← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 152

Sashe 132

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin takun sauri Big guy ya nufi bedroom dinsu dake a down stairs, wata’ƙil aci sa’a ya ganta, hankalin shi ba akwance yake ba, saboda ya bincika ko’ina na part dinsu saƙo da lungu babu cikon yarinyar da yake nema, ba ƙaramin ruɗewa yai ba, fargabanshi kada ace wani wajen taje ta faɗa takasa fita, ɗaya bayan ɗaya ya ke shiga dakunan matan babu kowa, yabi hanyar da zata kaishi bedrooms din mazan, A bakin ƙofar dakin su Naufal Yaci burki, Ya dafe jikin glass door din, slowly kofar ta zuge, leƙawa ciki yai, a kwakkwance ya same su saman shimfiɗeɗan gadonsu, sun cunkushe kamar kinfin gwangwani, gaba ɗaya sun lullu6e jikinsu da bargo, buga ƙofar yai ranshi a jagule Ya juya zai fuce daga ɗakin ganin mazane zalla kuma gaba ɗayansu suke aɗakinsu naufal, Cak Ya tsaya da tafiya kwakwalwarsa ta soma tariyo masa abunda ya gani, da sauri Ya koma dakin ya tsaya daga bakin gadon yana kallon ƙafafuwansu da suka leƙo daga cikin bargon, a hankali ya ɗaura eye balls dinsa kan kafar da yake hasashen ta macace bata namiji ba, shape dinta ya banbanta data mazan kuma tafi kafafuwansu ƙaranta, hannu ya miƙa ya damƙi kasar bargon ya yaye shi, lokaci ɗaya big guy yasauke nannauyar ajiyar zuciya, hankalin shi ya kwanta ya samu natsuwa, Hanna ce a tsakiyar mazan ta ƙanƙame gabriel kamar zata koma cikinsa, Yayi mamakin ganinta tsumu tsumu acikinsu, gefenta na dama naufal ne da haris, daga 6angaren hagun katifar gabriel ne da javed, sunyi nisa acikin baccinsu.
Acikin zuciyarshi ya furta”Kin tayarmin da hankalina” ya ambaci hakan tare da sakin bargon Ya juya ya fuce daga ɗakin nasu.

*Unaisah Angel💋❤*

Fitowa tayi daga cikin toilet, fuskarta da alamun lemar ruwa, Salsabeel yana daga zaune saman gadon Ya jingina bayanshi jikin headboard yayin da Giant snake din yake a kwance gefenshi ya daura kanshi saman laps dinsa.

Jin motsin fitowarta ne ya janyo hankalin salsabeel ga kallonta, baiwar Allah ba ƙaramin tausayi take bashi ba, ƴar ƙarama da ita ta ɗaurama kanta damuwar da ko wani babban bazai Iya jurarta ba, ganin yana kallontane yasa ta dan sakin fuskarta data kumbura suntum.

“Fuskarki kika wanko”?

Girgiza mashi kai tai”a’a alwala nayi”
“Amma ba’a fara kiran sallar asuba ba”
“Nafila nake so nafara Yi, kafin a kira sallar asuba, Inaso zanyi ma danish ɗina addu’a ne”
Murmushi salsabeel yasakar mata, dama saida ya ayyana hakan aranshi
“Kina kaunar ɗan uwan nan naki”
“Fiye da yadda nake ƙaunar kaina” ta furta hakan tare da juyawa ta nufi kofar fita dakin don taje nasu ɗakin ta ɗauko Hijabin da zatayi sallah, har ta kusa fita daga dakin kamar ance ta waiwayo ta kalli gadon

Ba zato ba tsammani macijin Ya girgiza Yana kokarin tashi
Da sauri ta furta”yanzu zan dawo my Man, kada ka biyoni, Nima bazan Iya yin nesa dakai ba, Hijabin sallah zan ɗauko a ɗaki” komawa macijin yai tare da daura kansa saman laps din salsabeel.

Ajiyar zuciya ta sauke haɗi da yin ƙayataccen murmushi, salsabeel dake kallonta shima murmushin yake yi, lamarin Danish na matuƙar bashi mamaki.

Juyawa tayi da sauri ta fuce daga dakin.

Moving quickly take tattaka matakalar benan, kasancewar ko’ina na part din da haske tamkar da rana baka ta6a gane lokaci saika kalli agogo, a tsanake take bin ginin da kallo Yayin da take saukowa down, zuciyarta tayi mata nauyi, zazza6in jikinta sai ƙara nunkuwa yake yi, Ita kadai tasan halin da take aciki, da ace zata Iya dauke ma danish abunda ke damunshi da kuwa tayi hakan, zaifi mata sauƙi akan taganshi a wuyanci hali.

Tana gab da zata dira ƙafarta kan floor din falo, ranta ya bata cewar akwai mutun awurin, wurga eye balls dinta tayi akan first floor bataga kowa ba, A hankali ta mayar da eyes din nata kan Second floor, rass taji gabanta Ya faɗi ganin mutumin nan da ta ta6a gani a gym room yana motsa jiki, Ya juya mata baya, bata Iya ganin fuskarshi da kyau, batasan ya akai ta tsinci kanta da yi mashi kallon kurulla ba, bakomai take son gani ba face fuskarshi, sai dai kash takasa ganinta, faffaɗan bayanshi kadai take kallo, Ba ƙaramin jikine da shi ba, murdadden damtsen hannayensa take kallo, da alama Ya ruƙe wani abu yana sha a cup, duba da yadda hannun shi na dama ke motsi, yayin da ɗayan hannun nashi ya zura shi a shorts pocket dinsa.

