← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 152

Sashe 36

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Shureim, Idan na tashi tafiya abuja atare da kai zamu tafi, bazan barka a gidan nan ba, don Na fahimci akwai masu takura maka, Shiyasa duk ka rame kayi duhu,” Cikin kulawa yake yi mashi maganar, hannun shi ɗaya asaman kafaɗar dr shureim ɗin, Layla ta yi mamakin jin abunda yace, mutumin da ko ƴa’ƴan shi bai sakar masu fuska shine ya ke zancen zai tafi da shureim, kwa6e fuska ta yi don ta fahimci so ya ke ya ƙuntata mata.

Alhaji ubaid yana murmushi yace”naji dadin jin hakan, wata’ƙil idan kuka je can yafi sakewa, don na fahimci shureim baya son zama gida...” kafin ya ƙarasa maganar, layla ta katse shi da cewa ‘’ae sai ku tsaya kuji ra’ayin shi ko? Idan ya ce yana son zuwa can ɗin,” Tana rufe baki Alhaji musa yace”ai ba shawara nake nema dashi ba, Umarni ne” Cikin isa Ya furta hakan, Kafin ya kalli dr shureim, ka shirya komai naka idan muka tashi tafiya atare zamu tafi”

Lamarin ya ɗaure mata kai, shi dai Dr shureim yai shiru bai tanka masu ba, Girgiza kai Hajiya layla tayi’bazai yiwuwa ba, haba dan Allah duka yaushe muka samu shureim ɗin ya dawo wurin mu, Sannan kuma yanzu kace zaka tafi dashi? Aɗan bari ya huta mana, Shi kaɗai fa nake gani inji daɗi,” rai a6ace take magana, Sun natsu suna sauraronta, sai da takai ƙarshen Aya tukunna Alhaji ubaid yace da ita”meye na tada jijiyoyin wuya? Guduwa zai yi dashi ne? Bafa raba ki zaiyi dashi ba, Yana so ya zauna gidan shi na ɗan wani lokaci,” fuskar Alhaji musa aɗaure yace”idan na ga dama zaici gaba da zama awurina ne kuma ke baki isa ki hana shi ba” murmushin fuskar Alhaji ubaid bai washe ba yace”ba girmanku bane ku tsaya kuna sa’insa akan Shureim sai kace wani ƙaramin yaro, ko da ya ke laifin ka ne shureim tuntuni nake baka shawarar kayi aure ka ƙi yi, da ace kana da Iyali babu wanda ya isa yai iko da kai” da zolaya yayi maganar, Shureim dai ya natsu yana jinsu, Ya jima yana jin takaici yadda rayuwa ta canza mashi, Ya koma tamkar ƙaramin yaro a idon kowa, saboda raunin zuciyarshi.

daƙyar Alhaji ubaid ya samu Ya maida sa’in sar tasu Wasa, dama can basu jituwa tsakanin Layla da ƙanin shi tunfil azal.
“Yakamata mu tashi muje muci abinci, zainab ta shirya mana a dining” layla ce tayi maganar, Ɗaya bayan ɗaya suka miƙe tare da nufar Dining room.

*Kaɗan daga Cikin Na sati mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya*

*Evil forest*

Sautin Ƙarar Danƙararen Helicopter mai saukar angulu Ƙirar UH-60 Black Hawk mallakin Sojin Ƙasar america ne Ya karaɗe ko’ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza suke yi saboda ƙarfin iskar fankar Jirgin, Shawagi jirgin yake yi a saman Iska Yana kewaye ko’ina na tsawon mintuna talatin, Yayin da Hot soldiers din dake a tsaye saman jirgin cikin shigarsu Ta ka ki sun ɗaura ɗamarar Yaki, Sai dai ga dukkan alamu Sun kammala gudanar da abunda Ya kawo su Cikin Dajin, Ɗaya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ƙofar helicopter ɗin Hannun shi ruƙe da tactic phone Wayar da sojoji suke yin amfani da ita wurin yin sadarwa ga Manyansu dake acan Headquater, Cikin Harshen turancin Yake Yin magana muryarshi na fita da amon murya saboda ƙarfin iskar Dajin

“We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S. with the eleven children we found in the forest.”

Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya miƙi hanyar komawa ƙasar da ya fito......, Nima kuma na ajiye alƙalamina.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E11🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

Gaba ɗaya Haris ya fidda rai da rayuwa, tun da halittar nan ta zura ƙafafuwansa cikin wawakeken bakinta, tsabar tsoro da firgici sun hana shi motsawa jini duk ya wanke bakinsa har saman rigar sa, jikinsa yai wani irin mahaukacin zafi na fitar hayyaci, Bawan Allah sai sambatu ya ke yi yana ambaton Sunan Danish dana sauran ƴan uwan su don su kawo mashi agaji.

Ba zato ba tsammani ya ji Sautin dirar wani abu daram! tamkar zai fasa kunnansa, tsabar firgitar da yai ne yasa nan take ya sume saman koraren ciyayin.

Wani Gabjejen Bature ne A tsaye cika shigar Kaya na tatattun Ƴan ta’adda babu ɗigon Imani akan fuskarsa, Hannunsa ɗaya ya ruƙe da Bindigar da yai amfani da ita wurin harbin Halittar da ta nannaɗe Jikin Haris, yayin da ɗayan hannun ya ke ruƙe da cigarette.

