← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 152

Sashe 51

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga ɗakin Ringing wayar Aneelerh Ya daki dodon kunnan shi, Da sauri ya nufi wayar dake Ajiye saman pillow Ya haye gadon ya janyo ta.
Jikinshi har kerma yake yi wurin yin Picking call ɗin ya kara wayar a kunnanshi.

Da ƙarfi Ya furta”Wanene”? Shiru ba”a tanka masa ba.

Hakan baisa ya fasa yin maganar shi ba

“Mommy bata nan tana a palour suna magana da su Abie, I’m the only one in the room.” still ba’a tanka mashi ba, Surutu Yaci gaba da Yi

“Angel ce ke kira”? Shiru ba amsa”Sister Angel, say something! It’s your brother, Baby Junaid. I miss you so much”

Da shagwa6a ya yi maganar, Sai lokacin Muryar mutumin da ya kira a wayar ta bayyana da sauti mai matuƙar Ratsa zuciya.

“Where is the owner of the phone?” ta6e baki Junaid yai”ai na faɗa maka tana a palour”
“Okey ina son yin magana da ita, ko zaka Iya kai mata wayar” Tuntsirewa Junaid Yai da dariya yana faɗin”a’a Sai dai ka yi magana dani, sai in faɗa mata”
“Pls ka kai mata wayar, “ maƙe kafaɗa Junaid Yai kamar yana agabanshi”ni dai a’a, Ka faɗamin sai in faɗa mata saƙon”

“Shekarunka nawa”? Ga dukkan alamu wanda ya kira wayar ya fahimci ƙaramin yaron ne ya ɗaga tun daga kan voice ɗinsa.

“Huɗu Biyar shidda” Sautin dariyar mutumince ta ratsa kunnan junaid.

“No wonder ashe babban mutun ne kai, zamu iya zama abokai” maƙe kafaɗa junaid yai”to aini yarone kai kuma babba”.
“Okey yanzu faɗamin Ina yayarka Angel”? Kwa6e fuska junaid yai cikin muryar shagwa6a yace”ta 6ace 6era ya cinyeta ita da daddynta da daddyna sun mutu nima mommyna ta faɗa min” sosai mutumin Ya fashe da dariya, jin wautar Junaid

“Ka hana Ni Yin magana da mommynka, gashi kanata cinye min kati”
“Ae nace ka faɗamin saƙon sai In gaya mata” mutumin yace”Okey, ka faɗa mata DADDYN UNAISAH NE ya Kira”!

“To zan faɗa mata Sai anjima” Yana kai ƙarshen magana Yai rejecting call ɗin tunkafin mutumin yai mashi sallama, Pillow Ya janyo ya zuge zip ɗin Ya curo ring box ɗin Yana Kallon zoben
“Na Angel ne wannan, Bazan bashi ba Allah tun da ya cinye min chocolate ɗina” Yana magana yana ta6e la66ansa.

Shigowa Mahboob Yai cikin palourn Hannun shi ruƙe da Kyautar wani abu Mai faɗi an rufe shi da wrap sheet mai Ƙyalƙyali, Karasowa Yai agaban sofas din da Uncle Abdallah Yake zaune Ya sauke gift ɗin kafin ya miƙa mashi key ɗin motar, Kar6a Uncle Abdalla yai”nagode sannu da ƙoƙari” muryarshi ƙasa ƙasa Ya amsa da”yawwa” Juyawa yai da sauri Ya nufi Sashen kitchen ganin Ana na zarya kai abinci a dining.

Tunkafin a buɗe Kyautar kowa Ya ƙagara da son ganinta, musamman zahra ta ƙura idanuwanta kamar na mazuru.
Ummi na murmushi tace”masha Allah wannan kyauta tunkafin abuɗe mun fara zumuɗin ganinta” Mami tace”ni kaina a ƙagare nake Allah”
A hankali Uncle Abdallah Yake warware wrapping sheet ɗin, slowly Kyawawan idanuwanta dara dara suka Fara Bayyana, da mamaki su ke Kallon juna cikin rashin fahimtar wacece wannan Kyakkyawar Matashiyar.

Lokacin da ya warwaro wrapping sheet ɗin dai dai Saitin hancinta ya ƙarasa 6an6are ledar gaba ɗayanta, adai dai time ɗin Mahboob da Ana sun fito daga kitchen Hannun shi ruƙe da glass Na lemu Karaf Idanuwanshi suka sauka akan Hoton zanan fuskar Angel, Nan take ya saki glass ɗin hannunshi gaba ɗaya ya tarwatse ruwan lemun dake acikinsa ya tsiyaye saman tiles.

