← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 152

Sashe 100

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu san wanene ba, amma saida taji gabanta Ya faɗi, ganin kakin dake a jikinshi na baƙaƙen Kaya, kuma ya rufe fuskarshi da face mask, 6oyewa tayi bayan Danish ta ƙanƙame shi tana leƙen mutumin da ke tunkaro su.

Bugun zuciyarta na ƙaruwa kamar zai fasa ƙirjinta.

Miƙa ma Danish hannu yai da niyar su gaisa, Danish Yaƙi bashi hannu saboda rashin yardar da shi, gyaran murya ya ɗanyi kafin ya soma magana a tsanake”zaku Iya kira na da Boss man, ina ɗaya daga cikin masu kula da ku,” ya faɗi hakan ne don su saki jiki da shi.

Ajiyar zuciya Angel ta sauke, jin muryarshi ta kamilallun mutane.

Dawowa tayi daga gaban shi ta tsaya tana dubanshi, ido cikin ido suke kallon juna ba tare da ƙyaftawa ba.

Tsawon mintuna kafin ta furta”Ina kwana,” ya amsa mata”lafiyalou Angel, kin tashi lafiya? Ya kuma gajiyar tafiya”
Tace”lafiyalou, gajiya tabi jiki, mun gode da kulawa” da alamun jin daɗin maganarta ya furta”Naji daɗin ganinki da ranki da lafiyarki, ina fata baki da wata damuwa” maganarshi taɗan so ta ruɗar da ita, amma sai ta basar tace”nima haka” da ƙyar ta furta ganin irin kallon da yake binta dashi, duk saita sha jinin jikinta, ta rasa gane kallon menene yake yi mata, dauriyace kawai yake yi, yaso ace zai iya bayyana mata kanshi a yanzu sai dai bazai yiwu ba.

“Ciki zamu shiga Ni da Danish, suna jiranmu a dining” ta fada don ta samu damar guduwa daga kallon da mutumin yake binta da shi.

Ɗagowa yai da ido ya dubi fuskar danish, har saida yaɗan ji gabanshi ya faɗi ganin yadda ya ɗaureta tamau babu annuri, dama tunda ya shigo falon yake mamakin kyawunshi da body structure dinshi don shi sai yanzu ya samu damar ganin shi, abakin abokan aikinsa yaji suna zuzuta kyan yaran da kamanninsu da Chief dinsu.

“Ɗan uwan naki bai magana ne? Yaƙi bani hannu mu gaisa” murmushin yaƙe tasakar mashi”rashin sabone, Yana da wuyar sha’ani amma idan kuka saba zai saki jiki da kai”

Jinjina kai boss man yai”okey, mu shiga ciki, Nima can zanje” a fakaice ta yamutsa fuska, aranta ta ayyana wannan mutumin zai takura mata ga shi da kallon tsiya kamar zai lashe mutun” a fili kuma taja hannun dashi suka nufi dining room din, Boss man na abiye da bayansu, kwata kwata babu alamun ƙauyanci atattare da Danish, sai dai jefi jefi yake satar kallon kayan alatun dake acikin katafaren falon.

Lokacin da suka shiga dining room din da sallama abakunansu, gaba ɗaya hankulansu Baful Ya dawo kansu, Ummin america tuni ta samu wuri ta zauna, ganin Angel da suka yi da danish nan fa suka fara sakin murmushi kamar wasu zautattu, kujera taja ma danish ya zauna Yana fuskantar ummi, ita kuma Angel ta zauna daga gefen shi, Sai daga bisani su Gabriel suka lura da Boss man daya shigo, kallon juna suka yi da alama sun ɗan tsorata da ganinshi saboda dressing din jikin shi yayi shige dana Giants din kurkukun ƙaddara.

Sai da Angel tace”ku gaishe shi, sunan shi Boss man, Yana ɗaya daga cikin waɗanda zasu dinga kula da mu” har suna haɗa baki wurin furta mashi gaisuwa, a mutunce ya amsa masu yaji daɗi yadda Angel tayi masu bayanin wanene shi.

