← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 152

Sashe 144

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗaga mashi kai boss yayi alamar eh, fuskarshi da damuwa yace”ubangiji Allah yaba shi lafiya, Allah kuma ya kawo mashi ƙarshen wahalar shi”Boss ya amsa mashi da ameen kafin yace”yanzu haka Prime minister da ɗan uwanshi, sun shiga dashi bathroom zasuyi mashi wanka, sheikh imam ne ya bada shawarar yin hakan”
Zaro ido big guy yai da zolaya yace”Yanzu wannan ƙaton balagaggen zasuyi ma wanka? Yaron fa yakai chief dinmu girman jiki,”
Harara Boss man ya jefa mashi”laifina ne dana tsaya yin magana da ɗan ƙwaya, sai kace ba ka ji nace maka bai iya ɗaga koda yatsansa ba, lalura ce ko kai kanka akwai ciwon da sai dai adinga yi maka wanka, ba fata nake yi maka ba, ina dai kwatanta maka ne babu wanda yafi ƙarfin ƙaddara”
Dariya big guy yasaki”Haba mutumina, nima fa wasa nake yi, nadai jinjina lamarin ne, amma baka fadamin ba prime minister baiyi mamakin ganin fuskar yaron ba”?
Dariya boss yayi kafin yace”daɗina da kai shegen son gulma uwa mace”
Cike da zumuɗi big guy yace”ni dai ka amsa min tambayata na ƙosa naji”
Boss man yace”kallo yabarka, hankalin prime minister ba ƙaramin tashi yayi ba, kusan fa hauka yayi mana gaba ɗaya ya rikice tunda yayi tozali da fuskar yaron, daƙyar fa muka shawo kanshi, duk yabi ya ruɗe......” a tsanake Man ya labarta mashi komai.
Dariyar shaƙiyanci Big guy yasaki hada tafa hannayensa yana fadin”ni dama nasan za’a rina wallahi, nifa tuntuni nake mamakin kamanninsu da yaron, koda ake maganar yana kama da chief namu saida na raya arainacewa duk ranar da hateem yayi arba da yaron sai ya sha mamaki, donni nafi ganin kamanninshi da nashi, sai gashi maganata ta tabbata” da ƙwarin gwiwa ya ƙare maganar, boss da zolaya yace”sannu malamin duba, aikinka na kyau, ka tsareni da surutu kamar kanyar da bata da daɗi, ka hanani ƙarasawa inda zanje”
“Ina zakaje ne”? Big guy ya jefa mashi tambayar.
“Sheikh imam ne Ya buƙaci atara mashi sauran yaran yana son ganinsu”
Big guy yace”ai ƙwara yagansu domin kuwa suna buƙatarshi kodan saboda wannan jarin taka, ni ina da tabbacin ba’a rasa almatsutsai akanta.....”dariyace ta kubce mashi daƙyar ya ƙare maganar, ganin yadda boss man ya haɗe fuskarshi.
Harara ya jefa mashi”Idan ka isa ka maimaita maganarnan agaban chief”
Big guy yace”ai ko giyar wake nasha bazanyi wannan gangancin ba,”
Fuskar boss ɗauke da fara’a Yabi ta gefen big guy Ya yi gaba abunshi
Ɗaga murya big guy yai tare da cewa”Yaran suna a ɗakin Jarinka gaba ɗayansu na tarasu anan”
Murmushi taj yasaki, haɗi da girgiza kanshi, bakomai yasa shi yin hakan ba face sunan da big guy yake kiran Babynsa angel, wato JARI, saboda yace mashi chief zaiba auranta yafi son inda zata huta shine fa ya ruƙe abun azuciyarshi har yake tsokanarshi da sunanta.

Idan muka koma 6angaren su unaisah, tuni sun kammala yin breakfast dinsu, kowa yaci ya ƙoshi yayi hani’an, sai dai damuwa ta hanasu sakat, Hankalinsu ba akwance Yake ba, sunyi zugudum saman carpet, kowa ya zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, jefi jefi sukan buɗe baki suce Allah sarki danish dinmu, ko awani hali yake a yanzu, a lokacin ummin america ta shiga toilet din dakin nasu.

