← Book details Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 152

Sashe 30

Dan Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Ta sake fashewa da kuka,Annie tana ta rarrashinta sai data saurara da kukan sannan ce "Tsoro nake ji"

       Annie tace "Ki kwantar da hankalin ki babu abunda zai faru in sha Allah"

      Ta girgiza kai tana cewa "Bana son zuwa"
      Annie taga hankalinta ya fara tashi tace tayi shiru to su zasu je ta fad'a mata address d'in gidan,tana share hawaye tace "Kada kuje kuma,ko kunje ba zasu yarda da abunda zaku fad'a ba"

      Annie ta kalleta tace "Saboda me ba zasu yarda ba.!?"

      Ta sake share hawayen da suka zubo tace "Bcos of my stepmother" Annie tana ta kallonta tace "Ur stepmother.!?"

      Ta girgiza kai tace "Duk abunda tace yayi shi yake yi,ba zai yarda ba shima"
      Annie tana jinjina kai data tuno maganar da aljanun nan suka yi da Malam sai tayi shiru tana tunani a ranta,zuwa wani lokaci ta d'ago ta kalli Nusrah tace "Bani dai address d'in gidan,idan munje basu yarda ba shi kenan mun fita hak'k'in ku duka" ta goge hawayenta ta fad'awa Annie address d'in. Suna gama maganar Annie tace ina ta ajiye ledar da ta bata d'azun,ta mik'e a hankali tana d'agowa suka had'a ido da shi yana tsaye daga bakin k'ofar bedroom d'in,ta sunkuyar da kanta ta wuce kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki,ta d'auko ta dawo Annie tasa Bareerah ta kawo mata garwashi a kaskon turare tayi mata hayak'i.

    Washe gari da rana Annie suka shirya ita da Nuraz zasu je gidan su Nusrah,tunda taga suna shirin fita hawaye yake ta zubo mata,ta d'aga kanta a hankali ta kallesu,Annie tayi mata sallama suka fita,,gidan ba b'oyayye bane kamar yadda ta bada address d'in haka suka dunga bin kwatancen har suka tsaya bakin get d'in gidan,babban gida ne sosai na alfarma daga gani kasan masu gidan suna hutawa sosai,yayi parking a bakin get suka fita tare,Annie tana gaba yana binta suka yi knocking get man d'insu ya bud'e yana kallonsu ya gaishe ta,Annie ta wuce tana amsa gaisuwarsa suka nufi entrance d'in gidan,a bakin k'ofa suka tsaya suka danna doorbell,mintuna biyu suna ta tsaye a wajen sannan aka bud'e. Sanye take da bak'in skirt daya tsaya kasan guiwarta sai white long sleeve na mata,wuyanta da butterfly bak'i,kanta ya sha kitson attach,yanayin shigarta shi ya bayyana musu matsayinta na christian and maidservant,ya tab'e baki yana d'auke kai dan yadda ta tsaya ta kafe su da ido,Annie tayi mata murmushi kad'an kafin ta tambaye ta
      "Are they here!!?"

     Ta kalli Annie ta kalli Nuraz da fuskar rashin fahimta tace "who are u looking for.!?"
       Nuraz ya kalleta a kyankyame yayi siririn tsaki,duka suka kalleshi a tare,ya banka mata harara bai ce komai ba,Annie ta sake kallonta tace "the owners of the house.!"
      Gyad'a mata kai tayi ta basu hanya,suka shigo parlor'n,aljannar duniya komai na more rayuwa zai yi wahala ace babu shi cikin gidan,ta nuna musu armchairs tace "sit here,,lemme give her a call" shi dai Nuraz kallon gidan kawai yake yana mamakin dalilin da zaisa har ayi mata wani abu dan a cutar da ita,suna zaune maidservant d'in ta d'auki telephone ta kira ta sanar da matar gidan akwai bak'i a k'asa,mintuna kad'an ta ajiye ta fad'a musu tana zuwa,Annie kad'ai ta amsa,sun d'auki mintuna sama da thirty suna jira Nuraz ya mik'e tsaye cikin b'acin rai yace "Annie! Let go home,baza su fito ba fa!"

