← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 152

Sashe 2

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Danish bai rasa idonshi ba, Sun samu sa6ani da Gabriel ne, Har takaiga ya naushi idon shi, wanda silar hakan Giant yazo ya tafi dashi, Na 6oye maki hakan ne saboda bana son hankalin ki ya tashi, Kuma Ni da kaina Danish ya faɗa mini cewa Lafiyar shi qalou ba abunda ya same shi, ' Angel ce ta kora mata jawabi, Hankalin batul yaƙi kwanciya da kalamanta, jikin ta yayi sanyi, hawaye tuni sun soma yin sintiri saman kuncin ta.

"Shikenan Yanzu ki faɗa mana Taya za'ae mu ga ɗan uwan mu Danish? Idan ma ta kama Ni zan bi ki mu shiga prison ne don mu nemo shi" Gabriel ne yai maganar da ƙwarin gwiwarsa, Har yanzu yana nan da rashin tsoronshi.

Girgiza kai Angel tayi"wannan aikina ne, Ni kaɗaice zan Iya dawo da Danish Cikin mu, In sha Allah, "

"But how could you do that? Bayan babu wata ƙofa da zaki Iya shiga prison"? Har ta buɗe baki da niyar Ta amsa Ma Naufal tambayar da yai mata, kwatsam! ba zato ba tsammani Kunnuwanta su ka jiyo mata motsin buɗe ƙopar ɗakin su, hakan yasa tai saurin Katse maganarta, Idanuwanta azazzare Take kallon su.

"Kamar buɗe ƙofar ɗakin Mu ake yi? Mun shiga uku, Asirin mu zai tonu, wlh mu gudu daga Cikin toilet ɗin nan," Parveen ce tai maganar, hankalinsu idan yai dubu toh ya tashi, Gaba ɗaya duk sun bi sun ruɗe, a sukwane Angel ta juya da gudu ta nufi Ƙofar toilet ta buɗe ta, Fucewar ta keda wuya suma suka bi bayanta, garin gudu har suna bangaje juna, Adai dai lokacin da suka faɗo tsakiyar ɗakin, kowannansu ya tsaya da tafiya, Idanuwansu azazzare su ke bin benan da kallo, sai faman haki suke yi babu mai sauran kwanciyar hankali acikin su, babban abunda su ke jima fargaba kada ace Tsohuwa zafreen ce, Ilai ko hasashen su Ya zama gaskiya, ƙofar na ƙarasa buɗewa kunnuwansu suka soma jiyo masu takun takalmanta Har wani sauti su ke badawa ƙwas ƙwas! Jikinsu Ya hau kakarwa zufa ta dinga tsastsafo masu ta ko'ina a jikin su.

Cikin muryar raɗa Deeja tace"Mun shiga uku Angel mun manta bamu maida tukunyar fulawar nan ba! Yanzu idan ta shiga toilet ɗin ya zamu yi?

Ƙasa ƙasa da murya Angel ta ce"In sha Allah ma ba zata shiga ba, Idan ma tai yunƙurin yin hakan zan dakatar da ita," ita kanta da ta ke yin maganar a tsoroce ta ke furtata, ƙarfin halin ne kawai.

Ahankali ta ke tunkaro in da suke atsaye Cikin shigarta ta jajayen kaya, Yau babu mask a kan fuskarta, Daga bayanta Giants ne Guda Biyu masu ƙirar Samudawa, ko da ta ƙaraso dab dasu saita dakata da yin tafiyar A tsanake ta ke binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Saboda tsabar ruɗu da kama kai, Jikin Angel na 6ari ta russinar da kanta Ƙasa muryarta babu natsuwa ta furta"Ina kwana" Tun da tsohuwa zafreen ta kafe ta da ido sam ta kasa motsawa, Lamarin ne ya ɗaure mata kai, Yadda Angel ta duƙa mata wurin gaishe da ita.....
Da sauri su Haris suka russinar da kansu tare da gaishe da ita Cikin girmamawa.

Babu wanda ta amsamawa a cikinsu, Tsawon mintuna biyar kafin ta ɗan yi gyaran murya tare da basu Umarnin su ɗago da kawunansu, bayan sun ɗago ta tsare fuskar angel da blue eyes ɗinta, Suspicious looking ta ke binta dashi Hatta tsigar jikin Angel sai da ta tashi haiƙam, Sam takasa yarda su haɗa ido da tsohuwa zafreen, ta dage tana ta wasa da yatsun hannunta, ta harɗe su acikin na juna, Su ta ƙurawa ido.

