Sashe 99
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana tafiya Hips dinta na jujjuyawa kamar ana kaɗasu, agabansu ta tsaya haɗi da Goya hannayenta saman tudun kirjinta tana kallonsu, idan ta kalli Angel sai ta kalli Batul, kamar wasu munafukai sunyi wuƙi wuƙi da ido, musamman Batul duk tasha jinin jikinta, saboda mugun jin shakkarta take ji, har ƙwara Angel ashirye take da tayi mata rashin kunya idan har ta ƙetare iyakarta.
“Ke! Meye sunanki”! Ta jefa ma batul tambayar, muryarta na rawa ta furta”BATUL”! ta6e baki ummi tayi tare da daura idonta kan Angel”ke fa”?
Ɗaure mata fuska Angel tayi kamar bazata tanka mata ba tace”UNAISAH”
“Me kuke nema ne”?
Angel ce tayi ƙarfin halin bata amsa da cewa”ɗan uwana ke jin yunwa, shine na fito don in sama mashi abun da zai ci”
Ta6e la66a ummi tayi”An shirya maku breakfast din ku a dining, dama ku nake jira ku farka” ta faɗa tana nuna masu dining room da hannunta, atare su ka kai idonsu ita da batul suka kalli ɗakin.
“Ku koma ku tada sauran ƴan uwan naku, su fito mu yi breakfast, idan mun kammala inaso zanyi magana da ku”
Amsa mata su ka yi da toh, da sauri suka juya suka nufi bedrooms din ƴan uwansu, tana a tsaye tana bin bayansu da kallo, bakomai yafi bata mamaki da yaran ba face doguwar sumar kansu data lullu6e bayansu kamar hijabi, aranta ta ayyana ɗawainiya da yaran nan ba abune mai sauƙi ba, gyaran gashin kansu kaɗai wata wahalar ce mai zaman kanta, gashi an faɗa mata babu shige babu fuce balle tace zata kai su saloon, kuma babu damar a gayyato masu yi din suyi masu, dole sai dai ita ce za ta gyara su.
Daya bayan ɗaya suka bi ɗakunan yan uwansu suka shiga domin tada wadanda basu farka daga bacci ba, saida suka taimaka ma Azeeza da jamimah suka wanke fuskokinsu da bakunansu, tukunna suka fito daga ɗakin, Kayan jiya ne a jikinsu sai mayafin da suka yafa akansu, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, musamman azeeza tun da tayi tozali da ƙwan fitilun falo jikinta Ya hau yin kerma, duk ta firgice, Parveen kuwa baki yaƙi rufuwa kamar lefen sakarai sai faman zazzare idanuwa suke Yi, saboda yanzu ne suka samu damar ganin ko’ina na cikin gidan dakyau, Hanna kuwa daƙyar take taka tiles din floor, da takalmi ta fito amma saboda tsabar ruɗu a hannu ta ruƙe takalman ta rungumesu a ƙirjinta, gani take kamar in ta taka ƙasan da takalman zai fashe, Naufal da Javed har tuntu6e suke yi garin yin kalle kalle gidan yayi matuƙar ruɗar dasu, shi ko Haris jiki sai kerma yake yi basa ban ban, shima crystal Chandelier din ceilling ne Ya ruɗar da shi ga sanyin A.c da yayi mashi yawa, hatta gabriel dake da wayewa yau dai an ƙure shi, sai faman jinjina kai Yake yi yayin da yake bin katafaren falon da kallo, abunda zai baka mamaki jamimah hankalinta kwance babu abunda ya ruɗe ta koya tsoratar da ita, sai faman washe baki take Yi komai ta kalla saita nuna shi da yatsa tace”menene wancan” ta ishe su da tambaya kamar rainon ɗan jarida, Ummin america dake a tsaye bakin ƙofar shiga dining room din, lamarin ya ɗaure mata kai, tayi matuƙar yin mamakin ƙauyancin su, gasu dai a halitta kamar ƴa’ƴan masu kuɗi, tafiya suke yi tamkar suna jin tsoron taka floor, sunƙi maida hankali su shigo su ci abinci, sai faman ƴan kalle kalle suke Yi kamar wuyansu zai cire.