Ummi ta dube shi awayance tace”barka” ya amsa mata da”yawwa ya kike fatan kin wayi gari lafiya” a yayin da yake ƙokarin zama gefen kujerar dake a kusa da ita, wadda ke fuskantar Angel, don yaji daɗin kallonta.

Ummi tace “Lafiyalou,” daga haka ta miƙe ta soma yin serving dinsu, a plates ta zuzzuba ma kowannansu abinci, ta dauki cups ta tsirara masu tea dake acikin flask, Bayan ta gama ta koma ta zauna”

Yatsun hannun parveen har karma suke yi wurin ɗaukar cup din tea, duka ta kur6e shi, ta soma cin wainar kwai hannu baka hannu ƙurya.

Batul kuwa wani sabon salon ƙauyanci, tunda ta dafi plate din noodles tasha romo da kayan haɗi, da hannu take ɗaukar indomie din tana Jujjuyata kafin ta turata abaki, ɗaya bayan ɗaya Angel ke kallonsu, Kunya duk ta kamata, koda ta daura idonta kan Jamimah robar zuma ta ɗauka ta dinga matsata a tafin hannunta ta sanya harshe tana lasa hada tanɗar baki, Angel ji take kamar ta fasa ihu.

Ummin america da boss man duk suna kallonsu sai faman sakin murmushi suke Yi.

Gyaran murya ya yi masu jamimah ta dago tana kallon shi yace”kidaina shan zumar ita kadai, ga mahaɗinta nan ki zuba asama sai ki ci” ya faɗa yana nuna mata plate din pancakes da robar yougurt’ washe mashi baki tayi tana fadin”wallahi zaƙi gareta, kunnuwana har motsi suke yi” gaba daya suka sanya dariya, Ummi kamar zata shaƙe tsabar dariya, Angel dai abin duniya ya isheta, ita ala dole mai aji kada a zubda mata mutunci su kuwa ba ruwansu bayin Allah basu san ma menene ƙauyancin ba.

“Malama, ki dauki spork da shi zakiyi amfani ki ci noodles din ba hannu ba” ummi ce tayi maganar tana nuna batul da spoon din hannunta, bata Iya cin abinci da cokali ba cos sunfi sabawa da hannu, jiki asanyaye batul ta ke faman ƴan kame kame ta rasa ina zata ɗauki cokali, Angel ce ta ɗauko shi ta miƙa mata, ta kar6a ta tsoma shi cikin indomie din batasan yadda zata kwasota ba, ganin yadda ummi take yi masu dariyar shaƙiyanci yasa ran Angel ya 6aci ta haɗe rai, muryarta aƙula tace da batul”idan bazaki Iya ci da shi ba, Ki ajiye shi ba dole” kallonta ummi tayi aikuwa ta galla mata harara, mamaki ya kama ummi ganin abun da Angel tayi mata.

Batul kuwa ta ajiye cokalin taci gaba da ci da hannunta,
Maganar Angel ta burge boss man, sai ƙara dubanta yake yi, abinci yake ci amma hankalin shi na akanta.

Haris dai tun da ya dafi chips babu maijin motsinshi, sai idan anyi magana ya ɗago da ido Ya dube su.
Mutun ɗayane baya cin abinci, Ya rasa sukuninsa, saboda mutun biyu dake zaune acikinsu, bayason baƙuwar fuska, uwa uba ummi dake ta kallon shi jefi jefi take bin shi da kallo kamar zata haɗiye shi.

Sam Angel bata lura da yanayin da yake aciki ba, sai da Boss Man ya furta”meyasa baka cin abinci ne”? Tukunna ta ɗago ta dubi Danish don ta gane dashi yake magana.

“Bakomai yake iya ci ba, danish me kake son ci”? Ta jefa mashi tambayar, shiru bai bata amsa ba, kamar tayi magana da kurma.
Ummi tana yamutsa fuska tace”ai na lura kamar mune muka takura mashi, ƙwarama ka saki jikin ka, saboda atare zamu cigaba da rayuwa acikin gidan nan”

Boss man yace”baya son baƙin fuska ne, amma tunda naga yafi sakewa da shi, Ki jaraba bashi wannan muga idan zaici” yai maganar tare da ruƙo plate din farfesu ya miƙa mata, bayan ta kar6a ta furta mashi”thank u” ta tura plate din agaban Danish.

