Sashe 44
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ƙalla likitoci sun shafe tsawon awanni akansu, wani abu da yai mugun ɗaurewa Likitocin kai Ƙoshin Lafiyar Danish da kyawun surar shi! Tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin mutun mai rai da lafiya irin shi ba, gashi yaƙi farfaɗowa sun rasa gane wani kalar bacci ne ya ke yi, kuma sam babu wata lalura da ke gare shi, bacci ne kawai yake ta shara abin shi, Duk sun ƙagara da su ji bayani daga Gare su, Amma sun bari sai Yaran sun ji sauƙi tukunna su ji daga bakinsu menene ya haddasa masu depression? Da ƙananun shekarun su, mutun ɗaya da Sojojin su ke tsammanin Jin bayanai daga gare shi, Tun acikin jirgi da suka yi mashi allurar bacci bai ƙara farfaɗowa ba, Yanzu haka Yana akwance saman gado sai sharar baccinsa Ya ke yi.
Till Wuraren ƙarfe 12 Na rana, Gabriel ya soma mutsun mutsun farkawa daga bacci, Dama jiran shi suke Yi ya tashi, Kasancewar akwai na’urorin cctv a kowace kusurwa na medical rooms ɗin ta hanyar su likitocin su ka san da tashin sa.
Slowly ya buɗe idanuwanshi Akan ceilling ɗin ɗakin, Tamkar a mafarki Ya ke kallon shi, tsantsar mamaki ne da al’ajabi akan fuskarshi, Tambayar kanshi ya soma yi cikin ruɗanin zuciya, Ina ne nan? Wanene ya kawo ni? Anya ba mafarki nake Yi ba”? da wata irin kasala Gabriel ya miƙe zaune Yana faman wurwurga ƙwayar idanuwansa akan haɗaɗɗen room ɗin da ya ke a ciki, Lamarin ya ɗaure mashi kai, Daddafe kanshi yai da hannayenshi biyu tamkar zai fasa ƙara, abunda ya ƙara rikitar da shi Uniform ɗin da aka canza mashi, daga jajaye zuwa light blue Riga da wando, Ƙasa ƙasa da murya yake ambaton sunayen ƴan uwan shi
“Azeeza! Angel! Danish! Batul! Naufal! Javed! Par.....” bai ƙarasa maganar ba sakamakon Jin motsin buɗe ƙofa, A firgice ya zazzare idanuwanshi akan masu shigowa.
Uku daga Cikinsu asanye suke da scrub suit, Kayan Likitoci, biyun da ke biye da su cikin kakin Sojoji masu ruƙe da muƙaman Major da Captain wakilai ne da aka turo daga can headquater, likitocin uku dake atare dasu Turawa sun haɗa da md (medical director) Dr. mark Johnson, bayan shi sai Hospital Ceo Dr. laura Davis babbar macace fara jawur, na ƙarshen su health records technician ne Dr. Danial Brown hannun shi ruƙe da Apple ipad.
A gaban gadon shi su ka tsaya suna dubanshi
Cikin harshen turanci suke Yin magana
“Fatan ka farka Lafiya? Ya jikin naka”? Dr Brown ne yai mashi maganar, cikin kulawa,.Muryarshi adabarbarce ya furta”Ina ƴan uwana suke”? Tambayar farko da ya fara jefa masu.
“Did you forget that we found you in the forest? (Kamanta a daji muka tsince ku”?) Major ne Yai mashi maganar, Gabriel was silent as he tried to remember what had happened. They could see that he was confused and would need time to sort out his memories.
Nuna mashi screen ɗin Ipad dr bown yai, hotunansu Angel ne a jere da suka ɗauka yayi saving ɗinsu akan wayar, ƙura ido gabriel yai akan screen ɗin, a tsanake ya ke ƙare masu kallo, nan take ya zaro ido wani irin farin Cikine Ya lullu6e shi, hada murmushin sa.
