Sashe 139
Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Satin da su Annie za su bar UK Nusrah ta tada rikici ganin da gaske babu su za'ayi tafiyar,ta same shi lokacin yana aiki cikin study room,har da kuka wai ita dai tana son zuwa,yace a'a tayi hakiri baza su jeba yanzun sai ta haihu,because idan tayi dogon tafiya da k'aramin ciki komai zai iya faruwa and shi ba ya son wani abu ya faru da su,ta dage lallai ita dai ta fi son zuwa tare da su Annie,yaga sai lallab'ata yake yi tana cewa ba haka ba yace shi dai ta yi hakuri ta bari ta haihu because bai sani ba ko iya rabonsu kenan,yana jin tsoron kada shima suyi asararsa,duk kukan da take masa ya dage yana lallab'ata tayi hak'uri tak'i ji,he was not ready to face her yana d'aure fuska yace "fice ki ba ni wajen ina aiki kina damuna,didn't i tell u ba na son kuka a inda nake?" Tana kallonsa idanunta duk hawaye tace "kora ta kayi fa?" Ya sake had'e rai yace "yeah! Fita nace kafin na b'ata miki rai" ta goge hawaye bata sake magana ba ganin da gaske yake korarta,tana fitowa ta wuce bedroom nan ta fara fushi tana fad'ar maganar duk da ya yiwa ranta,wai ya koreta ne saboda yaga ya samu abunda yake muradi yanzun ita ya daina sonta,shi kam tana tafiya yayi dariya tunawa da wancan lokacin da yace taje ta nuna ba ta so har fad'a suka yi,yanzun kuma wai ita da kanta take son zuwa,after he had completed his research ya fito yaga sai b'ata rai take yi,a lokacin shi ya manta ma sunyi haka da ita,yana zuwa inda take sai ta matsa,yayi murmushi ya rik'eta sosai a jikinsa yace "me aka yi miki ne kike fushi?" Haushin tambayar da yayi ya cikata,nufinsa zai ce ya manta abunda yayi mata ne? Da ya dameta da fitinarsa tun bata kulashi ba har ta sauka da kyar tana cunkushe fuska tace "ba kai bane dan ka samu abunda kake so za ka fara wulakanta ni" ya zare ido yana kallonta da tsananin mamakinta yace "waye yace miki abunda nake so kenan a gurinki?" Bata yarda ta d'aga idanunta ta kalleshi ba tace "ko ba'a fad'a ba ai ni ba yarinya ce k'arama da zan kasa ganewa" mamakinta sosai ya cikasa yana ci gaba da kallonta idanunsa sun d'an birkice saboda maganar ta sosa masa zuciya but yayi k'ok'arin danne b'acin ransa yace "ba don idan muka yi aborting nasa Allah zai kama mu da laifi ba,surely a yau da sai an fitar da shi saboda na tabbatar miki ba abunda nake buk'ata daga gare ki ba kenan" saurin kallonsa tayi da mamaki because she had never expected to hear it from him,ya kad'a mata kai cike da tabbatarwa,a hankali take kallonsa hawaye suna taruwa cikin idanunta tace "Why would u say that?" Strictly yace "u said because i get what i want from u na fara mistreat naki,what have i done to u kike fad'a min haka? Me nayi miki Roohii?" Tayi shiru bata iya cewa komai ba,ya girgiza kai ya tashi a hankali cikin takaici yana fad'in "I never thought ko fad'a muke yi muna yankan jikin juna this kind of words will come out of ur mouth,sam ban tab'a kawowa a raina irin wannan tunanin zai iya zuwa kwakwalwarki ba,but i'm probably misunderstood,yayin da soyayyarki ya rufe min ido,i see nothing but u,i don't understand anything anymore,ba na jin ko wane yare sai naki,since i first found myself in deepest love,a kullum na kasance maudu'in da na fi iyawa shi ne soyayyarki,at that time when u didn't know anyone nor anything,anytime tunani da damuwata shi ne wane hanya zan bi na cire ki daga tsananin ciwon da kika samu kanki ciki,tun ranar da na tsince ki Allah (S.W.T) has tested my life with ur love,dai² da second d'aya my love for u has never changed from what it was,but i kept it hidden zuwa wani lokacin,kin san adadin damuwar da nayi going through lokacin da kika bayyana min soyayyarki da wani na?" Girgiza kai yayi idanunsa sun yi wani irin jaa yace "Ba zan tab'a misalta miki adadin k'uncin da na shiga dalilin kin zab'i soyayyar wani na ba,ba zan manta da fifita soyayyar wani na akan nawa da kika yi ba,but duk da hakan ban tab'a kallon ki da wannan laifin ba,na zargi kaina da k'in bayyana soyayyata,but lokacin da na rasa mafita ubangiji shi yayi min jagoranci,because da farkon i just decided to leave u not because idan na same ki ba zan amsa ba but u to live a happy life together with wanda zuciyarki yake muradi,wannan abu d'ayan da na rik'e yayi guiding d'ina,bayan na kai kukana ga Ubangiji,i just found my mind tana shaidan min na aikata duk wani aikin alkhairi da zai k'aramin kusanci da ubangijina,here na je umrah har ban san adadi ba,i fasted without knowing how many days have i spent,na yi sadak'a because i have sacrificed abu mafi daraja da sai bayan nayi hakan na gane nayi kuskure,continuing to beg him ya ba ni hakur'i