← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 152

Sashe 22

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin farin ciki ne Ya lullu6eta haƙiƙa ta yi al’ajabin wannan iko na Allah, kamar zautacciya haka ta dinga ɗaura kanta saman ƙirjinsu haɗi da jogana kunnanta saitin zuciyar su don ta ji idan tana bugawa, daga kan Jamimah ta fara tana ɗosa kunnanta bugun zuciyar jemimah ya daki dodon kunnan, nan ta ke ta fahimci cewa bacci su ke yi, Tambayoyi ta shiga jefawa kanta, Ta ya ya akai haka ta faru? Dama wanda ya mutu yana tashi? don ita dai a iya saninta idan an mutun ba adawowa, ɗaura kunnanta ta yi saman ƙirjin Azeeza lumshe idanuwanta ta yi wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, jin bugun zuciyar azeeza na har6awa, matsawa ta yi gaban Parveen tunkan ta ɗaura kanta saman ƙirjinta idanuwanta su ka sauka akan ƙaramin bakinta ganin yana motsi yasa ta fahimci tana araye, Lamarin yai matuƙar ɗaure mata kai, ta ya akai su ka rayu! Kuma Danish da kanshi ya tabbatar masu cewa Heart attack ne yai silar mutuwarsu, duk da bata da ƙoshin lafiya hakan bai hana smart brain ɗinta aiki ba, Zurfin tunani ta shiga idan har su Jemaimah su ka iya jure abunda ya faru dasu ya kenan ta 6angaren Sauran ƴan uwansu da su ka baro? Waro idanuwanta waje ta yi yayin da zuciyarta ka harbawa da sauri da sauri, a fujajen ta zabura ta miƙe kamar an zungure ta, ta juya ta nufi Danish dake a zaune Ya ɗan lumshe idanuwanshi, ƙoƙari ya ke ya hana kanshi yin bacci gudun kada yaja masu matsala, zuƙunnawa tai agabanshi

“Danish taya akai su Jamima su ka rayu? Bayan kai da kanka ne ka faɗa mana cewa zuciyarsu ce ta buga” ware idanuwanshi yai akan fuskarta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, damuwarta akan ƴan uwanta, bata damu da kanta ba, ƙarantar shekarunta yafi komai ɗaure mashi kai, yadda harta iya jure waɗannan wahalhalun rayuwar wanda yayi imanin ko wani babban ba zai Iya jurarsu ba.

“Danish bana so ina magana kana share ni, ka faɗa min ta ya ya akai su ka rayu? A iya sanina idan mutun ya mutu baya tashi, Sai gashi su Azeeza sun tashi, ko dai ka yi amfani da sihirinka ne wurin dawo masu da rayuwarsu...”? A ruɗe tai maganar babu kwanciyar hankali atattare da ita, a hankali ya ɗan motsa la66ansa.

“My Angel, u should stop talking about them, ba ki da lafiya u need a rest,” damƙar wuyar best ɗin jikin tai sosai ta fashe mashi da kuka tana faɗin”Danish ka faɗa min dama kasan suna araye shi ne ba ka bari mun goyo su Deeja mun taho da su ba? Me yasa ka yi mana ƙaryar cewa zuciyarsu ce ta buga”? Tana magana tana ku ka, raunin gefen bakin ta tuni ya fara tsastsafo da jini.

Ranta yai mugun 6aci zuciyarta ta harzuƙa, A haukace ta miƙe tana faɗin”Zan koma na taho da su Deeeja, ban damu da in rasa raina ba,” a hanzarce ya miƙe jin abunda tace, ido cikin ido su ke kallon juna”Am sorry Angel i don’t mean to hurt u, kinsan bana ƙarya, sannan bani da amsar da zan baki that’s why nayi shiru, hatta su Azeeza ban san suna araye ba, a daren jiya na yi ƙoƙarin binne su cos bana son ku farka ku taras da gawawwakinsu, hakan zai fama ma ku ciwon da ke a cikin zuciyarku, nayi amfani da sihirina wurin tsaga ƙasa har na fara sanyasu a ciki idona ya sauka akan yatsun ƙafafuwansu dake motsi, i was shocked cos ban yi expecting din zasu rayu ba, kin ji yadda akai nasan suna a raye”

kamar ta so ta fahimce shi sai dai wani sashe na zuciyarta yaƙi aminta dashi, girgiza mashi kai tai”Ni dai zan koma kurkuku in ɗauko su Deeja, Saboda ina ji araina cewa Suna araye”

