Sashe 84
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba ɗayan su suka sanya dariya, ban da Danish, sam babu kwanciyar hankali atattare da shi, Hakanan Yake jin haushin mutane babu gaira babu dalili, ji yake kamar ya rufe su da bugu har sai sun mutu. Su Batul kuwa duk sun sha jinin jikin su, ganin Jami’an Isod suke Yi tamkar mutanan prison, tun da suka shigo ko motsin kirki sun gaza yi, Sai faman binsu da ido suke yi, ko magana jami’an su ka yi sai sun razana babu wanda Ya lura da hakan.
Bayan Dr. mark ya kammala sanya mashi mask din, ya juya ya ruƙo hannun Angel acikin nashi, a jere suka nufi Hanyar fita daga ward din Yayin da dr laura da mark da brown suke Abayansu, su kuma jami’in Isod suna a kewaye da su, domin basu tsaro, duk inda suka gifta a sibitin ido na akansu, ba marasa lafiyan ba, ba ƴan zuwa dubiyan ba, ba Ma’aikatan cikinsu ba, kowa hankalin shi na akan su, Danish sai ƙara matse mata hannunta yake yi a cikin nashi, hankalin ta ba akwance ya ke ba don ta fahimci akwai wani abu dake damun shi.
Kaitsaye suka nufi parking space na asibitin, wasu danƙara danƙaran motoci ne masu numfashi jigunannun gaske, a killace a harabar, da su akazo ɗaukarsu, hankalin su Batul Ba ƙaramin tashi yai ba, Basu ta6a ganin abu irin wannan ba, Motocin dake a killace aharabar suke ta faman bi da ido, Angel ce tayi amfani da harshen hausa wurin yi masu magana akan su natsu kada su tsorata, abun hawa ne da akeyin anfani dasu wurin tafiya mai tsayi wadda ƙafa bazata Iya yinta ba, sai da tayi masu bayani cikin kwantar da murya tukunna suka fara sakin jikinsu.
Kafin su shiga motar sai da aka fara sanya kayan su a boot, akwatuna ne da duffle bags kusan guda biyar, Suturar da dr laura ta siya masu ce, tare da Takalmansu da magungunan da zasu dinga sha, da sauran care product da zasu yi amfani da su. Bayan an kammala shigar da kayan cikin motocin ɗaya bayan ɗaya jami’an suka bude masu car doors din, motar farko Danish ne da Angel sai Batul suka zauna a mazaunin Baya, Mota ta biyu Gabriel ne tare da Haris da Hanna, Mota ta uku Naufal ne da parveen sai Javed.
Dr. laura ta nemi alfarmar jami’an akan tana son su bata damar ɗaukar jemimah da Azeeza a motarta, Jami’an suka ce mata zata Iya ɗaukarsu ba wani abu, A back seat na motarta, Azeeza da Jemimah suka shiga, Ita kuma ta zauna A driver seat domin Yin driving dinsu, Dr mark da dr bown suma hada su za a tafi kaisu airpot din, A cikin motocinsu zasu tafi tare da Nurse jessica da rebecca.
Tun da prisoners suka shiga cikin mota, suke ta ƴan kalle kalle wa yaga baƙauye yazo birni, duk sun sha jinin jikinsu, Fargaba suke Yi kada a cutar dasu, badan Angel ta kwantar masu da hankalinsu ba, da kuwa Anga hauka, kusan A lokaci ɗaya masu tuƙa motocin suka tada su, Jemimah ta rungume Azeeza jin sautin tashin motarsu, Jikin su ya hau yin kerma kamar waɗanda sanyi ya kama, Dr laura dake kallonsu ta madubin motar, fuskarta ɗauke da murmushi ganin yadda suka ƙanƙame tace masu su kwantar da hankalin su, babu abunda zai same su.
A motar su Parveen Ta ƙanƙame naufal saboda tsoron da taji, hada javed sun haɗu sun mannewa juna kamar kifayen gwangwani.
