← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 152

Sashe 14

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryar Angel na rawa ta soma ambaton sunayen su”Ha..ris..Mubeen..Naufal..Javed..”! akace labarin zuciya a tambayi fuska, Tun kan ma su yi mata bayanin abunda ya faru da gudu ta faɗa cikin ɗakin tsohuwa Tamira da ke a buɗe, Idanuwanta Azazzare take kallon Ƴan uwanta dake kwance ƙasa ba numfashi, Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki ta fitar hayyaci wadda tayi silar faɗowar Danish dasu Haris cikin ɗakin sai lokacin su ka ga mummunan abunda tsohuwa zafreen ta aikata ma ƴan uwan su. Silar ƙarar da Angel ta fasa ne yasa Batul raba jikinta daga na salsabeel fuskarta jaga jaga da hawaye ta ɗago idanuwanta, tana yin tozali da Angel da gudu ta nufota tare da faɗawa saman ƙirjin ta suka ƙanƙame juna suna yin kukun zuci, Cikin shessheƙar kuka Batul ta labarta mata duk abunda ya faru bayan tafiyarta, Tasha kuka kamar ba gobe, ta yi fatan ace dukkan su ne suka mutu hada ita, gaba daya shirin su ya tarwatse taya zasu iya barin kurkuku Bayan ƴan uwansu duk sun mutu, Alƙawarin data ɗaukar masu bata samu cika shi ba, Ga danish ɗin ta ci nasarar dawo dashi sai da kash Ta faru ta ƙare, ƙaddara ta riga fata, Cikin raunatacciyar murya ta wanda ya gama sarewa da rayuwar duniya ta furta”Nashiga Uku na bani na lalace! Ya Allah zunubin me muka aikata mu ke fuskantar irin wannan mummunar jarabawar daga gare ka? Idan ba ka son mu, ka ɗauki ran mu mu huta, Mun gaji mun gaji Wayyo Allah na Na rasa Azeeza na rasa jemimah na rasa Deeja da sauran Ƴan uwana, To ni zaman uban me zanyi acikin duniyar nan wlh bazan rayu ba dole in kashe kaina......” Cikin fitar hayyaci ta furta kalaman, kamar mahaukaciya, ta juya da niyar ta je nemo makamin da zata halaka kanta dashi, Cikin zafin Nama Salsabeel Ya damƙi hannunta, tare da juyo da ita ta yadda zata fuskance shi”Meye ribar ki idan kin kashe kan ki? Dama ba sai da na faɗa maki Ba lallaine ku rayu ku dukan ku ba, Yanzu idan kika mutu Kinsan adadin rayukan da za’a cigaba da 6arin jinin su a gidan kurkukun nan? Idan har bamu lallashi zukatan mu ba mun kawo ƙarshen Azzaluman da suka cutar da ƴan uwan mu Duk wani ƙoƙarin mu ya tashi abanza kenan! Ya ku ke so inyi da raina ne? saboda ku na rasa mahaifiyata Ni kaina ashirye nake da in rasa raina in dai akan ku ne, Don haka kada wanda Ya ƙara Yi mana kuka Ya isa haka !! Mutuwa dole ce ko muna so ko bamu so, Kuma mutuwa sauƙi ce agare su saboda rayuwar duniyar bakomai bane acikinta face ruɗani, cike take da ƙalubale iri iri, ni banga amfanin yin kuka don wani ya mutu a cikinmu ba, Saboda Allahn daya halicce su wanda yafi mu sonsu shine ya kar6i abunshi, Sai sunfi jin daɗi fiye da na duniyar nan......’ sosai Salsabeel ya yi masu nasiha har saida yaga sun dawo hayyacin su tukunna Yace dasu babu isasshen lokaci su wuce su tafi, Danish Zai buɗe masu ƙofa, shi zai kula da gawawwakin Ƴan uwansu da suka mutu, Tun shigowar Danish ɗakin kusan suman tsaye yayi, saboda tsabar Kiɗima da ganin halin da ƴan uwan shi su ke aciki, Ya rasa bakin magana, Ya yi matuƙar girgiza da ganin yadda aka wulaƙanta rayuwar Ƴan uwan shi, Hankalin shi yai mugun tashi, Zuciyar shi tamkar zata faso ƙirjin shi ta 6allo saboda tsabar ƙunar da ta ke Yi mashi, Ya fusata Iya fusatuwa, ganin yadda yake huci ƙirjin shi na motsi ga wata narkakkiyar zufa dake wanke mashi fuskarshi, yasa Salsabeel yin saurin dakatar dashi ta hanyar yi mashi magana”Danish ka sassauta fushinka idan ba haka ba giant’s heart ɗin ka zata iya motsawa, pls ka ceci rayuwar su ku gudu daga kurkukun nan, duk wani abu da ya toshe maka kai, Unaisah zata yi maka bayani idan kun fita” daƙyar ya samu Danish ya iya sarrafa fushin sa.