Ya fahimci damuwace ke ƙoƙarin zautar da ita, Zaiyi wuya ta fahince shi, yasan halin kayansa da rigima ga kafiya da taurin kai, juyawa ta yi tare da nufar ƙofar fita daga kogon dutsen, da sauri Ya bi bayanta tare da ruƙo arm ɗinta ya janyota zuwa jikinshi, sosai ya matseta.

“Angel daji ne fa, ba mu a kusa da kurkukun ƙaddara, ta zarar awanni ce, A daren Jiya bayan mun fita ni ne na ɗauko ku na dawo da ku nan duk don na sauƙaƙa maku wahala” daƙyar ya ke magana, damuwace ƙarara akan fuskarsa, ƙoƙarin raba Jikinta tayi daga nashi.

Zuciyarta ce ke azalzalarta sam bata fahimtar kalamansa, idanuwanta sun makance

“Ka sake ni Danish, nasan ko nace kaje ka ɗauko min su Deeja ba za ka je ba, don haka ni zanje, saboda ina ji araina ƴan uwana suna araye basu mutu ba gashi mun baro su a hannun Azzaluman mutanancan.....” cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa maganar, duk yadda yaso ya hanata tafiya taƙiya, har kwatanta mata haɗarin da dajin gare shi amma ta kafe akan sai taje, sakinta yai idon shi akan bayanta, sam babu kuzari a jikinta ahaka ta fuce daga cikin kogon dutsen, Hasken ranane ya galle mata idonta da sauri ta lumshe su na ɗan sakanni kafin ta ware su tana ƙarewa ƙurmin Dajin kallo, Daddaɗar iskar dajin ce ta ratsa sassan jikinta ni’imtacciyar gaske, hatta sumar kanta sai kaɗawa take yi saboda ƙarfin iskar, saboda taurin kai irin na Angel da kasada, Ahaka ta soma tafiya tana nufar cikin dajin ita ala dole saita gano inda kurkukun ƙaddara ya ke, tun kan aje ko’ina ta fara tsorata da ganin ƙananun halittun da ke yawo Saman bishiyoyi, duk da haka bata sare ba taci gaba da tafiya hada ɗan saurinta da gudunta, ko takalma babu a ƙafarta.

Tun bayan fitarta Danish Ya fito daga cikin kogon dutsen, ya goya hannayenshi saman faffaɗan ƙirjinshi Yana kallon bayanta, Ta yi matuƙar bashi mamaki, duk da ya fahimci babu hankali atattare da ita, in ba haka ba ta ya ya wanda ya tsira yake ƙoƙarin komawa ga halaka. Yarinta ce ke damunta da kuma son ƴan uwanta.

Tana cikin yin tafiyar nan, kukan namun dawa Ya dakatar da ita cak ta tsaya tana ƙarewa wurin da take atsaye kallo, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Snake ɗin dake bin jikin bishiya yana ƙoƙarin saukowa ƙasa, zaro ido waje tai a gigice ta fasa ƙara tare da juyawa da gudun gaske tamkar zata tashi sama, majicin na ƙarasa saukowa yabi bayanta, tashin hankali duk ta bi ta rikice don ta fahimci ita yake bi, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a yin tozali da maciji ido da ido ba sai yau da Allah ya haɗosu, Tarasa gane ta wace hanya zata bi ta koma cikin kogon dutsen.