A motar su Gabriel kuwa, Hannah da Haris sun ƙanƙame shi, sai faman tiƙar dariya yake yi, shi dama wayayye ne bakomai ne Ya manta na memory dinsa ba, Hannayen shi biyu ya sanya saman bayansu Ya ƙara tighting dinsu ajikinshi yana kwantar masu da hankalinsu.
Danish kuwa tun da suka shiga motar, ya kwantar da kanshi saman kafaɗar Angel, ko motsi baiyi, Yana zaunea left hand dinta, yayin da Batul take a zaune saman seat din dake a right hand dinta, Ganin yadda Batul ta ruɗe jin tashin mota, Hannayenta biyu ta ɗaura saman kanta, kamar zata fasa ihu da sauri Angel ta damƙo hannunta tare kwantar mata da kanta saman laps dinta, ƙanƙameta tayi sosai tana faman sauke ajiyar zuciya, abun ne yazo masu wani iri basu saba ba.
Slowly motocin suka nufi hanyar babban gate din asibitin, gaba da bayansu motocin Jami’an isod ne, Sun sanya motocin da aka ɗauko su dana su dr. laura a tsakiyar nasu motocin domin basu tsaro.
Da matsakaicin gudu motocin suka haura saman titi, prisoners sun ga abunda yafi ƙarfin idanuwansu, Ta glass din window su ke Hangen danƙara danƙara gine ginen birnin san antoni, masu ƙayatarwa, ga wuraren shaƙawata da kuma mutanan dake zarya ta ko’ina, sun natsu suna kallon ikon Allah abun ya ɗaure masu kai.
“My man, bacci zaka yi”? angel ce tayi mashi magana tana duban fuskarshi, tayi mamakin ganin zufa na tsastsafo mashi saman forehead dinsa, duk da sanyayyan Sanyin A.c na motar, Batool tuni ta miƙe daga saman laps din Angel, ta koma bakin windown motar tana kallon Ikon Allah.
In a low voice ya furta mata”Am not feeling well, ina jin wani iri a jikina kamar wani abu zai faru dani” shafa sumar kanshi tayi da hannunta”In sha Allah ba abunda zai faru da kai My Man, Ina atare dakai, so ka kwantar da hankalin ka, bari nayi maka addu’a” ta faɗa haɗi da manna la66anta saman lallausar sumar kanshi, addu’o’i ta soma karantowa tana tottafa mashi asaman kanshi.
Muryar Batul ce ta katse mata hanzarinta”Angel wai su mutanan duniya dama haka suke da gudu kamar zasu tashi sama”?
Dariya ce ta kubcewa Angel, ta wurga idonta kan batul data mannewa glass din tagar motar, ta ƙura ido tana kallon al’amurra.
“Batul ba mutane bane suke Yin gudu, Abun hawan da muka hau ne ya ke yin gudu damu”
Ba tare da batul ta juyo ta kalle ta ba tace”Oh, yanzu na fahimta” daga haka bata ƙara cewa komai ba.
*UMMIN AMERICA💋*
A hankali motar su take tafiya saman shantalelen titi, tana a zaune saman front seat, ta ɗauki wankan pant suit sunyi bala’en yi mata kyau, dogon wandone fari da sexy vest fara ta matse ta kirjinta Ya fito sosai, don ma ta ɗaura Blue coat daga sama, ta canza launin sumar kanta zuwa blue, light make up ne asaman face dinta , fararen idanuwanta suna a manne da farin glass hakan ba ƙaramin ƙara mata kyau ba, Matar dake driving dinta, ƙawarta ce *NATASHA* baturiyar England, Aminnan junane, sai dai daga ganinta babu digon imani a zuciyarta, fitsararrace ta bugawa a jariga. Kayan dake a jikinta da su da babu duk ɗayane, doguwar rigarta tamkar net take shara shara kana Iya hangen inners din ta, A yayin da take zaune saman driver’s seat, Cigrette ce a hannunta na hagu, ɗayan hannun kuma da shi take juya sitiyarin motar daga gani ta ƙware a iya driving, Tsabar Iya shan taba harta hanci ta baki take huro hayakinta.
fira suke ɗan ta6awa a tsakaninsu cikin harshen turanci.
