Sashe 97
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dafa ƙofar glass din Nayi da hannuna ɗaya, Na’ura ta tantance ni aka bani iznin shiga ciki, Slowly glass din Ya soma zugewa, Na baza ido ina kallon tsaruwar Falon da kallon shi kaɗai zai Iya faranta zuciya, launukan painting cikinsa black, gold and white, An ƙawata shi da manya manyan sectional Chersterfield sofas, saiti biyu ne a palourn, Ƴan ubansu masu numfashi masu tafshi da daɗin zama ga jerin Throw pillows launuka daban daban saman kowace sofa, daga tsakiyar Katafaren falon wani faffaɗan Glass table ne daga saman shi an ɗaura flowers Vase, Furannin har ƙyalli suke Yi masu launi daban daban, bayan haka a kowani sofa hand din akwai Round glass table, mai dauke da kayan ƙyale-ƙyale na ado, daga saman jigunan ceilling din falon wasu ƙayatattun Crystal chandeliers ne masu girman gaske, An ƙawatasu da ado, kusan guda Uku ne a saman silin din, Haskensu Ya mamaye ko’ina tamkar da rana, Idan ka kalle su sai ka yi tsammanin zasu rubzo maka saman kai, sobada girman su, ga wata faskekiyar flat screen tv wadda idan kana kallo da ita sai ka yi tsammanin mutanan ciki zasu fito waje saboda girmanta, Bayan sofas din falon akwai hamshaƙan armchairs har guda biyu, hatta saman floor din falon Kayan adone aka ɗaura samansu, sparkling floor lamps ne ajiye a kasa suna bada nasu hasken mai ƙyalƙyali, akwai Kayan jin sauti, Ga Dogayen labulaye dake kewaye da falon an zuge su, A ƙalla Part din Yana ɗauke da Faluka sun kai Uku, bayan wanda na zayyana ma ku, daga cikin falon farko kana Iya hangen furniture din da ke a cikin falo na biyu ta hanyar Glass window, komai zaka Iya gani, Gidan fa Ya haɗu Ga glass elevator gefen twins stairs din dake a falon, ta ko’ina sanyayyan sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikin bil’adama mai ni’imar gaske, bayan haka ta cikin glass din falon zaka Iya hango Sashen da tanƙameman swimming pool din gidan Yake, ruwan dake acikinsa launin sky blue ne, da wasu kujerun shaƙatawa a gefenshi, da sauran ababen more rayuwa, Idan muka koma Dining room wato ɗakin cin abincin gidan abun ba’a magana, shima a kewaye yake da floor-to-ceilling glass windows, kana Iya hangen abubuwan dake wakana daga wajen ɗakin cin abincin, An ƙawata shi da haɗaɗɗun dining tables, na farko zungureren table ne mai mazaunin mutun goma sha biyu, da me mazaunin mutun shidda, da kuma tabur mai mazaunin mutun uku, kowan nan su saman shi an ƙerashi da zallar glass, ƙafafuwansu kuma wooden legs ne, wasu haɗaɗun gujerune kewaye da tables din, daga saman ceilling din ɗakin cin abincin ƙaton kwan fitila ne ke haskaka cikinsa, ga kuma Zungureriyar floor lamp, Itama nata hasken Daban Yake, agurguje zamu leƙa Cikin Bedrooms din dake a part din, A ƙalla ɗakunan kwanan dake a cikin part din sun kai goma sha biyar, Just for one part, ƙofar shigar kowani ɗaki ta glass ce sai dai baka Iya hangen abunda ke ciki idan har na cikin ɗakin ya zuge curtain dinsa ba, ƙofar da kanta take zugewa da zarar mutun Ya kusance ta take sliding a hankali, Idan ka shiga ɗakin idanuwanka zasu fara Yin Arba da wallpaper ta bango mai matuƙar jan hankali, kowani room Yana ɗauke da hamshaƙan king-side beds masu tausasan Katifu kalar wanda ko mutun bai jin bacci idan Ya hau su sai dai aji sautin minsharin shi, saman gadon shimfiɗe yake da tausasan bedsheet, da jibgegen bargon lullu6a kafi mage laushi, ga jerin matassan kai daga gaban gadon.