Tsabar Al’ajabi da mamakine Yasa Aneelerh da mami Yunƙurawa a sukwane suka miƙe tsaye Suna ƙare ma Zanan Kallo Yasha fenti kamar horonta aka ɗauka.

Gaba ɗaya sun Rasa bakin magana, zanan yayi bala’en Yin kyau, fuskar Angel ta fito raɗau Kyakkyawar matashiyar balarabiya bugu da ƙari buzuwa a 6angaren Mahaifinta” Zahra Ko sai faman Yarfa hannu take yi tana ambaton Wow wow Tabarakallahu ahsanul khalikin! Gaskiya koma wanene portrait artist ɗin da ya zana hoton nan ba ƙaramin ƙwararre bane ya baje basira”

Ummi tace”Masha Allah, Yarinyar ba ƙaramar kyakkyawa bace, kamar tajuddeen Ya yi kakinta, Kamanninta sak Kalar nashi, Hasken fatarne ta ɗauko Na mahaifiyarta benazir”

Lamarin ya ɗaurewa Ana kai Ganin yadda Mahboob Ya fasa glass cup ko ajikin shi, Hankalin sam baya atare dashi, Zanan Fuskar Angel Ya tafi da Imaninsa, dama can tun fil azal Mahboob Mayen mata ne.

“Mahboob Meke damunka ne? Baka ga 6arnar da ka yi ba ne’?

Ba tare da ya kalli fuskar Ana ba Ya furta”dama akwai matan Hurul aini A duniya”?

Girgiza kai Ana ta yi Fuskarta ɗauke da murmushi ta nufi dinning, don ta jera kayan tray din hannunta.

Farin Ciki Ya hana Aneeleeh furta kalma, agaban zanan da ke a jingine jikin hannun sofa, ta zuƙunna saman gwiwowinta, yatsun hannayenta na kerma ta ɗaura su saman fuskar Angel, Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka ta kifa kanta saman zanan

“Haba Aneelerh menene abun kuka? Ke da za ki yi farin Ciki”? Mami ce tayi maganar

Hajiya adama ta miƙe ta nufi Aneelerh ta ɗan ranƙwafa ta ɗaura hannunta saman kafaɗarta.

“Share hawayen ki Aneelerh, banaso pls, Ni ban Kawo maki zanan nan don ki yi kuka ba, saboda farin Cikin ki yasa Nasa aka yi min shi, nasan zaki ji daɗi sosai” Abie yace”in dai ko bazaki daina kukan nan ba, zansa su koma da zanan” sai lokacin ta ɗago da rinannun idanuwanta da suka kaɗa jawur ta kalli fuskokinsu cikin shessheƙar kuka tace”Nadaina, wlh kukan farin cikine Ya kubce min, Inason Angel sosai, na kasa jurewa ne, da na ga zanan nan sai naji na ƙara ƙagara da son ganinta a shekarunta Na yanzu” Mayar da idanuwanta ta yi a kan hoton

“Allah sarki my Angel, ɗiyata ƙanwata kuma ƙawata abokiyar firana, Na yi missing ɗinki sosai bazan ta6a mantawa dake ba har abada” Kifa kanta tayi saman hoton Hawaye suka cigaba da wanke fuskarta, ta yi matuƙar karya masu zuciya.

*Middle step A gidan Alhaji ubaid*

Tun lokacin da Dr. shureim Ya kammala kimtsawa ya zauna gefen gadon shi ya natsu yana kallon hotunan abar ƙaunarsa, Ƙarfe Goma sha Biyu Na bugawa, Kiran Alhaji musa Ya shigo wayarsa.

Da sauri Yai picking call ɗin Ya kara a kunnanshi

“Shureim Ina Jiran ka a palour!”

Abun da Ya furta mashi kenan, Ajiyar zuciya ya sauke Tare da miƙewa Ya fito daga Bedroom ɗinsa, Yana mai jin kewar ɗakin nashi, tafiya yake yi tamkar bayason Taka ƙasa, Ji yake kamar In yabar gidan zai ƙara nisanta kanshi da ita ne, duk irin yadda yake zumuɗin barin gidan hakan bai hana wani sashe na zuciyarshi ƙin amince masa ba, Saboda acikin gidan ne, abar ƙaunarsa ta kafa tarihi acikin zuciyarshi.

