← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 152

Sashe 113

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magiya hajiya falmata tadinga yi mata akan tayi haƙuri su koma da kuɗin, ta yafe masu, amma Aneelerh taƙi yarda, mahboob ne yace ta jira zasu yanke shawara a tsakaninsu, ruƙo hannun Aneelerh yai acikin nashi yajata zuwa gefe ɗaya akwai tazara tsakaninsu da hajiya falmata, tayi kasake tana kallonsu
“Aunty aneelerh tunda tace ta yafe kuɗin mu koma dasu kawai, ai ba roƙonta mukayi ba”
Girgiza kai aneelerh tayi”nidai hankalina bai kwanta da matar ba, wallahi irinsu shaiɗanune Mahboob, inajin tsoron ace wani tuggun zata kitsa mana shiyasa tace ta yafe kuɗin, ƙwara mu maida mata aniyarta”
Yamutsa fuska mahboob yai”aunty aneelerh just ki gane, ni dai na yarda da ita, sau dayawa zaki ga mutun yana aikata ba daidai ba idan Allah yaso shi da rahama saiki ga ya shiryu cikin sauƙi batare da ansha wahala ba, Yanzu ki duba matar can, hada fa kukanta kuma har zuƙunnawa tayi saman gwiwowinta tana roƙonmu, why bazamu yafe mata ba? Komai ya wuce, ita kanta zahran ba ƙaramin daɗi zataji ba saboda tana son fatima ƴarta aminnan junane tun tuni, sannan taci burin zuwa obie estate, bayan haka aikin nan da take Yi a companyn su ba ƙaramin ƙaruwa take Yi ba, ita kanta tana faɗi da bakinta irin alheran da take samu ta silar aikin da suke Yima mutane, idan ma da wata manufa tace hakan to mu barta da Allah, In sha Allah babu abunda zata Iya yi mata,” gyaɗa kai Aneelerh tayi”shikenan na amince da buƙatarta, mu koma mu faɗa mata” komawa sukayi cikin falon, bayan sun sanar da ita shawarar da suka Yanke ta dinga yi masu godiya farin ciki duk Ya cikata, kafin tafiyarsu saida ta roƙe su alfarma akan su taimaka mata, tana so zahra taci gaba da ganinta a matsayin mahafiyarta, tasan ayanzu bata da sauran mutunci a idonta.
Aneelerh ce tabata shawarar yadda zata tsara ma zahra, duk don ta amince da cewa ba halinta bane, sun jima agidan kafin daga bisani sukayi mata sallama, sunyi rabuwar mutunci da hajiya falmata, har musayar number sukayi da Aneelerh saboda acigaba da zumunci.

( kunji abun da Ya faru, kafin washe garin ranar da zahra taje kaima Hajiya falmata kuɗinta)

Wuraren ƙarfe takwas na dare, motar drivern da yaje dauko su Alhaji ubaid daga airport ta kunno kai gate din gidan, tunkafin ƙarasowarsu, Dr Shureim da zeenatu suna atsaye bakin Entry hall din falo, hannunsu ruke cikin na juna, daga ita har shi jallabiyace ajikinsu, ta yafa mayafi akanta, tsantsar farin cikine akan fuskokinsu, sunyi matuƙar ƙagara da son ganinsu.
Zeenatu sai faman washe baki take Yi, tunda tayi tozali da motar dake shigowa tana tunkaro bakin entry hall din
Da zamudi tace”ya shureim kana ganin aunty benazir zata Iya gane ni kuwa? Saboda mommy ta fadamin tun ina jaririya ta 6ace ba’a ganta ba”
Fuskarshi dauke da murmushi yace”idan ma bata gane ki ba, da zarar anyi mata bayani zata shaidaki, zan faɗa mata cewa zeenatu ce ɗiyar uncle musa, and my wife to be” tuntsirewa tayi da dariya taji daɗin maganarshi, muryarta da shagwa6a tace”amma ya shureim ai ni banaso ka faɗa mata, wallahi kunya nake ji, ko mommy layla ma kada ka fada mata please da daddyn ku” ta faɗa tana duban face dinshi.
“Ai ni nafiso suji My zeenatu, saboda a fara shirye shiryen shafa fatihar auranmu” zaro mashi blue eyes dinta tai kafin tai saurin sanya tafukan hannayenta biyu ta rufe fuskarta cikin jin kunyar maganarshi ta furta”dan Allah yaya shureim dina kada ka fada masu yanzu, nidai kunya nake ji”

“Kunya kamar bafullatana, kin manta mommynki baturiya ce, daddy musa kuma Hausa fulanine, kakarmu bafullatana ce kakan mu namiji kuma bahaushe ne, Ni bansan inda kika gado Kunyar nan taki ba, a haka zamuyi aure kina jin kunyata”?

