Sashe 135
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Uwar gida sarautar mata, Gimbiyata, Ina neman afwarki ranki shi daɗe, bai kamata gimbiya tana fushi da bawanta ba, Ni fa a karkashin inuwarki nake, da taimakonki nake samun natsuwa da kwanciyar hankali, taya zanso na 6ata maki rai? Bayan kece linzamin dake sarrafa ni....”
Tun da yafara gaya mata daɗaɗan kalamansa, ta fara sassauta fushin fuskarta,
A hankali ta buɗe idanuwanta kan fuskarshi, da sauri ya kama kunnuwansa Yana fadin”Am sorry My wife, na gane kuskurena”
Ta6e mashi baki tayi”Ni so nake ka fadamin meke damunka? Da har yai silar hanaka runtsawa, kalli fuskarka duk ta yamutse, idanuwanka sun ƙanƙance saboda rashin baccin da baka yi ba” ta faɗa tana faman 6ata fuska, yayi shiru yana kallonta batare daya furta mata komai ba.
“Kai nake sauraro! Meke damunka? Sannan naji kana waya ɗazu, akan za’a tura da jet zuwa sudan, wa za’a ɗauko”? Ta jefa mashi tambayar cike da son jin amsar shi.
Ya rasa amsar da zai bata, Ta kafe shi da ido.
Gyara muryarsa yadanyi kafin yafara magana a tsanake.
“Sheikh imam nake son gani, baya a ƙasarne ya tafi sudan, Ina buƙatar ganinsa da gaggawa akwai taimakon da zaiyi mani”
Fuskarta da alamun mamaki ta furta”meyasa kake son ganin shi? Wani kalar taimako zaiyi maka”
“Wani matashin yarone yake fama da aljanu sun hana rayuwarshi sakat, jiya ina zaune tare da baba muna yin firar yaushe rabo, a lokacin da bamuyi tsammani ba, yaron ya faɗo falon gwanin ban tausayi, duk mai imani idan yaji irin jarabtar da yaron yake fuskanta sai ya tausaya mashi.....” tun da ya fara magana gimbiya mujeedat ta yunƙura ta miƙe daga zaune tana dubanshi, Ya fayyace mata komai sai dai bai faɗa mata da suffar da ya ga yaron ba.
“Na yanke shawarar yin magana da sheikh Imam akan halin da yaron yake aciki, Ina da tabbacin zai taimaka mashi In sha allah, yanzu haka da nake yi maki magana, sheikh imam Yana akan hanya, Ina tsammanin nan da ƙarfe goma jirgin daya ɗauko shi zai yi sauka a nigeria.
Yanayin fuskartane Ya canza, yayin da take kallonshi, Ya rasa gane kallon menene take yi mashi, har dai yagaza jurewa jin shirun yayi yawa yace”baki fahimci abunda nake fadi bane? Ko bakiji dadi bane”?
Girgiza mashi kai tayi”ko ɗaya mijina, wani abune yadan bani mamaki, nasan halinka ne yin taimako, indai abune daya shafi aikin Allah kana akan gaba, amma tunda nake arayuwata ban ta6a ganin tausayi da ya kai wannan ba atare dakai, saboda yaron jiya ba ka yi bacci ba, aduk lokacin da ka dawo gida a yanayi na damu nasan yadda zan shawo kanka in kwantar maka da hankalinta harma kayi bacci, amma adaren jiya saboda damuwar halin da yaron yake, waɗannan dabarun nawa basuyi maka aiki ba, bayan haka ka tura da jirgin da zai dauko malamin da zai duba shi daga Sudan zuwa Nigeria, saboda kana buƙatarshi da gaggawa don ya duba yaron....” ta faɗa fuskarta da alamun ruɗani, yayin da Hateem ya natsu yana sauraronta abunda bata sani ba ayanzun ma da take yi mashi magana hankalin shi yafi karkata kan agogon dake sanye a wrist din hannun shi, burinshi goma ta buga.
“Abunda yafi ɗaure min kai mijina, wanene yaron? Menene alaƙarka da shi? Yanayin yadda ka nuna damuwa akanshi ko ɗan cikin ka sai haka”
Jim ya ɗanyi kafin ya furta”bani da alaƙa da shi, bansan shi ba! Kuma ban ta6a ganin shi ba, kamar yadda na faɗa maki adaren Jiya idanuwana suka fara yin tozali da shi, tun daganan sai naji ƙaunarsa ta kama ni, har naji ina son na taimaka mashi, sai nake jima kamar nike da alhakin ciwon shi, idan har ban taimaka mashi yaji sauƙi ba Allah zai iya kamani da laifin ƙin tallafa masa da banyi ba”
Murmushin gefen fuska Gimbiya mujeedat ta sakar mashi har fararen hakoranta suka bayyana.
“Kai din na dabanne mijina” ta faɗa tana matsawa kusa dashi, ta ɗaura hannunta na dama saman sumar kanshi.
“Samun miji kamarka a duniyar nan abune mai wuya, kana da tausayi da jinƙan na ƙasa dakaina, sannan kowa naka ne, burinka ka faranta ma wanda yake acikin kunci koda ta silar hakan kai zaka rasa naka farin cikin, ni kaina ina ilmantuwa da kyawawan ɗabi’unka da halayanka, shiyasa nake alfaharin mallakarka da nayi a matsayin mijina” lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kalamanta ba ƙaramin faranta mashi suke Yi ba, tamkar tana ƙarfafa mashi gwiwane.