Gefe da gefen gadon nightstands ne, wadanda ke ɗauke da bedside lamps, daga bakin gadon faffaɗan wooden table ne mai ɗauke da drawer chest a jikin shi, ga wani haɗaɗɗen rag carpet shimfiɗe ƙasa mai dumbujejen gashi gashi ajikinshi tsaf mutun zai Iya kwanciya saman shi saboda laushinshi, ga wani ƙayataccen dressing mirror gabanshi haɗaɗɗiyar kujerace, daga can cikin ɗakin akwai dressing room, aljannar duniya kamar ka shiga company saboda haɗuwar Large walk in closet din daya mamaye kowani bango na dakin sanya suturar, suturun sanyawa ne an jera su, daga waje zaka Iya ganin kayan dake a cikin closet din, 6angaren Kayan bacci, dana Dogayen riguna, 6angaren english wears dana atamfofi ga laces, da jerin coat, ga 6angaren takalma kala kala, dana jakkuna, kai komai fa an zuba shi babu ce kaɗai ke babu, shima ɗakin Yana da nashi dressing table, mai ɗauke da oval-shaped mirror, Mai Kyan gaske.
Ataƙaice Idan fa nace zan tsaya zayyana daular Owais sharafudden tabbas zamu ƙare littafin akan bayyana kyawunsa, sai dai mun shiga cikin labarin sannu a hankali zan ƙarasa zayyana maku haɗuwar wasu 6angarorin na gidan.
*CHIEF OWAIS✊*
Gajiyar tafiya ta hana shi ta6uka komai, ga6o6in jikinsa sunyi mashi nauyi, tun da ya fito daga bathroom yake a kwance saman katafaren king bed dinsa, ya lullu6e surar jikinshi da Cashmere robe launin dark navy, Iya gwiwarsa rigar ta tsaya mashi, ya ɗaure igiyarta daga saiting flat waist dinsa, mutumin fa akwai ƙirar ƙarfi, Kyawawan idanuwanshi A lumshe suke tamkar maiyin bacci, Yalwatattun eye lashes dinsa sun kwanta luf, a hankali Yake motsa soft thin lips dinsa tausasa launin pink, dogon hancinsa Yayi tsaye babu lanƙwasa Yayin da yake fitar da numfashi cikin kwanciyar hankali, ya zagayo da hannun shi ɗaya ta saman yalwatacciyar sumar kanshi, ba za ka ta6a gane a wani yanayi yake aciki ba, ya tada kansa asaman tattausan pillow.
Alert ne ya shigo wayarshi, tamkar baisan motsawa A hankali ya miƙa ziraran yatsun hannunsa na dama ya janyo wayar dake ajiye saman nightstand, daƙyar yake iya buɗe eyes dinshi akan screen din wayar, Doorbell alert ya gani alamar wani yana son shigowa room dinsa, unclock button ya danna, a hankali ƙofar room ɗin ta zuge, mutun biyu ne sanye cikin kakinsu, baƙaƙen kaya, dogon wando tare da black shirt, daga sama sun ɗaura long coat, kowannansu ya 6oye fuskarshi da face mask, idanuwansu ne kaɗai zaka Iya gani, suna da faffaɗan ƙirji, agaban gadon shi suka dakata da yin tafiya, cikin girmamawa suka haɗa baki wurin furta
“Barka da safiya Yalla6ai, fatan ka tashi lafiya, Ya gajiyar tafiya” tun da suka fara magana basu ɗago da ido sun kalle shi ba, saboda a ƙa’ida shi ba’ayi mashi magana ana kallon cikin idon shi, hakan babban laifi ne.
Bai da niyar yi masu magana, bai kuma buɗe idanuwanshi ba tun da ya lumshe su, aran su su ka ayyana yau qasaitar tashi ce ta motsa, kamar gumaka Ya shanyasu a tsaye suna jiran amsar shi, sai da ya mula yasha iska kamar baison motsa la66ansa Ya furta”Lafiya” muryarshi tamkar ana busa sarewa.