Batool ta kwantar da kanta kan kafaɗar unaisah, Azeeza ta ɗaura nata kan a shoulder din Sajeed, hannayensu ruƙe cikin na juna, Jemimah ta haye bisa laps din haris idanuwanta alumshe sai faman firgita take Yi tana jan numfashi kamar baccine ke ƙoƙarin yin awon gaba da ita, parveen da naufal sun jingina bayansu jikin gado fuskokinsu babu walwala, hannah kuwa ta ɗaura kanta saman laps din javed, sunyi shiru babu mai magana, daga tsakiyar carpet din tray din kayan abincin da suka kammala ci ne ba akaiga kawar da su ba, wasu daga cikinsu sai faman lumshe idanuwansu sukeyi alamun bacci suke ji.

Jin motsin buɗe ƙofar toilet yasa Batool yin saurin runtse idanuwanta ta ƙanƙame unaisah, gudun kada ta haɗa ido da aunty ummi, fitowa tayi daga cikin toilet din, sautin takalman ƙafartane ya fargar da masu gyangyadin cikinsu, gaba daya suka ware idanuwansu akan ummi dake tunkarosu.

Ta fahimci tsantsar damuwace atattare dasu, tun ɗazu da suna cin abinci ta lura da kyar suke cusa abinci abakunansu, tasan bai wuci damuwar halin da ɗan uwansu yake aciki bane”
“Aunty ummi, Inaso zanje dakin danish in duba jikinshi” unaisah ce tayi maganar
Ummi tace”a’a, ba’a bada iznin wani daga cikin ku Ya fita ba”
Ya mutsa fuska unaisah tayi tamkar zata fashe da kuka ta kuma cewa”aunty ummi batool ta manta doguwar rigarta a ɗakinki jiya da su ka je kwana, zanje na ɗauko mata”
Girgiza kai ummi tayi”basai kinje ba, zuwa anjima da kaina zan dauko mata rigarta” zumbura mata baki Unaisah tayi duk yadda taso tayi ma ummi wayau taƙi barinta ta fita.
A ƙule unaisah tace “To waimu haka zamuyi ta zama a ɗaki kamar an kulle kaji a keji”
Dariya ummi tasaki har fararen haƙoranta suka bayyana tar dasu kamar gonar auduga
“Kin gaji ne”? Ɗaga mata gira unaisah tayi alamar eh.
Gyaɗa kai ummi tayi”okey, bari na taimaka maku ku girgije jikinku,” basu fahimci me take nufi ba.
Zura hannu tayi cikin aljihun doguwar rigar jikinta ta zaro iphone dinta, duk sun ƙura mata ido suna jiran ganin me zatayi da wayar.
Zira ziran yatsun hannunta ta ɗaura kan screen din wayar ta soma yin pressing dinta, jim kaɗan daddaɗan sautin kiɗa ya soma karaɗe bedroom din nasu, taken waƙar ed shareen mai suna Shape of you.

Fuskarta ɗauke da shu’umin murmushi take kallonsu, sun ƙura mata ido suna kallonta, ganin ta fara jujjuya qugunta tana taka rawa.

“Idan kuna ra’ayi ku taso muyi rawa” ɗaure fuska Unaisah tayi ranta a6ace take dubanta har ta buɗe baki zatace mata bazasuyi rawarba, Sajeed Ya miƙe Yana taka rawa ya nufi tsakiyar ɗakin, miƙewa Azeeza tayi da sauri tabi shi Ya ruƙo hannunta Yana jujjuyata, tuntsirewa Ummi tayi da dariya tana kallon su, abu kamar wasa sautin kiɗan yafara kai masu karo, Naufal ya miƙe ya ruƙo hannun Parveen suka nufi tsakiyar ɗakin suma suka fara yin rawa, Aruɗe unaisah take kallonsu kamar waɗanda akayima asiri, lallai ummi ba ƙaramar shaidaniya bace hakanan taja hankalinsu da sautin kiɗa, ruƙo hannun Hanna javed yai suka miƙa suma suka nufi tsakiyar dakin, Haris Ya miƙe Jemimah ta like mashi tana fadin itama zatayi rawar, ya ruko hannunta suka bi sahu, Ya rage saura Unaisah da Batool su kadai ne suka ki tashi.

