← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 152

Sashe 143

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sanin nauyin jikin Danish yasa salsabeel nannaɗe hannun jallabiyarsa ya daddage Ya ruƙo kafaɗunsa da hannayensa ya juyar dashi ya fuskanci ceilling, still fuskarshi bata bayyana ba saboda yalwatacciyar sumar kanshi data rufeta.
Cike da zumuɗi prime minister yace da salsabeel”please, ka jinginar dashi kan headbored, Ka nannaɗe min sumar kanshi daga kan fuskarshi inason ganinshi da kyau”
Cikin girmamawa Salsabeel Ya amsa mashi da toh, Kafin Ya daddage Ya ɗago da Danish Ya jinginar dashi jikin headboard, A hankali Ya soma janye sumar kanshi daga kan fuskarshi,
Tunkafin Ya ƙarasa kau da sumar, Hankalin prime minsiter yai matuƙar tashi haiƙam, zuciyarshi ta soma harbawa da matsanancin speed, Yayin da idanuwanshi suka zazzaro waje, tamkar eye balls dinsa zasu fado ƙasa, haƙiƙa yayi matuƙar girgiza da ganin abunda idanuwanshi suke nuna mashi, kowa dake a ɗakin saida ya lura da yanayin da prime minister ya shiga na tsantsar mamaki da Al’ajabi, bashi ba hatta sheikh imam da Chief owais al’ajabine akan fuskokinsu.
Muryar prime minister na rawa ya furta”Sheikh...! Owais Kuna ganin abunda nake gani kuwa? a ruɗe ya furta maganar yana ƙarema fuskar Danish kallo.
Sheikh Imam da al’ajabi Ya gama kamashi, Baisan sa’dda ya furta”amma dai wannan yaron Jininka ne ko? don wannan yafi ƙarfin ace kamanceceniyace ta halitta sai dai ta jini, saboda kamanninshi sun 6aci dakai da kuma yarinyar wurinka Nazli, Tamkar kayi kakinsa, komai nashi kalar naka ne, tun da Allah Ya halicceni ban ta6a ganin kama irin wannan ba, gaskiya nayi mamaki.....”
Boss man yace”ai ba tun yau ba, nasha faɗama chief owais cewa Yaron Yana kama dashi, bani ba hatta abokanan aikin mu sun shaida hakan, sai dai wani abu daya ƙara ɗaure mun kai ayau, Yaron yafi kama da prime minister hateem, bai baro komai nashi ba, tun daga kan shape din bakinsu, dogon hancinsu da idanuwansu, Yalla6ai da zaka ga launin idonshi zaka sha ruwan mamaki, domin kuwa kalar nakune”
Dafe kai prime minister yayi da hannun shi ɗaya, Hankalinshi Yaƙi kwanciya da kamanninsu da yaron.
Gyaran murya salsabeel Yayi kafin ya soma yin magana yana duban su
“Ni kaina na jima ina mamakin kamannin dake a tsakanin Chief owais da Danish, komai nasu kala ɗaya ne banbancinsu launin fata ne da kuma tsayin sumar kai, wani iko na Allah sai gashi Yalla6ai Hateem Yafi kama da Danish”
Runtse ido prime minister yayi, baisan ya akai yake jin wani irin yanayin atattare dashi ba.

Muryarshi araunace ya furta”ban haɗa komai dashi ba, bani da alaƙa da shi, Yauce rana tafarko dana fara yin tozali da fuskarshi, amma meyasa nake jin wani abu agame dashi? Dan Allah ku fahimtar dani na shiga ruɗani, ya akai komai nashi kalar nawa”? Yana magana la66ansa na kerma.

“Owais ka faɗamin wanene Yaron nan? Su wanene Iyayenshi? Meyasa yake kama dani da ƴata Nazli”? Da kakkausar murya ya furta maganar saboda aruɗe yake da lamarin.
Shi kanshi chief owais din Ya kasa furta komai, Lamarin Ya ruɗar dashi ya rikirkitar mashi da tunaninshi, bai ta6a tsammanin kamanninshi da yaron sun 6aci har haka ba.

A hankali Ya soma yin taku Izuwa gaban Prime minister hateem dake dubanshi fuskarshi a yamutse.