da juriya and to pray to God that idan har al'amari na dake alkhairi ne ya tabbatar da kasancewarsa ba tare da na sha wani wahalar ba" numfashi ya ja yana kallonta kafin da wani irin muryar tausayi yace "do u think this love will one day come to an end? Mutumin da yayi shekaru yana d'awainiya da soyayyar ki kike tunanin akwai wani abu da zai gifta ciki? Is it just justice to the heart that doesn't love anyone sai ke? In my own world nake fad'a miki if there's wani abunda nake so after soyayyar Allah da manzonsa da ya zama wajibi and then my parents,surely soyayyar ki ne,soyayyar da nake yi miki tunda nake a rayuwa na ban tab'a son wani abu makamancin haka ba,is it wrong if i want something from u? Annabi (S.A.W) yace kuyi aure ku hayayyafa,saboda ranar alk'iyama nayi alfahari da ku,is it wrong if i want children from u? Or would u like me to marry someone and hoping to get some from that side? Wannan shi ne tukuicin soyayyata daga gareki? Ko jini nane ba kya so?" Shiru tayi kamar wacce ruwa ya cinye,banda hawaye babu abunda take yi but ta kasa tayi magana,he slowly breathed out yana ci gaba da kallonta with his cloured eyes yace "Sure sai wanda ake so ne ake fatan a haihu da shi,but idan duka wad'annan su ne damuwar tabbas zan bawa zuciya na hak'uri,ban yi tunanin cewa soyayyata zai zamo laifi ba,ban yi tunanin cewa na yi kuskuren kai kaina inda bai dace da ni ba sai a wannan..." Bai k'arasa fad'ar abunda yake bakinsa ba tayi sauri ta fad'a jikinsa with a loud burst of tears,muryarta da jikinta banda rawa babu abunda suke yi take fad'in "I'm so sorry Hayat,Please forgive me for hurting u,sam ban san maganar zai kai da haka ba da tun farkon ban fara ba,ka yafe min na tuba,ni bance ba na sonka ba,at all ma ni maganar Aatif tun farkon ban san mene ne ya rud'e tunani na ba,but na sani cewa sam bai dace da ni ba,idan nace ba na sonka sure na san ban yiwa kaina da zuciyana adalci ba bcos i really love u,wannan maganar ba wai ina fad'arsa ne just because i missed that opportunity ba,daga k'ark'ashin zuciya na yake fitowa,duk abunda kake so ina jin sonsa Hayat,me yasa zan k'i wani abu daga gareka? Ka yi kuskuren fahimta ta ne,idan kace na haifa maka yara why wouldn't i? Even kace sabon gari market kake so na haifa maka idan har Allah ya bani iko zan yi without being tired,when i was like an orphan wacce kowa yake kyamatar zama da ita,kai ne mutum na farko that were good to be with me,ka kawo ni cikin family'n ka,ka ba ni parents ka bani wajen zama,ka kula da lafiyata,ka zame min garkuwa,ka zame min d'an uwa makusanci,at last kuma ka amince muyi rayuwa tare,do u think i have the right to live in this world after u?" her cries that became more intense yasa muryarta sark'ewa,a hankali ya fara bubbuga bayanta yana fad'in "it's ok,kukan ya isa haka nan,u're not good enough for ur situation,i understand u,i love u" kai ta kad'a masa a hankali,yayi cupping fuskarta yana kallon cikin idanunta ya fara goge mata hawayen but sunk'i daina zubowa,ya dakata ganin ta k'i dainawa yana had'e rai yace "za ki bari ko a'a?" A hankali cikin muryar kuka tace "na bari" wasu hawayen suka sake zubowa,ya rufe ido cike da damuwa yace "didn't i tell u i don't want crying? Do u really want to see me in angered?" Da sauri tace "ka fad'a" idanunsa suna rufe har lokacin yace "ok then?" Tayi shiru ta kasa cewa komai sai share hawaye take yi,jin shiru ya fara yin yawa a hankali ya bud'e ido yana kallonta sai kuma ya bud'e mata hannu,da sauri ta shige jikinsa tana yin ajiyar zuciya,haka suka ci gaba da tona asirin zuciyoyinsu until he made sure that he dealt with the issues,tayi murmushi tana kallonsa despite his eyes didn't go back to normal but she just realized ya sauke fushin. Ranar Friday flight d'in su Annie ya baro UK,da su Nusrah suka yi accompany d'insu to airport lokacin suna sallama idanun Nusrah shab'e² with tears for being left alone ta rik'e hannun Annie,because har Hajiya ma da ita za'a je Nigeria za taje Yola ziyara,shi dai kallonta kad'ai yake yana b'oye dariyar da ke son kamashi ya san idan yayi rikici za ta saka masa kuma,bayan tafiyarsu Annie suka koma gida. Tun da su Lolly suka taho Nigeria gidan ya zama wani quite daga su sai securities da maidservant,but for them it also allows them to create a new chapter of love,idan ma ba su suka so ba sai su yi kwana biyu basu fito even entrance nasu ba,idan weekend ya zagayo kuma haka zai shiryata su fita yayi ta zagayawa da ita wajen shak'atawa,ire²n kulawar da yake gwada mata a yanzun su suka yiwa zuciyarta wani irin damk'an da ita kanta ta sake yarda ta sakankance lallai soyayyarta a ransa daban take.