← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 152

Sashe 52

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matsawa ya yi kusa da ita, fuskarshi ɗauke da murmushi yace”auntyna zan tafi asanyamin albarka” yai maganar tare da duƙar da kanshi, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, Ƴan hawayen da ta ke matsewa tuni sun soma shararowa saman kuncinta.

Tafin hannunta ta ɗaura saman arab turban ɗin dake naɗe akanshi, a tsanake take jero addu’o’i tana tottofa masa a ƙarshe ta ƙara da cewa”Allah yasa Silar komawarka can ka samu farin Ciki na har abada” Ya amsa mata da ameen ameen”Allah ya saukeku lafiya shureim” ya ƙara amsa mata da ameen

Daga Haka Ya juya ya nufi Mahaifinshi Alhaji Ubaid.

Fuskarshi ɗauke da murmushi yake duban shureim”daddyna, asanya min albarka”

Da buɗar bakin Alhaji ubaid sai cewa yai “Shureim sai ka ce zaka Bar ƙasar, irin wannan bankwana haka! Na lura Jikinka duk Yai sanyi, Ko kamanta Abuja ne zaka je gidan ƙanina”? Harara Hajiya layla ta jefa ma Alhaji ubaid a fakaice.

“Lokacin da ka ke ƴan guje gujenka ba tare da sanin kowa ba, Ka ke barin ƙasar nan sai yau don zaka tafi gidan uncle ɗinka kake Neman albarkarmu”?

Da mamaki akan fuskar Dr Shureim ya ke kallon Alhaji ubaid, Ran Hajiya layla ya 6aci A harzuƙe tace”Dan Allah Ya isa haka! Me yakawo wannan maganar? Saboda kawai yace ka sanya mashi albarka? Idan baza ka sanya mashi ba sai ka ƙyale shi Ya tafi, dama albarkar uwa aka fi buƙata, bata uba ba”

Runtse ido shureim Yai, Maganar daddynsa ta ta6a mashi zuciyarshi tuni ƙwalla sun Ciko idonshi, Hatta zainab ta ji ɗacin maganar Alhaji ubaid ji take kamar ta kikkifa mashi maruka a kuncinsa.

Still da murmushi akan fuskar Alhaji ubaid ya ke dubanta, kafin ya maida dubanshi ga shureim.

“Ka ji abunda Mommynka tace, babu buƙatar albarka ta, Don haka zaka Iya tafiya” cikin jin ƙunar rai Yace”daddy na roƙe ka, Ka sanya min albarka ina buƙatar taka”! hawaye tuni sun wanke fuskarshi, Jinjina kai Alhaji Ubaid Yai, Kafin Ya janyo Dr shureim Ya rungume shi, Yana tofa mashi albarka, Hankalin shi ba ƙaramin kwanciya ya yi ba.

Miƙewa Alhaji musa yai daga saman sofa ɗin da ya ke azaune, ko kallo basu ishe shi ba, Cikin takun nan nashi na izza, ya juya ya fuce daga falon don shi arayuwarshi Ya tsani 6ata lokaci.

Tsoki Hajiya layla taja aranta tace”abanza, Uban Ji da kai, ai ni da za ka burgeni, ka kama Hanya ka yi tafiyarka, kabarmin ɗana”

Ruƙo Hannun dr shureim Alhaji ubaid Yai, Yaja shi suka nufi Hanyar fita falon, Da sauri Zainab Tabi su Hajiya layla kam zama tayi dirshan saman sofa tana faman cije le6e.

Abakin Engry hall na gidan, Zungureriyar motar da zata ɗauki Alhaji musa zuwa airport tayi parking, Hamshaƙiyar gaske Ƴar ubansu mota mai numfashi.

Yana daga kishingiɗe a ɗaya daga cikin back seat na motar, tamkar yana acikin bedroon ɗinsa saboda tsabar haɗuwarta, slowly murfin motar ke zugewa Dr shureim na ƙoƙarin shiga ciki, Muryar Zainab ta katse masa hanzarinsa.

“Namanta da wannan, kai na haɗamawa” juyowa yai tare da kallonta, Ledar hannunta ta miƙa masa, fuskar shi ɗauke da murmushi ya kar6a Yana yi mata godiya, kafin daga bisani yayi masu sallama, yasa kai cikin motar, daddaɗan Sanyin a.c ya ra6i sassan jikinsa shi kanshi Ya yi al’ajabin haɗuwar motar.