Danish ta dinga ƙwalawa kira kamar maƙoshinta zai 6allo, sai da ta gama galabaita cikin rashin sa’a tai tuntu6e da dutse gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa, ƙiris ya rage ta kife ƙasa a lokacin da ba ta yi tsammani ba taji Ya damƙo ta tare da kwantar da ita saman chest ɗinsa.

ƙanƙameshi tayi sosai ta fashe mashi da kuka tana zazzaga mashi masifa akan me zai barta ita kaɗai acikin daji? Idan ma don saboda ta yi mashi kafiya ne, bai ga ita yarinya bace, tun da fara mashi faɗa bai tanka mata ba, hannayen shi biyu suna tallabe da ita, sai da ta yi mai isarta, tukunna ta buɗe kumburarrun idanuwanta akan fuskarshi, tun daga kan tausasan red lips ɗinsa ta soma bi da kallo har izuwa ga dogon hancin sa kafin ta ɗauke idon nata ta ɗaura su kan sexy eyes ɗinshi masu matuƙar jan hankali.

ƙoƙarin shagala su ke yi da kallon Juna, tunawa da ƴan uwansu da su ka baro a kogon dutse ne yasa tayi saurin katse masu kallon ƙurullan da suke bin juna dashi”Danish mu koma kada wani abu ya same su” girgiza mata kai yai in a smoky voice ya furta mata”ba abunda zai same su, ina sane dasu, na rufe kogon dutsen babu wani abun cutarwa da zai Iya tunkarar su”Sam hankalin bai kwanta da kalaman shi ba

“Danish ni dai mu koma,” ashagwa6e tayi mashi maganar, ita kanta batasan ta sanya shagwa6a ba’

“Zamu koma, but before that, Inaso ki raka ni cikin Dajin in nemo mana abunda zamu ci, ko kina so su farka suna Jin yunwa ne”?

Girgiza mashi kai tayi”a’a amma ni ba zan bi ka ba, Ka maida ni cikin kogon dutsen in ya so kai sai ka je nema mana abunda zamuci” kafe ta da ido yai, hakan yasa ta jefa mashi harara haɗi da murguɗa mashi baki, munin fuskarta bai hana shi ganin kyanta ba, musamman da ta yi mashi abunda ke jan hankalin shi gareta, Harara da murguɗe abun A jinin ta ya ke.

“Idan ba za ki bi ni ba, Ga hanya nan ki koma kogon dutsen ni kin ga tafiyana” yai maganar tare da nufar Cikin dajin, da ido tabi bayanshi da kallo, ranta a 6ace yasan ba zata iya kai kanta ba shiyasa yace ta koma, Tunawa da macijin da ya biyota ne yasa ta zabura da gudu tabi bayanshi, Yana cikin tafiya yaji ta zura hannunta cikin nashi, ƙayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi.

Ta yi tsammanin Iya abincin da zasu ci ne zasu nemo, ba ta san plan Ya shirya mata ba, Yanayin Iskar dajin ba ƙaramin ni’ima ta saukar masu ba, Suna tafiya suna kallon Juna, wani irin Sanyi ne ke ratsa zukatan su, dakatawa tai dayin tafiyar ta ɗan kalli fuskarshi”Na gaji Danish ƙafata ciwo ta ke yi min” ba tare da ya amsa mata ba, ya juya mata bayan shi, ta gane me yake nufi, da sauri ta haye Saman bayan Ya miƙe ɗauke da ita, ba ƙaramin daɗi taji ba, shin me yafi ranta gata ga garkuwar kurkuku, ta ƙanƙameshi sosai, lumshe idanuwanta tayi sai faman shaƙar mashi fatar wuyan shi take yi, bai sauke ta a ko’ina ba sai abakin wani tabkeken ruwa mai gudana, Ta jikin dutse ruwan ya ke gangarowa tsaftatacce fari ƙal dashi.
Chapter 22 · 0% Book details