← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 152

Sashe 38

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun kafin sojojin su ƙarasa Gabansu yai wani irin faɗuwa saboda razanar da su ka yi da ganin shi, Wani abu ya ɗaure masu kai, har saida su ka kalli junansu da alamun ruɗu akan fuskokin su, Ba Iya kyawun Fuskar Danish bane Ya girgiza su, Zazzafar surar Jikinshi Ta yi matuƙar rikitar dasu, Kaf a cikinsu babu mai kalar ƙirar ƙarfin shi, Hakan ba ƙaramin kokwanto Ya saka masu ba acikin zuciyoyin su, har sun fara kokwanton Anya kuwa ɗan ta’addan da suka Biyo ne yai garkuwa da yaran? Ta ya ya za’ai ɗan ta’addan Ya iya sato wannan jibgegen ƙaton mai ƙirar sadaukan Yaƙi, a ganin su ko shi ɗan ta’addan bai kama ƙafar Matashin yaron ba wurin zubin halittarshi.

Muryar Gabriel da sassarfa yake Ambaton sunan danish Hannayenshi duka biyu akan jikinsa sai jijjigashi yake yi yana faɗin”Danish ka tashi, mun samu taimako za’a fidda mu daga cikin daji, Har ma an tafi dasu Angel, pls ka tashi, Bana so mu tafi mu bar ka”

Ko motsi Danish bai yi ba, ganin haka yasa shi juyawa yana kallon Sojojin, Sun ƙame a tsaye suna kallon Abun al’ajabi kusan suman tsaye sukayi yayin da suke kallon Danish
“Dan Allah ku taimake ni, ɗan uwanmu ne, haka Allah ya halicce idan Yana yin bacci yakan ɗauki tsawon awanni bai farka ba,” a ruɗe yake kora masu bayani, duk don ya samu su tafi da Danish kada suce zasu barshi anan, don ya fahinci tashin shi ba yanzu ba

Daƙyar ɗaya daga cikin sojojin ya iya shanye mamakin shi ya sarrafa kanshi wurin furta” bai da lafiya ne? Ko ya suma ne”?

“A’a, bacci ya ke yi, kuma ba zai Iya farkawa yanzu ba, ....”tun kan ya ƙarasa maganar ɗaya daga cikin soldiers ɗin Ya zaro penlight ya zuƙunna agaban shimfidarsa, da yatsun hannayensa yai amfani wurin gwale idanuwan Danish ya haskasu ya tabbatar da yana araye ga numfahi na fita a tsanake, Kallon sauran sojoji yai”he’s alive” jin haka yasa suka gasgata maganar Gabriel, mutun Biyu suka ranƙwafa tare da ɗaura hannayensu da nufin su cuccu6i Danish sai dai wani abun ɗaure kai ko motsi baiyi ba, saboda tsabar nauyin sa duk irin ƙarfin da Allah ya yi ma sojojin na halitta da kuma na horon aikin da suka samu baisa sun Iya cuccu6ar Danish ba, A ƙarshe suka Yanke shawarar zuwa ɗauko stretcher domin ɗaukar shi, zaifi Yi masu sauƙi, abun ɗaukar Majinyatane da ake amfani dashi, Yana da maruƙi a jikin sa, saman shi faɗine dashi kamar allo, bayan sun ɗauko stretcher ɗin Saida suka haɗa ƙarfi su huɗu tukunna su ka iya cuccu6ar Danish tare da ɗaura shi saman abun ɗaukar, su ka ɗaga shi har zuwa Bakin helicopter din kafin suka samu damar shigar dashi ciki, Bayan sun tafi da danish Ɗaya daga Cikin Sojoji biyu da suka rage Ya ɗauki Back pack ɗinsu da ya gani a jikin bishiya, don suna buƙatar duk wasu shaidu da za su zamar masu hujja.

da hannu ɗaya ya ruƙo jakar ɗayan hannun kuma ya ruƙe hannun akwatin kayansu Yaja shi zuwa Bakin jirgin.