Mutun Biyune agaban motar, Driver ɗinsa da kuma p.a ɗinsa wani gabjejen mutun mai ƙirar Ƙarfi daga gani yana gym saboda ko’ina na jikinsa a murɗe Yake, wankan suit ne a jikinsa Baƙi wulik baida fara’a a fuska.

Kaitsaye Airport Suka nufa, already An shirya mashi privet jet dinsa, Bayan shigarsu cikin jirgin wanda Tsayawa zayyana Haɗuwarshi 6ata lokaci ne, abune da hankali bazai ɗauka ba, saboda an kashe dukiya kamar ba asan zafin nemanta ba, Kai kace saman bishiya ake tsinko kuɗin ana amfani da su. (😂)

Dr. shureim Yaga aljannar duniya, Bayan tashin jirgin Cikin mintuna da basu wuci arba’in ba Suka ƙaraso Airport ɗin Abuja, Tun kafin jet ɗinsa ya ƙaraso airport ɗin tuni Escords ɗinsa sun hallara abakin motocin su cikin shiga ta baƙaƙen suits domin tarbarsu da kuma basu tsaro.

*EX-PRISONERS❤*

Tun Bayan da suka kammala Cin abinci kowan nan su yai kulu wash rabu hani’an, Nurse ta shigo ɗakin ta kwashe kayan abincin da suka ci ta fuce da su waje.

Gaba ɗayansu suna A saman gadon zazzaune Sai Yanzu su ka samu damar ƙarewa ɗakin kallo.

“Angel menene wancan”? Parveen ce ta yi maganar tana nuna mata plasma tv dake manne a jikin bango.

“Tv ce da ita ake yin kallo”
“To ki kunna mana mu gani mu ma” girgiza kai Angel ta yi”a’a Parveen ku bari sai munje gidan daddyna tukunna”

ta faɗi hakanne don tasan muddin ta kunna masu kallo zasu birkice mata ne, a ƙarshe ay abun kunya, tun da basu ta6a gani ba.

Tambayoyi suka dinga jera mata kamar ƴan jarida, komai na ɗakin sai sun tambayeta menene shi ya akeyin amfani da shi, ita kanta ba komai ta sani ba saboda ba kalar ɗakinsu na gida bane, Iya abunda ta sani take amsa masu.

“Zan shigo toilet” Batul ce ta yi maganar, saukowa ta yi daga saman gadon ta nufi ƙofar da take tunanin ta toilet ce ta tura da hannu ta shiga, tun da ta shiga take bin ko’ina da kallo sauƙin ma toilet ɗin su na prison na zamani ne, da ko anga ƙauyanci sai dai da banbanci sosai, don wannan akwai sink da bathtub hada shower ga mirror da sauran Kayan amfani.

Agaban madubi Batul ta tsaya tana kallon fuskarta, bata ta6a ganin Kyanta irin na yau ba yatsun hannunta ta tura cikin Curly hair ɗinta tana cakuɗa shi.

Acan bedroom ɗin Bayan shigarta toilet, zuciya da saƙe saƙe Angel sai ta dinga ayyanawa aranta ga Batul can ta kunna Ruwan zafi amaimakon na sanyi” Jiki Na rawa ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ɗin, ko neman excuse babu ta shigo toilet din kamar an jeho ta.

Jin motsin shigowar mutun yasa Batul Juyowa a firgice don ganin wanene. Kusan atare suka sauke Ajiyar zuciya

“Dama ba wani abu za ki yi a toilet ɗin ba”?
Murmushi Batul ta sakar mata”Inaso ne in ƙare ma ko’ina kallo,”

“In dai wannan ne kada ki damu zan yi maku bayanin komai, amma Yanzu ki fito mu koma ɗaki” Amsa mata ta yi da toh ta juya ta nufi Angel ta ruƙo hannunta suka fito, shugowarsu ɗakin ke da Wuya Aka buɗe ƙofar, Dr Daniel brown ne tare da Nurse rebecca.

Fuskokinsu ɗauke da murmushi, cikin harshen turanci ya soma yi mata magana.