Cikin muryar raɗa tace”pls ka saki jiki ka ci, tunda gani atare dakai, banason kana damuwa” jinjina mata kai yai alamar toh, duk don ya saki jikin shi yasa ta sanya hannu a plate din ta soma ci shima ya sanya hannun shi suka cigaba da ci atare.
Sun dauki lokaci suna cin abincin, sunyi kulu wash rabu hani’an kafin daga bisani ɗaya bayan ɗaya suka fara miƙewa,

Masu aikin gidanne suka tattara kayan abinci, bayan sun kwashe komai suka gyara dining room din tamkar ba’a ta6a 6ata shi ba.

Falo suka koma, kowannansu ya zamu wuri saman sofa ya zauna, kamar yadda Man Ya basu Umarni, yana daga zaune shida ummi suna fuskantar su, sanyin A.c sai ratsa fatar jikin su ya ke.

Sun natsu suna jiran jin me zaice”da farko dai Ina yi maku barka da zuwa gidan nan, ina fata kunji daɗin kasancewa acikin shi” ya faɗa yana dubansu.
Amsa mashi suka yi da eh, yace “good, ina fata zaku bamu haɗin kai, mu zauna peacefully babu faɗa babu cacar baki,” ɗaga mashi kai sukayi alamar eh.

Ya ƙara da cewa”na fahimci bakomai ne kuka sani ba, to duk abunda baku gane ba kada kuce zakuyi gamon kanku, hakan zai iya haifa maku matsalar da bama fata, idan kunga abu kunaso kuyi amfani dashi baku san yarda akeyi ba, Ga auntyn ku nan yai maganar yana nuna ummi dake zaune saman sofa ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya.

“Ku tambayeta zata koya maku, kada kuji shakkar komai, ku ɗauke mu tamkar iyayenku ko yayyanku, ina fata kuna jina”? Jinjina mashi kai su ka yi, Angel tayi shiru tana kallonshi, muryarshi ta tsaya mata aranta, ji take kamar tasan me irin muryar sai dai takasa gano komai.

“Zaku Iya tambayar Ƴar uwarku Angel itama, don na fahimci kamar tafi ku sanin wasu abubuwan” amsa mashi su ka yi da toh.

“Sannan duk abunda kuke buƙata ta 6angaren aike ni zaku yi ma magana, in sha Allah zanyi maku shi, Idan time din sallah yayi zanzo in tafi da mazan dake acikin ku muyi sallah akwai wurin da muke yin ibada acikin gidan nan, ina fata gaba ɗayan ku musulmai ne” ya faɗa yana dubansu
Parveen tai karaf tace”banda Danish da Gabriel sunƙi kar6ar shahada” zaro ido ya ɗanyi yana duban fuskar Danish daya haɗe rai babu annuri.

Gabriel Yace”nifa ƙarya take yi min, Nima musulmin ne”

Da zolaya boss man yace”idan har dagaske kai musulmi ne to ya akai naji sunanka bana musulmai ba”?sunnar dakai ƙasa Yai yana faman sakin murmushi.

Angel tace”nice namanta ban biya mashi shahada ba, ya faɗamin yana so ya musulunta shima” jinjina kai boss man yai, ya dawo da dubanshi gareta”shifa danish? Wani addini yake yi”?

“Bashi da addini” dafe kai boss man yai”Eyyah banji daɗin jin hakan ba, kuma bashi da ra’ayin ya musulunta kamar Gabriel”? Girgiza mashi kai Angel tayi”bayasoma anayi mashi maganar ai, ranshi 6aci yake yi, shiyasa muka ƙyale shi”

“Okey, kada hakan ya dameku, in sha Allah asannu zamuja ra’ayin shi” ta6e baki Danish yai jin abunda boss man yace.
Chapter 100 · 0% Book details