← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 152

Sashe 66

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Misalin k'arfe 9:00pm yana zaune a bakin pool yayi shiru yana tunanin abunda zai yi,maganganun Aatif suka dawo masa saurin tashi yayi ya bar gurin,parlor ya dawo da niyyar yin magana da ita ya tarar Annie bata nan,ya juya fuskarsa a had'e ya kalli inda Nusrah take yace "Annie fa.!?" Tayi shiru tana kallonsa da tunanin me yake damunsa ta ga idanunsa sun canja yayi making snap a dai² fuskarta yace "Magana nake kinyi shiru" lower lip d'inta ta tsotsa tace "Tana bedroom" juyawa yayi da sauri ta bishi da kallo,sai da yayi knocking kafin ya shiga,a zaune ya ganta da alamun tana neman wani abu ne mai muhimmanci,Annie ta kalleshi tace "Habibiiy.!" Ya k'araso ciki yana kallonta yace "Annie ina son muyi magana" tace "Toh.! Ina saurarenka" Ya nemi guri ya zauna,Annie ta dawo da hankalinta kansa tace "What happened.!?" Ajiyar zuciya yayi yace "Annie kin tuna wannan guy d'in.!?" Tayi saurin katse shi tace "Wane saurayi.!?" Yayi squeezing face yace "what's his name.!? Yawwa Aatif ko.?" Tayi ajiyar zuciya tace "Wani abu ya faru.!?" Ya gyad'a kai a nutse ya bata labarin komai,ranta taji ya d'an b'aci tace "A can gidan kuka had'u.!?" Yace "Ehh!" Ta jinjina kai tace "Bari zan tambayi Maimunatu mene ne alak'arsu da shi",a take ta kira Maimunatu bayan ta d'auka suka gaisa Annie tace "Yawwa Maimunatu dama wani abu nake son tambayar ki idan babu damuwa",Maimunatu tace "Toh Adda Maryam Allah yasa na sani" Annie tace "Habibiiy said that they saw Aatif in ur house,and if there is no worry can i know ur relationship with him!?" Maimunatu tayi ajiyar zuciya tace "Laa! Babu komai Adda maryam i thought ko something had happen ne" Annie tace "A'ah nothing had happened,i just asked bcos we knew Aatif long ago" Maimunatu bata yi tunanin komai ba tace "Aatif ai d'an gida ne shi d'in d'a ne ga abokin Rafeek,they worked together in washington,to da suka tashi dawowa nan ma sai suka taho tare" Annie tayi ajiyar zuciya tace "Okay.! Na fahimta,na gode sosai" suka yi sallama da Maimunatu,tana ajiye wayar tayi masa bayanin komai as Maimunatu informs her,he bowed his head in anticipation of the punishment he is going to make,duka sunyi shiru kowa da tunanin da yake yi,zuwa can ya d'ago kai yana kallonta yana tunanin ko zata yarda da abunda zai fad'a,ya daure dai yace "Annie i thinks this is the right time for us to go to Nigeria" ta kalleshi tana jiran k'arin bayani ya lumshe idanunsa a hankali yace "Ina nufin ya kamata muje mu nemi y'an uwanmu" Annie ta zuba masa ido tace "i don't think so habibiiy" yace "Annie ya kamata muyi hakan,bcos zuwa yanzun ina da tabbacin everything has changed,it has been taken for a long time ya kamata ku koma gida kuma,to that point i think everyone should understand the consequences of what he has done and i feel that hak'k'i na ne a yanzun na had'a ku da y'an uwanku,itama Nusrah ina ganin lokaci yayi da za mu sake neman mahiafinta muji daga garesa,if har yanzun baya sonta,shi kenan sai na nemi izinin neman aurenta daga gurinsa,saboda hak'k'in sa ne a nemi aurenta a gurinsa,i'm tired da jin irin wad'annan maganganun,gaba bamu san me wani zai sake fad'a ba,raina yana b'aci gaskiya,,but even if they do not understand,shi kenan sai mu sake basu lokaci har zuwa sanda za su gane..."

