← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 152

Sashe 78

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dr fawan, Na yarda da jazz sai dai a yanzu na fara zargin shi, wallahi If I find out that he’s doing something wrong, sai ya ɗanɗani kuɗar shi,” rai a6ace ya furta maganar, ya ƙara da cewa “dr fawan nagoda da bayanan da ka bani, zaka iya komawa bakin aikin ka” jiki na rawa dr fawan ya fito daga cikin motar, Bayan yayi masu sallama Ya nufi cikin asibitin yana faman sauke ajiyar zuciya.

Shiru su ka yi babu wanda ya ƙara magana acikin motar, Lamarin ya ɗaurewa Sir mubarak Kai, Mamakin shi ƙaryar da jazz yai mashi na cewa Sun buɗe gidan kaji, da kuma zuwa aikin da yake yi ashe duk ƙarya ne.

Driver-operator, Ya fahimci halin da sir mubarak ya shiga na damuwa, cikin kwantar da murya yace”Sir, pls kada hakan ya dame ka, nasan ba daɗi mutumin daka yarda dashi ya sa6aka, sai dai fa har yanzu bamu da tabbacin abun da dr jazz ya ke yi, mu kyautata mashi zato, sannan shawarar da na ke so in baka yalla6ai, me zai hana mu fidda rana ɗaya, Mubi bayan shi ba tare da sanin shi ba, a lokacin da ya shirya zai tafi aiki,”

Ta cikin mirror din motar Yake duban sir mubarak, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon drivern yace “Ka kawo shawara mai kyau, tabbas inason sanin me jazz yake aikatawa, nagode da shawararka, zamu Iya tafiya”

Cikin girmamawa Ya amsa mashi da toh, sannan ya tada motar Ya fito da ita daga cikin harabar ajiye motocin, atsanake ya ke yin driving har suka haura saman titi, sir mubarak bai dai na cizon yatsanshi ba, saboda Ya damu da jazz, Ƙaunar da ya ke yi ma mahaifiyar shi ce ta shafe shi, ko ƴa’ƴan shi da ya haifa bai jin su kamar yadda yake jin jazz, hankalin shi ba zai ta6a kwanciya ba idan har bai gano abun da ya ke aikatawa ba, ya jima yana danne zuciyarshi akan ƙin amincewa da zargin yaron da ta ke yi, abun da ya jawo shi ga bincikar shi a yanzu ya fahimci aduk lokacin daya kama jazz yanayin waya da zarar Yaganshi yake rasa natsuwarshi, Jikinshi ya hau kerma, shiyasa ya fara suspecting dinsa.

❤ANEELERH❤

Tun kafin ta sallame sallar azahar wayar ta dake ajiye saman drawer take ta buga ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, sai da ta kammala sallar ta ɗaga hannu tayi addu’a ta shafa a fuska, kafin ta miƙe da sauri ta nufi drawer ta ɗauki wayar, murmushi ta saki ganin sunan surukar arziƙi ya bayyana akan screen din wayar, aranta ta ayyana halan baby junaid ne ya matsa a kirani awaya.

Bayan ta ɗaga kiran ta manna wayar a kunnanta, kafin ta furta sallama muryar junaid ta katse mata hanzarin ta.

“Mommy, baby junaid ne, ni ne na kira ki awayar granny,” har sai da ta ji gabanta Ya ɗan faɗi, da mamaki tace”junaid da gaske kai ka kirani? Ina mommy adama? Ko dai itace ta baka wayar don ka yi mini magana”

muryarshi da shagwa6a yace”mommy ai bata nan, suna a falo, Ni kaɗai ne a ɗakin...” tun kan ya ƙarasa maganar tace”Junaid bana hana ka ɗaukarwa mutane waya ba? Faɗamin ya akai ka iya buɗe mata waya”?

