← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 152

Sashe 126

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Abun da Unaisah ta faɗi gaskiya ne, tsammaninmu yazo ɗaya, azzaluman kurkukun ƙaddara ne suke sarrafashi ta ƙarfi da yaji bada son ranshi ba, kuma sunayi mashi hakanne don mutane su ƙyamace shi kowa ya gujeshi, shi kuma zaiji ya tsani kanshi saboda ƙyarar da mutane suke yi mashi, daga haka zai fara tunanin komawa prison wannan shine abunda suke ƙoƙarin yi”

Tun da yafara magana big guy yake jinjina kanshi alamar gamsuwa da jawabin shi, Muryar chief ce ta sa shi dakatawa yana sauraronshi, babu mai iya jin voice dinshi sai shi da yasanya abun sauraron akunne.

Cikin harshen turance yace “Ka faɗa mashi, muna atare dashi, bazamu ta6a rabuwa dashi ba har iya ƙarshen numfashinmu, babu wanda zai ƙyamace shi, duk runtsi zamu kasance atare dashi don mu bashi ƙwarin gwiwa kuma zamu tallafa masa don ganin mun raba shi da miyagun dake atare dashi, in sha Allah komai yazo ƙarshe ya kwantar da hankalinshi”

Jinjina kai big guy yai haƙiƙa yaji daɗin kalaman Chief owais, magana yasoma yi masu”chief yace in isar mashi da sakonshi zuwa ga Danish .....” mayar da hankalin sukayi akanshi suna sauraronshi, a tsanake ya faɗa masu abunda chief yace.

Wani irin farin cikine ya lullu6e Unaisah, har cikin ranta taji daɗin kalaman shi duk da batasan wanene shi ba, ba ta ta6a ganin fuskarshi ba, ko ɗazu da taji an dauketa lokacin data lullu6e Danish da bazar rigarta batasan wanene ya dauketa ba saboda bata acikin hayyacinta, idanuwanta sun makance.

“Wanene chief? Yaushe ya faɗa maka sakon”? Ta jefa ma Big guy tambayar yayin da take dubanshi.

Nuna mata earbuds din kunnanshi yai da yatsan hannun shi, nan take ta gane abun jin magana ne a ear dinshi tanan suke yin communicating da shi.

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke muryarta adisashe ta furta”idan na samu natsuwa zaka kaini wurinshi muyi mashi godiya” Big guy yace”a’a shi ba’ayi mashi godiya, sai dai idan kinason ganinshi zan nema maki izni daga gare shi, amsa mashi tayi da toh inaso”

Kallon salsabeel Yai”menene mafita? Muna son musan wani hali yake aciki” kafin ya bashi amsa unaisa tayi saurin cewa”nayi magana da boss man, na fada mashi inda na ajiye wasiƙar adreshin gidanku daka bani, inda zamu samu ruwan zam zam din”

Fuskarshi da matsanancin damuwa yace”ai babu zamzam din nan! Tun lokacin da kuka faɗa hannun sojin america suka damƙa case dinku hannun hukumar Isod, nasan da zamanku, munyi ƙoƙarin samu ruwan zam zam saboda gudun kada giant’s heart dinsa ta motsa, sai dai kash lokacin da muka je gidanmu na kaduna tare da jami’an isod bamu samu komai ba, Gidan ma an canza mashi kamanni, magada ne suka koma da zama cikinshi, su kansu da mukaje basu san Wanene ni ba, munyi ƙoƙarin yi masu bayani amma sai suka fada mana cewa babu komai na habibullah dayai saura agidan....” aruɗe Unaisah tace”ya zamuyi yanzu”? Ta faɗa tana zazzare idanuwanta.
Salsabeel yace”akwai hanyoyi da dama, da zamu Iya samun ruwan zam zam sai dai bamusan wasu irin addu’o’ine ko ayoyin alƙur’ani ake amfani dasu ba wurin tofe ruwan ba” ya faɗa yana dubanta.

“da za’a samu babban malamin addini kamar mahaifina habibullah ina da tabbacin zai iya taimaka mashi”

Shiru suka ɗanyi suna kallon kallo atsakanin Salsabeel da Unaisah, ga macijin yayi kwance saman jikinshi daya nannaɗe.

