Sashe 27
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Harara zaid ya watsa mashi”nifa ban gane ba, Taya zaka dinga yi min magana akan macen da nake son in mallaka? Kasan dai haramun ne muyi sharing mace ɗaya a gidan aure ko?, awaje ne muke da ikon yin hakan duk da shima yin hakan haramun ɗinne” ta6e la66ansa yai”Zaid ni ba zan yi jayayya dakai ba, just Kada kamanta ni ne gidan kuɗi, na gaban goshin mommy, mata kuma saida kuɗi”
Dariyar shaƙiyanci zaid ya sakin kafin yace “Nima ina da daddy, kada ka manta komai na mommy mallakinsa ne” Sakin baki Zayn yai saida Zaid ya karasa maganar tukunna yace”Daddy ai ɗan koren mommy ne, mutumin da ke zaune agidan surukansa? Mommy ce fa silar arziƙinsa, tayaya zaka hada kan ka da Ni? baya kasan Mune ke da dukiyar Ku kuma Bayin mu ne, Sai mun ɗan watsa maku hatsi tukunna kuke samun wanda zaku tsastsaga.....” Kallon al’ajabi Zaid yake bin ɗan uwansa dashi, yadda yake magana Yana kushe mahaifinsu yai matuƙar ɗaure mashi kai, da ace wani bare ne yai wannan maganar, hada shi za’a haɗu wurin cin ubansa, don sun tsani gorin da akeyiwa mahafinsu akan yana zaune gidan surukansu.
“Assalamu Alaikum” Muryar Sophia ce ta katse masu firar tasu, daga wajen bakin ƙofar ta tsaya”Yalla6ai ga coffee din na canza wani” har suna haɗa baki wurin furta”we don’t need it!” ranta ya 6aci, duk wahala da tasha a ƙarshe sunce basu sha, gyaɗa kai ta yi tare da juyawa ta bar part ɗin nasu.
“Zayn ba ka da mutunci, daddyn namu ka ke yi wa gori? Yunƙurawa yai tare da mikewa zaune A harzuƙe yace”ƙarya nayi ne?ni ban ta6a ganin Mutun mai matattar zuciya irinta daddy ɗinmu ba, har yau in na tuna gorin da akeyi mana raina 6aci yake yi, Allah ya hore mana komai na rayuwa amma daddynmu yaja mana abun magana” Jinjina kai Zaid yai”Nima fa abun na ƙona min rai yana yi min ciwo a zuciya, amma ya zamuyi dole mu rungumi ƙaddararmu” saukowa Zayn yai daga saman gado Ya nufi toilet ya shige, ya rage saura Zaid a ɗakin ya tasa mirror gaba yana kallon fuskar shi, bakomai yake tunanowa ba face fuskar *UMMIN AMERICA*.
*MIDDLE STEP💋*
Daga alkalamin Boss✍️
Kishingiɗe yake saman lallausar Darduma, a Cikin Haɗaɗɗen Garden ɗin gidansa, jikinsa na asanye da Voile sky blue riga da wando, Kayan sun zauna mashi, Fari ne Ba irin sosai ɗinnan ba, dukkan wasu alamun tsufa sun bayyana akan fuskarshi da jikinshi, A ƙalla zai kai shakara tamanin a duniya, daga ganin fatarshi hutu ya zauna mashi, kan shi babu hula, tsufanshi bai 6oye mashi Kyawun fuskarshi ba, tsabar kyan Da Allah yayi mashi zaiyi wuya mutun yai mashi kallo ɗaya ya kauda kai, saboda haɗuwarshi da iya ɗaukar wankanshi, sumar kanshi akwance take tasha gyara hurhura duk ta lullu6e ainin launin gashin nasa, daga gaban goshin sa akwai siraran hurhura, da akayi gayu da ita, ba ƙaramin kyau ta yi mashi ba,Yana da tsayin fuska, da Manyan idanuwa, Launin gray mutunne shi ma’abocin son ƙamshi, tamkar Da ruwan turare ya ke yin wanka saboda tsabar yadda jikin shi ke fitar da daddaɗan fragrance mai kwantar da tarzoma, Dogon gemun shi fari fat ya sauko har saman ƙirjin shi, Yana da yalwatacciyar suma.
