← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 152

Sashe 131

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zeenatu dake a la6e tana sauraronsu, takasa fitowa daga toilet din, zuciyarta ta kwaɗaitu da son jin wacece yarinyar auntynta benazir? Ya akai bata ta6a ganinta ba? Kamar dai ta ta6a jin labarin jinjirar da benazir ta bari awajen mommynta sarah.

Lokaci ɗaya dr shurem yadaina yin dariyar, hawayen dake taruwa cikin idanuwanshi suka soma gangarowa saman kuncinsa.

Da sauri ya kifa kanshi on his laps,
Hankalin benazir ba ƙaramin tashi yai ba, Jiki na rawa ta mike daga kan dardumar ta koma gefenshi ta zauna haɗi da daura hannunta ɗaya saman bayanshi”yaya shureim meke faruwa? Meyasa ka zubar hawaye? Yanzu fa kake yin dariya? Kona fadi wani abune daya 6ata maka rai? Shiru bai ɗago ba, duk tabi ta ruɗe, zeenatu dake yi masu la6e jikinta yai sanyi jin dr shureim dinta yana zubar da hawaye, muryar benazir taci gaba da jiyowa tana fadin”dan Allah kayi min magana yayana nakaina, kasan bana son ganinka acikin damuwa” bazata iya jurar halin da dr shureim dinta ya shigaba, Har ta miƙa hannu zata buɗe kofar toilet din, sai kuma tafasa ta dan buɗe kadan ta yadda zata iya leƙen su

Ɗagowa yai da kanshi, hawaye sun wanke fuskarshi, benazir dake kallon shi itama hawayen ke fita a idonta
Zura hannunshi yai cikin aljihun jallabiyar jikinshi ya zaro wayarshi, batare dayace komai ba, Ya miƙa mata wayar, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskarta Yarinyar dake akan wallpaper dinshi.

Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, da sauri ya sanya tafin hannunshi ɗaya ya toshe mata bakinta, haɗi da girgiza mata kai, alamar tayi shiru, daƙyar ta haɗiye kukanta, yayin da suke kallon juna, sai yanzu tagane dalilin zubar hawayenshi.

A hankali ya zame tafin hannunshi daga saman bakinta, hakan ya bata damar yin magana Cikin rauni na murya ta furta”munyi babban rashi yaya shureim, babu rabon suyi rayuwa tare da ƴata Angel, yarinyar tana kama damu, kamar ni na haifeta, mutuwa tayi mana yankan ƙauna, Allah ya jiƙanta” daƙyar ta ƙare maganar a hankali ta mayar da rinannun idanuwanta kan hoton jinjirar yarinyar dake a nannanɗe cikin towel fari ƙal, an sanya mata kayan sanyi, farace sol kamar ka ta6a jini ya ɗigo, dara daran idanuwanta sun buɗe sosai.

“Bani da abun kallo daya wuce hotonta, da ita nake kwana da ita nake tashi, na mutu akan ƙaunarta, bazan ta6a daina sonta ba, kuma bana tunanin koda ace nayi aure zan samu madadinta a duniyar nan........ ⁉️❗

“Nayi danasanin abunda na akaita mata, har yau idan na tuna cewa da hannuna nayi hakan sai inji gaba ɗaya na tsani kaina....” cikin jin ƙunar yai ya ƙare maganar.

Tsananin tausayinshi ne ya kama Benazir, idanuwansu sun kada jawur
Harta bude baki zatayi magana, Motsin buɗe kofar toilet Ya dakatar da ita, sam ta manta da zeenatu a toilet, da sauri ta goge hawayenta, dr shureim ma ya share hawayen shi muryarshi adisashe yace”wanene a toilet”?
Kafin ta bashi amsa, zeenatu ta fito, fuskarta da alamun lemar ruwa, tamkar batasan me suke tattaunawa ba, Har kuka tayi masu saboda sun bata tausayi duk da bata fahimci kan zancen nasu ba, ita a tunaninta Yaya shureim dinta ya ta6a son wata, sannan hoton daya ta6a nuna mata awayarshi amatsayin nata yake kallo yanzu ta gane ba ita bace, ya 6oye matane, har cikin ranta ba ta ji dadin hakan ba, jikinta yai sanyi tamkar wadda ka zarewa laka.

Sun ƙura mata ido suna kallonta, fatansu Allah yasa bata ji me suke tattaunawa ba”

“Zeeentu dama kina acikin toilet tsawon lokacin dana shigo ɗakin”?

Jinjina mashi kai tayi”eh yaya shureim bansan ka shigo dakin ba, Uziri ne Ya ruƙe ni a toilet”

Ajiyar zuciya ya sauke jin tace batasan ya shigo ba.

“Ina kwana, ka tashi lafiya” muryarshi araunace ya amsa mata”lafiyalou” duban benazir tayi wadda tayi shiru tana kallonta, daga ita har dr. shureim din fuskokinsu sunyi jawur saboda kukan da suka sha, a hake suke ƙoƙarin 6oye mata damuwarsu bayan ga alama nan ta gani.

