← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 152

Sashe 56

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Agaban mirror Ta tsaya tana kallon Kyakkyawar fuskarta, batasan lokacin da murmushi Ya kubce mata ba, nan take dimples ɗinta biyu suka lotsa, yatsun Hannayenta, ta tura cikin sumar kanta, a hankali ta soma barbaza gashin, aranta ta ayyana inama akai su saloon Agyara masu gashin kansu ba ƙaramin kyau za su yi ba, fanfo ta kunna Ruwa Ya soma kwararowa cikin sink, ta shigo da niyar ta wanke fuskarta sai kuma ta tsinci kanta da sha’awar son Yin alwala, nan take ta canza ra’ayinta, Tsarki ta fara yi kafin ta soma Yin ta a tsanake, bata manta komai na daga yadda akeyin alwala ba, bayan ta kammala Yi, ta fito daga Cikin toilet ɗin tana Tunanin tayaya zata Iya yin sallah bayan babu Hijabi? Buɗe ƙofar da akayine yasa ta ɗago tana kallon mai shigowa nurse ce ta shigo hannunta ruƙe da tray na kayan breakfast ɗin Angel asaman table ta ɗaura mata shi.

Ɗagowa tayi suka hada ido da juna”Is there anything you need?”

Da sauri tace”Hijabi da abun sallah inaso zanyi”
Da murmushi akan fuskar nurse ɗin tace”are u muslim”? Ɗaga mata kai Angel ta yi alamar eh, nurse ɗin tace”Okey, ki jira ni yanzu zan dawo”

Fuce wa tayi daga ɗakin, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tana ƙare ma ɗakin kallo, shigowa nurse ɗin tayi hannunta ruƙe da hijab da Prayer mat ta miƙa mata, Farin Ciki a wurin Allah bakinta yaƙi rufuwa.
“Thank u so much” nurse ɗin na murmushi tace da ita”never mind” ita kanta batasan Ina ne alƙibla ba, sai da ta tambayi nurse ɗin tayi amfani da wayar hannunta wurin yi mata bincike ta gano mata Alƙiblar da zata fuskanta tukunna ta shimfiɗa carpet ɗin, a tsanake ta kabbara sallah, saman chair nurse din ta zauna tana jiranta, Raka’a Biyu Angel tayi kafin ta sallame sallar, wani irin daɗi take ji yau tayi sallah, bakinta yaƙi rufuwa, tafin hannayenta biyu ta ɗaga sama tana karanto addu’o’ kirari tafara yi ma Allah kafin tayi ma ƴan uwanta da suka rasu addu’a, da su kansu a ƙarshe ta roƙi Allah akan Ya haɗa ta da ƴan uwanta ba tare da ta sha wahala ba, Allah yasa daddynta Yana araye, da auntynta Aneelerh. bayan ta kammala Yin addu’ar, Ta shafa a fuska, ta yunƙura ta mike, ta nannaɗe prayer mat ɗin da hijabin ta dubi nurse ɗin

“Kin gama” ɗaga mata kai Angel tayi alamar eh, Miƙewa tayi tare da zuwa gaban angel ta kar6i carpet din da hijabin juyawa tayi ta nufi closet ɗin ɗakin ta buɗe ta sanyasu aciki.

“Aduk lokacin da kika buƙaci yin ibadarki zaki iya ɗauka ki yi” godiya Angel tayi mata, daga bisani ta zauna zaman Cin breakfast, lafiyayyan kalaci aka haɗa mata, tana ci tana tunane tunane sam tamanta da sojojin dake jiranta.

Sai da ta kamalla cin abincin ta ƙoshi, Nurse ɗin ta tattara komai ta fuce dashi, Zama tayi gefen gadon idonta akan ceilling ta ƙurawa haɗaɗɗen kwan ɗakin ido, Yayin da zuciyarta ke tariyo mata abubuwan da suka faru.

Ba zato ba tsammani ta tsinkayi muryoyinsu a yayin da suke shigowa ɗakin, A hanzarce ta miƙe tana faman zazzare gray eyes ɗinta akansu, sojojinne tare da likitocin, saman doguwar sofa ɗin ɗakin suka zauna a jere suna fuskarta, Dr Laura davis ta zauna gefenta, Kamar wata mara gaskiya duk ta kama kanta, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba.