Dattijon Arziƙi kuma gwarzon Namiji mai ɗauke da suffofin Jagoranci, waɗanda su ke da Jan hankalin Jama’a, mutunne shi mai daraja, Wadatar Arziƙi, kaifin basira da bajinta, Jajircewa, Mai cikar kamala, ga iya mu’amala Da mutane, kaifi ɗaya ne kuma bai Sa6a alƙawari,Ta ko’ina Allah Ya hore mashi, Kuma duk mun tarin dukiyar da ya mallaka Hakan bai gusar dashi daga Yin ibadarshi ba, Hakokin Ubangiji kama daga fidda zakka, sadaka, Da kyautatawa al’umma, mutun ne mai jin ƙan talaka, Shi nashi arziƙin bai ɗaura mashi Girman kai da maƙo ba, Da kuma ƙyamar Talaka, kowa Nashi ne wannan kenan.
daga bayan shimfiɗar shi Sandar shi ce jingine da bishiya wadda aka ƙerata da zallar Gold kuɗin ta kaɗai sun ishi bawa yai maganin talaucinsa, Yayin da iskar Garden ɗin take ratsa sassan Jikin shi, A hankali ya ke ɗan lumshe idanuwanshi yana buɗesu haɗi da ƙarewa ƙayatattun kayan alatun da ke a garden ɗin kallo, a duk lokacin da kewar jikanshi ta addabe shi yakan ke6ance kanshi daga Cikin Jama’a, ba tare da sanin kowa ba, ya ke shigowa garden shan iska, yasan muddin masu kula da lafiyarshi suka gan shi shi kadai agarden sai sun kira ya’yanshi sun faɗa masu daga nan su kuma zasu rasa kwanciyar hankalinsu, har sai sunzo sun duba shi, sun tabbatar da lafiyarshi tukunna hankalinsu zai kwanta, shi kuma bayason ya katse masu aiyukansu, saboda suna ƙoƙari wurin zuwa ganinshi akai akai, Suna matuƙar ƙaunarshi, Babbar damuwarshi a yanzu Jikanshi daya mutu akan ƙaunarshi yayi nesa dashi, ya kwallafa rai akan son shi, ko ƴa’ƴanshi da ya haifa baya yi masu irin son da ya ke yi mashi, gaba ɗaya hankalin shi na akan, kyawawan furannin cikin garden ɗin, Da Halittun dake yawo acikinsa irinsu ɗawisu da filfilo Yana matuƙar son ganin su.
Shu’umin ƙamshin Humran Jikinta ne ya daki Hancinsa, tun kan ta ƙaraso Ya ɗago da idanuwanshi Ya kalle ta kafin Ya kawar da idon shi gefe ɗaya sam babu walwala akan fuskarshi
Ƙarasowa tayi daga gabanshi Ta ɗan russina ta gaishe shi cikin girmamawa, shiru bai tanka mata ba, hakan da yai mata yasa ta fahimci babu lafiya, ba ta ta6a ganin damuwa akan fuskar dattijon ba sai yau, cikin sanyin murya tace”Yalla6ai na duba acikin gida baka nan shiyasa nazo duba ka a garden, fresh fruit ne na kawo maka” tai maganar tare da ɗukawa ta ajiye mashi kayan marmarin.
Da buɗar bakinsa sai cewa yai”Owais Ya dawo gidan nan”! murmushin gefen fuska Hajjaty tasaki”yalla6ai owais Ai baya a ƙasar Ko kamanta ne” yamutsa fuskarshi yai” Oh toh na manta, “har zata miƙe ta kuma cewa”Ko kana buƙatar wani abun ne”? Girgiza mata kai yai”bana son kowa yasan ina a garden”! amsa mashi tayi da toh kafin ta kama hanyar fucewa Kaitsaye ta nufi Entry hall na shiga gidan, Zuciyarta a cunkushe take da tunanin meke damun dattijon? Ta ya ya zata Iya sani? Duk ta damu kanta akanshi saboda Kyautatawar da yake yi masu bazata so ta gan shi a irin wannan yanayin ba.
Adai dai Ƙofar shiga Falon suka ci karo da matashin dake ƙoƙarin fitowa, Dogo siriri bai da ƙiba ko misƙala zarratin, Fari sol dashi daga ganin shi farar fata ne bai haɗa komai da jinsin baƙaƙe ba, Jikinshi na sanye da Kayan likitoci farin wando, Farar shirt daga sama ya ɗaura Lapcoat, Fararen idanuwashi na manne da farin glass, Masha Allah Kyakkyawan gaske, Sumar kanshi har saman wuyanshi,
“Jazz! “ yanayin yadda ta ambaci sunanshi ne yasa shi cin burki, Yana kallonta, fuskar shi a ɗaure yace “Me kike buƙata? Allura ko tiyata”? Dariya ta ɗan saki har fararen haƙoranta suka bayyana.
