Sashe 110
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Dan Allah ka tashi kayi min magana meke damunka? Baka da lafiyane”?
Daƙyar ya samu damar ware idanuwanshi Akan fuskarta,
A daddafe ya samu Ya miƙe zauna yana dubanta, Short din Jiyane a jikinshi da singlet.
Yaji dadin ganinta a room dinshi, Jiya yai zaman jiranta yai tunanin zata zo gare shi har bacci yai awon gaba da shi bata leƙo ba, till now.
“Kayi shiru baka ce min komai ba, danish zafin jikin ka yai yawa, kodai inje in faɗa ma Boss Man Yazo Ya duba ka”? Girgiza mata kai yai, kafin ya motsa la66ansa Ya furta”babu abunda ke damuna, Lafiyata qalou, kece kika 6ata min rai”
Hankalinta bai kwanta da kalamanshi ba, aɗan ruɗe ta furta”ba haka bane danish, dole akwai abunda ke damunka ba Iya 6ata maka rai da nayi bane, cos babu yadda za’ai Jikinka yadau zafi rau batare da dalili ba, Please ka faɗamin idan ba haka ba hankalina bazai kwanta ba, sannan kayi hakuri dan Allah, abunda ya faru Jiya wanda ya 6ata maka rai, In sha Allah bazan ƙara bari Hakan Ya faru ba”
Cikin kulawa take Yi mashi magana, Jinjina mata kai yai”kiyi min alƙawarin ba zaki ƙara rungumar wani ƙato a jikinki ba, idan bani ba koda su Naufal ne” kiris ya rage ta saki dariya jin abunda yace
Jinjina mashi kai tayi”in sha Allah My man kai kaɗai kawai,” ajiyar zuciya ya sauke Ya samu sassaucin radadin da zuciyar shi ke yi mashi
“Tunda naga yanzu hankalin ka ya kwanta fada min meke damunka? Menene ya haddasa maka zafin jikinka”? Ta faɗa tana duban ƙwayar idonshi, la66ansa duk sun bushe ƙamas.
“Dagaske nake Yi maki babu abunda ke damuna, Nima bansan ya akai jikina ya ɗauki zafi ba”
“Nidai hankalina bai kwanta ba, ka ba ni dama inje in faɗa ma boss man halin da kake aciki,” haɗe mata fuska yai jin ta ambaci sunan boss man, sam bayason ji.
“Bana buƙatar kowa ya dubani, ki kwantar da hankalin ki, zafin jikina baiyi min illa ba, don haka kija baki kiyi shiru”
Jinjina mashi kai tay”maganar abinci fa? Jiya kace min ba ka ci dinner dinka ba, ni sam Na shafa’a”
Yamutsa mata fuska Yai, hada jifarta da harara, murmushi tasakar mashi
“Bari naje na duba dining, idan an shirya mana abincin breakfast dinmu, zan shigo maka da naka a ɗaki tunda baka son fita” ɗaga mata gira yai alamar okey.
Miƙewa tayi da sauri ta fice daga dakin ta sauko down stairs, koda ta duba ɗakin cin abincin ba a jera masu komai ba, saboda time din da suke zama Yin breakfast bai cika ba” yanke shawarar neman ɗakin Ummi tayi don ta fada mata game da ɗan uwansu dake jin yunwa, wata’ƙil ta sama mashi abunda zaici kafin a shirya masu abincinsu.
Batasan ina zata nemo room din ummi ba, tadaisan acan upstairs Yake, cos ta ta6a ganin tana saukowa saman bene, da sauri ta nufi stairs din tana tafiya Hijabin Jikinta naja da ƙasa, babu kowa a palourn duk suna adaki.