Muryar Angel adisashe tace dashi”Ni bazan Iya tafiya in bar gawar su Azeeza acikin wannan ƙazamin ginin ba, inaso na cika masu burin su duk da basa araye zan fitar da gawarsu waje in yaso sai mu binne su a akan hanya, dan Allah ku taimaka min” Tana magana hawaye Na wanke fuskarta.

“Unaisah bamu da isasshen lokaci pls ku tafi kawai ku barni dasu zan san inda zan 6oye gawarsu” fashe mashi ta yi da kuka kamar zata haɗiyi zuciyarta, Hankalin Danish gaba ɗaya ya dawo kanta, tsananin tausayinsu duk ya kama shi.

“Bazai yiwu ku iya tafi da su ba! Kubar su a wurina zan tsaga ƙasa In binne su” acewar Salsabeel

Ataƙaice zan yi bayanin yadda su ka gudu daga KURKUKUN ƘADDARA, Angel ce ta goya Jemimah abayanta tare da sanya Mayafin kayan su da ta ɗauko acikin akwatin su, Gabriel ya goya gawar Azeeza abayanshi ya ɗaureta da mayafi, Naufal ya goya Parveen asaman bayanshi, Haris yaso ya goya Deeja abayanshi sai dai Salsabeel Ya hana shi gudun kada su ja ma kansu wata wahalar, Iya waɗannan kaɗai su ka ɗauka sauran Sun bar su awurin shi bayin Allah badan sun so ba, kusan mutun shida daga Ciki hada Deeja, Sarah, Eve, Yasmin, Rubina da Hibba, Danish ya yi ƙoƙarin yin amfani da sihirin shi wurin farfaɗo dasu, mutun ɗaya kaɗai ta samu damar tashi Hannah, a ƙarshe ya tabbatar masu da cewa Heart attack ne Yai silar mutuwar su, zuciyar su ce ta buga.

Ƙululun baƙin Ciki kamar su Zauce, Kafin tafiyar su Mubeen ma ya yanke jiki ya faɗi, Don dole suka haƙura da shi, Lamarin ya yi matuƙar gigitar da su.

Salsabeel ya yi masu alƙawarin Zai yi nesa da gawarwakin Ƴan uwan su, tare da ta mahaifiyarshi ba zai bari a wulaƙanta su ba, sun yi kukan rabuwa dashi, har magiya Angel ta dinga yi mashi akan ya zo su tafi atare da shi, amma yace masu ba zai iya bin su ba, su yi haƙuri su tafi idan Allah yasa yana da tsawaicin kwana zasu sake haɗuwa ne duk da yasan abune mai wuya ya rayuwa ko dan saboda 6arnar da suka aikata dole matsafan su azabtar da shi.

