← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 152

Sashe 80

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefen gadonta ya zauna Yana dubanta, calmly ya furta”Zeenat ina son yin magana dake
Shiru tayi bata tanka mashi ba, tayi tunanin Tani ta fada mashi cewa bacci take yi kamar yadda tace ta gaya mashi.

“Nasan Kina Jina zeenatu, Ki amsa mini, nazo ne don in baki haƙuri, nasan ban kyauta maki ba, Yanzu haka da nike yi maki magana na kammala shiryawa ke nake jira mu tafi”

Cikin disasshiyar murya tace”yaya shureim bana jin daɗin jikina, bazan iya fita ba, sai dai zuwa gobe”

“am sorry zeenatu, fushi kike yi da yayan naki? Ba za ki yi mini uziri ba?

“Yaya shureim ni ba fushi nike yi dakai ba, fitarce na fasa, Bana jin daɗi”

Ya rasa ya zai yi ya shawo kanta don ta amince su fita.

Yanke shawarar Yaye Bargon Jikinta yai don ya samu damar lallashinta dakyau.

Tsautsayine Yakai hannun shi saman bargonta, Ya ruƙo shi tare da jan shi, Ras yaji gabanshi ya faɗi da sauri Ya maida mata bargon a jikinta, Yana faman jan numfashi da ƙarfi da ƙarfi, miƙewa yai da wani irin Yanayi ya nufi ƙofar fita daga ɗakin Yayin da la66ansa ke ambaton sunan Allah, Har ya kusa kaiwa ƙofar ɗakin Muryar zeenatu ta katse mashi hanzarin shi.

“Yaya shureim kai da kanka ka faɗa mini cewa baka ta6a yin soyayya ba, amma meyasa kake kallon hoton wata awayarka”

Ta gaza haƙura har saida ta amayar masa da abunda ke cikinta, shi kuwa Man din duk ya rasa natsuwarshi, tunda Yaja bargonta Yayi arba da undy din jikinta shara shara Hakan ba ƙaramin tada mashi hankalin shi yai ba, ga dukkan alamu ita batasan ma ya buɗe bargon ba saboda ta ƙudundune kanta, idanuwanta suna arufe.

“Zeenatu, abun da na faɗa maki da gaske ne, banyi maki ƙarya ba, Ni ban ta6a yin soyayya ba” A hankali Ya ɗan Juyo yana dubanta, a lokacin ta fiddo da kanta daga Cikin bargon, Yalwatacciyar sumar kanta, ta rufe mata gefen fuskarta, Jan bakin data shafa ya dame fuskar saboda kukan da tasha, har saman kumatunta jan bakin ne, duk da kwalliyar fuskarta ta 6aci ba ƙaramin kyau tayi mashi ba.

Muryarta da shagwa6a tace”ka faɗamin wacece ka ke kallo awayarka? Idan ba budurwar ka bace.

Ƙayataccen murmushine Ya bayyana akan fuskarshi, sai yanzu ya gane dalilin dayasa take haukan nan, wato kishin shi take Yi saboda yana kallon hoton wata wayarshi, aranshi ya ayyana da ace tasan hoton wacece yake kallo da batayi haukan nan ba.

“Zeenatu, dama saboda hoton wayata kike kuka”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh.
“Okey, Ki kwantar da hankalin ki, ba budurwata ba ce,” maƙe mashi kafaɗa tayi”ni ban yadda ba yaya shureim, idan har dagaske kake yi min ba budurwan ka bace to ka nuna min hoton in gani”

Lumshe idonshi ya ɗanyi tare da waresu kan fuskarka, duk da tazarar dake a tsakanin su, ba ƙaramin Kyau take yi mashi ba musamman yanzu daya fahimci irin zazzafan son da take yi mashi.

Ganin ya tsareta da ido, ba tare daya furta komai ba yasa tace”Yaya shureim magana fa nake yi maka, kayi shiru baka ce komai ba, Ni dama nasani baza ka nuna min hoton in gani ba”

Yadda take yin maganar tana jujjuya eyes balls dinta ne suka ƙara rikitar da shi.