“Sanya damuwa aranku bazai ta6a yi maku maganin matsalarku ba, Ni taimakon ku nake sonyi don na fahimci baku san me ake nufi dajin dadin rayuwa ba, kunfi so kuyita ƙuntata kanku bayan kowani ɗan adam yana da damar da zai sanya kanshi farin ciki, If you let me do my job, you’ll see the positive results soon.”......” muryarta da kwarkwasa take yin magana tana kallon Batool da Unaisah.

“Idan kunaso mu zauna lafiya daku, to ku bani haɗin kai, Ni kuma zan wayar maku da kanku, zan sanyaku farin cikin da zai kawar maku da damuwarku” da shaƙiyanci take yi masu magana tana ɗage girarta.

Sunyi shiru babu alamun zasu tanka mata, shu’umar dariya tasaki tare da cewa”Na fahimci unaisah kece mai taurin kai, Saboda ke Batool taƙi tashi ta taka rawa ko”? Murguɗa mata baki unaisah tayi.
“Idan kika bani hadin kai mukayi rawa zan barki ki fita daga ɗakin nan kije wurin ɗan uwanki danish....”tunkan ummi ta rufe baki unaisah tayi saurin furta”a’a sai dai ki bari in fara zuwa dakin shi, Idan na dawo sai muyi rawar”
“Zaki rasa damar da kike da ita” acewar ummi, Ta furta maganar tare da miƙa ma batool hannunta alamar ta taso suyi yawa, cike da jin shakkarta Batool take kallonta, fuskar ummi a ɗaure tace da ita”Come to me” sai da batool tafara kallon unaisah jikinta sukuku kafin ta yunƙura ta miƙe tare da ɗaura hannunta na dama saman hannun ummin america, gam ta ruƙe hannun tajata zuwa tsakiyar ɗakin rawa suka soma takawa kamar mace da namiji haka take juya batool tana rungumeta idonta akan unaisah data haɗe fuska tana satar kallonsu.

Canza masu waƙa tayi ta sanya masu waƙar rema mai taken baby come down, tunda sautin kiɗan Ya fara ratsa mata zuciya takasa jurewa ji tayi kamar ana janta a hankali ta miƙe tsaye tana kallon ƴan uwanta dake ta tiƙar rawa suna dariya, itama sai taji tana buƙatar yin nishaɗin kota ɗebe kewar danish dake damunta.
Ganin ta miƙe tsaye sototo tana kallonsu yasa ummi miƙa mata hannu ɗaya alamar tazo gareta.
Maƙe mata kafaɗa tayi alamar bazata zo ba, batool tace”please sister kizo muyi yawa atare dan Allah” harara ta watsa ma batool, muryar sajeed ce ta janyo hankalinta ga dubanshi.
“Sister zo mu taka mana, muna buƙatarki afilin nan” murguɗa mashi baki tayi.
“Genie dan Allah kizo muyi rawa, kinga ni banda abokin yi haris baiyi dani” da shagwa6a jemimah tayi mata maganar, hada marairaice mata fuska.
Magiya suka dinga mata akan tashigo suyi rawar, tun tana maƙe masu kafaɗa, har dai jemimah tazo taja hannunta suka shiga filin, ai tunda tafara taka rawa kamar ɗiyar roba, daɗi ya kamasu ganin unaisah ta saki jiki tana tiƙar rawa, nan fa kowa ya bada himmah, sosai suke jijjiga qugunansu, wani abun ƙayatarwarma sai sun yarfar da sumar kansu kamar indiyawa, sautin kiɗan ba ƙaramin ƙara masu ƙaimi yake yi ba, ummi ce kaɗai take bin waƙar suma tun basu iyaba har suka fara bi saboda harshen turancine tamkar yarensu ne........:
Dawo da waƙar farko tayi jin sun fara dauka suna bi, aikuwa gaba daya suka kware murya suna bin waƙar

Baby, calm down, calm down
Girl, this your body e put my heart for lockdown
For lockdown, oh, lockdown
Girl, you sweet like Fanta, Fanta
If I tell you say I love you no dey form yanga, oh, yanga
No tell me no, no, no, no, whoa-whoa-whoa-whoa
Oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh
Baby, come gimme your lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-love
You got me like, “Whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa”
Shawty come gimme your lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-love, mm-mm
Chapter 144 · 0% Book details