← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 152

Sashe 39

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon abdallah ta yi fuskarta ɗauke da murmushi, da hannu yai mata nuni da surukansu da ke a tsaye suna fuskantar su

“mu je ko?” Sai lokacin ta lura da su, tafiya suka soma Yi a jere tunkan su ƙaraso Zahra take ta faman ingiza kafaɗar aneelerh

“ki je ki tarbo su,”

kunya ta hana Aneelerh zuwa, har saida suka ƙaraso, Abie Yana dariya Ya ruƙe hannun Abdalla suka fara yin gaisuwarsu ta manya”Marhaban marhaban lale surukai na gari, Sassannun ku, kun sha hanya, ku ƙaraso ciki” Ya ja hannun abdallah, Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su ɗauke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta miƙe mata hannu suka gaisa a mutunce”Sannu da zuwa Hajiya, mu shiga daga Ciki” ta yi maganar, tare da jan hannun hajiya adama wadda idonta ke akan Aneelerh, sai faman noƙe kai ta ke yi,
“Kunya kamar bafullatana, Ni kaina da nake bafullatana Bani da kalar kunyarki,” da zolaya hajiya adama ta yi maganar, Yayin da su ke shiga cikin babban falourn gidan, daddaɗan ƙamshin turarensu ya gauraya da sanyin A.c.
A saman soma mai mazaunin mutum uku Mami da ummi da hajiya adama su ka zauna, Abie da Uncle ɗan iya su ka zazzauna saman 2 sita, Aneelerh tana zaune saman one sita, Yayin da zahra ta ɗan zauna saman hannun sofa ɗin da Aneelerh ke zaune, sai faman sakarwa juna murmushi suke Yi, Gaisuwa ta musamman suka ƙara yiwa junan su cikin girmama juna da mutuntaka.

Uncle ɗan Iya Yana faman washe baki Yace”Abdallah Kai ne ka koma haka?gaskiya mun daɗe bamu haɗu ba, tun lokacin da ka fito daga cikin mota, idanuwana su ka yi tozali da kai sai da gabana ya faɗi araina nace ina muka samu baƙin Bature, Abdallah hutu ya zauna maka daga kai har Hajiyar taka kun yada zumunci ko in ce mun yada zumunci Allah dai ya shiryemu” dariya suka saki gaba ɗayan su.

Ummi tace”Ya gajiyar tafiya? Nasan Kun jigata sosai, tafiya daga jos zuwa abuja ba abune mai sauƙi ba, kun ma yi ƙoƙari dana ganku da kuzarin ku”

mami ta ɗaura da cewa”Alhamdulillah mun gode ma Allah da ya kare mana ku ya tsare mana ku har ku ka ƙaraso Lafiya, wannan abun farin ciki ne agare mu, gamu ga surukanmu, mutane masu ƙima da daraja, muna ƙara yi maku barka da zuwa” Maganar Mami ta yi matuƙar faranta zuciyoyinsu.

Musamman Hajiya adama har saida ta ɗan saki murmushin da ya bayyana jerarrun fararen haƙoranta.

A tsanake tace “A gaskiya ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, ni dama tun da muka fito daga cikin mota raina Ya bani munzo gidan mutunci da karamci musamman da naji gidan Uncle ɗan Iya ne Masha Allah, Fatan mun same ku lafiya” atare suka haɗa baki”Lafiya lou Alhamdulillah”

Uncle abdallah ne ya soma yin magana cikin dattako da halin girma
“Mun jin daɗin samun ku cikin ƙoshin Lafiya, Abun farin cikine wannan kuma muna godiya da irin tarbar da muka samu, Ina yi mana fatan kamar yadda muka haɗu anan, Ubangiji Allah Ya haɗamu A gidan aljanna alfarmar Annabi muhammad SAW, kusan atare suka haɗu wurin furta kalmar SAW