Chief Owais dake a kwance saman bed matress dinsa Yana sauraronsu, ƙarar shigowar message ce ta janyo hankalinshi ga buɗe eyes dinshi, phone dinsa Ya ɗago da ita yana duban screen din.

Text message ne aka turo mashi, yayi mamakin ganin saƙon Uncle dinsa, A irin wannan lokacin ƙarfe biyu da rabi na dare, hakan na nufin bai runtsa ba.

Karanta text message din Ya soma yi acikin zuciyarshi.

_”My son, I can’t sleep because of that child, I don’t know why I’m so worried about him. Please help me. I want to see him before I go back to Canada next week. na jaraba kiran layin Sheikh imam munyi magana dashi ashe baya kasar ya tafi sudan, na nemi alfarmar inason ganinshi da gaggawa, yace min in sha Allah zai dawo ƙasar a gobe, saƙo daga Prime minister Hateem Obinna_

Bayan kammala karanta message din, Owais Yai mashi reply kamar haka

_”Nima ban runtsa ba kawuna, saboda yaron, ƙoƙarin da muke Yi kenan don ganin mun taimaka mashi ya canza halittarshi zuwa ta suffar mutane, amma inaso ka kwantar da hankalinka ka yi bacci, in sha Allah zaka haɗu dashi kafin komawarka kanada, har ma kuci abinci atare”_

Tura mashi sakon yai, within minutes saiga wani sakon daga prime minister

_thank u, sai mun hadu gobe da wuri zan shigo gidan naka idan sheikh iman ya ƙaraso_

Lumshe ido owais yai, A hankali ya furta sunan big guy, on the other hand big guy ya amsa mashi da na’am yalla6ai”

“Sako ya shigo min daga Uncle Hateem, Zuwa gobe da safe Sheikh Imam zaizo Nigeria, yayi tafiya ne zuwa sudan, ka yi ma brother din yaron nan magana ya tambaye shi idan yana jin yunwa ya fadi me zai iya ci akawo mashi” amsa mashi yai da toh.
Ya mayar da dubanshi ga su salsabeel”tun da yana jin maganarka ka tambayar mana shi me zai Iya ci akawo mashi, sannan pls kace mashi ya kwantar da hankalinshi zuwa gobe insha Allah sheik imam zai shigo Nigeria, shahararran malamin addinine muna da tabbacin zai Iya taimaka mashi”

Gyaɗa kai salsabeel yai”ay yana sauraronka, Yanzu haka magana yake yi min.

“Meyasa kuka harbe shi? Duk da harsashin bai fasa jikinshi ba yayi mashi illah saboda babu kakin giant a jikinshi”

Hankalin Unaisah dana Big guy ya tashi matuƙar, muryarta na rawa ta furta”meya faru dashi? Yaji ciwo ajikin shi”
“Bazan Iya sani ba, sai ya dawo suffarshi ta mutane tukunna zamu ga illar da yayi mashi, sannan ya fadamin yana son kayan marmari su kadai yake sha’awar sha”

Damuwace ƙarara akan fuskar Angel”meyasa bazai Iya cin abinci ba”? Ta fada tana duban salsabeel.

“A halin yanzu Danish dinki, ba mutun bane Giant snake nake, bazai Iya cin kalar abincin mu ba, har sai ya dawo cikakken mutun.

Kwa6e fuska tayi tana duban kan macijin, har yanzu bai dagoba tunda ya kwantar da kanshi saman jikinshi daya nannaɗe.

Miƙewa tsaye big guy yai”ka zauna atare dasu, zan je na kawo mashi kayan marmarin” amsa mashi salsabeel yayi da toh.

