← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 152

Sashe 51

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

#Kuji iya shege.! 😨😨😨

#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*      

                   *'DAN MACE..*
              (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*    
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 25.
#A ʀᴇᴍɪɴᴅᴇʀ

      Fitarsu Nuraz a gidan babu jimawa,Maimunatu ta sauke dogon ajiyar zuciya,duk yadda Annie tayi da ita akan ta zauna amma fir tak'i tace za ta dawo tunda Allah ya sa ta ga gurin da suke zaune,Annie tace "shi kenan babu damuwa",tayi mata sallama Annie ta rakata har bakin entrance,Lolly ma dai were not able to speak anymore cos tuni ta bar musu wajen tunda ta farko daga suman da tayi,suna tsaye Maimunatu tayi shiru kamar mai tunani Annie tace "Dan Allah Maimunatu kiyi hak'uri da abunda yaron nan yayi miki,in sha Allah i will talk to him,ban san a ina ya koyo wannan halin ba" Maimunatu tayi murmushi tace "Laa! Adda Maryam wollahi ba sai kin yi masa fad'a ba,ni duk abunda family ku za suyi ba zan tab'a jin haushi ba,it's my brother's fault so that must affect us,but in sha Allah when i get back we will talk" Annie tayi mata godiya,itama haka sannan ta juya ta tafi,har ta shiga mota suna d'agawa juna hannu,suna fita daga arean Annie ta fito harabar apartment d'in ta duba bata ga motarsa ba,ta wuce ciki tana fad'in "Is this boy really going to leave home.!? Ita kuma Nusrah ina taje ne? Kada ace binsa tayi.!" Har ta koma ciki bata fasa yiwa kanta tambayoyi ba,but babu wanda zai amsa mata.
      Har suka shiga mansion Maimunatu tunani take akan abunda ya faru sai da Clark ya gyara parking ya fito ya bud'e mata k'ofar sannan ta dawo hayyacinta ta san sun dawo gida,ta fito ta wuce cikin apartment d'in d'an uwantan bcos ta san can zata tarar da Hajiya tunda ba cikakkiyar lafiya ne da Rafeek ba,tana shigowa yaranta suka fara rigegeniyar welcoming nata ta amsa ta wuce su,a bedroom d'insa ta tarar da su yana kwance saman bed rabin jikinsa a rufe,tayi musu sallama ta shiga,Hajiya ta kalleta da mamaki "Har kin dawo.!?" Tace "Umm!" Tana zama saman armchair dake cikin bedroom d'in,but Rafeek were unable to speak because he's in pain,Hajiya tayi ajiyar zuciya tace "Ko dai baki same su ba.!?" Ta girgiza kai tace "A'a Hajiya na same su" Hajiya ta zuba mata ido tana kallonta cikin son k'arin bayani,tayi ajiyar zuciya tace "bcos of what he did a bayan we had to face the punishment" ya bud'e idanunsa da kyar masu cike da bacci ya kalleta,Hajiya tayi ajiyar zuciya tace "u didn't get a chance to talk to them!?" Tayi shiru tana tunani kafin tace "A'a munyi magana da Adda Maryam but not for that matter" Hajiya ta tari numfashinta "Kin ga Hauwa'u.!?" Ta girgiza kai tace "Na ganta babu wanda ban gani ba tsakanin Hauwa da Nuraz,sai dai ban samu damar yin magana da su ba" yadda komai ya faru ta sanar wa Hajiya,Rafeek was silent and listening Hajiya tayi ajiyar zuciya "In sha Allah zuwa na gaba tare za mu tafi since and u find out that she is not married,but what binds me is yaya aka yi suke tare da maryam.!?"
    Maimunatu tace "Who knows.? Allah dai yasa ba abunda ya yiwa Hauwa ne ya shafeta ba" Hajiya ta zuba mata ido tana nazari,tayi ajiyar zuciya tace "It would be difficult to say so" Maimunatu tace "Hajiya zai iya kasancewa saboda idan baki manta ba,when i met u in U.S na fad'a muku abunda mahaifinsu ya yiwa ita Hauwa" Hajiya ta jinjina kai tace "Haka ne amma dai Allah yasa it was not" Maimunatu tace "Ameen Hajiya nima addu'ar da nake yi kenan" duka suka yi shiru kowannensu da tunani dake ransa,Rafeek yayi d'if yana juya maganganunsu a zuciyarsa har ya samu wani irin baccin wahala ya d'auke shi.