Kafin ta bashi amsa, motarsu Alhaji ubaid ta ƙaraso gab dasu, bayan drivern yai parking, da sauri Dr shureim Yaja hannun zeenatu suka ƙarasa bakin motar, yakai hannu ya buɗe masu murfin back seat, a hankali ta zuro da ƙafarta dake sanye cikin takalma, ƙarasa fitowa tayi tun daga ƙasa dr shureim yake binta da kallo, wankan atamfa ne a jikinta riga da skirt, ta kashe daurin dankwalinta, yalwatacciyar sumar kanta ta sauka gadon bayanta, gyalen asaman kafaɗa ta yafa shi, idan kaganta ahaka bazaka ta6a ce wa ta ta6a yin aure ba, kamar budurwa saboda babu abunda ya canza a jikinta, dama bata ta6a shayarwa ba.

Wani irin kallon so da ƙaunar ƴan uwantaka suke jefa ma juna tsakanin ta da shureim, idanuwan kowannansu ya ciko tab da ƙwalla, La66anshi na kerma ya furta sunan ta”be.. Nazir! Yar uwata rabin raina, Jinin jikina Dagaske ke ce idanuwana suke nuna min? Fashewa tayi da matsanancin kuka, gaba ɗaya ta faɗa saman chest dinshi, ya zagayo da hannayenshi biyu ya rungumeta tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi, Zeenatu dake tsaye tana kallonsu hawaye tuni sun wanke fuskarta, tsananin tausayin benazir ne Ya kamata, Fitowa Alhaji ubaid yai daga cikin motar shida Hajiya layla, ya dauki wankan shadda, itama layla Atamfar ce ta sanya sunyi anko da benazir hatta daurin dan kwalinsu da mayafin da ta daura a kafaɗa iri dayane dana benazir, idanuwansu na akan dr shureim da benazir, sun ƙanƙame juna sai kuka sukeyi kamar waɗanda suka rasa mafaɗi a duniya, zagayawa zeeenatu tayi ta 6angaren da su hajiya layla suke koda sukayi arba da ita, Hajiya layla ta buɗe mata hannu da fara’a akan fuskarta take fadin”Zonan My daughter zeenatu” kamar jira take yi da sauri ta ƙarasa ta faɗa jikin Layla, rungumeta tayi sosai, tana dan bubbuga bayanta ta furta”kin ƙara girma daughter, tsawon lokaci bamu haɗu ba, Daddynki Ya hanaki zumunci da ƴan uwanki, baison kina taka wajen mu, gashi mu kuma muna ƙaunarki” ta faɗa tana raba jikinta da na zeenatu, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, kallon Alhaji ubaid tai”sannunku da zuwa daddy” miƙa mata hannu yai da sauri ta ƙarasa gare shi, Yai hugging dinta yana fadin”fatan mun same ku lafiya,” ɗagowa tai da kanta tana fadin”Lafiya lou daddy mu shiga daga ciki”
Drivern daya daukosu Yana daga tsaye ya jingina bayanshi jikin motar, Yace”yalla6ai ku ƙarasa shiga gidan, za’a shigo maku da kayan naku” amsa mashi sukayi da toh, layla tace da su shureim ayi haƙuri adaina kukan ya isa haka mu shiga cikin gidan inyaso kun ƙare kukan naku acan” Alhaji ubaid na murmushi yace”ke ko kibarsu mana, An daɗe ba’a haɗu ba, Jini ɗaya ba wasa ba, mundai godema Allah daya bayyana mana ita da ranta da lafiyarta ubangiji Allah Ya ƙara tsare mana ita, layla da zeenatu suka amsa mashi da ameen,
Gaba suka fara Yi, Ya rage saura zeenatu data ƙura ma benazir da shureim ido.