Mutum ɗaya ce babu acikinsu, Angel da ta tafi bedroom ɗin Danish, Batul dai tana atare da su Haris.
Gyaran muryar da ummi tayi masu ne ya janyo hankalinsu ga kallonta.
Da hannu ta nuna masu ƙofar shiga”ku zo ku shiga” ba tare da sun tanka mata ba, suka nufi ɗakin cin abincin, koda suka shiga sai suka koma suna bin ko’ina da kallo, Parveen ce ta furta”La’ha’ilah! Wannan duk namune”? Ta jefa tambayar tana nuna kayan breakfast din dake a jere saman zungureran table.
Ummi ce ta bata amsa da cewa”naku ne, kowa ya samu wuri ya zauna” su parveen anga banza, tuni taja kujera ta zauna, ɗaya bayan ɗaya kowannansu Ya samu wuri ya zauna, sai faman baza ido suke Yi suna bin komai da kallo, jamimah tana jinjina kai tace”Yau zamu ci daɗi, wallahi munji daɗi muma mun zama ƴan gayu, gidan daddyn genie akwai abinci da kayan wasa”
Azeeza taƙi ɗagowa dakai, ta ƙanƙame jikinta saman kujera, ita kwan fitila ne damuwarta, na ɗakinsu bai kai na falo dana dining room girma ba, sun hanata sakat, Gabriel dake kallonta cikin muryar raɗa ya ambaci sunanta”My azeeza” ɗagowa tayi da ido tana kallon shi sai faman yamutsa fuska take Yi
“Meke damun ki”?
Da index finger ta nuna mashi saman ceilling ba tare da ta kalla ba, muryarta ƙasa ƙasa tace”zai Iya faɗowa saman kanmu”
Murmushi ya sakar mata”ki kwantar da hankalin ki, ba zai ta6a faɗowa ba, idan ma zai faɗo sai na tare maki shi, hakan yayi maki”? Sai lokacin ta ɗan saki murmushi jin abun da yace ta jinjina mashi kai alamar eh.
Parveen sai faman haɗiyar yawu take yi ta ƙosa su fara ci, sai dai sun gaza sanya hannu ganin yadda Ummin america ta tsare su da ido ko kyaftawa ba tayi, tana daga tsaye bakin glass door din dakin, ta lura basu cika ba shiyasa ta tsaya tana jiran sauran su ƙaraso don su fara ci.
“Menene wannan abun” jamimah ce tayi tambaya tana nuna wata roba
Kallon robar Gabriel yai a jikinta an rubuta Honey.
“Zuma ce a ciki, kin ta6a sha”? Girgiza mashi kai tayi alamar a’a, ta kuma nuna dafaffan ƙwai tace”wannan luluyayyan abun fa”? Harara ya dan jefa mata”Ƙwai ne, pls ki daina yi min tambaya baki ga ana kallon mu ba”? Ta6e mashi baki tayi”to aini inason in sani ne ko,” har tayi shiru can kuma kamar an cikare ta tace”Gabriel kace ƙwai ne, to shima kamar ƙwan fitila mai bada haske Yake”shiru yayi yana kallonta ba tare daya furta komai ba,
(abun da yasa take tambayarshi saboda bakomai ne suka sani dangane da nau’ikan abinci, ko a kurkuku snacks da nama suke ci da kayan marmari, haka zalika a asibiti da suka zauna bakomai ne suka sani ba yawanci duk kalar abunda suke ci a prison ne, yau sunci karo da wasu nau’ikan abincin dana sha wanda basu ta6a yin tozali da su, shiyasa jemimah ta tsare shi da tambayoyi kamar ƴar jarida)
Batul dai sai satar kallon ummi take yi ita kanta ummin ta lura da kallon ƙurullan da Batul take Yi mata, shiyasa ta tsaida idonta akanta, tunda tayi hakan batul ta saddar da kanta ƙasa cikin jin kunyarta.