“Yakamata mu fara yiwa annabi Salati” Abie ne yai maganar, tare suka ɗaga hannuwansu bayan sunyi salati ya ci gaba da jero masu addu’o’i Suna amsawa da ameen ameen Bayan ya kammala, Uncle ɗan Iya ya wurga idon shi kan Aneelerh da ke ta faman sakin murmushi tana noƙe kai
Jin Muryarshi tasa ta ɗago da ido tana kallon shi
Daƙuwa ya sakar mata”Ungo nan, jira ki ke sai mun ce ki je ki gaishe da surukan naki? yarinya sai ka ce jinin fulani” Tsuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayansu, Yadda yai magana yai matuƙar basu dariya hada Aneelerh, Da sauri ta miƙe daga saman sofa ta nufi Hajiya adama daga ƙasa saman carpet ta zauna gefen ƙafar Hajiya adama, muryarta ƙasa ƙasa ta furta”Sannunku da zuwa, Ya gajiyar tafiya, ya kuma aka baro mutanan can” ɗaura hannu hajiya adama tayi saman kafaɗar Aneelerh

“Lafiyalou daughter in-law Fatan na same ki Lafiya”
Aneelerh ta amsa da lafiyalou, kafin ta matsa gefen uncle abdallah Ta gaishe da shi, da fara’a ya amsa mata

Bayan sun gama gaisawa da aneelerh, Zahra ta gaishe dasu, suka amsa mata
Kafin daga bisani, Mami tace”bismilla mu shiga ciki, Ku huta kada mu Cika ku da surutu, “ ta faɗi hakan ne don tasan yanayi na matafiya yafi buƙatar hutu, Miƙewa su ka yi Mami da Abie na agaba Hajiya adama da uncle abdallah suna abiye dasu, wuce abie yai da uncle abdallah zuwa ɗakinsa, Itama mami ta wuce nata ɗakin tare da hajiya adama bayan tafiyar su.

Fira ta 6arke tsakanin Zahra da Ummi, a lokacin Uncle ɗan Iya ya fita waje domin amsa kiran da akayi mashi a waya

“Wlh ummi takalman ƙafarta kalar na saratu obinna ne, kinsan ko kuɗinsu yakai dubu talatin” Ɗan zaro ido Ummi ta yi” Tab Aneelerh ashe surukan ki Attajiran masu kuɗi ne, ai naga sarƙar wuyanta da awarwaron hannunta duk na zanari ne, gaskiya kin taki sa’a, Yarinya mai ƙashin arziƙi,”

kwa6a fuska Zahra ta yi”ni kuma mai ƙashin tsiya ko”? ummi na dariya tace”Ni dai bance ba, kema ina maki fatan miji na gari da surukai na gari” yatsina fuska ta yi ƙasa ƙasa da murya ta furta”Suruki na gari kamar Owais, surukai na gari hamshaƙan masu kuɗi irin hajiya sarauta” Aneelerh dake zaune saman carpet ta miƙe ta koma saman sofa ta zauna
Ummi ta kalleta”nasan zasu buƙaci ganin jikansu, gashi ya tafi school till 6 na marece za’a tado su saboda lesson na Islamiya da ake Yi masu, “ zahra tace”Zan kira mahboob A waya ya je ya ɗauko shi, Ni fa dama can banso aka sanya shi hada islamiyyar ba, ace kullum sai ƙarfe shidda zai dawo gida, in banda weekend,”

Harara ummi ta ɗan watsa mata”Sannu Uwarsa, islamiyarce ke ba ki so ya yi kenan sai dai na bokon” Girgiza kai zahra tayi”Ba haka nake nufi ba ummi, Yaron ya yi ƙaranta brain ɗinsa ma ƙarama ce ta ya ya ki ke tunanin zai Iya ɗauke duk abunda aka koya masa”

Tun da suka fara magana aneelerh ta yi shiru tana kallonsu, acan ƙasan zuciyarta kewar baby junaid ce ta addabeta, maganar zahra tasa duk ta ji ba daɗi ita kanta ba ta son Yana kaiwa har ƙarfe shidda sai dai ba yadda za ta yi ita kanta tana so yaronta ya saba da karatun boko dana addini.