Gyaran murya ya ɗanyi kafin yace”Idan har Ki ka amince zaki shirya mu fita, Ni kuma zan nuna maki wacece nake kallo awayata,” zum6ura mashi baki tayi”toh, amma ka fara yi min alƙawari,”

“Nayi maki alƙawari”

“Yanzu zan shirya yaya shureim,” ganin tana ƙoƙarin miƙewa tsaye yai saurin fuce wa daga ɗakin gudun kada Ya ƙara ganin abunda zai hana shi Runtsawa.

Fitowa ya yi daga cikin gidan Ya nufi harabar ajiye motocin su, Wasu danƙara danƙaran motoci ne na Alhaji musa a killace a ƙalla sun haura goma shabiyar, kuma dukansu babu motar ƙasa da miliyan talatin, Manya manyan motocine tsadaddun gaske masu numfashi.

Motarshi Ya buɗe Ya shige Ciki Ya zauna a driver seat haɗi da ɗaura kanshi jikin headrest, bakomai Yake tunawa ba face maganar da Alhaji musa ya faɗa mashi akan Aiki da kuma aure, A yanzu ya fara tunanin ta yadda zai 6ullo mashi da zancen auran zeenatu, yafi buƙatar auren akan komai, saboda yanason ya samu natsuwar cigaba da gudanar da rayuwarshi, zeenatu ta kwanta mashi aranshi ɗari bisa ɗari, kuma yana da tabbacin zeenatu zata maye mashi gurbin abunda ya rasa.

Almost 15 mins, ƙamshin turarenta Ya doki hancinsa, Nan take ya fahimci ƙarasowarta, buɗe motar Tayi tare da samun wuri ta zauna gefenshi” ɗaura idonshi yayi akan face dinta, babu make up, zallar kyan da Allah yayi matane, ta canza kayan jikinta zuwa turkish gown launin black gray, Ta yafa mayafi akanta, Idanuwanta sun kumbura saboda kukan da tasha.

Kallon Juna suka somayi kamar zasu haɗiye kawu nan su, Ko ƙyaftawa basa yi, kunyar shi ce ta kama ta, da sauri ta daura kanta saman laps dinta.

“Zamu Iya tafiya” da shagwa6a tace”a’a yaya shureim, nafi so ka fara nuna mini hoton in gani”

Zaro wayarshi yai daga cikin aljahu Ya daddanata, Kafin Ya miƙe mata wayar”kar6i ki ganta, Kyakkyawa ce tafi ki kyau, ita nike da burin aure”

Gabanta na faɗuwa ta ɗago, tare da sanya yatsun hannunta dake kerma ta kar6i wayar da ya miƙo mata, idanuwanta rufe tabarsu, Gudun kada taga abun da zai hanata kwanciyar hankali.

Dr. Shureim dake kallonta, murmushine ɗauke akan fuskarshi

“Meyasa ki ka rufe idonki”? Muryarta na rawa ta furta”bana son inga abunda zai hanani bacci”

“In sha Allah ba zai hanaki yin bacci ba, sai daima ya sanyaki yin bacci cikin kwanciyar hankali, now Open your eyes slowly and look at the picture,”

She took a deep breath and tried to slowly open her eyes kamar yadda ya bata umarnin ta bude su a hankali.....”

(Kaɗan daga cikin na sati mai zuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya🤣 sai dai Allah yakaimu zamu gani, Very soon In sha Allah Zamu shiga Takun ƙarshe na labarin kurkukun ƙaddara)

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

سجن القدر❤🤍❤

_THE PRISONERS E24🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

Confusion of the heart💫

lokacin da ta ware idanuwanta akan screen din wayar wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta ganin fuskarta, hotonta ne tun tana ƴar shekara goma sha ɗaya a duniya, tsabar farin ciki Ya hanata rufe baki, hada hawayenta saboda farin cikin ganin hotonta ne yaya shureim yake kallo, bata kawo komai aranta ba saboda ta yarda da shi.