Bayan fitar big guy, ta ƙura ma salsabeel ido, har yanzu mamakin ganinshi take yi, abubuwa dayawa sun cunkushe mata brain dinta, tana son jin ya akai ya tsira daga kurkukun ƙaddara? Shin ya sauran ƴan uwansu suka ƙare sun mutu ko sun rayu? Tayaya Akai Ya haɗu da jami’an da suke kula dasu? Ko dai dama shima jami’insu ne!? ta ɗaura mashi alamar tambaya, tadai haƙura ne har zuwa time din da danish zai rikiɗa ya dawo mutun donjin amsar tambayoyinta, kamar yadda take kallon Salsabeel haka shima yake kallonta, yayi kewarsu sosai, kuma yaji dadin ganinsu, da ransu da lafiyarsu, bakomai yake tunawa ba face ranar daya fara haduwa da ita har yakaita dakin da suka tattauna, da kuma ranar da ya ceci rayuwarta lokacin da matsafa sukayi mata wanka da jini, ranar da ta azabtu ta galabaita, Allah kenan mai yadda yaso mai jujjuya al’amurra, yanzu tamkar ba’ayi ba, tayi haske abunta gwanin kyau har girma ta ƙara mashi akan yadda suka yi rabuwar ƙarshe a kurkuku.

Murmushi yasakar mata, itama ta mayar mashi da martanin murmushin, ya fahimci aƙagare take da son jin labarin ƴan uwanta daga gare shi.

*PRISONERS💔✍️*

Tun bayan fitowar Batul daga ɗakin Ummin america, a tsakar dare ta nufi down stair, baiwar Allah tana tafiya jikinta na kakarwa, hatta haƙoranta kerma sukeyi suna hadewa jikin juna, tsoro take ji ita kaɗai kamar aljana, sai faman firgita take yi gani take yi kamar macijin zai kawo mata hari.

Daƙyar take iya taka ƙafarta saman floor din falo, ga wani azababban tari daya farmata.

Sam ba ta ji takun tafiyar mutum ba, saboda hankalinta ba akwance yake ba, sai ƴan waige waige take yi tana faman hadiyar yawu.

Yayi mamakin ganin ɗaya daga cikin yaran tana yawo a tsakar dare, babu mayafi a jikinta, ƙura mata ido yai a ƙoƙarinshi naya gano wacece acikinsu, ya rasa gane batul ce ko Unaisah, saboda launin gashinsu kala ɗaya ne ga kuma nannaɗewar sumar kan nasu daya kasance iri ɗaya, zuciyarshi ce ta raya mashi cewa Unaisah tana adaki fa ya barota tare da salsabeel wannan ba ita bace sai dai ko ƴar uwarta ce Batul.

Da ƙarfi ya ambaci sunanta”Batul” rass taji gabanta Ya faɗi, a firgice ta waiwayo don ganin wanene, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar big guy dake sanye cikin face mask,l.

Tsabar tsoro da ruɗu yasa ta zabura zata watsa da gudu, sai dai kafin tayi hakan yai saurin haura ƙafa ya damƙo damtsen hannunta ya janyota zuwa jikin shi, ƙanƙame shi tayi atsorace ga tari da take yi.

Lamarin ya ɗaure mashi kai, ɗago da kanta yai daga saman ƙirjinshi ya furta”ke! Daga ina kike? Ya akai kika fito daga ɗaki”?
Daƙyar ta Iya buɗe baki tace”sanyi nake ji babu bargo shine na fito zani ɗaki in ɗauko”
“Awani ɗaki kike”?
“Ɗakin aunty ummi, boss man ne yace muje can mu kwana, saboda munajin tsoron kwana ana mu dakin”

“Meyasa baki tambayeta ta baki bargo ba”?
A tsoroce take yi mashi magana”tayi bacci ne, kafin ta kwanta ma saida nace ta taimaka ma parveen da kaya ta sanya saboda tayi ma nata fitsari sunjiƙe sharkaf amma taƙi bata sai dai ni na cire nawa muka yi musanya ta bani nata, kuma ɗakinta sanyi sosai”
Tunda tafara magana Big guy yake jinjina kanshi, ga dukkan alamu ya fusata matuƙa, bashi ba hatta chief owais dake acan room dinsa yana sauraron maganganunsu.

Ruƙo hannun Batul yayi acikin nashi ya juya da ita suka nufi ɗakin.

A lokacin Ummin america tana ƙoƙarin fitowa daga cikin toilet, ta gama sheƙe ayarta da gardin daya kirata awaya, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zura ƙafarta keda wuya hasken ɗakinta Ya kama, a firgice takai idanuwanta kan masu shigowa ciki, tunda tayi arba da big guy tare da batul gabanta yai mugun faɗuwa.
Chapter 126 · 0% Book details