*#Wata sabuwa...* 😂

#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

*Alhamdulillahillaziiy bi ni'imatihi tatimmus'salihaat..! Thank u so very much dearies for the prayers,na tabbata godiyata gare ku ba zai fad'u a baki ba,and i made sure that wannan d'an tak'aitaccen shafin nawa yayi kad'an na bayyana muku irin farin cikin da addu'o'in ku suke sani,,my parents and I have nothing to pay u for the prayers,but duk da hakan bahot² shukhuriya.*

Pᴀɢᴇ 31.
#Rᴇᴍᴏʀꜱᴇ

Since Nuraz walked out from his bedroom Rafeek could not lift his eyes daga kansa,and without even having the courage to speak har suka yi sallama da Hajiya suka bar gidan,after he made sure they left the house silently some tears of remorse da ke mak'ale a idanuwansa continued to pour over,ya jima yana kuka in such a moment har sai da yaji k'irjinsa ya fara masa wani irin ciwo,da kyar ya tsayar da hawayensa yana ta k'ok'arin d'ago hannunsa na dama sakamakon jikinsa da yake jin yayi nauyi ya dafe saitin zuciyarsa da yake jin tana masa wani irin azababben rad'ad'i,tunanin abubuwan da suka faru a baya ya dawo masa sabo kamar yanzun suke occurring,a sanyaye wasu sababbin hawaye suka sake gangarowa,kwatanta irin halin daya shiga in such a moment kusan za mu iya cewa abune mai wahalar gaske da har yayi sanadin da numfashinsa ya fara d'aukewa saboda damuwa da kukan da yayi,like an asthma patient haka ya shiga kokawa da numfashinsa yana fizgar iska da kyar,gumi kota ina sai keto masa yake yi,da kyar ya ja jiki ya zauna yana mik'a hannu a k'ok'arinsa na son d'auko bottle water,cikin wannan halin wani irin tari mai tsanani ya sake sark'e shi sakamakon yanayin da yake jan numfashi,a hakan yana tarin ba tare da ya samu damar aiwatar da abunda yake so ba yaci gaba da furta "Astagfirullah wa'atubu ilaiik.. Allahummagfirliiy warhamniiy",su Hajiya suna zaune a parlor kowa da abunda ya dame shi suka jiyo tarinsa,da sauri suka yo d'akin gaba d'ayansu lokacin yayi daf zai fad'o daga saman bed,a gaggauce Aryan da Maimunatu suka kamashi suka mayar saman bed d'in asking if he wanted something? Ya gyad'a kai da kyar yace he wanted to drink water,but no one understood what he was saying,Hajiya kam hankalinta duk ya gama tashi banda kiran sunansa da jera masa addu'ah babu abunda take yi,though halin da Rafeek yake ciki ya yi tsanani but that didn't stop him from smiling hawayen da suka taru gefen idonsa suka sake zubowa,muryarsa a can k'asa not being heard again yake cewa "Hajiyata please forgive me,and dan Allah ki rok'a min yafiyar duk wanda na yiwa ba daidai ba a tsayin rayuwata",kamar Hajiya ta ji abunda ya fad'a ta zauna daga gefensa tana jin zuciyarta a karye,hanunta ta d'ora akansa tana shafawa a hankali tana ta k'ok'arin ganin bata zubar masa da hawaye ba tace "In sha Allah ba zaka tafi ka barni ba",she saw that his mouth was moving but not being able to understand what he was saying,shi kuma a hakan bai fasa ba sai magana yake musu sai dai an rasa wanda zai fahimci abunda yake nufi,cikin wannan halin Dr Stevens ya tarar da shi,duk iya k'ok'arin da zai iya yayi akansa,bayan wuceqar wasu sa'o'i tarin yayi sauk'i sai dai numfashinsa da bai gama daidaita ba dole tasa ya sa masa oxygen.
Chapter 66 · 0% Book details