Lokacin da ya ƙaraso palourn, A zaune ya samu Alhaji musa da Uncle ubaid, Sai Mahaifiyarshi laila Da Mai aikin gidansu zainab, Hannunta ruƙe da shopping bag.

Yanayin fuskokin su Ya nuna alamun rashin jin daɗin tafiyar shi, musamman mai aikin gidansu zainab da kuma Mahaifiyarshi Layla, tana a tsaye ta ruƙe qugu fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin zallar 6acin raine.

Shi ko Alhaji ubaid sai faman sakin fara’a ya ke yi babu alamun zaiyi kewar ɗan nashi idan ya tafi.

Idanuwan dr. Shureim akan na mahaifiyarsa, da sauri ya nufi inda take atsaye, hannu biyu ta sanya ta rungumo shi a ƙirjinta, hakan da tayi mashine yasa shi jin hawaye sun cicciko idanuwanshi.

Bubbuga bayanshi take yi a hankali tana faɗin”Shureim ɗina, zanyi missing ɗinka sosai, naji takaicin tafiyar nan duk da ba wani wuri zakaje me nisa ba, sai dai sam hankalina bai kwanta da tafiyarka ba, Naci burin In gatantaka In baka kulawa ta musamman tuntuni, sai dai rashin zamanka agida da kuma gudunmu da ka ke yi, shi yasa ban samu damar yin hakan ba, Yanzu kuma na samu na shawo kanka, an nuna anfini iko da kai za’a rabani da kai,’ tun da ta fara magana Alhaji musa Ya haɗe rai fuskarshi a tamke ba annuri, don yasan dashi take magana.

“Mommy ki samin albarka ita nake buƙata daga gare ki, Sannan ki kwantar da hankalinki, Ni musulmine kuma nayi imani da Allah dashi na dogara, aduk inda zan kasance Allah yana atare dani, ballanta kuma agidan Uncle ɗina ne ba nisa zanyi ba, nasan za ku dinga zuwa akai akai kuna ganina, Nima kuma zan dinga zuwa gida” Maganar Dr. shureim ta yi matuƙar karya mata zuciya, Allah na gani tana son ɗanta sosai, Muryar Alhaji musa ce ta katse su”shureim bamu da isashen lokaci, ka wuce mu tafi”

Ɗagowa Yai daga jikin mahaifiyarshi ido cikin ido suke kallon Juna, Canza harshe ta yi zuwa larabci kafin taci gaba da magana

“Shurem hankalina bai kwanta da kawunka ba, Ni ban yarda dashi ba, Bai ta6a nuna damuwa akanka ba, tun lokacin da ƙaddarar nan ta risƙe ka har ka fara shaye shaye a ƙarshe ma kabar ƙasar gaba ɗaya, musa bai ta6a bibiyar rayuwarka ba, babu ruwanshi dakai Ƴa’ƴanshi kaɗai Ya sani, Ta ya ya hankalina zai kwanta da zuwan ka gidan shi? Allah kaɗai yasan mugun nufin shi akan ka” Tana magana tana shafa sumar kanshi da ta sauko saman wuyanshi, babu wanda Yasan me ta ke cewa, dama da biyu ta yi mashi maganar da larabci don saboda tasan basa Jin Yaren, mai aikinsu kaɗaice ta ke ji saboda itama balarabiyace, jikin zainab duk yai sanyi da jin maganar Hajiya layla, baiwar Allah duk ta damu da Shureim gani ta ke yi kamar idan ya tafi wani abu zai faru dashi.

Muryarshi araunace Ya soma magana da harshen larabci”Mommy kidaina wannan tunanin dan Allah bana so, ki kwantar da hankalin ki, Uncle musa bazai Ta6a cutar dani ba, duk da bai damu dani ba a lokacin baya, yanzu ya nuna yana ƙaunata zai Iya yiwuwa ko dan saboda tausayin halin da nake aciki ne, Nafi so ki yi mashi kyakkyawan zato mommy”

Gyaɗa kai ta yi “Shikenan shureim zan cigaba da yi maka addu’a akan Allah ya kare mun kai ya tsaremun kai daga sharrin duk wani abun cutarwa” Cikin harshen labaraci ta dinga jero addu’o’i tana tottafa masa Yana amsawa da ameen.

Bayan ta kammala ya ɗago da ido Ya kalli zainab, idanuwanta sun cicciko tab da kwalla.
Chapter 51 · 0% Book details