Hankalin shi a kwance ya ke zuƙar Tabar Cikin ƙwarewa Har ta hanci Hayaƙin Ya ke fita, kwarkwararrun idanuwanshi na akan Haris dake kwance Ya sume, Tuntsirewa Baturen Ya yi da dariya hada ɗan girgiza kanshi, da ƙarƙarfan muryar sa ta Mashaya giya cikin harshen turanci ya ke faɗin

“wani irin ganganci ne ya kawo ka ƙurmin daji da ƙananun shekarun ka, ba ka da hankali ne? Matashi da kai kake son ƙare rayuwarka abanza? Ina iyayen ka su ke”?

kamar zautacce Shi kaɗai ya ke yin maganar shi, sam bai fahimci Yaron Ya sume ba, Sai da Ya gama Magana kafin ya matsa inda Haris yake a kwance, Ya zuƙunna Bayan Ya soke pistol ɗin a qugunsa, Ya sanya hannayensa Biyu Da ƙarfi Yake jan jikin halittar, Har sai da yai nasarar zaro ƙafafuwan Haris daga bakinta, Allah yaso ba ta kai ga Gatsa haƙoranta akan legs ɗinsa ba, da ko ta yi mashi babbar illa, Bayan Ya zame jikin Halittar da karfi Ya jefar da ita gefe ɗaya, yunƙurawa yai ya miƙe tsaye yana kakka6e tafin Hannayensa, Zuƙar Tabar sa Ya ƙara Yi”Bani da zuciyar Imanin da zan Iya taimakon ka, ka gode wa Allah da na raba ka da dabbar nan, da ko yau Ka rasa ƙafar zuwa gidan Iyayen ka” Yana magana yana sakin dariya idanuwansa akan fuskar Haris.

Sautin kururuwar neman a gajin da ya Ji ce Tasa shi Kan ga kunnansa ga iska Don Ya ji da kyau, Muryar Naufal ce Ya ke faman Fasa Ihu, Da gudu Baturen Ya kutsa Cikin Dajin Yana Tunkarar inda sautin Ƙarar ke fitowa, ta wutsiyar idon shi ya hango gifcin mutune sanye da Jajayen kaya, Ta tsakantsakin jibga jibgan Bishiyoyin dake a kewaye da wurin da yake, Cikin Zafin Nama Ya daka uban tsalle ta tsakiyar wasu bishiyoyi, Kamar an jeho shi Ya faɗo Tsakar wurin da Su Naufal su ke, Gaba ɗaya sun fita hayyacin su, Halittun sun kewaye su sai gurnani su ke yi, Naufal da javed sun ƙanƙame Juna, Kuka hada majina fuskokin su jaga jaga da hawaye, wandunansu a jiƙe sharkaf da ruwan fitsarin da suka saki, Ɗan iskan murmushi dangerous terrorist Ya saki kafin Ya zaro bingidar da ke soke a qugunshi, Ya saita Jikin Halittun ɗaya bayan ɗaya yake sakar masu alburushi, duk wadda ya harba nan take Tsakiyar Cikinta yake tarwatsewa Ƴan hanji su fito waje, Sautin harbin bindigar da basu ta6a ji bane Yasa su rikicewa Kusan atare suke yanke jiki saman koraren Ciyayin suka faɗa a sume, Tuntsirewa Baturen yai da dariyar shaƙiyanci Yana faɗin

“Yaran nan kuna da ban dariya, Sai ka ce ba maza ba? Kun iya shiga daji amma ba ku Iya faɗa ba? Zaman gida da sanya buje zaifi da cewa da ku, In yaso kun cigaba da taya iyayen ku shiga kitchen yin girki” acikin harshen turanci ya ke yin maganar.

Gabanshi Ne yai mugun faɗuwa Jin ƙarar Jirgi A cikin kunnuwansa, Da sauri Ya kai idanuwansa saitin rassan bishiyoyin da suka lullu6e sararin samaniya, nan ta ke yanayin fuskar shi Ya canza daga annuri zuwa tsantsar baƙin ciki, fargaba da tashin hankali, Juyawa yai da gudun gaske tamkar zai tashi sama Haka ya dinga buga uban tsalle Yana gudun Ceton, ga dukkan alamu bai da gaskiya shiyasa ya ƙe ƙoƙarin gujewa waɗanda suka kawo mashi Hari, tuni Ya jima da jefar da tabar hannun sa, kwata kwata Baya a cikin Hayyacinsa, shi kansa baisan in da ya ke wurga ƙafafuwanshi ba, saboda tabar firgicin da ya shiga, ko ma su wanene su ka biyo shi sun shammace shi bai yi tsammanin za’a gano inda ya 6uya ba.

Sautin Ƙarar danƙareran Helicopter mai saukar angulu Ƙirar UH-60 Black Hawk mallakin Sojin Ƙasar amurka ne Ya karaɗe ko’ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza su ke yi saboda ƙarfin iskar fankar Jirgin, har wani jijjiga ya ke yi tamkar zai fasa dodon kunnan mutun, Shawagi ya ke yi a saman Iska Yana kewaye ko’ina.

Hot soldiers din da ke a tsaye baƙin ƙofar jirgin zafafan gaske fusatattun sojoji masu ji da ƙarfi, cikin shigarsu Ta ka ki sun ɗaura ɗamarar Ya ki, Ɗaya daga cikin su Hannayen sa biyu Na ruƙe da Telescope abun hangen nesa, Ya kanga shi saitin idanuwansa, Sojan da ke a gefen shi Yana Ruƙe da Tactical phone wayar da sojoji ke Yin amfani da ita wurin yin sadarwa da Manyansu dake acan headquater, Cikin Harshen turanci Ya ke Sanar da su cewa Sun ƙaraso Dajin ayanzu hake suna kewaye shi domin gano Location ɗin da ɗan Ta’addan Ya 6uya a dajin.
Chapter 36 · 0% Book details