   Annie tace "let's wait a little longer habibiiy if they don't come sai mu koma gida"

      Ya jinjina kai kawai amma bai zauna ba,again five minutes passed yaga nan ma shiru,ya kalli Annie ransa ya gama sosuwa yace "Annie.! We need to go home now,,I told u baza su zo ba,kina kallon fa yadda aka ajiye mu muna jira almost forty minutes,me muka zo nema ne da za'a wulak'anta mu.!? Ki tashi kawai mu tafi.."

       Annie ta girgiza masa kai ta rasa abunda zata fad'a masa,ta mik'e jikinta a sanyaye,ya jinjina kai ya juya ya fara tafiya Annie ta bi bayansa,k'arar sautin takun takalma yasa Annie tace "Habibiiy.! Munyi gajen hak'uri" bai damu ba yace "A'a Annie suma ai wulak'anci ne a sanar da su suna da guest su ajiye mutum almost an hour yana jira,ko dai wani abu mutum ya zo nema ai bai kamata ka yi masa wannan wulak'ancin ba"
       Suna fita ta k'araso cikin parlor'n tana zabgawa Binitta kira,daga kitchen ta fito a guje tana amsawa,ta zo gabanta ta durk'usa jikinta na kyarma tace "here i'm Aunty" ta kalleta tana gesturing face tace "where are the guests.!?"
    Tayi saurin kallon inda ta barsu taga basa nan,har ta juya zata ce mata wani abun ta hango sun fita,da sauri tace "Aunty look.!"
     Binitta ta fad'a tana nuna mata k'ofa,ta tab'e baki tace "Sai kije ki ce musu ga ni na fito ko.!?" Da sauri kamar zata fad'i ta mik'e tabi su Annie har tana had'awa da gudu.....

    #Anya za su dawo kuwa..!? Na ga Nuraz ya d'au zafi fa..

#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*

*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2

Pᴀɢᴇ 15.
#Aᴘᴘᴇᴀʀᴀɴᴄᴇ

*The hole 2dayz page goes to: My Rooh Hjy Maryam Alhassan (Mammanah),Aysha,Mmn Abdallah,Zainab,Amina,Nabeela Abduljalal,Queen Acid,Ummu Adnan,Xee Mama,Momy Faruk,Ummul Sudais,Fatima Bello Adam,Lilmama,Sa'adat (Momy's gurl),Maryam T Baliya,Mum Sudaiz,Xeinab Ismael Kassim,Zainab Ahmad,Amal,Ummu Razaan,Maman khaleed,Myrah Muh'd,Hussaina Isah Aliyu,Rabi'atu Maharazu,Napeesa,Mr's Yaseen,Aisha Idrees,Najida A Bicca Zulaiha Ibrahim,Kamala Minna,Smaishera,MSKutama,Muneerat,Aisha Isma'il,Maryam Uba,Maman Dijah,Ubeey,Aysherudahmad,Ummu Hummaira,Khadeejat M Zangina,Sarah,Hazeenat Usman,Raliya KK.*
*Kuji dad'in ku mutane na,yawan ku yasa har na kasa ci gaba da zayyano ku,aradu comments d'inku na tsumani bahot² khushu habibtiiys.💕*

