← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 152

Sashe 114

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin takun tafiyarsu yasa hajiya sarah ta ɗago tana dubansu, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin benazir, Jiki na rawa ta miƙe tana faman sakin fara’a fararen hakoranta tarr dasu ta nufi benazir tana fadin”ashe rai kanga rai? Benazir dagaske kece idanuwana suke nuna min? Wayyo Allahna, Idan ma mafarki nake Yi toh kada atadani abarni in tayi dan Allah” Rungume juna sukayi, Benazir ta fashe da wani sabon kukan bata ta6a tsammanin zata samu kyakkyawar tarba a wurin ahalinta ba, Tabbas sun bata mamaki tayi tunanin kamar yadda ta gudu babu wanda zai saurareta donta dawo gare su.
Hajiya layla sai faman sakin murmushi take Yi ita da Alhaji ubaid hankalinsu na akan Hajiya sarah data rungume benazir, Shi kuwa Alhaji musa ko kallo bata ishe shi ba, tamkar baisan sun shigo falon ba.

“Allah sarki benazir, Ashe da rabon zamu sake ganawa a duniyar nan! Tsawon shekaru sai yau Allah Ya nufa zan ƙara Yin tozali dake” ta fada tana duban benazir da hawaye suka gama wanke fuskarta
Cikin shessheƙar kuka tace”Aunty Sarah nayi danasani, naji haushin kaina, naji na tsani kaina saboda komai ya faru arayuwana laifina ne, tunda nida kaina na gudu na tafi batare da nayi shawara da kowa ba, Dan Allah ku yafe min, nasan na 6ata maku rai”
Idanuwan hajiya sarah tuni sun cicciko tab da ƙwalla, kasancewarta mace mai tausayi.
Cikin karyayyar murya ta furta”dan Allah ki daina fadin hakan, Komai ya riga daya faru kuma ya wuce”

Kafin benazir ta kuma yin magana muryar Alhaji musa ta katse masu hanzarinsu
“Idan kun gama jimamin, ku ƙaraso ku zauna” cikin isa Ya furta hakan, sai lokacin Benazir ta ɗago da ido tana dubanshi, Ya haɗe rai babu annuri sam a fuskarshi, gani take kamar baiyi farin ciki da dawowarta ba.
Ruƙo hannunta Hajiya sara tayi acikin nata, suka ƙarasa tare da samun wuri kowannansu ya zauna, zeenatu da dr shureim suna zaune saman lallausan carpet, Benazir kuma tana agefen hajiya sarah, ta ƙankame hannunta.
A tsanake Alhaji musa Yasoma yin magana batare daya ɗago da ido ba
“Da farko, Inayi maku barka da zuwa, yayana da kuma hajiya layla,’ kwa6e fuska layla tayi aranta tace”dallah jibarshi ɗan rainin wayau”
Numfasawa yai tamkar bayason buɗe baki Ya furta”benazir,” amsa mashi tayi da na’am.
Dawo nan ki zauna” yai maganar yana Nuna saman carpet daga gefen hannun sofa din da yake zaune, jiki asanyaye ta miƙe ta dawo inda ya bata umarni ta zauna.
Kowa ya natsu yana jiran jin me Alhaji musa zaice da ita.
“Meyasa kika gudu daga gidan auranki har na tsawon shekaru baki nemi kowa ba”? Kafin benazir ta bashi amsa hajiya layla tayi saurin cewa”Bai kamata kayi mata wannan tambayar ba, kodai mu da muke Iyayenta bamu tambayeta komai ba, duba da halin da tadawo gidan”
Ranshi a matuƙar 6ace ya dago da ido Yana binta da matsiyacin kallo batare daya furta komai ba
Sai Alhaji ubaid ne yace”wannan maganar bata shafeki ba, tsakaninshi da ɗiyarshine don haka ki daina sanya masu baki” harara ta wurga ma Alhaji ubaid”kaima ka sani bazan ta6a rufe baki na ba, akan me zai tambayeta meyasa ta tafi? Lokacin da ta gudun ya nuna damuwane akanta? Ko kuwa ya bada gudummuwar da za’a nemota ne eye? Daga zuwanmu gidanshi zai tsareta da tambaya? Dama ya kira mune don Ya tuhumi ƴar mu badan Ya tayamu murnar ganinta ba” tunda tafara zazzaga masifa hankalin hajiya sarah dana zeenatu ya tashi haiƙam, shi kanshi shureim jikinshi yai sanyi laƙwas, benazir dai ta saddar da kanta ƙasa hawaye na cigaba da wanke fuskarta.