“Do you remember everything now”? Major ne yai maganar, Jinjina mashi kai yai alamar eh, janye wayar dr.bown yai tare da kallon abokan aikin nasa da sojojin
“He needs some food and a cold drink” Jinjina kai su ka Yi, A waya Md Ya kira nurse Ya isar da saƙon abunda za’a kawo masu, cikin ƙanƙanin Lokaci Nurse ta shigo hannunta biyu ruƙe da round tray saman shi plate ne shaƙe da abinci sai bottles biyu na ruwa dana lemu mai sanyi, A saman table ɗin gaban gadon gabriel ta sauke tray ɗin kafin ta juya ta fuce, Zama suka yi saman sofa ɗin dake a ɗakin suna jiran shi Ya kammala ci.
Kafin ya fara cin abinci sai da ya fara ɗagowa ya kalle su”Ni zan ci”? murmushi suka sakar mashi Jin tambayar da yai masu
Md yace”’It’s all yours. Eat until you are satisfied. We need to talk to you when you’re done.”
A kan idonsu Gabriel Ke cin abincin sai da ya ci ya ƙoshi Ya kora da ruwan sanyi, tukunna ya dawo da duban shi gare su.
“Zamu iya farawa yanzu” ɗaga masu kai yai alamar eh
Major ne Ya fara yi mashi magana
“Zaka Iya fadamin alaƙar dake a tsakaninka da sauran yaran? Jinjina kai Gabriel yai”Eh, Ƴan uwana ne”
“Menene sunayenku da shekarunku”?
Duk wata kalma da Gabriel ya furta a rubuce dr. Brown ya ke shigar da bayanan cikin ipad ɗin hannunsa.
“Muna zargin Ɗan ta’addan da muka je kamawa A dajine yai garkuwa da ku don gujewa farmakin da zamu kai mashi Shin dagaske ne”? Ras Gaban Gabriel Ya faɗi, tuni yanayin fuskarshi ya canza baisan amsar da zai basu ba, jin shiru yasa Major ambaton sunanshi”Gabriel amsar ka mu ke jira, muna so mu tabbatar da hasashen mu ne”
idanuwanshi sunyi wuƙi wuƙi akan fuskokinsu, duk sun ƙagara da son jin amsar da zai basu, abunda yasa ya shiga ruɗani kokwantone yake yi Akan ya faɗa masu gaskiya ko kuwa ya 6oyeta gudun kada su ƙara jefa rayuwarsu cikin hatsari, Yana tsoron abunda harshenshi zai furta, Tunawa da Angel yasa shi saurin cewa
“I have forgotten everything, but my sister Angel knows everything.” ya faɗi hakanne don su ƙyale shi, don kuma su tuntu6eta don yasan tafi shi wayau ita kaɗai tasan yadda za ta yi ta fidda su.
Numfasawa Kowan nan su yai, sun fahimci har yanzu babu kwanciyar hankali atattare da shi
“Gabriel, please calm down and explain to us what happened. We’re medical professionals, and we have the right to examine your health and help you get better. And those soldiers you see are the ones who saved your life in the forest. If you cooperate with us, we’ll help you and reunite you with your family.” cikin kwantar da murya dr laura ta yi mashi magana.
wahalalln Yawu gabriel ya haɗiya muryarshi na rawa ya furta”Angel tasan komai, duk wani bayani da kuke son ji daga bakina ita zata faɗa maku,”
“Can you identify your sister from these photos? Wacece Angel a cikinsu”? Dr.brown ne yai maganar tare da nuna mashi hotunansu ta cikin ipad’s gallery din hannunsa
Ƙura ido gabriel yai akan fuskarta ya ɗaura yatsan shi”Itace”
Dr. mark ne ya soma yin magana
“muna son jin bayani dangane da abunda ke damunku”? Ya yi mashi tambayar ne saboda abun da ya ɗaure masu kai, na farko Depression dake damunsu da ƙananun shekarun su, na biyu dangane da matashin saurayin nan da ya tsone masu ido wato Danish da ya ƙi farkawa daga bacci.