Su Deeja duk sun sha jinin jikin su, ganin irin kallon da tsohuwa zafreen ke bin Angel da shi, Kuskuren da Angel ta tafka shine gaishe da zafreen da ta yi, Mace Dattijuwa irin zafreen wadda taga jiya taga yau, Taya zata Iya yi mata wayau? Yarinyar da bata ta6a gaishe da ita ba, sai yau Hakan ya ƙara sanya mata zargin wani abu na faruwa a ɗakin nasu, A hankali takawar da idanuwanta daga kan fuskar Angel ta soma bin fuskokin su Batul da kallo, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi, sam babu alamun gaskiya atattare dasu, duk wani motsinsu akan idonta.

Ba zato ba tsammani suka ga ta tuntsire da dariya mai sautin gaske hankalinsu ya ƙara ɗugunzuma, a firgice su ke bin ta da kallo, Lokaci ɗaya ta dakata dayin dariyar ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri.

"Meyasa ki ka yi gaggawar gaishe dani tun kafin in buƙaci hakan? Kamar daga sama Angel taji ta jefa mata tambayar.

Yawu ta haɗiya kutt a maƙoshinta, Idanuwanta na kallon Ƙasa azazzare ta soma magana Cikin rashin natsuwa

"Nagane kuskure na, kuma Na yi danasanin rashin kunyar da na yi maki a kwanakin baya, inaso na gyara tsakanina dake ne saboda nasan ban kyauta ba.." tunkan ta kai ƙarshen maganar tsohuwa zafreen ta soma sakin bazawarin murmushi, wanda silar hakan yasa ta kasa ƙarasa zancen da ta kamo.

"Saboda meyasa kike son gyara tsakanina da ke"? Ras taji gabanta ya faɗi, Daƙyar ta tattara natsuwarta kafin ta ci gaba da magana"Mahafina bai koyar dani rashin kunya ba, Tunkafin rasuwar shi yana yawan yi mini nasiha akan girmama na gaba dani, amma saboda rashin jin magana irin nawa ban bi abinda yake koya mini ba nayi danasani........" Sosai ta fashe da kuka gaba ɗaya idonsu Hibba akanta, Tsabar mamaki yasa suka saki bakunansu suna kallon Fuskarta, Ba ƙaramar ƴar drama bace.

Da buɗar bakin tsohuwa zafreen sai cewa tai"well done Unaisah! Dila sarkin wayau! Da ace ke ƴar film ce tabbas zaki iya cin gasar wadda tafi kowa Iya wasan kwaikwayo, Tun da nake ba ata6a rainin mini wayau irin na yau ba, Ƴar ƙaramar yarinyar da na yi jika da ita...." maganar tsohuwa zafreen ba ƙaramin ƙara ɗaga masu hankali ta yi ba, duk sun sha Jinin Jikin su.

"Ku faɗa min Me ku ke shiryawa ne" Shiru su ka yi ƙirjinsu na bugawa , Mirmushin gefen fuska ta saki tare da cewa"Dama nasani ba za ku faɗa mini ba, Idan naso zan iya yin anfani da sihirin da nake dashi wurin jin abunda zuciyarku ke saƙa maku, Ko in sanya ku yi mini magana da kunan ku,'

Yanayin yadda suka zazzare Ƙwayar idanuwansu tamkar zata faɗo ƙasa, tsoro da firgici ne tsantsa akan fuskokin su.

Ganin tana ƙoƙarin buga sandarta ƙasa Yasa Angel tai saurin cewa"Zan faɗa maki gaskiya, " tsayar da ido zafreen tayi akan fuskarta.

"Tattaunawa mu ke yi akan yadda zamu ku6uta daga Cikin kurkukun nan saboda mun gaji da rayuwar kulle, Muna so mu ma mu yi rayuwar ƴanci kamar yarda sauran mutane su ke Yi"

Daƙyar ta kai ƙarshen maganar tana mai haɗiyar yawu, Su Batul duk suna sauraronsu babu wani mai natsuwa a cikin su.