Lallashinta Alhaji ubaid Ya soma Yi, Alhaji musa kuwa sai faman jinjina kanshi yake Yi, Yama rasa bakin magana

Hajiya sarah na faman yarfa hannu tace”dan Allah kiyi haƙuri aunty, idan ranki ya 6aci, nasan ba’a kyauta ba, Ni tun farko banso yace kuzo nan ba, har magana nayi mashi akan mu yakamata mu taka muje tayaku murna amma ya hanamu zuwa....” daƙyar ta ƙare maganar ganin irin kallon da Alhaji musa ke binta dashi, ba arziƙi taja baki tayi shiru

Jinjina kai yaɗanyi kafin ya ɗaura da cewa”Allah Ya huci zuciyarki Hajiya layla, Naji bazan ƙara tambayarta ba,” tayi mamakin jin abunda yace, har saida ta kalli cikin idonshi, murmushin gefen fuska yasakar mata afakaice, kafin Ya maida dubanshi ga benazir”ina yi maki barka da zuwa My daughter, naji daɗi da kika yi tunanin dawowa gida, ki kwantar da hankalinki, kuma ki share hawayenki, abunda ya faru ya riga daya wuce”
Ajiyar zuciya benazir tadan sauke, cikin sanyin murya ta soma magana”nagode uncle, sannan idan na 6ata maka rai, kayi hakuri, nasan komai ya faru laifinane, dana kama hanya na tafi”
Lumshe idanuwanshi yadanyi kafin ya waresu akan fuskarta”kada ki damu ni ban ruƙe ki araina ba, kawai dai banji dadin guduwar da kikayi bane na tsawon shekaru batare da kin tuntu6emu ba, amma yanzu tunda kin dawo da ranki da lafiyarki falillahil hamdu, sai dai fatan Allah ya kyauta gaba, In sha Allah zanyi ƙoƙari dan ganin na inganta maki rayuwarki, duk wani abu da kike buƙata ki sanar dani zanyi maki shi, kada ki ƙara yunƙurin guduwa saboda muna buƙatarki, zaifi ki sanar damu idan ma wani abune ya 6ata maki rai a tsakaninmu zamu Iya sama maki solution, Ina fata kina jina”
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh, lamarin Alhaji musa ya ɗaurewa hajiya layla kai, bata ta6a tsammanin ya iya tsara kalami irin haka ba, hatta Alhaji ubaid yai mamakin yadda ya sakar ma benazir fuska yana yi mata magana cikin lallami, aranshi ya ayyana wata’ƙil tsananin tausayinta ne Ya kamashi, yaji dadin hakan, hankalin hajiya sarah ya kwanta dana zeenatu, sai faman sakin murmushi suke Yi, haka zalika dr.shureim shima murmushi ne akan fuskarshi.
“In sha Allah uncle bazan ƙara yunkurin guduwa ba, duk runtsi duk wuya zan zauna atare daku, nima nayi danasanin abunda na aikata,
Gyaɗa kanshi yai,
Hajiya sara tace”tun ɗazu fa na sanya masu aiki sun shirya maku lafiyayyan abinci, yakamata muje muci kada ya huce” da fara”a akan face dinta ta furta hakan,
Miƙewa sukayi atare suka dunguma zuwa dining room, benazir ta girgiza da ganin daular uncle musa, Gidan Ya tafi da imaninta.
Saman dining chairs suka zazzauna, ga kayan abinci an jera masu saman table,”
Tani da lami ne suka zo domin yin serving dinsu, Bayan sun gaishe da alhaji ubaid da hajiya layla, suka soma zuzzuba ma kowannansu abunda yake ra’ayin ci, hankalinsu kwance suke ci baka jin sautin komai saina ƙarar cokulansu.
Jefi jefi zeenatu take satar kallon benazir da zarar sun haɗa ido sai ta sakar mata murmushi, Ta fahimci yarinyar ba ƙaramin so take Yi mata ba, Dr shureim na kallonsu, shima murmushine akan fuskarshi, Hajiya layla dai taƙi sakewa, itafa har yau har gobe bazata ta6a yadda da alhaji musa ba, gani take yi kamar akwai wata manufa atare dashi, abincin ma daƙyar take cin shi”