Tsawon lokaci suna fira a tsakanin su jefi jefi har aka fara kiran sallah, Abie da Uncle abdallah suka fito da haramar zuwa masallaci, a harabar gidan suka yi arba da uncle ɗan Iya zaune saman Kujera Yana danna waya, Abie ya ce da shi Ya tashi su je masallaci, A nan suka jira shi ya shiga gidan ya ɗauro alwala kafin ya dawo suka ɗunguma zuwa masallacin dake a kusa da gidansu

Acan Cikin Gidan kowa ya koma ɗaki domin yin sallar magrib, hankalin Aneelerh Yaƙi kwanciya, Jin shiru mahboob bai dawo mata da yaronta ba, Gashi har an kira sallah. A zaune ta ke saman darduma hannayenta Biyu sama tana jera addu’o’i tasha dogon hijabinta.

Ba zato ba tsammani ta ji saukar mutun saman Bayanta, Ya ƙanƙameta Yana tiƙar dariya”babyn mommy is back” Gabanta harya faɗi sai da taji muryarshi tukunna ta sauke ajiyar zuciya, haɗi da ɗan sakin murmushi jin ya kirata da sunan da malamansu suke kiranshi wato babyn mommy, bayan ta shafa addu’ar, ta zagayo da hannunta ta ruƙo damtsen shi ta zagayo da shi tare da zaunar da shi saman laps ɗinta, Kamar kullum fuskarshi duk jirwayen hawaye, uniform ɗin jikin shi riga ce fara sai wando red colour, daga saman rigar akwai ƴar coat launin Ja, kafin ya ta fi school saida ta gyara mashi sumar kanshi amma yanzu da ta kalli sumar kan nashi A hargitse ta ke.
Idanuwanshi luhu luhu ya furta”Mommy, kin ga banyi kuka ba yau ko? Ai kince in daina” smiling softly tace”jirwayen menene akan fuskarka” tai maganar tana nuna hawayen da indext finger dinta, kwa6e mata fuska yai”mommy ai ni bake nayi ma kuka ba, uncle mahboob ne da safe da zamu school, Ya cinye min chocolate ɗina da kika saka min a basket”

idanuwanshi cike tab da ƙwalla yai mata maganar, ranshi ya 6aci.

Ɗaure fuska aneelerh tayi”Na rasa gane me ke damun mahboob, shi bai siya maka ba sai dai ya cinye maka? Tir wlh andai ji kunya”

“Mommy don’t worry, Ni ma ai na rama”
“Dame ka rama” da mamaki ta yi mashi tambayar, hannu taga ya zura cikin aljihun wandonsa, ya zaro ɗan ƙaramin box mai kyan gaske Ya nuna mata
“Menene wannan”? Shu’umin murmushi babyn mommy ya saki”pls mommy kada ki yi min faɗa, inaso yadda ya sani zubar da hawayena shima ya yi kuka, A motar shi na samu wannan, buɗe ki gani abun da ke a ciki” yai maganar yana miƙa mata box din, bayan ta kar6a ta buɗe akwatin, haɗaɗɗen zoben azurfa ne, na mata mai kyan gaske stone ɗin jikin shi har ƙyalƙyali Ya ke yi,
Jinjina kai aneelerh tayi”Lallai Mahboob Ya iya kashe na ƴan mata kuɗi amma bai Iya kashe ma ƴan uwan shi ba, dama irinsu babu mai cin moriyarsu sai mata, kowace mai sa’ar ce wannan Ya siyama zobe kuma daga gani mai tsada ne”
“Mommy daga ni sai ke, kada ki faɗa mashi ni na ɗauka, Mubar shi yai ta wahalar nema shima Ya ji idan akwai daɗi” Cikin 6acin rai ya ke yin maganar.
“Babyn mommy, ai ni farin cikinka shine nawa, don haka kar6i box ɗin nan ka 6oye mana shi cikin rigar pillow,” kar6ar zoben junaid yai da gudu ya nufi gado ya haye tare da ruƙo pillow ya zuge zip ɗinshi Ya tura box ɗin, abun mugunta ya samu sai faman sakin murmushi yake yi kamar gonar auduga
Chapter 39 · 0% Book details