Ta kwantar da kanta saman kafadarshi, yayin da hawaye masu ɗumi suke cigaba da wanke fuskarta, cikin muryar kuka take fadin”yaya shureim nayi danasanin duk wani abu daya faru arayuwata, wallahi nayi danasani mara amfani, bansan meke damunaba, hakanan na tafi nabar dangina nabar mijina, babban takaicina ƴar jinjirar dana bari cikin jini, na haura ƙafa na tafi nabarta saboda rashin hankali irin nawa, bansan meyasa na aikata hakan ba” cikin jin ƙunar rai ta ƙare maganar.
Ɗaura hannunshi yai saman bayanta cikin rauni na murya ya soma magana”kiyi haƙuri benazir, wallahi ba laifinki bane, ni nasan duk rashin jin maganarki bazaki ta6a iya aikata hakan ba, Ina yi maki kyakkyawar zato, ki kwantar da hankalinki My sister” cikin kwantar da murya yake lallashinta
Shessheƙar kukan zeenatu ne Ya janyo hankalinsu ga kallonta, idanuwanta sunyi luhu luhu, da mamaki akan fuskar benazir ta furta”yaya shureim a ina muka samu kyakkyawar matashiyar baturiya”?
Fuskarshi dauke da murmushi yace”zeenatu ce, nasan ba lallai kisanta ba, saboda ba’ajima da haihuwarta ba ki ka tafi, ɗiyar uncle dinmu ce, ki kalli fuskarta dakyau”

Farin cikine Ya lullu6e benazir, Yarinyar ta burgeta, Gata ƴar kyakkyawa da ita, miƙa mata hannu tai zonan ƴar uwata, Ina fata an fada maki wacece ni, idan ma ba’a sanar dake ba toh nidai sunana benazir, Ƙanwar dr.shureim” fashewa Zeenatu tayi da dariyar farin ciki, Hawaye nabin fuskarta.
“zonan In rungumeki ajikina, Nima yau inji ɗumin ƴar uwata” jiki Na rawa zeenatu ta nufi benazir suka rungume juna kamar zasu koma mutun ɗaya
Cikin shessheƙar kuka Zeenatu take fadin”Aunty benazir munyi kewarki sosai, Mommyna tana bani labarinki, najima ina son ganinki arayuwata, duk da bamu ta6a haɗuwa ba amma kullum idan nayi sallah sai nayi maki addu’a Akan Allah Ya bayyanar mana dake idan kina araye, Idan bakya araye Allah Yajiƙanki yakai rahama agareki, ashe da rabon zamu haɗu....”dakyar ta ƙare maganar saboda kukan daya cimmata, daga ita har benazir din kukan sukeyi, Kalaman zeenatu sunyi matuƙar ta6a mata zuciyata, tayi mamakin irin ƙaunar da take Yi mata, ita da bata ta6a ganinta ba, labarinta kaɗai aka bata, haƙika taji dadi mara misaltuwa, kaunar zeenatu ta shigeta, tayi fatan Ace itama ƴarta data bari tana yi mata addu’a.

“Aunty benazir dan Allah kada ki ƙara tafiya kibarmu, wallahi muna kaunarki nida mommyna” sosai benazir ta fashe da kuka tana fadin”in sha Allah bazan ƙara tafiyaba, nadawo kenan zeenatu, naji dadin kalamanki agareni, ƴar uwata rabin raina”
Dr.shureim Ya natsu yana kallonsu, idanuwanshi sun kaɗa jawur, hawayen dake gangarowa saman kuncinshi sai ƙara ninkuwa sukeyi.
Cikin sanyin murya yace dasu’Mu shiga cikin gidan” amsa mashi sukayi da toh, hannun benazir acikin na zeenatu suka dunguma zuwa babban falon gidan.
Lokacin da suka ƙarasa ciki, Alhaji ubaid da Hajiya layla suna a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, a yayin da Hajiya sarah ta zauna saman 3 sita, Alhaji musa yana daga zaune gefenta, kamar kullum fuskarshi babu annuri, kamar wanda akayiwa albishir da ranar mutuwarshi, shaddar jikinshi ta zauna mashi launin blue sky, daddadan kamshin turarenshi Ya karade hancin kowa, Hajiya sarah Lace ne ta sanya kalar shaddarshi, head dinta kalar takalman ƙafarta, sunyi kyau abunsu kamar sabbin ma’aurata
Chapter 113 · 0% Book details