Bayan sun kammala cin abinci, Hajiya sarah ta rakasu zuwa masaukinsu da zasu zauna, Hadaddun bedrooms aka ware masu, Zeenatu ta hana benazir sakat, tsabar Iyayi hada ɗauko bargonta da pillow ta dawo down stair dakin benazir donsu dinga kwana atare, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,

*SIR MUBARAK✊*

Yana acikin dangi suna ta yin firar yaushe rabo tare da Ƴan uwanshi, Wayarshi dake acikin aljihunshi ta soma Yin ruri, kusan sau uku kiran na shigowa yana yin rejecting batare daya ankare ba, saboda hayaniyar ƴan uwan shi da suke Yin fira a tsakaninsu, a babban katafaren falon gidan, a kira na huɗune, Senate lateef dake zaune gefenshi ya ankarar dashi ta hanyar yi mashi magana ka duba wayarka tun dazu nake jin sautin ringing ɗinta, amsa mashi yai da toh, sai da ya fara curo wayar ya duba sunan mai kiran nashi tukunna ya mike yai masu sallama Ya nufi ƙofar fita daga babban falon, bayan ya fitone Ya dakata da yin tafiya, Yabi kiran da aka yi mashi, bugu ɗaya aka ɗaga kiran
“Major, ince dai lafiya? Naga miss call dinkane”
On the other hand major yace”yalla6ai yaron nan na wurinka jazz Ya fita daga gida Yanzu haka da nakeyi maka magana munbiyo bayanshine muna asaman titi,”
Cikin saurin murya sir mubarak yace”gani nan zuwa, kubi a hankali kada ku bari yaganku yaron wayau ne dashi, yanzu zamu biyo diddiginku” tunkafin maijor ya amsa mashi yai saurin yin rejecting call din, Ya dannawa driver dinshi Kira bugu ɗaya ya daga”Ina jiranka abakin entry hall na gidan baba, kazo da mota ka daukeni”
Ya ƙare maganar tare da kashe kiran, Jikin shi har tsuma yake yi fatan shi Allah ya basu nasarar kama jazz don ganin menene yake aikatawa,
Badajimawa ba baƙar mota ƙirar Range rover ta shararo da matsakaicin gudu bata nufi ko’ina ba sai bakin entry hall adai dai nan Tiger Yai parking dinta, Jiki na rawa sir mubarak Ya buɗe front seat na motar ya shige tare da bashi umarnin su tafi, reverse yai kafin ya karya kwana Ya nufi tanƙameman gate din fita daga estate din dake a kewaye da jami’ai, tunda suka hango sir mubarak ta tagar motar basu yi gigin dakatar dasu ba, kaitsaye motarsu ta haura saman titi, da gudun gaske tiger yake driving dinsu tamkar zasu tashi sama, sir mubarak yai amfani da phone dinsa wurin bin diddigin su major, cikin sa’a suka samo location din da suke, dare ne tamkar da rana saboda hasken street light daya gauraye ko’ina, hanyar da suka biyo kwata kwata babu mutane, sababbin gine gine ne a unguwar, wani ginin ma ba’a kammala shi.
Chapter 114 · 0% Book details