Rabuwar su ta yi matuƙar ta6a zuciyar kowannan su, a gurguje su ka nufi sashen makewayin su, Tsabar tashin hankali yasa Gabriel mantawa da zancen Ƴar uwar shi Gabriella da ke a cikin kurkuku, tun da ya ga mutuwar ƴan uwan shi prisoners, yasa wa ranshi dangana.

Suna shiga Cikin Toilet ɗin, Danish Ya datse ƙofar da sihirin shi, ya Janye tukunyar fulawar daga kan ƙofar, nan ta ke ta bayyana duk irin wahalar da suka sha ta ƙi buɗewa shi Bugu ɗaya yayi mata gaba ɗaya ta 6alle murfin ƙarfen ya dare biyu, Sun yi mamaki da al’ajabi yace da su”Ba zai bi su ba, zai tafi da Akwatin kayan su tare da back pack ɗin su, za su tarar dashi a bakin ƙofar da zasu 6ula idan sun ƙarasa” hankalin su bai kwanta da maganar shi ba, gani su ke yi kamar wani mummunan abun zai faru da su idan baya atare da su, ganin sun toge sunƙi tafiya yasa shi Kwantar masu da hankali, daƙyar ya samu su ka Zuƙunna ƙasa tare da kutsa kai ɗaya bayan ɗaya su ke shiga cikin ƙofar da rarrafe, Bayin Allah ga yunwa ga ƙishin ruwa, ga raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu, Ita kanta hanyar da suka biyo Wata uwar ƙura ga yanar girgizo da ƙwari sai hawan masu jiki su ke yi, Amma saboda rashin kwanciyar hankali yasa basu damu da su ba. Babu mai magana acikinsu saboda ƙunar da ran su ke yi masu, Angel ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan suci gaba da ambaton addu’o’in data koya masu ko sun samu sassaucin a wurin Allah, sun ɗau ki shawararta ahaka suka Dinga tafiya da rarrafe babu ƙaƙƙautawa, idan suka gaji su kan ɗan zauna su huta kafin su dasa da wata tafiyar, A ƙalla sun shafe tsawon awanni Takwas suna rarrafawa ba tare da sun kawo ƙarshen Ƙofar ba, a takure su ke Bayin Allah sun ga rayuwa gwiwowin ƙaffuwan su duk sun gurje sun sage, maƙoshinsu ya bushe ƙamas, tun suna ambaton ƙishir ruwa suke ji har sun gaji sun yi shiru.........”😭

💔Prisoners💔

Sun ci baƙar wahala saboda tsohuwar hanyace da ta yi shekaru aru aru a datse ba tare da an yi amfani da ita ba, Muggan ƙwarin da ke a ciki sai ɗallinsu su ke Yi, amma saboda azabar raɗaɗin da zuciyar su ke yi masu yaci uban raɗaɗin harbin da ƙwarin ke yi masu yasa ba su ji, A makance suke tafiya basu ji basa gani, ga wani azababben zafi daya addabe su, kowan nan su ya haɗa uban gumi burin su kawai su cimma ƙarshen ƙofar, wani ƙarin tashin hankalin fitilun da ke a hannun su Batul hasken su ya fara ƙoƙarin ɗaukewa abunda basu ta6a yi masu ba, sun fuskanci matsanancin tashin hankali har sai da suka fidda rai da fita saboda ganin tsawon awannin da suka shafe ba tare da sun kawo ƙarshen ta ba, tun da suna rarrafawa Hannah ke kuka tana faɗin ƙaiƙayi ta ke ji a jikin ta, duk da halin da su ke aciki hakan bai hana su rarrashin ta ba akan ta yi haƙuri, a lokacin da ba su yi tsammani ba kwatsam! hasken fitilun hannun su Ya ɗauke ɗuff Innalillahi wani irin duhu baƙiƙƙirin ya mamaye idanuwan su, ko fuskokin su basa Iya gani, duk sunbi sun firgice saboda hanyar ta 6ace masu, Sunan Danish su ke ta kira a bakunan su, sun manta cewa baya atare da su.
Chapter 14 · 0% Book details