"Ban yarda da maganar ki ba, A iya sani na prisoners basu da hankalin Yin tunani mai kyau irin wannan balle har su baki haɗin kai ku tattauna da junanku, Ke ce kika tsara komai Unaisah, saboda kina son karkatar da hankalina don In yarda da maganar ki, "

Tun kan ta ƙarasa maganar ta soma bin ɗakin nasu da kallo, Kamar sakarkaru haka suka dinga binta da ido Cike da fargabatar karta faɗa sashen toilet ɗinsu asiri Ya tonu, A hankali take tafiya tana ƙarewa ɗakin Kallo Kafin Ta Juyo a sukwane Ta tun kari sashen toilet ɗin su, Tashin hankalin A matuƙar tsorace suke kallon bayanta, Giants ɗin dake atare da ita basu motsa ba, suna atsaye Kamar gumaka

Su Angel Ido ya raina fata, Sai faman Cizon yatsa ta ke Yi, Ji take kamar ta watsa aguje tasha gaban zafreen.

"Innalillahi Ya Allah ta makance kafin ta shiga, Ya Allah ka taimake mu! ya Allah ka hanata gani" Acikin zuciyoyinsu suke furta hakan, Suna ganin ta shige Ciki, Zufa ta soma wanke fuskokinsu, Azeeza tuni ta fara matse kwallo, sun san dole Taga abunda suke aiwatarwa, Idan kuwa harta gano zasu ɗanɗani kuɗarsu ne, Kowa zaiji a jikin shi, Babban abunda yafi damun Angel gargaɗin da Salsabeel ya yi mata akan su yi takatsantsan Yanzu idan asiri ya tonu gaba ɗaya taja masu masifa da bala'e.

Runtse idanuwanta ta yi sosai, hawaye ta ko'ina suka shiga wanke fuskarta, idanuwansu Deeja akanta, Tausayin kansu ne ya kama su, Har sun fara hasashen irin Azabtarwar da za'ayi masu kafin akashe su, Sai bin Juna su ke yi da ido babu mai magana saboda Giants ɗin da ke tsaye akansu.

Fitowa tsohuwa zafreen ta yi daga sashen toilet ɗinsu, Fuskarta ɗauke da shu'umin murmushin nan nata mai wuyar fassaruwa, girgiza mata kai su ka dinga yi ba tare da sun iya furta komai ba, Sun riga da sunsan taga ƙofar nan shikenan ta faru da ta ƙare, Watan Cin ubansu ya tsaya, sun kirawa kansu mutuwa tunkafin lokacin su yayi.

"Wallahi Allah!....' Azeeza ce ta yi su6ul da baka, da sauri Gabriel Ya toshe mata bakinta da hannun shi, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwansu, duk sun ƙagara su ji wani hukunci zata yanke masu tun da ta gano plan ɗinsu.

Walking magestically ta ƙaraso gabansu Tare da tsaida sandarta a ƙasa, Daya bayan ɗaya ta ke kallon su tsawon mintuna Uku kafin ta soma magana atsanake

"Furennin da ku ka shufka sunyi kyau sosai, Wanene ke basu ruwa A cikin ku? Zaro ido su ka yi akan fuskarta Mamaki Ya kamasu, Aransu suka shiga ayyana cewa" ko dai bata ga ƙofar ba ne? Ko kuwa Allah ne yaji kokensu ya hanata ganin komai.

"Kun yi shiru baku bani amsa ba"? Yawu Angel ta haɗiya Muryarta Na rawa ta ce"am..um..ni..nice..Ni nake bata ruwa, tare da ƴan uwana,"

Murmushi tsohuwa zafreen ta saki tare da cewa"Ku cigaba da bata ruwa inason furenni, Nan da wani lokaci zan ɗauke tukunyar fulawar in mayar da ita ɗakina..." tsabar zalama tunkan ta ƙarasa maganar Angel tai wuff wurin cewa"idan ma kinaso Yanzu saina ɗauko maki ita ki tafi da ita, ai mu mun fi son duk wani abu da zai faranta maki rai" kallonta tsohuwa zafreen ta yi da tsoffin idanuwanta"Kamar baki da gaskiya? Ina magana kina katse ni"! A kausashe tayi maganar.
Chapter 2 · 0% Book details