“Kinga sauri nakeyi Yanzu aka kirani awaya, Ina da patient” yai maganar yana ƙokarin bi ta gefenta Zai je wuce, ruƙo Hannun shi da tayi ne yasa shi yamutsa fuska Hada bubbuga ƙafarshi atakure Yake kallonta
Cikin sanyin murya ta soma magana”Jazz kana araye obinna ya ke6ence kanshi a garden? Hankalina ya tashi ganin damuwa akan fuskarshi....” Tunkan ta ƙarasa maganar Jazz Ya zame glass ɗin idon shi, Yanayin fuskarshi Ya canza sosai, ba tare daya ce mata uffan Ba ya nufi garden ɗin gidan, bin bayanshi tai da kallo fuskarta ɗauke da murmushi don tasan muddin Jazz yaje garden, damuwar obinna ta ƙare, Saboda kaifin basirar dake gare shi Tsab zaiyi mashi solving matsalar shi.
Kamar yadda Hajjaty Tabar Obinna haka Jazz ya same shi a kishingiɗe saman darduma, ya ɗan lumshe idanuwanshi, bai ta6a kayan marmarin da ta kawo mashi ba.
Sautin muryar Jazz ce ta daki kunnanshi”ina gwanin wani ga nawa!Kai ni fa bani da tamkar dattijon nan aduniya, Akanshi zan iya faɗa da kowa, duk mutumin da bai daraja gemunshi ba babu mutunci tsakanina dashi....” Cikin ɗaga murya ya ke yin maganar.
Hakan ba ƙaramin faranta zuciyar obinna yai ba, a tsanake yake kallon shi,
Kashe mashi ido ɗaya Jazza yai”ku fa tsaffin nan sai ana lallashinku ana tarairayarku, da zarar mutun ya haura shekara 70 a duniya sai kaga ya fara ɗabi’u irin na Yara, haba Uban mu maganin kukan mu, Idan Yunwa kake ji ba sai kai magana abaka abinci ba? Shine don rigima zaka ke6e kanka cikin garden salon ka jamana bala’e ace bamu baka kulawa yadda ya dace”? fuskarshi a ɗaure yai maganar, still murmushine akan fuskar obinna, A faɗace Jazz Ya nuna mashi hanya da yatsan hannun shi”maza tashi ka koma gida idan ba so ka ke Kaji ɗanyar geza a jikin ka ba, “ Wannan maganar da yayi tayi matuƙar bashi dariya sosai Obinna ya tuntsire da dariya yana kallon shi, jinjina kai Jazz yai hada ruƙe qugu yace”Na fahimci rashin mabugi ne ke damun ka, “ yai maganar tare da juyawa yana neman bulalar da zai buge shi, Dariya hada dafe ciki obie yake yi, Yayin da yake kallon shi,
“Mutun bai rasa ci da sha ba, Sutura Allah ya hore mashi, wadatar arziƙi da ta ƴa’ƴa mai yafi wannan aduniyar nan”? A faɗace yai maganar, kamar wanda aka 6ata ma rai, alhalin nan duk cikin zolayane, ganin yayi nasarar sanya shi farin ciki yasa shi matsawa kusa dashi.
Hannayenshi ya ruƙe acikin nashi”haba sanyin idaniyata, Dan Allah kafaɗin menene damuwarka? Ashirye nake dana sanyaka farin ciki,” fuskarshi amarairaice yai mashi maganar,
Lumshe ido obie ya ɗanyi kafin a hankali ya waresu kan fuskar Jazz
“Shi ne damuwata, Kafi kowa sanin hakan, bansan ya zanyi ba, inason ganin shi, ban ta6a tunanin zai ɗauki tsawon lokacin nan batare da yazo kawo min ziyara ba,” farin ruwane kwance acikin idanuwanshi, Hankalin Jazz ba ƙaramin tashi yai ba.
“Kamar yadda ka damu dashi, shima haka ya damu dakai! Ayyuka ne suka yi mashi yawa, pls ka yi mashi uziri....”
“Jazz Inaso Owais Ya halacci shagalin da za’ayi na murnar zagayowar ranar haihuwata, Amma nasan abune mai wuya ya iya zuwa” shiru Jazz ya ɗanyi yana kallon fuskarshi.