Abun da Ya faru, Lokacin da suka kammala tada ƴan uwansu Angel ta nufi ɗakin Danish, shigarta keda wuya ta taras dashi atsaye gaban mirror Yana faman yin haki Ya dunƙule tafukan hannayensa kamar wanda zai yi dambe, Kafin ta buɗe baki ta tambaye shi lafiya, idanuwanta suka sauka akan madubin daya fasa, ƙwaƙƙwaran naushi ya kai mashi gaba ɗaya ya zube ƙasa ya tarwatse.
Rass taji gabanta Ya faɗi, a tsananin tsoroce ta furta”Na shiga uku! danish meyasa zaka fasa masu madubi? Kasan kuwa tsadar dake gare shi? Wai meke damunka ne? So kake kaja mana bala’i daga zuwa gidan mutane har ka fara yi masu 6arna” hankalinta atashe tayi maganar tana duban bayanshi.
A hankali Ya jiyo yana kallon cikin sanyin murya ya furta”mutun na gani aciki Yana kallona, shiyasa na naushe shi” Zaro ido waje tayi can kuma ta tuntsire da dariya hada dafe ciki, ɗaure mata fuska yai ganin tana yi mashi dariya.
Nuna shi tayi da yatsa tana fadin”mutumin da ka gani acikin madubin kaine ba wani ba, ai saida naso in nuna maka kanka a mirror amma kaƙiya, ka nuna baka son kallon shi gashi nan Yanzu ka fasa masu madubi mai tsada, Ni dai ba ruwana” ta faɗa fuskarta da murmushi.
Kallon rashin fahimta yake binta da shi, ya rasa gane me take nufi, kamar bata fahimci abunda ya faɗa mata ba.
Gudun kada wani ya shigo ya taras da 6arnar da Danish yayi yasa tayi saurin juyawa tana yan dube dube cen idonta ya sauka kan wani abu yayi mata yanayi da tsintsiya da sauri ta ɗauko ta tattara broken glass din ta turasu kasan gadon shi dan bataga dust bin a dakin ba ajiyar zuciya ta sauke
Kafin ta ɗago tana dubanshi”kai kaɗai muke jira, zamu yi break fast, ka shiga toilet ka wanke face dinka da bakinka, idan mun gama cin abincin sai kayi wankan” toilet door Ya nufa, har ya kusa kaiwa ƙofar ta tuna da madubin toilet, da karfi ta furta”dakata danish” cak ya tsaya da tafiya, da sauri ta nufi ƙofar toilet din ta buɗe ta shige ciki, towel ta ɗauko ta rufe madubi, saboda tsaro tasan zai Iya Fasa shi kamar yadda ya fasa na room dinsa.
Fitowa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya ta dubi fuskarshi”nasan idan ka shiga ciki zakaga towel na lullu6e wani abu dashi, kada ka buɗe shi, madubi ne bana so ka fasa shi kamar yadda ka fasa na ɗakin ka, Idan ba haka ba zasu ce saika biya su ne kuma kaga bamu da kuɗi, kai ba kama san menene kuɗi ba, Ni zaka bari da aikin biyansu” ta faɗa tana yamutsa mashi fuska, bawan Allah yayi tsaye yana kallonta.
“Ina jiran ka, kada ka daɗe ka yi sauri ka fito suna jiran mu”
Amsa mata yai da toh, kafin ya bude kofar ya shiga, Ƴan mintuna ya fito daga ciki, har yayi brushing teeth dinsa, daga kasa har sama take bin shi da kallo, a ganinta basai ya tsaya sanya kaya ba tun da ba wanka yayi ba, Ruƙo hannun shi tayi acikin nata kamar wani ƙaninta”muje ko”? Ta faɗa tana ƙoƙarin janshi.
Adai dai lokacin da suka sauko falon, ƙofar shigowa cikinsa ta zuge a hankali, atare Angel da Danish suka juya baya jin takun tafiyar mutun.