“Babu” amsar daya basu kenan
Captaim yace”ka natsu kayi mana bayani, ba cutar dakai zamuyi ba, idan har baka bamu amsa ba zamu maida ku inda muka ɗauko ku ne” jin haka yasa Gabriel zazzare mashi ido, da sauri ya girgiza kai yana faɗin”Ni ai bansan komai ba Angel ce ta sani,” kansu ya ɗaure jin yanata ambaton sunan Angel
“We should wait until your sister wakes up and see if she can provide any information that might help us.” acewar dr. brown
Gaba ɗaya sunyi amanna da hakan, Miƙewa Sojojin sukayi tare da likitocin Bayan sunce mashi ya koma ya kwanta suka fuce daga ɗakin, A bakin ƙofar ɗakin suka tsaya suna tattaunawa a tsakaninsu, Hankalinsu yaƙi kwanciya da yaran, sun fara kokwanton Anya kuwa Jinsin su ne? Ko dai sun yi kuskure wurin ɗauko su a matsayin ɗan’ta’addan ƙasar su ne yai garkuwa da su, Kyawun yaran yafi komai tafiya da hankalin su, sun rasa da wani jinsi zasu danganta su, Saboda Kyawun prisoners Ya banbanta dana sauran mutane su ɗin na dabanne.
Bayan kammala tattaunawar su, Sojojin sun bar asibitin da niyar idan sauran Yaran suka farfaɗo daga bacci Ayi hanzarin kiransu da gaggawa don suna buƙatar ganawa da su.
Nauyayyar ajiyar zuciya Gabriel ya sauke tun bayan fitarsu yake ta sakin murmushi baƙin shi yaƙi rufuwa, tuni hawayen farin ciki sun wanke fuskarshi bakomai yake tunawa ba fa ce twin sister ɗinsa da sauran ƴan uwansu da suka rasa rayukan su a kurkuku, Ya ji raɗaɗin Rasa su da su ka yi da yanzu duk atare zasu ji daɗin rayuwarsu, don yana ji aranshi ƙarshen wahalar su ce tazo, babban burin shi a yanzu sauran ƴan uwansu su farfaɗo, Yasan zasuyi farin ciki Mara misaltuwa, fatan shi Allah yasa Idan Angel ta farfaɗo Ta yi ƙoƙari wurin yin magana da sojojin cikin hikma yadda zata yi masu hanyar komawa gidan daddynta ko dan saboda azeezarshi da ta ƙwallafa rai da son zuwa can.
Yayin da ya ke yin tunanin, hawaye basu daina yin sintiri akan fuskarsa ba, a saman pillow ya ɗaura kansa, ga sanyin A.c dake ratsa jikinsa.
Motsin buɗe ƙofa ya ji da sauri ya ɗan yunƙura ya miƙe zaune yana kallon mai shigowa ciki, Matashiyar Nurse ɗin da ta kawo masa abinci ce ɗazu, Fuskarta ɗauke da murmushi agaban gadon ta tsaya tare da goya hannayenta saman ƙirjinta
Fuskarta da murmushi ta soma magana
“Hello, I’m Sister Rebecca, May I know your name?”
Daƙyar ya iya buɗe baki ya furta suna shi “Gabriel” jinjina kai nurse rebecca tayi a wayance tace “It’s wonderful to meet you, Gabriel. How is your body? I hope you’re feeling better now,”
Rashin sabo ya hana ya saki jiki da ita, cikin rashin natsuwa yake amsa mata.
Ganin yadda take sakar masa fuska yasa shima sakin tashi fuskar
“Is there any part of your body that’s hurting?” cikin kulawa ta yi mashi tambayar.
Girgiza mata kai yai”A’a lafiyata ƙalau”
“Okay, is there anything you need?” again ta ƙara tambayar shi.
Ƙasa ƙasa da murya ya furta “No, thank you.”
“Okey, ko akwai wani abu da kake buƙata”? Shiru ya ɗanyi yana faman wurwurga eye balls dinsa ɗakin Ya ke bi da kallo
Ganin kamar tv yake kallo yasa tace” “Would you like to watch some TV?”
Numfasawa yai tare da mayar da idon shi akanta
“I wanna see my brothers, I want to know how they’re doing.”