Big Guy yace”Sir, is there anything you need?” ya tambaye shi ne don shi a ƙa’ida ba’ayi mashi abun da bai ce yana so ba, ko da kuwa abinci ne ka kawo mashi duk mun yunwar da yake ji in dai bashi yace yana so ba to zai ce maka ka koma dashi inda ka ɗauko shi sai in yaga dama ya ke kar6ar shi”
Jin yayi shiru yasa Big Guy kuma cewa”yalla6ai zamu Iya yin magana ta waya”? Sai lokacin Ya ɗaga mashi kai alamar eh, ajiyar zuciya Big Guy ya sauke tare da kallon mutumin dake a gefen shi wanda suke kira Boss Man, murmushi su ka sakar ma junan su, sun ƙwammace su yi magana dashi ta text message saboda wahala yake basu in dai a baki zai furta masu magana.
Slowly ya ware reddish brown eyes dinsa akan screen din iphone dinsa, a tsanake yake yin typing.
Jin ƙarar shigowar message ta wayar Big Guy ne yasa shi yin saurin curo wayar daga cikin aljihun coat dinsa Ya duba abun da Chief ya rubuta mashi
_I need My breakfast right now_
cikin girmamawa big guy yace “I’ll bring it to you immediately,”
Ya faɗa tare da Juyawa ya fuce daga ɗakin, Boss Man daya ya rage a tsaye ya natsu yana jiran jin me zai ce.
A lokacin da bai yi tsammani ba, muryar Chief ta katse shi”Have a seat” wuri ya samu saman doguwar sofa din ɗakin Ya zauna
“Check your phone, I sent you a message.”
Ya bashi umarni.
Da sauri Boss Man Ya zaro wayarshi daga aljihu ya soma karanta saƙon chief din nasu.
“Ya kake fatan ka tashi lafiya” murmushi ya saki har saida ya ɗago dakai Ya kalli fuskarshi, Yana matuƙar yin mamakin girmama shi da yake yi duk cikin waɗanda ke aiki a ƙarƙashinsa shi kaɗai Owais Yake gatantawa, suna mutunci da juna.
“Lafiyalou Alhamdulillah, Ina fata kaima lafiya, don na lura kamar gajiyar tafiya bata sake ka ba” abaki Ya furta mashi maganar, shi kuma Ya bashi amsa ta text message.
“Nagaji sosai, amma alhamdulillah, lafiyata ƙalou, Ina fata ka leƙa wurin Ƴar taka, “
Still fuskar Boss man da murmushi yace”ban kaiga zuwa ba, Yanzu nake shirin shiga na duba ta”
Text ya rubuta mashi”Make sure you give her a big hug. I know you’ve missed her for a long time.”
Idanuwan shi ne suka cicciko tab da ƙwalla, tuni jikinshi yai sanyi, cikin sanyin murya ya furta”in sha Allah, zanyi hakan, daren jiya ko runtsawa banyi ba saboda jiran ƙarasowarku Nigeria, duk don saboda Inyi tozali da ita, sai dai ban samu damar Yin hakan ba, saboda Bayan nayi sallar asubahi a masallaci bacci Ya dauke ni, saida na shigo gida nake jin labarin ƙarasowar ku......” dakatawa ya ɗanyin da yin maganar, ganin text din da owais Ya tura mashi.
“Don’t let the tears fall from your eyes, Otherwise, I won’t let you see your daughter.” fashewa yayi da dariya jin abunda yace mishi, har saida ya ɗago ya dubi fuskar Owais, Hankali kwance sam idanuwanshi basa akan fuskar Boss Man ɗin.
“Kana da mutunci, shiyasa muke ƙaunarka, wallahi tunda nake arayuwata ban ta6a ganin matashin saurayi mai wadatar arziƙi, da kyau da asali, mara girman kai irinka ba, saboda kowa naka ne, babu ruwanka ka ji daɗin rayuwarka, bazan ta6a mantawa da alheran da kayi mun ba, nasan bazan Iya biyanka ba amma ina fata Allah Ya wadatani da abunda zan faranta maka da shi”
Tunda ya fara magana Chief owais Ya natsu yana sauraron shi, idanuwanshi akan screen din wayarshi.