Cikin kwantar da murya ya furta”Uncle, bamu da masaniya akan su wanene Iyayen shi, saboda bai dasu a halin Yanzu, da shi da ƴan uwanshi dake ahannunmu bamusan komai nasu ba, tamkar marayu suke a hannunmu, Yarinya ɗayace mukasan Mahaifinta tajuddeen” ya faɗa yana nuna Boss man da hannun shi.
Girgiza kai yaɗanyi numfashinshi na fita da huci yace”Owais kada ku maidani mahaukaci, nafasan me nake yi, taya za’ace babu danginshi? Kyakkyawan yaro kamar wannan?ni kawai so nake ku faɗamin meyasa muke Kama”!!! Ga dukkan alamu prime minister ya fara zaucewa, wata irin zuface take tsastsafo mashi saman goshin shi.
Hankalin kowan nan su Yana akanshi, owais baisan taya zai fahimtar da uncle din nashi ba, Miƙewa Sheikh Imam yai tare da nufar prime minister Ya tsaya agabanshi, tare da kai hannu ɗaya ya dafa kafaɗarshi, a tsanake Ya soma yi mashi magana
“Ka kwantar da hankalinka, yakamata ka fahimci abun da Awaisu Yake ƙoƙarin faɗa maka, su kansu basu da masaniya akan yaron, kaɗan daga cikin ikon Allah kenan, kowani ɗan adam yana da masu kama da shi A duniya.....” tunkan sheikh Imam Ya ƙare maganar, prime minister yace”baba, wannan yafi ƙarfin ace kamace kawai, ka dubi fuskarshi dakyau, tamkar anyi photocopy dina, kamar dai nina haife shi, Ina jinshi tamkar jini na, ƙaunar da nake yi mashi kaɗai abun dubawace, ta zarce misali, saboda shifa na kasa runtsawa adaren Jiya, na damu da shi fiye da tunaninku.........” gaba ɗaya sun rasa taya zasu shawo kan prime minister, a iya sanin su da shi bai ta6a haihuwar ɗa Namiji ba, balle ace yarom shine daya 6ata.

“Yanzu abun da za’ai, tun da kana ƙaunarsa kuma yaron baida iyaye, mai zai hana ka ɗauki ragamar kula dashi kafin komawarka canada? Wata’ƙil hankalinka zaifi kwanciya” acewar sheikh Imam, ya fadi hakanne donya kwantar masa da hankalinsa ganin irin ruɗun daya shiga.

“hakan yayi shiekh, Uncle ka ƙaddara cewa jininka ne shi, kana da damar da zaka Iya bashi kyakkyawar kulawa” Chief owais na ya furta hakan.

Kalamansu sun tausasa mashi zuciyarshi, har cikin ranshi Yaji dadin jin hakan.

“Inaso na taimaka mashi yayi wankan ya sanya sutura a jikinshi, zan kira ɗan uwana awaya don yazo ya ganshi, nasan shi kadaine zai ƙara tabbatar min da abunda nake gani a idona, sannan Idan yaron yaji sauƙi kafin in koma canada, zan je dashi gidana don in nuna ma gimbiyata shi da ƴa’ƴana nasan zasuyi mamakin kamanninsa dani musamman Nazli, hatta hasken fatarshi kalar nata ne” murmushi ne akan fuskokinsu, sunji daɗin sakewar da prime minister yayi, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yayi ba.

Naɗe hannun rigarshi yayi, tare da cire agogon azurfarshi, da zoben hannun shi, Ya miƙa ma owais su, da sauri owais ya sanya hannu ya kar6a, gaba ɗaya kallon shi suke da mamaki akan fuskokinsu.

Murmushin gefen fuska yasaki har dimple dinsa ya lotsa”kada kuga ina zumuɗi akanshi ƙaunarsa nake Yi” da zolaya ya furta maganar kafin yace” wazai taimaka min mu shiga da shi bathroom room”? da sauri Salsabeel Yace”ni Yalla6ai”
“Yawwa, ruƙo min shi mu shiga ciki, ko da ya ke naga yana da girman jiki zaiyi nauyi, bari na kama maka” a hanzarce Ya zagaya ta 6angaren da salsabeel Yake, a lokacin sabeel Yayi koƙarin janyo danish da ƙyar ya kawo shi bakin gadon.
Kafaɗunshi suka rurruƙe shi da prime minsiter suka miƙar dashi tsaye, wanda badan ƙarfin giant da sabeel yake dashi ba da kuwa babu mai iya ɗaga shi, jikin shi ya saki tamkar wanda baida ƙashi, kanshi ya kalli kasa sumar kanshi ta lullu6e fuskarshi, idanuwanshi suna arufe gam, zufa ta ko’ina take tsasstsafo mashi, a hankali suke tafiya dashi suna nufar toilet, har suka yi nasarar shigar da shi ciki’
Bayan shigarsu, sheikh imam ya dubi boss man da owais
“Inason ganin sauran Yaran da kuke ruko a hannunku”
Da sauri Boss Man Ya amsa mashi da toh, Ya miƙa ma sheikh imam rawanin shi daya ruƙe a hannunshi tare da hularshi, godiya yayi mashi, har ya juya zai fuce muryar chief owais ta dakatar dashi
“Boss, Ka tara yaran a main falo, Yanzu zamu sauko down”
Amsa mashi yai da toh, kafin yasa kai ya fuce daga dakin Ya sauka down.

A hanzarce yake tattaka staircases din benan, har ya kusa saukowa down yai tozali da big guy dake tafiya cikin takun sauri, ganin boss yasa shi fadin”Ya ake ciki mutumina?
Boss yace”Alhamdulillah Danish ya dawo ainihin suffarshi, Sai dai babu kuzari ajikinshi, Ko yatsanshi bai iya ɗagawa, ga tabonnin harbin bindigar da akayi mashi ta ko’ina saman fatar shi”
Cike da jin alhini Big guy yace”bawan Allah, banji dadin jin hakan ba, wallahi yaron tausayi yake bani, ashe munyi mashi illa da harbin bindigar amma ina fata baiji mugun rauni ba ko”?
Chapter 143 · 0% Book details