Zame hannunta tayi daga kan sumar shi zuwa gefen fuskarshi idanuwansu cikin na juna
“Kamar yadda ka sani, duk abunda kakeso nima inason shi, koda bana son shi saina yi kokarin koya ma kaina yadda zanso shi saboda mijina yana son shi, don haka nima ina goyan bayanka akan Yaron, Allah ya baka sa’a mijina ya cika maka burinka na ganin yaron ya samu lafiya, A shirye nake dana bada gudummuwata wurin ganin mun inganta rayuwarshi”
Murmushine ya bayyana akan fuskar prime minister, kallonta kadai da yake yi natsuwa yake samu, musamman idan tana ƙarfafa mashi gwiwa da daɗaɗan kalamanta.
“In sha Allah zamuyi nasara, yaushe zaka bani iznin zuwa ganin yaron”?
“Na yanke shawara idan yaji sauƙi, zan gayyace shi zuwa gidan mu, zamu shirya mashi dinner.”
Tsantsar farin cikine akan fuskarta”naji dadin jin hakan mijina, wallahi har na ƙosa naganshi, duk na kagu gashi bazamu daɗe a ƙasar ba, kwanaki kadan suka rage mana” ta fada tana 6ata fuska alamar bataso hakan ba.
Damƙo hannunta yai da take kokarin shafa wuyanshi, fari sol dashi, ga wani shu’umin kamshi dake fita sako da lungu na jikinta, sumbatar tafin hannu yai, ba tare da ya sake shi ba ya dago da reddish eyes dinshi akan fuskarta”yaron marayane bashi da kowa, Owais ne ke kula da su, zan nemi alfarmar yabar min shi mu tafi canada atare, inaso ya maye min gurbin abunda narasa” sai yanzu ta fahimci damuwarshi.
Tausayinshi ne ya kamata, tuntuni tasan yana da burin samun ɗa Namiji, yaso ta ƙara haifa mashi ƴa’ƴa sai dai shiru babu alamun zasu sake samun ƙaruwa, kuma lafiyarta ƙalau saboda shi yasa bata yin tsarin Iyali, Allah ne bai nufa zata ƙara haihuwar ba.
Kafin ta buɗe baki tayi mashi magana, wayarsa dake ajiye cikin aljihun shi ta soma yin ringing, ya riga da yasan wanene Ya kirashi.
Da sauri Ya saki hannun Gimbiyarsa, Ya zura hannu ya zaro wayar picking call din yai tare da karata a kunnanshi, gimbiya mujeedat ta kura mashi ido tana kallon shi
“Alhamdulillah, Allah ya kawo ku lafiya,” iya abun da taji ya furta kenan, zame wayar yai daga kunnanshi yana dubanta yace”sun sauka lafiya”
Gimbiya mujeedat tace’shiyasa naga farin ciki akan fuskarka, sheik imam yaƙaraso kenan, bari nayi magana da masu aiki su shirya maku breakfast dinku”
Ta fada tana kokarin daukar phone dake ajiye on nightstand da sauri ya ruƙo hannunta, ta dago da ido suka kalli juna
“An shirya mashi breakfast dinshi, tun acikin jirgi, ina da tabbacin babu yunwa ko gajiya atare da shi, nafi buƙatar idan ya ƙaraso mu tafi gidan Owais din”
“Amma kaifa? Baka ci komai ba, Yakamata kayi breakfast dinka, zaka fi samun kuzari”
Girgiza mata kai yai”Bana buƙata, saboda bani da natsuwar cin abinci, Idan har yaron nan bai dawo dai dai ba, nafi son idan Ya samu sauƙi, muci abincin atare da shi”
Tsantsar mamakin kalamansa ne ya daure mata kai, bata ta6a ganin ƙauna kalar wannan ba, Ko a shirin film.
“Amma kasan bana iya yin breakfast ba atare dakai ba, idan har baka ci ba, nima bazan ci komai ba, har sai ka dawo gidan” cikin tausasa harshe tayi maganar.
“Yau kawai, Kiyi hakuri kiyi breakfast tare da su Yazrin, bazan jima ba, in sha Allah atare zamu yi lunch dinmu”
Kwa6e mashi fuska tayi hadi da marairaice mashi tamkar zatayi mashi shagwa6a ta furta”bazan takura maka ba, Na kar6i uzurinka”
“Ki tashi ki shirya inaso ku gaisa da shekh imam kafin mu wuce gidan owais” amsa mashi tayi da toh, kafin ta sauko daga saman gadon, shima ya miƙe yana bin bayanta da kallo, har ta 6ace ma ganinsa, jim kadan ta fito sanye da Abaya launin Maroon tayi rolling mayafi akanta, ruƙo hannunta yai acikin nashi, suka nufi kofar fita daga dakin.
Lokacin da suka shigo babban katafaren palourn gidan, masu yi masu hidimane suke ta gudanar da aikace aikacen su, kowan nan su sanye da uniform baƙin wando da farar shirt, matasan ƴan mata, duk inda Suka gifta jiki na 6ari suke gaishe dasu cikin girmamawa, yayin da su kuma suke amsa masu da fara’a.
Yanke shawarar zuwa bedrooms din Ƴa’ƴan su suka Yi, kafin ƙarasowar Ya sheikh, Yana da buƙatar suma su kasance cikin shiri donsu yi mashi kyakkyawar tarba.
elevator suka hau ta daukesu zuwa upstairs, bayan ta sauke su suka fito batare da sun saki hannayensu da suka ruƙe acikin na juna ba, kaitsaye suka nufi bedroom din ƴan matan su.