“Mommy wasa nake maki, itane ta bani wayar, ta fita falo, ni kaɗai ne a ɗakin”

A faɗa ce tace”ƙarya ka ke yi mini junaid, ba ita bace ta baka wayar, kaine ka ɗauka ka kira ni, maza ka aje mata wayarta tun kan na 6ata maka rai,” ta yi maganar tamkar ranta ya 6aci sai dai azahiri ta yarda bashi wayar akayi, kawai tana son ta hayaƙa shi ne.

Sautin kukan shi ne ya cika mata kunnuwanta.

“Mommy ba ki yi missing dina ba, shiyasa kike yi mini faɗa, Kin barni ni kaɗai agidan su, ni wlh gida zan dawo, ko dai kizo ki ɗauke ni ko kuma in gudu in 6ace kamar Angel” maganarshi tayi matuƙar bata dariya, cikin sigar lallashi tace”am sorry my baby boy, wlh nayi kewarka kamar zan zauce, yanzu dai ka yi haƙuri kadaina kuka, Mommyn ka bata son zubar hawayen ka”

Cikin shessheƙar kuka yace”ni dai kizo ki ɗauke ni mommy, ko in gudu” hankalinta ya dan tashi, zuciya da saƙe saƙe saita dinga tunanin ko dai wani abu akayi mashi ne wanda ya 6ata mashi rai har yake neman dawowa gida.

“Junaid, faɗamin meya faru? Basa baka abinci ne? Ko ba ayi maka wanka ne? Ko wani ya buge ka ne”! A jere ta furta hakan.

“Ni ba su yi min komai, ina cin abinci kuma mommy adama tana min wanka har sau biyu safe da dare, ni kawai ke nakeso kizo ki dauke ni, ko in gudu” ajiyar zuciya ta sauke, hankalinta har ya ɗan kwanta.

“My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, zasu dawo mun da kai nan bada jimawa ba,’

Rigima ya sanya mata”Allah in baki zo ba saina gudu” dariya ce ta kubce mata, jin sautin dariyarta ba ƙaramin 6ata mashi rai ba.

“Mommy dariya kike mini ko! Shikenan zan kashe wayar” da sauri tace”sorry nadaina, pls kada ka kashe min waya, Ina jin daɗin yin magana dakai, Yanzu faɗa min a kwance kake ko a tsaye”

“Saman gado” ya bata amsa atakaice, har ta buɗe baki zatayi magana ya katse ta da cewa”Mommy, na tuna sunan mutumin nan da ya kira ki a waya, ran nan, amma ba zan fada maki ba, In kina son ji kizo nan”

“Am sorry my baby boy, yakamata ka fahimce ni, babu yadda za’ai inzo, Zasu yi tsammanin ban yarda ɗazu bane shiyasa na biyo ka, dan Allah ka faɗa min sunan shi, ka ji yaron kirki”

cikin ƙagara da sonji tayi mashi maganar.
“Toh mommy, zan faɗa maki amma bana so kowa yaji har zahra” muryarshi da shagwa6a yake magana.

“Junaid, Ni kaɗaice a ɗakin, Zahra bata nan taje wurin aiki, Mahboob ma baya acikin gida, Abie da Uncle basu dawo gida ba, mami da ummi ne kuma basa a ɗakin, suna a can palour suna fira”

“To zan faɗa maki, amma kada ki faɗa ma zahra da mahboob” ta rasa ya za ta yi da shi, Yaƙi faɗa mata sai jan maganar yake yi kamar baya son fadi.

Kukan ƙarya ta soma yi mashi tana fadin”dan Allah baby junaid dina ka faɗamin, zuciyata zata iya bugawa idan ban ji ba” tuntsirewa yayi da dariya yana fadin”mommy wasa kike ba wani kuka ai na ganoki” gajiya tayi da tsayuwar, ta koma gefen gado ta zauna, tamkar tana agabanshi ta marairaice mashi fuska tana fadin”pls my baby boy, ka faɗa min, komi ka ke so zan yi maka”

“Zoben Angel, da ki ka ce zaki siya mini in bata tun da na maida ba mahboob nashi”

“Kada ka damu, kafin ka dawo gida zan siya maka zoben, Nayi maka alƙawari, Yanzu faɗa min toh”

