Sashe 81
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kusan Sau uku dr shureim yana jaraba kiran layin Alhaji musa bai ɗaga ba, zeenatu tace dashi”ka jaraba kiran Layin mommy, idan tayi masu magana zasu barmu mu fita” kiran Layin Hajiya sarah yayi ringing biyu ta ɗaga, bayan sun gaisa ya sanar da ita halin da suke aciki, tace dashi yaba ma Security guard din waya suyi magana da shi.
Miƙa masu wayar yai, bayan sun kar6a ya dubi zeenatu, yayi mamakin ganin zufa na wanke fuskarta duk da sanyin A.c na motarshi, ya fahimci tsoron su take ji.
“Ki kwantar da hankalinki zeenatu kina atare dani”
cikin sanyin murya ya ambaci hakan, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”yaya shuriem ni bana son tashin hankali, duk laifin daddyne ni banga amfanin ajiye waɗannan ƙattan ba acikin gidanmu, ai Allah ne ke tsare bawansa bawai mutun ba” da shagwa6a ta ƙare maganar, ruƙo hannunta yai acikin nashi, da sauri ta mayar da kanta saman kafaɗarshi tare da lumshe idanuwanta tana faman sauke ajiyar zuciya.
Miƙo mashi wayar Security guard ɗin yai”an baku iznin fita, amma bisa sharaɗin zaku koma mazaunin baya na motar, Ni zanyi driving dinku duk inda zaku je” zeenatu tamkar zata fashe da kuka tsabar jin takaicin jin abunda Security guard din ya fadi.
Dr shureim yace “ba damuwa mun gode da kulawa,” ya faɗa yana buɗe murfin motar, fitowa su ka yi daga front seat suka koma back seat na motar suka zauna,” security guard din ya shiga ciki Ya zauna a driver’s seat, Ya tada motar Ya fuce dasu daga cikin gidan lokacin da suka haura saman titi, security guard din ya tambaye su ina zasu je ne, zeenatu ce ta zayyana mashi wuraren shaƙatawar da zasu je, kafin dawowarsu gida sai da suka mori lokacinsu, kamar karsu dawo gida.
*EX-PRISONERS❤*
After two days (bayan kwana biyu)
Idan muka koma 6angaren prisoners sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa tafiya ta kankama, tun bayan da sojoji suka ƙulla yarjejeniya da ummin america, A ranar wuraren ƙarfe shidda na marece, sojojin suka zo kawo masu ziyara domin duba lafiyarsu, a ɗakin hutawar dr Laura, suka tattarasu gaba ɗayansu, sunyi matuƙar jin daɗin ganin Yaran sun samu sauƙi musamman Danish da suka barshi Yana ta faman sharar bacci, dama sun ƙwallafa rai akan son ganin ya farka, duk da bai sakar masu fuska ba sai da suka ja shi ajiki, kafin tafiyar sojojin sai da dr laura ta nemi izni akan tana so abata dama ta ɗauki Yaran zuwa gidanta na tsawon kwana uku, saboda tana so gobe zata kai su saloon agyara masu jikinsu da sumar kansu, sannan tana so zata siya masu suturar da zasu sanya, sojojin basu amince da buƙatarta ba, saboda chief na Isod Ya hana a fita da yaran ko’ina, yace kada a kuskura a fitarsu daga asibiti sai Airport idan zasu tafi, Sun bata haƙuri akan ƙin amincewa da buƙatarta sun kuma nuna mata illar yin hakan tun da su Yaran suna hasashen cutar da su akayi kuma dole asamu masu bibiyarsu, ba dan taso ba ta haƙura, sai dai kamar yarda tace zata siya masu suturar sanyawa tayi ƙoƙarin yin hakan duk da Commender yace kada ta wahalar da kanta, Chief na isod Ya ɗauki ɗawainiyar yaran duk wani abu da zasu buƙata a duniyar nan shi zaiyi masu, dr laura tace taji amma dole ta siya masu wani abun da zasu dinga tunawa da ita akai akai, commender yace mata ba damuwa, bayan tafiyar sojojin, tsabar farin Ciki awurin Angel kamar zata zuba ruwa ƙasa tasha, dr laura ce ta faɗa masu komai dangane da tafiyarsu Nigeria, da kuma damƙa case ɗinsu a hannun Chief of Isod, daren ranar da aka faɗa masu ko bacci bata yi ba, kwana tayi tana yin Nafilfili, har sai da idanuwanta suka kumbura saboda hawayen dake fita acikinsu, ƙafafuwanta suka fara yi mata zogin azaba, tukunna ta dakata dayin sallar asaman prayer mat bacci ya ɗauke ta.