“Masoyiya Allah fatan Kin wayi gari lafiya? Ya jikin naki” muryarta adabarbarce tace”da sauƙi sosai” cikin kulawa suke Yi mata magana da harshen turanci

Dr Mark jackson ne ya fara yi mata magana”mun nemi jin bayani daga bakin ɗan uwanki Gabriel sai dai bai bamu haɗin kai ba, Yace duk abunda muke son sani ke ce zaki amsa mana.

Jin wannan maganar yasa hankalinta ƙara ɗugunzuma.

Fahimtar yanayin ta ne yasa dr mark cewa” Ki kwantar da hankalin ki, Bamu zo da niyar mu takura maki ba, Ƴan tambayoyi ne zamuyi maki da zarar kin amsa mana zamu tafi, munfiso ki natsu kiyi nazari kafin ki amsa mana”

“Kin shirya”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh, duk tabi tasha jinin jikinta.
“Da farko zamu so ki fada mana Ya akai kuka tsinci kanku A daji? Waye ya kai ku can? Sojojin kasar mu suna hasashen ɗan Ta’addan daya gudu zuwa canne Yai garkuwa daku don ya kare kanshi daga farmaki da suka kai mashi, shin dagaske ne ko kuwa? Ƙura masu ido ta yi ɗaya bayan ɗaya take kallon fuskokinsu, tsabar fargaba ƴan hanjin cikinta sai kaɗawa suke Yi, Tarasa Tayaya zata fara basu amsar tambayarsu? sam ba ta jin zata Iya faɗa masu ainihin Abunda Ya faru da rayuwarsu, ita aganinta kamar idan suka ji zasu guje su ne, musamman idan Danish Ya farka a matsayin giant ba ƙaramar masifa zaija masu ba, Zaiyi wuya su yarda da abunda zata faɗa masu, saboda Labarin baƙar izayar da suka sha a prison ba kowane zai gasgata kalamanta ba, zama su Iya tunanin ƙarya take yi masu, bayan haka tana tsoron ta fada masu, su kuma su tara Ƴan jarida su sanar dasu a ɗauki hotunansu ayi share da labarin prison tabbas yin hakan zai jaza masu babbar matsalar da zata Iya ja su rasa rayukansu don tasan dole Shuwagabannin kurkukun ƙaddara su bibiyi rayuwarsu ko dan saboda abu biyun nan na farko Garkuwar kurkukun da su ka gudu da shi, Na biyu don kada su tona masu asiri.

duk da sanyin A.c dake ratsa fatar jikinta hakan bai hanata zubar da zufa ba, ta ko’ina take tsastsafo mata, Hakan ba ƙaramin ɗaure masu kai yai ba, farat ɗaya suka fahimci akwai wani gagarumin al’amari atattare da yarinyar sai dai zaiyi wuya ta iya sanar da su gaskitar zance.

Gyaran murya Commender yai mata, A hargitse ta wurga eye balls ɗinta akan fuskarshi

“Kin yi shiru baki ce komai ba meyasa”?

Dafa kafaɗarta dr laura tayi da hannu ɗaya”Ki kwantar da hankalin ki my daughter, Ki natsu ki bamu amsa, a shirye mu ke da mu taimaki yaruwarku, haɗin kanki kaɗai muke buƙata, kuma muna tabbacin zaki Amsa mana tambayoyin mu”

gaba ɗaya ta ruɗe saboda saƙe saƙen da zuciyarta ke yi mata, wani sashe Yana jan kunnanta akan karta kuskura koda gigin wasa tace zata faɗa masu abunda ya faru a rayuwarsu, Yayin da wani sashe na zuciyarta ke Jan hankalinta akan ta faɗa masu wata’ƙil su taimaka masu wurin kawo ƙarshen Azzaluman kurkukun ƙaddara, Yanzu idan ta 6oye masu taƙi faɗa masu gaskiya kwatsam wani abin da ba’a fata ya zo ya same su har su rasa rayukansu shikenan tarihin kurkukun ƙaddara zai cigaba da wanzuwa ne.

Sun tasata gaba kamar sun sami tv, duk sun ƙagara da su ji amsarta, gashi taƙi buɗe baki tayi magana.