A hankali take taka stair cases din Har ta samu ta haura can sama, Ta rasa wace hanya zata bi wadda zata sada ta da bedroom din Ummin america, Tafiya taci daga dayi tana bin ko’ina da kallo, aranta tana ƙara jinjina haɗuwar ginin, tana ta ƴan kalle kalle kamar baƙauya harta zagayo ta 6angaren Hagu batare data gano hanyar da zatabi ba, Ƙofar wani katafaren room Ta dakata da yin tafiyar, aranta ta tace”idan kuwa wannan ne ɗakin aunty ummi duk Yafi namu kyau” Ta cikin glass din ƙofar take hangen zallar haɗuwar kayan alatun cikinsa, kifa kanta tayi jikin ƙofar har ta danna madannin Jikinta batare data an kare ba, da alama mamallakin ɗakin Yayi recieving alert na neman iznin shigowa shiyasa ƙofar tafara ƙoƙarin zugewa slowly take sliding, da sauri Unaisa Ta saki glass din Jin yana motsi, abunka game karanbani, ganin ƙofar ta wage, sai kawai ta haura ƙafarta ciki, yau ta ga maƙurar aljannar duniya a ɗakin data faɗo, wuyanta kamar zai 6alle, tana tafiya tana ƴan waige waige kamar zatayi tuntube, tayi mamakin dukiyar da aka narka wurin tsara Kayan furniture din dakin, Yana da fadi da tsayi, ga wannan floor to ceilling window din a left hand din bangon ɗakin, Ta jikin glass din zaka Iya hangen wajen ginin Harma da manya manyan gine ginen dake acikin burnin abuja, bayan haka daga cikin bedroom ɗin zaka Iya hangen komai na cikin bathroom ta glass din ƙofar, sai dai da alama ba haka akeyin wanka acikinshi ba, da akwai hanyar da ake rufe glass din yai duhu idan mutun zaiyi using dashi.
Sai faman jinjina kai Unaisah take Yi, tajima tana mamakin wanene mamallakin daular nan da suke acikinta, bata ta6a yin tozali da shi ba, tadai ta6a jin sunan Chief of isod abakin Dr Laura.
Tabbas Da ace tasan ɗakin wanene da batayi gigin shigarshi ba, ta zaƙe sai kurɗaɗawa take Yi can ciki ta shige kamar ɗakin baba tajo, shi kanshi bedroom din Yana da katafaren falonshi Har yaci uban na down stair haɗuwa, tana ƙoƙarin giftawa ta wata ƙofa dake a ɗakin, kwatsam kunnuwanta suka soma Jiyo mata sautin daddaɗan kiɗa Yana tashi, na taken waƙar satisfya
Wani irin daddaɗan ƙamshi Ya ratsa hancinta sosai ta shaƙeshi, a hanzarce ta ɗaura idonta saman kofar ɗakin rubutun sama ta karanta kamar haka
*Gym room” nan take ta fahinci dakin menene, wato wurin motsa jiki ne” aranta ta ayyana bari ta dan leƙa taga wanene Ya kunna sautin kiɗa.
Kasancewar ƙofar abuɗe take, Unaisah ta zura kai kamar 6arauniya tana bin ko’ina da kallo, an ƙawata room din da injinan motsa jiki, kala kala, ga kayan jin sauti, sam bata lura da shi ba, kamar yadda shima bai lura da mutun ba, Yadaisan akwai wanda ya shigo dakinshi saboda alert din da yai recieving awayarshi, saida Ya bada iznin shigo ciki tukunna ƙofar ta buɗe.
Sai faman wurwurga eye balls dinta take tana bin ko’ina da kallo, lokacin da tayi arba dashi wani irin mugun bugu ƙirjinta Yai, har saida ta dafe shi da hannu, tayi matuƙar firgita da ganin shi, Ya tattara hankalinshi gaba ɗaya akan Punching bag din da yake kaima naushi da hannayensa waɗanda ke sanye cikin boxing gloves, Cikin zafin nama yake motsa jikinshi, Ya haɗa uban gumi, zufa ta ko’ina take tsattsafo mashi, ƙirar ƙarfinshi Ta bayyana ga wannan sick pack din ƙirjinshi ruɗu ruɗu, Damtsen hannayenshi sun murmurɗe, Yana naushin jakar motsa jikin Breast muscles dinshi na shaking, babu riga ajikinshi, black short ne kaɗai Ya sanya wanda Ya tsaya mashi dai dai gwiwarshi, bata samun damar ganin fuskarshi dakyau ba, saboda ba ita Yake fuskanta ba.