Tsawon kwana Biyu Kacal, a tsakani Shugaban Isod, Ya shigo birnin San Antonio Texas, Ya kama Yau kenan Monday, Kuma A yau din zasu Bar America, Da zarar ya fito daga meeting din da suka shiga ahead quarter tare da Chief of army staff, da commender da sauran sojojin dake da alhaki akan Tsintar Yaran A daji, tattaunawa ce ta musamman da zata dauki tsawon awa nni suna Yinta.
*UNAISERH ANGEL💋*
Mutuniyar tun da ta farka, bakinta awashe kamar wadda akayima Albishir da gidan Aljanna, sai faman zarya take Yi a ɗakin ta kasa zama, jefi jefi ta kan wurga eye balls dinta kan wall clock dake a ɗakin don ganin lokaci idan yana tafiya, ta ƙosa su kammala meeting din azo a ɗauke su, don ita a takure take da zama america.
Ta zuba hannayenta biyu acikin aljihun wandonta, bakomai take tunawa ba face Aunty Aneelerh da daddynta, ta sanyawa ranta cewa idan suka koma Nigeria, zata ganshi a gidansu.
Zame hannayenta tayi daga cikin aljihun wandonta, ta goya su saman ƙirjinta, abun nayine.
“Masoyiya Angel,” muryar dr Laura ce ta fargar da ita ga kallonta, har batasan lokacin da ta furta”Sun gama meeting din”? Fuskar dr Laura dauke da murmushi ta ƙaraso ciki, hannunta ruƙe da ƙatuwar shopping bag.
A gefen gado ta ɗaura jakar kayan, tare da miƙa hannu ta rungumo Angel a jikinta.
“Zanyi missing dinki masoyiya Angel, sai dai na lura kamar ke ba za kiyi kewata ba ko”? Ta fada tana raba jikinta daga na Angel.
Duƙar dakai Angel tayi cikin jin kunyarta tace”Idan nace bazan yi missing dinki ba, Nayi ƙarya, ba ma ke kaɗai ba, duka nurses da likitocin da suka taimaka mana wurin samun lafiyarmu, zamuyi kewarku sosai”
Shafa gefen fuskarta dr. laura tayi da tafin hannunta.
Cikin karyayyar murya ta furta”masoyiya Angel, saura mintuna ƙalilan suka rage maku a asibitin nan, Ƴan uwanki duk sun shirya cikin sabbin Kayan da na Siya masu, Kema ga naki nan” ta faɗa tana nuna mata jakar kayan data ajiye mata saman mattress.
“Sannan akwai Waya dana siya maki, na yi maki Saving phone number dina tare dana Dr brown dana dr mark, da duk numbers na nurses da suka kula da ku, idan kin sanya layi akan wayar ki kira mu pls” Daƙyar ta karasa maganar, idanuwanta sun cicciko tab da ƙwalla, Jikin Angel duk yai sanyi, zuciyarta ta karaya.
Cikin murya tamkar tame Yin raɗa, dr laura taci gaba da cewa”Abu ɗaya da ban faɗa maku ba, dama na yanke shawarar Sai mun ke6e dake in sanar da ke, saboda Na yaba da hankalin ki da kuma kaifin basirarki da wayon ki,’ Angel ta natsu tana sauraronta.