A harabar gidan Binitta ta iske su suna shirin shiga mota,ta ci burki a gaban Annie cikin hausarta da bata fita sosai tana haki tace "Madam ka yi hak'uri,ga aunty d'in can ya fito bai same ka ba."
Nuraz ya kalleta a fusace saboda ya je mak'ura a jin haushi yace "Go back and tell ur madam not asking for her help brings us here and we didn't came for the capable of being humiliated,we just come up for our own opinions.."
Annie ta kalleshi taga ransa a b'ace,a hankali ta d'agawa maidservant d'in hannu alamar taje,a tsorace Binitta ta kalli Annie za tayi magana Annie tace "Je abunki zamu dawo" tayi springing tace "Thank u Hajiya" sannan ta juya da gudu²,Annie ta kalli Nuraz tace "Sorry habibiiy! Muje" ya kalleta yace "Annie gaskiya banda yau,kawai mu koma gida" ta girgiza kai tace "A'ah muje" zai yi magana ta katse masa hanzari "Ka san bana son musu da jan zance ko.!?"
Kansa ya sauke k'asa ya fara tafiya without ya furta even a word ta biyo shi a baya,har suka dawo bakin entrance d'in inda suka iske Binitta tana jira,tayi sanyayyar ajiyar zuciya da ta gansu sannan ta wuce tana fad'in "Aunty ga su nan" tana hakimce a saman armchair na wani rantsatstsen royal set tayi facing k'aton plasma dake manne jikin wall ta amsa "Su k'araso" not to look at their direction,Nuraz ya sake k'ulewa yayi k'wafa,Annie tayi masa ido akan kada yace komai,ya daure suka k'arasa tana danna remote tace "Sit here" tana nuna musu chairs dake side da nata,k'atuwa ce ta gaban kwatance,yadda fuskarta da jikinta suke lub² farare tas da su kamar a tab'a jini ya fito kad'ai ya isa tabbatarwa mai kallonta tana cikin jin dad'i,ta d'auki kusan mintuna biyu kafin ta waiwayo ta kalle su tana yatsina,akan dank'eriyar aura batik ta over 100+K dake jikin Annie idonta ya fara sauka akai,kafin ta hango bangles da manyan a gold rings guda hud'u,da wuri tayi gaggawar gane bak'in ba irin wad'anda suke zuwa neman taimako bane,amma da yake akwaita da izza and bata yarda ace wani ya fita bata kuma k'aunar a rainata,a wani iri ta yatsina fuska tace "Sannu ko.!?"
Annie ta daure suka gaisa duk da ta fahimci matar tana wulak'anci,yallab'ai kuwa ko kallon inda take bai yi ba bare yasan Allah yayi halittarta a wajen,ta kalleshi tana jira taji ya gaisheta taga ko gezau bai yi ba,ta kalli Annie kafin tace "Meke tafe da ku.!?"

Annie ta gyara zama tace "Ehh! Toh a zahirin gaskiya Hajiya wani al'amari mai girma ya kawo mu gurinku.."

Ta sake yatsina fuska tace "Gurinnu kuma.!?" Annie ta girgiza kai,tana kallon gefen da yake zaune yayi crossing leg's yana pressing iPad d'insa cikin k'warewa tace "Ok! Ina sauraren ki" Annie tace "Shin ko kin san *NUSRAH.!?"*

Tayi jim kafin ta tab'e baki tace "Ehh! Wani abu ne ya same ta.!?"

Ba don ta damu da sani ba tayi furucin,daga Nuraz har Annien suka kalleta da mugun mamaki,Annie ta girgiza kai tace "Ehh! To zan iya cewa wani abun ya faru da ita,but for now sai dai muce Alhamdulillah.!"

Tayi saurin kallon Annie tace "Kamar yaya.!?" Annie tace "Ehh! Kamar yadda kika ji na fad'a,tabbas rayuwarta ta shiga had'ari a baya.. But now she's safe" tayi squeezing face looks like tana buk'atar k'arin bayani,tiryan² Annie tayi mata bayanin yadda al'amarin ya faru,tun daga had'uwarsu da Nuraz,kawo ta gida zuwa abunda ya faru a jiya zuwansu gurin Malam,,abunda ba su yi tunani ba shi ne ya faru,bayan Annie ta gama bata labari,babu damuwar komai akan fuskarta ta kalli annie tace "Kun kyauta kam da kuka taimaka mata,but zance kun yi rashin sa'a bcos mu nan gidan ba mu da wata yarinya kuma mai wannan sunan,idan ban manta ba ina tunanin da jimawa ta mu Nusran ta b'ace,munyi cigiya har gidan televisions,so da bamu same ta ba muka yi jana'izarta,,ina ganin kunyi missing road gaskiya,ba nan gidan kuke nema ba"

Tun da ya zauna bai fi sau d'aya ya d'ago ba yana ta pressing phone sai data fad'i wannan maganar,ya janye wayar gefe a hankali ya d'ago kansa ya zuba mata idanunsa,the way take yi tana magana ta gama tabbatar masa ba ta da gaskiya and duk abunda ya faru a jiya yanzun ya tabbatar she's the devil da ta shirya komai,,muryar Annie ya ji tana cewa "Amma Hajiya,ko dai mun yi b'atan kai ya kamata ki ganta ko Allah zai sa y'arkun ce da kuke nema.!"
Chapter 30 · 0% Book details