“Aunty Benazir, bari naje daki in yi sallar acan, namanta jiya ban ɗauko hijabina ba” ta fadi hakanne don ta basu damar cigaba da tattaunawarsu

Benazir tace”A’a basai kinje daki ba, Ga hijab dina kiyi da ita” ta fada tare da cire hijabin ta miƙa mata, da sauri zeenatu tace”a’a, Kibarshi, nafison naje daki nayi acan, naga kamar kuna yin magana ne keda ya shureim”

Murmushin yaƙe Benazir tasakar mata”kada ki damu ƙanwata, bawani abu muke tattaunawaba, kema zamu Iya yin firar dake”

“Assalamu alaikum!” Mom layla ce ta doko sallama, gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta, doguwar rigace a jikinta milk colour, ta yafa mayafi akanta, fuskarta dauke da fara’a take dubansu
Har suna haɗa baki wurin gaishe da ita”ina kwana mommy? Kin tashi lafiya”?

Cikin kulawa ta amsa masu da cewa”lafiyalou Alhamdulillah, fatan na same ku lafiya, zeenatu ya akai naganki atsaye”?

Washe baki zeenatu tayi tana fadin”yanzu na fito daga toilet, nayi alwala ne zanyi sallah”
Mom layla tace”okey, yakamata kiyi kada ki makara” amsa mata tayi da toh, da sauri ta nufi kofar fita dakin ta fuce cike da fargaban kada Aunty Benazir ta dakatar da ita, bayan ta fita daga dakin ajiyar zuciya ta shiga saukewa, haƙiƙa taji takaicin halin da taga dr shureim dinta da aunty benazir, ta shiga damuwa tabbas tana ji aranta wani mummunan abunne ya ta6a faruwa da su, a ƙagare ta ke da son jin wacece Yarinyar benazir dinta? Sannan kuma wacece matar da taji yaya shureim dinta yana magana akai har yake fadin bazai samu madadinta ba koda ace yayi aure, burinta ayanzu shine taga hoton matar da ya shureim yake nunawa benazir a wayarsa.

Da wannan tunanin ta nufi dakinta dake acan upstairs.

Bayan fitar zeenatu, dr shureim da Benazir suka miƙe tsaye suna fuskantar mahaifiyarsu dake binsu da kallon mai tattare da alamar tambaya.

“Meke damunkune? Ya akai naga fuskokinsu sun yi ja kamar wadanda suka yi kuka”! Tambayar data fara jefa masu kenan

Benazir ce tayi kokarin cewa”Ni da ya shureim ne muke yin firar yaushe rabo, mun tuna da rayuwar mu ta bayane kafin mu rabu”

“Hmm, yakamata ku manta da abunda ya wuce, tuna bayan nan baida amfani, tun da ba abun arziƙi bane ya faru”

Dr shureim yace”hakane mommy, zamuyi kokarin yin hakan”
Shiru tadanyi na wani lokaci tana kallonsu.

Har dai Benazir ta fahimci kamar akwai wani abu dake akasan zuciyar mahaifiyar tasu
“Mommy, kina son yin magana damu ne”?
Girgiza kai tadanyi kafin tace”tausayin rayuwarku nake ji, ina jin fargaban ranar da zan mutu in barku a duniyar nan mai cike da ruɗani, saboda mahaifinku bazai iya tsaya maku ba, shi kanshi juya shi akeyi.....” jikinsu ne yai sanyi jin abunda tace, tamkar tana basu wasiyya ne, matsawa tayi kusada su tare da ruƙo hannayensu acikin nata.

“Bazan 6oye maku ba, ji nake kamar wani abu zai faru”

“Mommy ki daina fadin hakan, Ki kwantar da hankalinki, Allah yana atare damu, ni bana so naji kina zancen mutuwa” dr shureim ne yai maganar.

“Addu’arki kadai muke buƙata mama, kidaina sanya damuwa aranki” benazir ce ta fadi hakan.

Gyaɗa kai Mom layla tayi”shikenan nadaina, Benazir yaushe zaki je gidansu Aneelerh?
Murmurshi benazir tasaki kafin ta bata amsar tambayarta dr shureim ya riga ta fadi “zuwa jibi in sha Allah, zan kaita gidan dakaina”

Mom layla tace”naji dadin jin hakan, zanyi magana da mahaifinku shi yake da layin mahaifin Aneelerh, in yaso saiya fada mashi game da zuwanku, tun da babu wanda yasan gidan nasu, sai sun tura mana da adress dinsu.

Benazir tace”hakan yayi mun gode mommy, ki kwantar da hankalinki, don na lura kamar bakya jin dadi”

Murmushi mom layla tasakar masu, lokaci ɗaya kuma yanayin fuskarta ya canza ganin wani abu ajikin benazir, harta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa tana kokwanto acikin zuciyarta.

“Mommy lafiya”? Benazir ce ta fargar da ita, ganin ta ƙura ido tana kallon wuyanta”
Girgiza kai tayi’bakomai, bari na koma daki, namanta banyi azhkar ba, Ina fata kuma kunyi naku, koda yake nasan ma shureim yayi ke fa”? Ta fada tana kallon benazir hankalinta yafi karkata akan jan ta6on da tagani gefen wuyan benazir kamar Yakushinta akayi fatar wurin duk ta karkarce.

“Nayi mommy, bayan na kammala sallar asuba”
Jim ta danyi kafin tace”okey, ku cigaba da firar ku, amma dan Allah adaina tuna bayan nan”
Murmushi kowan nan su yasaki, insha Allah mommy”

Juyawa tayi ta nufi kofar fita dakin, zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, ta rude da abunda tagani, tambayoyi ta shiga jefa ma kanta me yakawo jan tabo da sahun yakushi saman wuyan benazir?
Da wannan tunanin ta nufi dakinta.

(Abunda ya faru bayan Big guy ya fita neman hannah)
Chapter 131 · 0% Book details