“Matar da sojoji suka damƙa amanarku a hannunta, Mistress ce,” kai tsaye sunan Ya daki dodon kunnan Angel, cikin rashin fahimtar ma’anar hakan ta maimaita kalmar mistress.
Jinjina kai Dr Laura Tayi”tantiriyar ƴar bariki ce mai zaman kanta, shaidaniyace a fagen iya karuwanci, ta shahara sosai, babu wanda baisanta ba, tayi ƙaurin suna a America, maca ce mai haɗarin gaske, Namiji baya Iya ganinta Ya kawar da idonshi, saboda kyawun surar dake gareta, Nayi ƙoƙarin Fahimtar da sojojin Akan illar damƙa amanarku a hannunta amma sunƙi su amince min Angel, ni nasan da wuya ta Iya baku kulawar daya ce, in ma bata gur6ata maku rayuwarku ba, Musamman Ƴan uwanki maza........” Hankalin Angel Ba ƙaramin tashi yai ba, duk da Sanyin A.c na ɗakin zufa ce ke tsastsafo mata saman goshinta, idanuwanta azazzare take kallon fuskar dr Laura dake kora mata jawabi.
“Ni damuwata depression din dake damunku, da kuma ɗan uwanku mai fama da ciwon zuciya, idan har aka cigaba da ƙuntata maku zaku Iya rasa rayukanku, shiyasa banso suka damƙa amanarku a hannun karuwa ba, donni a sanina da matar masifaffiyace tana da girman kai, bata ta6a yin aure ba, kuma bata san ciwon haihuwa ba, abunda ta sani shine ƙwacewa matan aure mazajensu tayi fasiƙanci da su, matar ta zama tamkar annoba, ta raba aure da dama saboda hatsabibancinta” dakatawa tayi da yin jawabin idonta akan Angel, tsantsar tashin hankali take gani acikin ƙwayar idonta, Jikin Ta ƙaura Yai la’asar, An gudu ba’a tsira ba.
Muryarta Na rawa ta furta”Aunty, amma meyasa suka damƙa amanar mu a hannunta? Babu wata ne sai ita? Kuma ai mu bamu buƙatar wadda zata kula damu, idan ma akwai abunda zamu buƙata bai wuce jami’an da su bamu tsaro ba....” bata ƙarasa maganar ba dr laura ta katse ta da cewa”dalilin dayasa suka damƙa amanarku a hannun ummin america, kamar yarda major ya sanar dani, matar tamkar ma’aikaciyarsu take, ta saba yi masu aiki wurin jan hankalin tantiran ƴan ta’addan da suka gagara a ƙasa, suna yin amfani da ummi wurin ɗana masu tarkon da zasu kamasu, kuma suna cin nasara, Masoyiya Angel ban faɗa maki hakan donna tada maki hankali ba face don ki dage damtse wurin Yin yaƙi da ita akan ƴan uwanki, kada ki kuskura ki bari ta ke6e da ɗaya daga cikin Samarin dake a jikinku, Idan ba haka ba za’a Iya samun matsala, saboda bata da linzami matar, duk da A yanzu ina kyautata mata zo, tun da har sojojin suka aminta da ita suka damƙa mata amanar ku, hakan na nufin sun san zata Iya ne, Bayan haka sun ƙulla yarjejeniya da ita akan baku kula ta musamman da kuma gujewa duk wani abu da zai 6ata maku rai, kamar yarda na gani dai dai da tsawa tayi maku babban laifine, don haka Zan tura maki sharuddan da sojojin suka gindaya mata akanku ta whatsapp, saboda inaso kiyi amfani da su wurin ja mata kunne idan ta sa6a maku,” jinjina kai Angel tayi alamar toh ta ƙara da cewa “bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya, Allah ne kaɗai zai Iya biyanki, saboda kyautatawar da kukayi mana, gashi kun ɗauke mu tamkar ƴaƴan ku, “