← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 152

Sashe 148

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A haka suka nufi cikin gidan, banda Major wanda tuni Ya nufi sauran ƴan uwanshi sojoji dake kai komo a cikin gidan.
A zaune yake saman Sofa, ya ɗauki wankan dark jeans and white V-neck shirt kayan sun bi shape din jikinsa, hankalinshi a kwance yake operating laptop din gabansa dake ajiye kan table,
Fitowa mom turai tayi daga cikin kitchen hannunta ruƙe da mugs guda biyu na coffee, ta nufi cikin falon fuskarta asake taje gaban table din Zaki ta ɗaura cup ɗaya
“Ga wannan My son, Nasan zaka buƙace shi” ɗagowa yayi fuskarshi ɗauke da murmushi ya furta”mom nagode da kulawarki agareni, kina ji da ɗan nan naki”
Kafin ta kuma cewa wani abu muryar ibad ta janyo hankulansu ga dubanshi, fitowarshi kenan daga cikin ɗaki Sai faman yin miƙa yake yi haɗi da yin hamma, daga shi sai short a jikin shi
Muryarshi da shagwa6a ya furta”mommy nifa”?
Zaki ne ya bashi amsa da cewa”Na ƙarfi ne zoka ƙwata, ɗan rainin wayau sai yanzu ka ga damar tashi daga baccin”
Tur6une fuska yayi”babban yaya jiya fa bamuyi wani isasshen bacci ba, shine nake yin ramuwar na jiyan”
Dariya mom turai tayi shagwa6ar ibad har mamaki take bata, duk da shima jazz idan abun ya motsa yana yi mata shagwa6a
“Ranka zai 6aci ne idan ka ci gaba dayi min shagwa6a kamar wani ƙaramin yaro,”
Bubbuga ƙafafuwanshi yayi hada ruƙe qugunsa wato yayi sai dai ayanka shi
Mom turai tace”sai fa kana haƙuri da shi, kasan autane kuma kai ka rainesa duk abun da yayi kai ne ka sangartar da shi”
Ta6e baki Zaki yayi tare da kau da idonshi daga kan fuskar Ibad Ya miƙa hannu ya ɗauki mug Ya soma kur6ar coffee..
“last born zoka kar6i wannan” girgiza mata kai yayi”no mommy, na hannun shi nakeso yasha ya rage min, wannan nakine ki sha” a sukwane Zaki ya dakata da shan coffeen Ya waiwayo yana dubanshi, Ya rasa gane dalilin dayasa Ibad yake yi mashi haka, aduk lokacin da zai ci abu saiya sa rigima akan yaci ya rage mashi kamar wani tsaran wasan shi
“Kada ka damu zan shiga kitchen in haɗa nawa, kai dai kar6i kasha” mom turai ce tayi maganar
Ibad ya maƙe mata kafaɗa”mom ni ai nafison yasha ya rage min”
Girgiza kai Zaki yayi tare da kallon mom turai yace”zan rage mashi”
“Amma ai baida yawa taya zai isheku ku biyu abunda baifi rabin cup ba”
“Idan bai ishe mu ba, zan turo shi ya ƙaro mana wani a kitchen”
Gyaɗa kai tayi okey, Har ta nufi sofa zata zauna, sallamar sir mubarak ta katse mata hanzarinta,
Kusan atare suka kai idanuwansu ga duban ƙofar falon
Shigowa Sir mubarak yayi hannunshi dafe da dr jazz, tsabar firgice Yasa mom turai ta saki mug din hannunta gaba ɗaya ruwan coffeen Ya zube kan floor, Jikinta na 6ari ta nufe su, Hankalin kowan nan su ya tashi, zaki tuni ya dakata da shan coffeen a hanzarce ya miƙe ya nufi sir mubarak, Ibad kuwa hannayenshi biyu ya ɗaura saman kanshi yana ambaton”mun shiga uku, ɗan uwa Jazz meya same ka? Kayi hatsarin mota ne?

Muryar turai na rawa take fadin”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, babe meya faru da jazz ɗina? idanuwanta har sun fara fitar da ƙwalla,
Sir mubarak bai sauraresu ba, Ya nufi sofa da sauri zaki Ya taimaka mashi suka zaunar da jazz.
A Hankali Ya ɗago Yana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin ya tsayar da idanuwanshi kan mom turai da tafara sharar ƙwalla, Jikinta asanyaye ta nufo su ta zauna gefen jazz ta ruƙo hannun shi acikin nata,
“Kayi shiru bakace komai ba? Meya faru da jazz”?
“Daddy kai muke sauraro,” acewar Ibad wanda tuni ya dawo gefen ɗan uwanshi zaki ya tsaya hadi da ruƙe qugunshi
A tsanake ya soma yi masu magana”ku kwantar da hankalinku.....” tunkafin ya ƙarasa maganar, mom turai ta katse shi ta hanyar yi mashi tsawa tana fadin”taya zakace mu kwantar da hankalin mu? Yaro ya fita gida lafiyarshi qalau yanzu kuma ka dawo dashi goshi ɗaure da bandage ga tabonni akan fuskarshi, sannan babu kayan da ya fita da su a jikin shi, ni dama tun jiya hankalina bai kwanta da fitar jazz ba, babe ka faɗamin meya faru da yarona”!! idanuwanta azazzare tayi mashi maganar.

Tun da yake da turai bata ta6a gigin katse shi yana cikin yin magana ba sai yau, hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa ranta yakai maƙura a wurin 6aci,
“Mommy, yaya zaki, Ibad” dr jazz ne ya ambaci sunayensu, a hanzarce suka kai dubansu gare shi.