Sai da ya mula ya ishe iska tukunna Ya furta”wai ma...waima daddyn Unaisah, haka yace min fa” shiru tayi jimm tana tunanin sunan daya furta mata daddyn unaisa? Wanene daddyn unaisa? Ita kanta unaisan wacece ita!, sunan ya shige mata, jin tayi shiru yasa Baby junaid ambaton sunanta”mommy kin yi shiru baki ce komai ba”

“Junaid, na ruɗe ne, na kasa gane wanene daddyn unaysa, amma shi mutumin Iya abun da ya faɗa maka kenan”?

“Eh, bai faɗa min komai ba, Mommy ki kira shi ki ji toh wanene shi, ko daddyn Angel dina ne?”

lokaci ɗaya taji gabanta Ya faɗi Jin Ya ambaci ƙila daddyn Angel ne, nan take ƙwaƙwalwarta ta tunano mata sunan wacece Unaisa, a sukwane ta mike tsaye Tana faman zare idanuwanta, zurfi tunani ta shiga duk duniyar nan mutun ɗaya ta sani mai sunan daddyn unaisa, wato Tajuddeen, ta gaza yarda da abinda zuciyarta ke faɗa mata.

La66anta na kerma ta furta”ka tabbata haka sunan yake? Ko dai abakina ka ta6a jin na ambaci sunan daddyn Unaisa?

“Mommy wlh dagaske nike maki haka yace min wai in faɗa maki daddyn unaisa ne, mommy zan kashe wayar, ga mommy adama nan zata shigo dakin” kafin ta yi mashi magana yai rejecting kiran.

Hakanan tadinga jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, jiki asanyaye ta koma gefen gadon ta zauna, tsawon mintuna zuciyarta nayi mata kokwanton maganar da junaid Ya faɗa mata, har dai a ƙarshe ta yanke shawarar cire nombar daga black list, don ta kira ta ji wanene mutumin da junaid ya fada mata cewa daddyn Unaisa ne, fatanta Allah yasa Dagaske ne hasashenta.

Yatsun hannunta har kerma suke Yi wurin daddana wayar, bayan ta cire number daga black list, ta danna call cikin sa’a Kiran Ya shiga, wayar ta fara ringing, tsabar zumuɗi jikinta har kerma yake yi, Har kiran yayi rejecting ba’a ɗaga ba, Miƙewa tayi tsaye ta zame dogon hijabin jikinta ta jefar saman mattress, safa da marwa ta cigaba da yi a tsakar ɗakin, ta ruƙe wayarta a hannunta, a Ƙalla Ta Kira layin kusan sau biyar Yana ringing ba’a ɗaga ba, Hankalinta yaƙi kwanciya burinta taji wanene mutumin nan daya kira kanshi da sunan daddyn Unaisah.

Har ta fidda rai da za’a ɗaga Kiran, Unexpected A kira Na shida data yi mashi sai gashi Anyi picking call din.

Cikin rashin natsuwa ta furta”Assalamu alaikuma” maimakon ta ji muryar Namiji sai taji muryar matashiyar mace tana yi mata magana da wani yare.

“Baiwar Allah, bana jin harshen da kike yi mini magana dashi, Idan kina jin hausa mu yi magana da shi”

Ko da Aneelerh ta ambaci hakan, matashiyar sai ta canza harshenta zuwa Yaren hausa ta ƴan koyo tace”wanene ke magana”? A ƙagare Aneelerh tace”sunana Aneelerh, dalilin dayasa na kira Layin, kwanakin baya ana yawan kirana dashi, Ina tunanin ko wani ne ke nema, pls ina neman me wayar” ta faɗi hakan ne don junaid ya fada mata cewa Namiji ne Ya daga kiran lokacin da aka kira.

Matashiyar budurwar tace”Ni ce me wayar, wato irin kune ku ke bibiyar mazajen mu don ku ƙwace mana su ko”? Sakin baki Aneelerh tayi jin abun da matar tace.
Chapter 78 · 0% Book details