“Idan har baki bamu amsar tambayoyinmu ba, zamu maida ku Dajin da muka ɗauko ku”! Acewar Major

Ras Taji gabanta ya faɗi, Lokaci ɗaya ta fashe masu da matsanancin kuka mai ratsa zuciya Cikin shessheƙar kuka take faɗin”Ni bansan komai ba, Bazan Iya tunawa ba, Namanta komai, ɗan uwana danish shi ya sani”

Ta ƙara rikita masu lissafi, Captain yace”kun haɗa baki ne? Mun tambayi ɗan uwanki Gabriel ya faɗa mana cewa ke kaɗaice kika san komai, Yanzu kuma mun tambayeki kince kema bakisan komai ba A tambayi Danish! Why kuke son Yi mana yawo da hankali....? Da alama Ya Hasala ne dan muryarshi a kausashe yake mata magana.

Da sauri dr laura ta katse shi”Sir, bata da ƙoshin Lafiya, Ni a ganina bai kamata mu tsareta da tambayoyi ba a yanzu, ƙaramar yarinya ce sai ana lalla6ata”

Sassauta fushin fuskarshi Yai, Cikin kwantar da murya yaci gaba da cewa”Okey, Share hawayenki, ki daina yi mana kuka bama so” Muryarta Na rawa ta amsa mashi da toh.

Miƙewa Dr laura ta yi ta nufi fridge ta buɗe ta ɗauko mata fanta me sanyi, ta haɗo mata da tissue, Ta dawo gefen gadon ta zauna tare da miƙe mata tissue ɗin, Hannayenta na kerma ta kar6a ta soma goge ƙwallarta da hancinta, Bayan ta gama share hawayen dr laura ta miƙa mata lemun kar6a tayi tare da yi mata godiya.

kamar tasan Mayyar fanta ce, Buɗe wa tayi agaban su ta kur6i ruwan lemun kusan sau uku tana sha, Sun tsareta da ido suna kallonta, hakan ba ƙaramin rikitar da ita yake yi ba.

“Pls Masoyiya Angel, Ki taimake mu ki taimaki rayuwarki da ta sauran ƴan uwanki, Ki faɗa mana gaskiyar abunda Ya faru a rayuwarku wanda yai silar haifar maku da ciwon damuwa, Idan har baso kikeyi mu maida ku daji ba” acewar Captain.

“Abunda mukeson sani shine Ya akai kuka tsinci kanku a ƙurmin dajin Evil forest? saboda ɗan ta’addan ƙasarmu da muke hasashen shine Ya kai ku can mun titsaye shi akan ya faɗa mana menene alaƙar shi da ku, Ya faɗa mana cewa Baisan komai dangane da ku ba, Ya taimaki wasu daga Cikin ƴan uwanku ne, Munyi dogon nazari akanku, da farko munyi tunani ƴan ƙasarmu ne ku, sai kuma muka ji kuna magana da wani harshe wanda bana nahiyarmu ba! Mun rasa gane daga wani Jinsi ku ke? sannan menene maƙasudin haddasa maku ciwon damuwa da baƙin ciki? lamarin ya ɗaure mana kai da ƙananun shekarunku? hada me fama da ciwon zuciya! Wani abun al’ajabin ɗaya daga cikin Ƴan uwanku yaƙi farkawa daga bacci mun rasa gane meke damun shi......” tun da major ya soma yi mata magana a tsanake ta tsare shi da ido tana kallon la66ansa har ya ƙare maganarsa, tukunna ta fara magana
“Gaskiya ne abunda ɗan ta’addan ya faɗi, bashi ne yakaimu daji ba, Mun jima Acan kusan zance tun kafin mu mallaki Hankalin mu, bazan Iya tuna abunda Ya faru arayuwar mu ba, kome yakai mu Dajin, abunda na sani shine Munci baƙar wahalar rayuwa dani da ƴan uwana, wanda silar hakan yajaza mana depression....”
Kallon Juna su ka yi, still sun fahimci bazata faɗa masu abunda suke son ji ba, sam bata son su sani babu alamun zata yarda da su.

Murmushin gefen fuska Major ya sakar mata”Ni dama tunda naga idanuwanki da ƙaramin bakin nan Naki raina ya bani kina da wayau sosai,” duƙar da idonta ƙasa Ta yi zuciyarta na bugun uku uku.
Chapter 56 · 0% Book details