ta kallonsa,tana son yin bacci saboda a lokacin har kanta ya fara ciwo amma babu dama,a tak'aice dai haka rainonka ya kasance ga mahaifiyarka da dare baka bacci da wuri,tsoro da tunane² dake d'awainiya da ita kuma suka sa ko ta kwanta bata iya bacci,da safe hidimar ka and baka bari ta kwanta bare ta samu baccin ko yaya ne,kullum ya kasance mata da matsanancin ciwon kai take rayuwa,tun yana mata kad'an² yana damunta har ta saba ya daina damunta,ta rasa yadda zata yi ga tunanin gida da yak'i barinta ta huta,but tsoron abunda zata tarar yasa ta kasa samun sukunin zuwa,ranar da ta cika sati da komawa gidan,ta gaji ta yanke shawaran zuwa ta sake zuwa ta rok'i Baba gafara duk da ta san bata aikata abunda ake zaginta da shi ba,idan ya yarda shi kenan sai tayi masa bayanin komai da yadda ya faru idan kuma yak'i saurarenta zata ci gaba da hak'uri har zuwa lokacin da Allah zai sa ya sakko ya yarda ta koma gidan,,ta gama shiryawa ta fito ta kulle gidan ta samu napep da zui kaita k'ofar Na'isa,misalin 12pm ta sauka ta sallami mai napep,ta kama hanyar da zata sada ta da gidan mahaifinta,tunda ta tsinci kanta a k'ofar gidan mahaifinta take jin k'irjinta yana sake tsananta bugawa.....

   *#😢😢  Yah Allah ga baiwarka nan,kasa ko mene ne zai faru ya zo mata da sauk'i...*

#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

   *I just finished typing the page,,but don't know how wollahi na yi deleting,be patient with how the page comes to u my people.😢*

Pᴀɢᴇ 11.
#Uɴᴇᴀꜱʏ

      Gefe guda ta samu ta tsaya da tunanin yadda za tayi ta samu damar yin magana da ni,ta jima sosai tsaye tana kalle² da tunanin wanda zata aika ya kira ni,tana nan tsaye ta rasa mafita k'arshe taga tana b'ata lokaci,ta yanke shawaran zuwa da kanta,,ta nufo k'ofar gida tana tunanin idan ta samy Baba a gida kuma fa.!? suka kusa bugar juna,yana k'ok'arin fita zuwa wajen taron su na siyasa,tayi saurin komawa baya muryarta na rawa tace "Kayi hak'uri Baba,ban san kana hanya ba"

    Ya kalleta ya d'aure fuska cikin hayaniya yace "Wa kika zo nema a nan.!?"

    Tayi shiru tana sunkuyar da kanta k'asa,a bakin hanya ya kafe ya kama waist ya k'i matsawa,ta d'ago a hankali tana gaida shi,bai amsa ba sai tambayar daya sake jefo mata "waye tazo nema a gidansa.!?"
    Ta daure tana jin fad'uwar gaba sosai tace "Baba na zo naga Yaya Maryam ne"

      Ya kalleta kamar zai yi magana ya fasa,cikin gidan ya wuce ya barta a tsaye,zuciyarta a lokacin har ta fara saka mata Baba ya tafi ya kira mata ni,kamar yadda tayi zato haka ce ta faru sai dai sab'anin da aka samu,ko da Baba ya sako ni a gaba muna fitowa ya kalleta yace "Ita ce wannan.!?"

    Hauwa ta gyad'a kai tana kallonsa idanunta cike da hawaue,Baba ya juyo ya kalkeni yace "Maryam kin san wannan.!?"

     Jikina yana b'ari na amsa na santa,yace "Wace ce ita kuma mene ne alak'ar ku.!?"

    Nayi shiru ina tunanin tambayar da amsar daya dace na ba shi,ya daka min tsawa,cikin hargari yace "Ba da ke nake magana ba dan uwarki"

       Ban iya kallonsa ba nace "Na santa" yace "A ina.!?"

     Nace "A nan gidan"

      Ya girgiza kai "ita wace ce d'inki.!?" Na d'ago kaina na kalli Hauwa a sanyaye nace "Y'ar uwata ce."

        Wani irin girgiza kai naga babanmu yana yi,kafin ya juyo kaina yace "Maryam.!" Na amsa "Na'am" yace daga yau "ita ba y'ar uwarki bace"

         Na d'ago zanyi magana baba yace "Kul! Kika ce min wani abu,yanzun nan zan sallamaku duka" nayi shiru ban ce komai ba,ya kalle ni yace "kin ji me nace!?"
Chapter 22 · 0% Book details