A can Cikin Dajin Gabriel ne Ya rage tare da Sojan nan, Suka kuma kutsawa cikin dajin Don ya sanar mashi akwai sauran Ƴan uwanshi, Abun dai ya ɗaurewa Sojan kai, Su fa duk a tsammaninsu ɗan ta’addanne ya yi garkuwa da su daga ƙasar su america Ya shigo da su Dajin, Saboda Yaran sunyi kama da mutanan ƙasarsu, Hasken fatarsu da Doguwar sumar kawunansu, a hasashensu kenan, sai dai duk da haka sun ɗanyi mamakin wasu abubuwa da suka sanyasu yin al’ajabi, tayaya har ɗan ta’addan ya iya guduwa dasu bayan ƙasarsu tana da mugun tsaron da babu wani shege da ya isa Ya ƙetare ta cikin Salama, Abu na biyu Ta ya ya Ɗan ta’addan Ya iya ɗaukar mutun mai mugun Nauyi irin matashin saurayin da suka gaza ɗagawa? Abu na uku da ya ɗaure masu kai Uniform ɗin Jikin yaran masu ɗauke da numbobi sunyi mamakin hakan.

Suna Cikin yin tafiya, Zuciyar Gabriel na dakan uku uku tamkar zata faso kirjinshi ga kishirwa da ya ke ji, babban tashin hankalin shi Ina Su Batul suka kutsane a cikin Dajin? Ga dare yana shirin yi masu adajin, fargabansa kada sojojin su ce zasu tafi.

“Kana tunanin ƴan uwanka zamu same su? Lokaci Yana ƙure mana” Sojan ne yai mashi maganar, gabriel bai samu damar amsa mashi ba saboda tashin hankalin da ya ke aciki, Sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansa ya ke yi akan bishiyoyin dake a kewaye dasu, Suna Cikin yin tafiya suka ƙaraso gaban wannan ramin mai ɗauke da ta6o, har zasu gifta shi Kwatsam Sojan Yaji ya taka wani abu, Da sauri Ya ɗage ƙafarshi yana kallon Warin Slipper ɗin dake asaman ciyayin, Gabriel na ganin takalmin Ya zuƙunna tare da kai hannu ya ɗauke shi, Gabansa ne ya faɗi A gigice ya kalli sojan tare da furta”Takalman Ƴar uwata ne!” Ya gane slippers ɗinsu ne Da tsohuwa Tamira tai masu kyautarsu, dama tunda suka shigo Dajin da takalmansu suke yawo a ƙafafuwansu, shiyasa ko ƙaya ba ta ta6a shigarsu ba.
“Dan Allah ka taimaka mun, wlh takalmansu Batul ne ƴan uwana” Muryarshi na rawa yake maganar, cikin ƙagara.
Waige-waige Sojan ya ke yi yana bin ko’ina Na dajin da kallo, Kafin ya sauke idonshi akan Ramin ta6on, kasancewar Sojoji suna da ƙwarewa wurin sanin takan Daji, Nan take ranshi ya bashi cewar Ta6on da ke a wurin Ramine, mutun zai Iya rubzawa cikinsa, musamman wanda ke gudu cikin fitar hayyaci.

Matsawa yai gaban ramin, Bayan ya soke bingidar hannun shi a ƙugun shi, Ya ɗan zuƙunna saman ƙafarshi, a tsanake Ya tura hannun shi Cikin ramin ta6o, Cikin sa’a Ya damƙo gashin ɗaya daga Cikin su, matsar da hannun shi yai ya ruƙo Hannunta, Ya ɗago da ita gaba ɗaya jikinta ya 6aci kaca kaca da ta6on baka Iya ganin komai na fuskarta, hatta Gabriel bai gane wacece a cikin su ba, A ƙasa sojan ya kwantar da ita tare da ƙara zura hannun shi Ya ƙara cafko hannun wata ya curo ta, bayan ya kammala zaraso duka ukun Gabriel Yace mashi suke nan babu saura, Jin haka yasa Sojan Zaro wayarshi Ya sanar ma sojojin dake a bakin helicopter din cewa sun ƙara samu Yara Uku azo da stretcher a ɗauke su, Cikin ƙanƙanin Lokaci sai ga sojoji sunzo da abun ɗaukar, duka ukun suka ɗaurasu saman shi kamar tsummokarai haka suka nannaɗe.