“Zanyi maku bayanin komai”
“A’a jazz shi nake so yayi min bayani, gaba daya a raunace kake, ka daina yin magana zaka fama ciwonka” ta faɗa tare da kallon sir mubarak wanda yayi shiru yana kallon fuskarta...
“Meyasa ka tsareni da ido? Ba zaka yi min bayani ba”?
Bai tanka mata ba har saida ya samu wuri saman sofa dake fuskantar su, Ya zauna, tukunna ya samu natsuwar yin masu bayanin komai daya faru.......
A ƙarshe yace”bana buƙatar wani yaji abun nan saboda aikin sirri ne sukeyi, basu buƙatar kowa ya sani, Na faɗa maku ne don na wanke kaina daga zargin da zakuyi min na halin da na jefa jazz”
Cikin sanyin murya turai tace”am sorry dear, nayi maka tsawa bisa rashin sani, kayi hakuri dan Allah, hankalina ne ba akwance ba”
“Na fahimce ki,” atakaice ya furta hakan
Mayar da duban ta tayi akan jazz”dan Allah nan gaba kada ka ƙarayin wannan gangancin, duk wani abu da zakayi ka sanar da mahaifinka koda ace ni bazaka sanar min ba,” amsa mata yayi da toh,
Kafin ta juyo da dubanta kan sir mubarak”Babe, babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin yi maka godiya saboda irin kulawar da kake ba jazz.....” kafin ta ƙare maganar sir mubarak yai hanzarin katseta”Kada na sake jin kinyi min godiya saboda nayiwa jazz abu, kinsan banaso” cikin sanyin murya tace”nadaina in sha Allah”
“Daddy, sannu da dawowa, nayi missing dinka sosai, meyasa jiya baka faɗamin halin da kake aciki ba ai da nazo asibitin na tayaka jinya” zaki ne yayi maganar yayin da yake ƙoƙarin zama gefen jazz
Murmushi sir mubarak ya sakar mashi”sanyin idaniyata, ina fata na same ku lafiya”?
Mayar mashi da martanin murmushin Zaki yayi”lafiyalou, sai dai jiya dukkanmu bamu runtsa ba saboda rashin ganinku da bamuyi ba”
Sir mubarak yace”shiyasa naga idanuwanku sun kumbura, ashe bani kadai na kwana azaune ba”
Tun da suka fara magana ibad ya haɗe ranshi,
“Daddy ni baka ganni bane”? Ya faɗa yana duban sir mubarak
Girgiza kai ya ɗanyi kafin yace”naganka ibad, amma nida kai wanene ya dace ya fara gaishe da wani? Yamutsa fuskarshi yayi ƙasa ƙasa da murya ya furta”sannu da dawowa dad” ta6e baki sir mubarak yayi saida na roƙa, bubbuga ƙafa ibad yayi
Mom turai tace”mu shiga ciki, in taimaka maka kayi wanka” zaro ido Ibad yayi haɗi da furta”Mom wa zaki ma wanka? Jazz ko daddy”? Duk da halin da suke aciki na damuwa hakan bai hanasu yin dariya ba, shi kanshi jazz din saida ya murmusa,
“Daddynku nake magana akai,” hannu biyu yasa ya toshe bakinshi, Idan ya kalli sir mubarak sai ya kalli mom turai
Ko kaɗan batajin kunyar ƴa’ƴanshi, saboda ita aganinta bawani abu bane donta furta hakan agabansu.
“My son, zamu shiga”
Zaki yace”okey, zan tafi da jazz ɗaki, zan taimaka mashi yayi wanka ya canza kayan jikinshi’
“Hakan yayi,” ta faɗa tare da duban Ibad Har yanzu mamaki bai sake shi ba, sai kace baiyi rayuwa a turai ba.
“Akwai kayan abinci dana shirya mana a kitchen, ka shiga ka dauko su a dining zaka jera”
Amsa mata yayi da toh, da sauri ya juya ya nufi hanyar kitchen
Miƙewa zaki yayi tare da ruƙo jazz ya miƙar dashi,
“Allah ya baka lafiya my jazz,” amsa mata yayi da ameen, kafin suka nufi ɗakin shi
Bayan tafiyarsu ta dubi sir mubarak”ina ƙara baka hakuri, kasan ba halina bane”
Murmushi yasakar mata”kada hakan ya dame ki, ni dama fargabana halin da zaki shiga, but Alhamdulillah tun da kin fahince ni, yanzu bani da sauran damuwa” Ya faɗa tare da ruƙo hannunta suka nufi bedroom dinshi
“Jiya nayi kewarka, idanuwana sunyi maraicin ganinka, dole na haƙura na rungume pillow amadadinka” tayi maganar ayayin da take taimaka mashi wurin cire Rigar jikinshi
Daɗaɗan kalamanta ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya sukeyi ba, shiyasa akoda yaushe yake ƙara jin sonta, saboda ƙaunar da take nuna mashi, tun farkon auransu bata ta6a barin ya shiga toilet yin wanka shi kadaiba sai idan wani uzirinne mai ƙarfi ya hanasu shiga atare, sannan ta hana ya ajiye mata masu aiki agida ba yadda baiyi da ita ba akan baison tanayin aikin wahala amma taƙiya saboda kishinshi da take yi, batason wata ta ƙwace mata mijinta,
Atare suka shiga toilet.

*ANEELERH❤‍🔥*
Chapter 148 · 0% Book details