Ta natsu tana kallonshi, Ko idonta bata ƙyaftawa, ba zato ba tsammani taji an damƙi wuyanta ta baya, harta buɗe baki zata fasa Ƙara taji anyi saurin toshe mata baki, tsoro Ya kamata jikinta ya hauyin kerma, ɗungurugum taji an dagata sama Anjata zuwa cikin bedroom din, sai faman wuntsila ƙafafuwanta take Yi a ƙoƙarinta nata kwace kanta daga hannun mutumin daya dauketa, har ƙofar ɗakin Ya fito da ita Ya direta ƙasa, A firgice take dubanshi, bakomai bane face Big guy, kayan kakinsu ne a jikinshi, ya sanya face mask a saman fuskarshi, idanuwanshi na akan fuskarta, La66anta na kerma ta furta”wa..wa.. Wanene kai? Meyasa ka daukoni? Idanma saboda nashiga ɗakinne aini bansan ya akai na shiga ba, rashin sanine, ɗakin aunty ummi nake nema, danish ne Yake jin yunwa jiya baici dinner din shi ba kuma na duba dining ba’a shirya mana abinci ba” tsabar ruɗune yasa take yi mashi zuba har abunda bai tambayeta ba, taƙi barima Yai mata magana
Sai da ta dasa aya tukunna Ya soma yi mata magana cikin muryar raɗa”kinsan ɗakin wanene kika shiga”? Girgiza mashi kai tayi alamar a”a gyaɗa kai yai”kada ki kuskura ki ƙara yunƙuri shiga ciki, Idan ba haka ba jikin kine zai gaya maki, Ni nayi mamakin ma taya akai kika samu damar shiga bayan ita kanta ƙofar sarrafata akeyi, Kodai ba mutun bace ke”? Ya fada haɗi da ɗage mata gira alamar yana jiran amsarta.
Duk tabi tasha jinin jikinta, sai faman zare mashi gray eyes dinta take Yi, daƙyar Ta iya fadin”nifa bansan komai ba, ai na fada maka dakin aunty ummi nake nema” ta ƙare maganar tana murguɗa mashi baki.
Har murmushi yasakar mata batare data gani ba saboda mask din fuskarshi, dama Yaji labarin rashin jin maganarta, gashi yanzu ya tabbatar dahakan”
“Okey, ki koma ɗaki, yanzu zanzo in kawo maki abunda shi ɗan uwan naki zaici, kafin Ashirya maku naku abincin” amsa mashi tayi da toh, jikinta har rawa yake Yi wurin yin saurin haura ƙafa ta kama hanyar komawa ɗakin danish, tana tafiya haɗi da waiwayan big guy, Yana atsaye yana kallonta har saida ta 6ace ma ganin shi, tukunna ya kawar da idonshi daga gareta.
Tun da ta koma ɗakin danish bata daina tariyo suffar mutumin da tayi tozali dashi a gym room ba, Ya tsaya mata aranta, taso ace sunyi ido biyu da shi, don ta samu damar ƙare ma fuskarshi kallo, shin wanene shi? Tabbas tanaso ta sani!
Bada jimawa ba, Big guy yai sallama dakin danish, hannunshi ruƙe da tray din Kayan abinci ashake, bayan ta kar6a tayi mashi godiya, asaman carpet suka zauna ita da danish, ta dinga bashi abaki Yana ci, suna kallon juna yayin da acan ƙasan zuciyarta tunanin ɗan ta halikin nan take Yi, shi kanshi danish Ya lura da canzawarta, saboda tsabar tunani har a hanci tai ƙoƙarin cusa mashi abinci, saida ya damƙo hannunta tukunna ta ankara, yace mata me take tunanine tace mashi bakomai, badan ya yarda ba ya ƙyaleta, A ɗakinshi ta zauna duk don ta faranta mashi, sai da tasanyashi yai wanka ya canza kayan jikinshi tukunna hankalinta ya kwanta, damuwarta ɗaya yanzu zafin jikinshi sai ƙara ninkuwa yake Yi.
*Obie Estate*