***
    "I'm sorry please.! Ba don ni ba,kada kaga kamar dama na saba aikatawa ne,sharrin zuciya yasa na fad'a maka hakan amma ba haka nake ba" yayi shiru bai kulata ba idanunsa a lumshe har lokacin,she bowed her head and wiped tears da siririyar muryarta ta sake cewa "If u remember what happened that day in our home Mommy ta fara fad'a and banyi tunanin ranka zai b'aci ba shi yasa na maimaita yanzun,though i knew i have no value a gurin wasu mutanen i guess i was like that a gurin kowa,da ace ka nemi wasu matan without even realizing their situation,suna da cikakkiyar lafiya ko babu,they have a serious illness or not,shi yasa na fad'a maka haka,a tunani na da na rok'i alfarma kace sai ka yi da gasken za ka aikata.." Ta sake fashewa da sabon kuka,bayan ta yi mai isarta bai kulata ba ta sake dakatawa tace "Kuma ko da muka je can d'in nima ba da gaske nake yi zan sha ba,duk na yi haka ne dan na gani za ka sha ne da gaske ko a'a,lokacin da na fahimci ba sha za kayi ba na takura sai na sha kayi k'ok'arin k'wacewa,shi ne nace ka sha har ka buge ni,ni ko gurin ma ban tab'a sani ba,ban tab'a zuwa ba sai yau.." A hankali ya bud'e idonsa da suka yi wani iri saboda b'acin rai ya saki bayananniyar ajiyar zuciya,a hankali ta furta "Kayi hak'uri in sha Allah i'll never do it again",bai yi magana ba ya bud'e motar ya fita ta goge hawayenta ta bud'e ta fito itama,a cikin harabar apartment d'in ta tarar da shi a tsaye she didn't think saboda ita ya tsaya,zata wuce shi yace "come here.!" Ta dakata a hankali tana kallon k'asa yana tsare gida yace "Even if Annie ask u don't tell her anything,idan ta yi magana zan fad'a mata da kaina" ta girgiza kai a hankali yace "Maganar Mommy take ko waye nema.!?" Ta gyad'a masa kai yace "From this day on i don't want u to remember it again,maganar baki da daraja babu wanda zai aureki shima haka,kin san gaibu ne da za ki munanawa Allah zato.!?" Ta girgiza kai a hankali yace "don't say it again kin ji.!?" Tace "Toh! In sha Allah i won't" yayi shiru yana kallonta a hankali kamar mara lafiya yace "And tgen marin da nayi miki,,shima kiyi hak'uri kin ji..!? Raina ya b'aci ganin ina miki magana kina neman mayar da ni abun wasa.." Ta girgiza kai a hankali tace "It was my fault,da na ji abunda kace tun farko da hakan bai faru ba" yayi shiru yana kallonta,haka nan yaji wani irin tausayinta yana sake bijiro masa,a hankali yace "Ok! Shiga gida to ina zuwa" har ta fara tafiya ta tsaya,ya kalleta bai yi magana ba,ta dawo a hankali har inda yake tsaye tace "Where are u going then.?" Yayi ajiyar zuciya yace "I have no where to go zan rufe mota ne" ta jinjina kai ta wuce a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki,tana zuwa bakin entrance ta tsaya,har yaje ya rufe motar ya dawo bata shiga ciki ba,ya kalleta da mamaki kafin yayi magana ta danna doorbell,Bareerah ta bud'e musu k'ofa tana binsu da kallo,suka wuce ciki Nusrah tana sunkuyar da kai k'asa,Nuraz kam kai tsaye ya wuce zai shige bedroom Annie ta kira shi,ya tsaya a inda yake,tace "Daga ina kuke.!?" Yace "munje wani guri ne" yana fad'a ya wuce dan wani haushin abunda ya faru d'azun daya sake turnuk'e masa rai,ta kalli Nusrah dake tsaye tana kame² tace "Sai ki wuce ai ki bani guri" sum² ta bar wajen,babu wanda ya sake ce musu komai,,da safe lokacin suna zaune a dining dukansu Annie ta kalli yadda suke harhad'e rai ta kalli Lolly taga itama tun bayan gaisuwa bata sake magana ba,duka a cikinsu gara Nusrah itace kad'ai ta riga ta san damuwarta bai shafi abunda ya faru a daren ba,but itama kana kallonta zaka san tana da damuwa,shi kuwa gogan his face alone was enough to express his feelings,tayi shiru bata cewa kowa daga cikinsu komai ba har suka gama,suna niyyar tashi tace "ku dakata i want to talk to all of u.!"
Chapter 51 · 0% Book details