Sojoji biyu ne suka tafi dasu zuwa Inda jirgin ya ke, Hankalin Gabriel Ya ɗan kwanta sam ya manta da Haris saida suka kamo Hanya zasu Nufi jirgin ba zato ba tsammani su ka ci karo da haris a sume, Ba tare da 6ata lokaci ba, Sojan da suke atare Ya sa6e shi saman kafaɗa, suka nufi Jirgin Bayan sun Shiga su dukansu. Matuƙar jirgin suka Tada shi, Da wata irin jijjiga tayoyin jirgin su ka soma motsawa suna yin tafiya sannu a hankali, Gabriel da ya kasance shi kaɗai idon shi biyu, farin Ciki duk ya cika shi, sam baiyi tunanin wace ƙasa za’a kaisu ba, hankalin shi bai kai nan ba, fatan shi su bar dajin Cikin ƙoshin lafiya.

Bayan tashin jirgin sama Ɗaya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ƙofar helicopter ɗin ne Ya kanga Tactical phone ɗin hannunsa jikin kunnansa Yana magana Cikin Harshen turancin muryarshi na fita da amon murya saboda ƙarfin iskar Dajin

“We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S. with the eleven children we found in the forest.” (Munyi nasarar cafke mai laifin, yanzu muna akan hanyar mu ta dawowa U.s, tare da yara goma sha ɗaya da mu ka samu a dajin)

Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya miƙi hanyar komawa ƙasar da ya fito.

*Alhamdulillah Finally Ex-prisoners sun Bar Evil forest Fatan Nasara*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E12🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

*GIDAN ƊAN IYA*

Gaba ɗayan su sun Hallara a bakin Entry hall na shiga palourn gidan, Mommy da Mami sun yi matuƙar yin kyau cikin shigar Lace, Zahra da Aneelerh sai Abie da Uncle ɗan Iya sun yi shiga ta alfarma, Bakomai ne yasa su fitowa ba fa ce tarbar Su Hajiya adama, A ƙagare su ke da ganin baƙin nasu, badajimawa ba su ka kira Aneelerh awaya su ka sanar da ita cewa sun shigo garin abuja, har ta tura masu da addrress ɗin gidan.

Ƙarar Horn ɗin motarsu ne Yasa kowan nan su Sakin fuskarshi, da sauri mai gadi Ya fito daga ɗan ɗakin sa, Ya je ya buɗe masu gate.

A hankali Danƙareriyar Motar uncle abdallah ƙirar Kia optima ta kunna kai cikin gidan kai tsaye ya nufi wurin Ajiye motocin su, bayan yai parking ɗin motar, Ya fito daga ciki fuskar nan ɗauke da annuri, ya ɗauki wankan shadda gezna, ƙafafuwanshi na asanye da patent leather shoes launin Shaddar shi, ƙamshi ta ko’ina.

Zagayawa yai ta other side ɗin motar ya buɗe ma Hajiya adama ƙofa, ƙafar ta ta fara zurowa nan take Zahra ta ɗan zaro ido tare da kallon Aneelerh, murmushi gefen fuska Aneelerh ta sakar mata don ta fahimci abunda ya sa zahra mamaki, wato tsadar High hills ɗin dake ƙafar Hajiya adama.

Zahra ta ƙware wurin sanin farashin Kaya, A kunne ta yi ma Aneelerh whispering

“Surukar ki Ta ji naira yasin, Takalman ƙafarta kalar na saratu obinna ne” girgiza kai Aneelerh ta yi ba tare data tanka mata ba.

Lokacin da Hajiya Adama ta ƙara sa fitowa daga Cikin Motar ba ƙaramin tafiya ta yi da imaninsu ba, saboda tsabar wankan kece rainin da ta ɗauka na tsadadaddan Swiss cord lace launin brown mixed wit yellow, Riga da zani ne ta daura, kanta yasha ɗaurin ɗan kwali, sarƙar wuyanta da awarwaron hannun ta, da zabbanta duk na zinari ne, ta yarfa mayafin kayan saman kafaɗarta, babu make up a saman fuskarta zallar kyan da Allah ya yi mata ne, Hajiya adama akwai kyau ga diri.
Chapter 38 · 0% Book details