‘Masoyiya Angel da ƴa’ƴanta, fatan na same ku Lafiya” Amsa mashi sukayi da lafiyalou
“Ya jikin naku? Ko akwai inda ke yi maku ciwo “? Atare suka girgiza mashi kai

“Okey, Starting tomorrow, you’ll be receiving injections for three days, and you’ll also be taking regular medication to improve your health.” cikin kulawa dr brown ke yi masu magana idonshi akan fuskar Angel.

Murmushi ta sakar mashi”mun gode sosai da kulawarku agare mu, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku”

“Kada ki damu, aikin mu ne, Ko akwai wani abu da kuke buƙata”?

Cikin raɗa Batul ta yi ma Angel magana a kunne”muna son ganin Haris da Danish”

“Doctor, can we see our brothers?” kamar mai jin shakkar shi ta yi maganar.

Jinjina mata kai Yai alamar eh, Kafin ya ɗaura idonsa akan Nurse rebecca” Ki kai su ɗakin Ƴan uwansu”
“Okey sir” Mayar da idonshi yai kan Angel” pls muna so ki samu natsuwa sosai, ki kwantar da hankalinki dana ƴan uwanki, akwai magana da zamuyi dake tare da sojojin da suke ceci Rayuwarku, sunce da zarar kin farka a sanar da su, Ni kuma na bari sai zuwa gobe idan kin ƙara wartsake wa duk da naga jikin naki da ƙwari”

shiru Angel ta yi tana faman zazzare mashi gray eyes ɗinta aranta ta ayyana komai suke son sani? fatanta Allah ya bata ikon amsa masu tambayoyin da zasu Yi mata

“Haɗin kanki mu ke buƙata Masoyiya Angel” murmushin yaƙe ta sakar mashi wanda bai kai zuci ba.

Bayan fitar shi daga ɗakin, Nurse ta kalli faces ɗinsu”zamu Iya tafiya” A hanzarce suka sassauko daga saman gadon suka bi bayanta, tun da suka fito daga ɗakin gabansu ke faɗuwa ganin haɗaɗɗen wurin da suka tsinci kansu a cikinsa, Asibitin Har ya gaji da haɗuwa, babu tazara a tsakanin ɗakunansu da inda aka kwantar da su Haris duk acikin amenity ward ne.

Abakin ƙofar ɗakin da aka kwantar da Haris suka tsaya, sai da nurse ɗin ta fara tura ƙofar ta shiga tukunna Ɗaya bayan ɗaya su ka soma shiga cikin ɗakin cike da zumuɗin son ganin ɗan uwansu, tun kan su ƙarasa suka hango Haris kwance magashiyan saman medical bed an sanya mashi robar oxygen a hancin sa.

Da sauri suka ƙarasa gaban gadonshi, gida biyu suka raba kansu, gefen dama Gabriel ne da Javed sai Naufal da Parveen ta 6angaren hagu Angel ce da Batul, Jamimah da azeeza sai Hannah, tsananin tausayin Haris ne Ya kamasu, tuni idanuwansu sun cicciko tab da ƙwalla.

Cikin shessheƙar kuka Angel ta ambaci sunansa”Haris!” har cikin dodon kunnanshi Kiran Ya isar mashi, sambatu ya soma yi masu Yana ambaton sunan Deeja yana faɗin”mu koma ku ɗauko ta, Deeja na tana araye suna can suna azabtar min da ita, dan Allah ku taimakamin ku cece rayuwata ku ɗauko min deeja na” tuni Hawaye sun wanke fuskokinsu, Hatta nurse rebecce Dake atsaye jikinta yai sanyi ganin hawayen su, Duk da bata iya jin abunda ɗan uwan nasu ke cewa

“Haris”! Muryar Angel ce ta ƙara ratsa kunnan su, A hankali Ya soma ƙoƙarin buɗe idanuwansa da suka kumbura jawur ya ɗaura su akan fuskarta, Ware su yai sosai, Ganin Yana ƙoƙarin miƙewa yasa Nurse ɗin Yin saurin matsawa bakin gadon ta rankwafa ta zame mashi roban oxygen din daga hancinsa, ta taimaka mashi Ya miƙe zaune Bayan ta sanya mashi pillow a tsakankanin bayan shi da headboard na gadon.
Chapter 52 · 0% Book details