Ɗagowa tayi idonta acikin nashi ta furta”yaya shureim dama hotona kake kallo”? Ɗaga mata gira yai alamar eh, ta kuma cewa”yaya shureim wannan ai tsohon hotona ne a ina ka same shi”

Fuskarshi ɗauke da murmushi yace”nima tsohuwar ajiyace a cikin memory dina, saboda inason hoton bana so na rasa shi, bama shi kaɗai ba akwai sauran hotunanki a gallery ɗin wayar zaki Iya dubawa ki gani”

Yatsun hannunta na kerma ta bubbuɗe sauran hotunan tana kallonsu hada wanda tun tana jaririya akayi mata shi, abunda ya ɗaure mata kai gaba daya gallery na wayarsa hoton mutun biyune acikinsa daga hotonta saina ƙanwarshi benazir.

“Yaya shureim tun yaushe kake kallon hotuna na”? ta faɗa da mamaki akan fuskarta.

Muryarshi ƙasa ƙasa tamkar tame yin raɗa ya furta mata”tun lokacin dana fahimci kece ƙaddarata” wurga mashi blue eye balls dinta tayi akan face dinsa.

“Ƙaddararka? Kamar yaya kenan”? Cikin rashin fahimtar kalaman shi ta ambaci hakan.

“Lokaci zai ƙure mana zeenatu, ki bari idan muka dawo gida zan fahimtar dake abunda nake nufi” amsa mashi tayi da toh, haɗi da miƙa mashi wayarshi Ya sanya hannu ya kar6a, ya turata a aljhu, har cikin ranshi ba ƙaramin daɗi yaji ba, ganin bata kawo komai aranta ba, Duk da ya 6oye mata ainihin hoton da yake kallo.

“Allah sarki aunty benazir, nayi missing dinta Yaya shureim, tsawon lokaci babu ita, Allah dai yasa aganta da ranta da lafiyarta” cikin sanyin murya zeenatu ta yi maganar, ya amsa mata da ameen.

Yana ƙoƙarin tada motar, ba zato ba tsammani yaji zeenatu ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi, wata irin kasalace ta soma baibaye shi sakamakon ƙamshin turarenta dake kashe mashi jiki.

A hankali motarsu ta miƙi Hanyar babban gate din gidan, Gate security officers ɗin dake tsaron gidan suna ganin motarshi gaba ɗaya suka yunƙuro suka nufo motarsu, hannunsu ruƙe da jibga jibgan bindigu, ba arziƙi dr. shureim Yaci burki, Jin ya dakata da yin driving din yasa zeenatu ɗago da kanta daga saman kafadarshi ta dube shi.

“Yaya shureim meyasa ka dakata da yin driving din”

“Masu tsaron gidan nan ne suke tunkaro mota ta,” ya bata amsa a takaice.

Dafe kai tayi da hannu ɗaya”Namanta ban faɗa ma daddy ba, Ni nasan daƙyar zasu bari mu fita, idan har bai basu umarnin su ƙyale mu ba, gashi baya agidan, Mommy ma har yanzu bata dawo daga office ba” ta faɗa tana faman zare ido.

“Yaya shureim ka kira daddy awaya ka sanar dashi” a tsoroce take yi masa maganar don ita kanta mugun jin shakkar masu tsaron gidan nasu take ji, ƙirar jikinsu kaɗai abun tsoratarwa ne, sannan basa wasa da aikinsu, gashi babu annurin akan fuskokinsu.

Kafin dr shureim Ya zaro wayarshi tuni sun cimma masu, ƙawanya su ka yi mata motarshi.

Ɗaya daga cikin su ne yai knocking glass motar, da kakkausar murya yake ya ce “wanene acikin motar? Muna baka umarnin ka zuge glass din motar ka”

zeenatu ce ta sauke glass din, Ya zuƙunno Yana dubansu A tsanake miryarta na rawa tace”yanzu zai kira daddy awaya, yayana ne shureim zamu fita yawo ne”

Security guard ɗin yace”oh, meyasa baki faɗa mashi ba’a fita dake waje ba tare da iznin daddyn ki ba”?

Still muryarta arude ta furta”ai mantawa nayi ban fada mashi ba” jinjina kai mutumin yai”okey, Muna jiran umarninsa”
Chapter 80 · 0% Book details