“Zanyi kewarki ummi, yanzu idan kika tafi yaushe zaki dawo? Natasha ce ta jefa mata tambayar.
Numfasawa tayi kafin calmy ta furta “bazan daɗe ba, temporary guardianship ne ba permanent ba, da zarar na kammala yi masu aiki zan dawo America”
Dariyar shaƙiyanci Natasha ta saki, tana mai cigaba da hura hayakin tabarta.
“idan ki ka yi wata ɗaya baki dawo ba, zan biyoki Nigeria don bazan Iya jure rashin ki ba” ta fada tana duban fuskar Ummi.
“Zaki tafi ki barni da mutananki, don nasan ba zasu ƙyaleni ba, da zarar sunji ki shiru ni zasu tuntu6a,” Ummi tace”Zaifi ki canza layin wayar ki, kafin in dawo, don bana so kowa yasan da zancen barina ƙasar nan ko kuma inda zanje, Yana daga cikin sharuɗɗan da sojoji suka gindaya mini.”
“Ai nayi mamaki da kika amince zaki kar6i jagorancin kula da yara har goma sha ɗaya, idan nice bazan Iya ba, kema nasan ba hakanan kika kar6i aikin ba. akwai wata manufa a ƙasa” ta ƙare maganar tana dariya.
Ummi tace”kamar kin shiga zuciyata, tabbas inaso naje Nigeria ne don karan kaina bawai don aikin da sojoji suka bani ba, nima akwai abun da zai kai ni, da ba don haka babu abun da zai sa in bar America.
Natasha tace”yayi kyau mutuniyata, ina fata zaki cigaba da sheƙe ayarki, bana so silar zuwan ki ƙasarki ki shiryu nafison ki ƙara lalacewa ki 6ata masu mazajen auransu,” dariya suka sanya gaba ɗayansu.
Ummi tace”Yaran fa da aka bani in jagoranta kyawawane fa akwai wani zazzafan Yaro acikinsu, yana da kyawun sura” lumshe ido natasha tayi muryarta tamkar ta mashayin giya tace”kice yaron babbar harka ne, tun kafin ma in ganshi na ƙyasa”
Ummi na dariya tace”yadda kike shaiɗaniyar nan nayi imanin idan kika ganshi daƙyar zaki Iya runtsawa, kallon shi kaɗai zai tada maki da maitarki, Natasha nayi mu’amala da maza kala daban daban amma shi wannan Yaron na musamman ne, Kamar dai Chief Owais, kinsan shima Yana da zazzafar sura.
Natasha tace”Har yau ban daina kallon hotonshi ba saboda bana gajiya, aduk lokacin dana rasa abokin harka hoton shi nake kallo in rage zafi, gayen ya haɗu duniyace shi” cikin jin shauƙi Tayi maganar”
Ta ƙara da cewa”ƙawata zan baki shawara, matasan Yaran da za’a baki rainon su, kada ki raga masu, idan jarabarki ta motsa kibiya buƙatarki da su, ai ke wannan Aikin da sojoji suka baki gaba ta kai ki, in banda abunsu sun ta6a ganin inda aka ba kura ajiyar nama”? Da shaƙiyanci ta faɗa tana sakin shu’umin murmushi na tantiran ƴan duniya.
Ummi ta ɗan zaro ido haɗi da cewa”ba zai yiwu ba natasha, ke kin san wanene Chief owais, yafi bomb bala’i, akan shi na fara jin tsoron namiji a duniyar nan, Mutumin bai da fara’a Yana da kamun kai, sannan bai da imani idan ya damƙi Mara gaskiya, idan har na kuskura na ƙetare Iyakata akan Yaran wlh tsaf zai Iya kasheni har lahira, ni ko dai ban shirya mutuwa ba, akwai sauran bururrukan da nakeson cimmawa.