Aranta ta ayyana ko wanene wannan mutumin? daga gani yana da ƙarfi da tarin dukiya, komai nashi cikin ƙasaita yake yin shi, dai dai da yanayin tsayuwarshi abun kallo ce, yaɗan jingina bayanshi jikin benan.

Hankalinta ya karkata akanshi, ta manta da hijabin da zata je daukowa, ta tafi wani tunanin daban, ita so take taga wanene shi? Ranta yafi bata cewar Chief din da taji ana fadi ne,

“Unaisah” firgigit ta ɗauke idonta daga kallon chief da take Yi, Jin muryar Boss, da sauri yake tunkarota shigowarshi kenan part din, jallabiya ce a jikin shi, Ya sanya face mask a fuskarshi, tayi mamakin ganinshi a irin wannan lokacin, abunda bata sani lokacin da boss Ya ambaci sunanta, Chief owais Ya juya don ganin wanene ke magana, dai dai sa’adda ita kuma ta kawar da kanta, Natsuwa yai yana dubansu daga can saman second floor.

“Ba ki yi bacci ba”? Tambayar da boss ya jefa mata kenan a yayin daya ƙaraso gabanta yaci burki ya tsaya yana kallon fuskarta.

“Banjima da farkawa ba, amma meya hana ka bacci” ta tambaya tana kallon rinannun idanuwanshi masu dauke da tsantsar damuwa
“Taya zan Iya yin bacci? Bayan kema bakiyi ba”
Matashin murmushin ta ɗan saki, har cikin ranta taji dadin maganarsa, shi kuwa ji yake kamar ya rungumeta ko dan yaji sanyi aranshi, ya damu da halin da suke aciki ita da ɗan uwanta, tausayinsu ya hanashi sukuni har ya gaza runtsawa shiyasa ya fito don yazo ganin su.

“Yakamata ka kwanta ka huta boss, na fahimci ka damu dani, meyasa”?
“Taya bazan damu dake ba? Kefa jinina ce, jinin dake yawo ajikina shi yake yawo ajikin ki.....” da sauri Ya katse maganar, Jin su6ul da bakan da yai, murmushin gefen fuska tayi mashi, ga dukkan alamu taji dadin maganarshi

“Boss kayi shiri baka ƙarasa zancen ba? Ni wallahi idan kana Yi min magana sai inji kamar mahaifina”

“Meyasa kikace haka”?

“Saboda Yana ƙaunata fiye da yadda yake kaunar kansa, ya sadaukar da farin cikinshi saboda ni, nayi rashin ji aƙuruciyata, na azabtar da daddyna amma duk idan na tuna ayanzu sai inji haushin kaina......” sambatu take yi mashi sam batasan me take furtawa ba, abune ya haɗe mata ga radadin da zuciyar ta keyi mata shiyasa take yi mashi zuba, tana magana hawaye na taruwa acikin idanuwanta.

“Amma meyasa kike jin haushin kanki ayanzu”? Muryarshi araunace ya furta mata maganar.

Shesshekar kuka ta soma yi mashi tana fadin”saboda nagane cewa bani da masoyi a duniyar nan daya wuce shi, bani da tamkar shi har abada, Har yau idan na tuna cewa shine silar duk wani abu dana koya aduniyarnan ba ƙaramin dadi nake ji ba.....” kasa ƙarasa maganar tayi, sakamakon janyota da yai zuwa jikinshi ya rungumeta sosai, haɗi da daura hannayenshi saman bayanta yana lallashinta, bata kawo komai aranta ba, sai dai bugun zuciyarta da taji ya ƙaru, tajima tana mamakin yanayin da take tsintar kanta idan Boss yana akusa da ita, sakankancewa takeyi taji kamar daddyn ta ne ya dawo.

“Ya isa haka, ki daina kuka Unaisah, In sha Allah, daddynki zai bayyana, bama ke kadai ba da sauran ƴan uwanki duk zamu binciko maku danginku”

Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, takasa raba jikinta daga nashi, tamkar zata koma cikinshi.

Duk wannan abun dake faru atsakanin Boss Man da Unaisah, akan idon chief owais, yayin da yake kur6ar coffee dinsa.

Tunawa da Hijabin da zata daukone yasa tayi saurin furta”boss namanta, alwala nayi zanje daki na dauko hijabi da prayer mat, yakamata na tafi idan danish yaji na dade zai Iya biyoni, yanzuma da ƙyar ya bari na fito” ta fada tana raba jikinta daga nashi.
“Nagode da kulawarka agaremu,”
“Kada ki damu, muje na rakaki ɗakin,”
“Banaso na takura maka, naga idanuwanka sun kaɗa jawur, baccine a idonka yakamata kaje ka kwanta” ta fada tana kokarin kakaro murmushi
Ruƙo hannunta yai acikin nashi da zolaya yace”saifa na biki Allah, ai tunda baki runtsa ba nima bazan yi bacciba, zan zauna atare daku har sainaga abunda ya turema buzu naɗi”
Dariya tadan saki jin maganarshi ta ƙarshe, atare suka jera zuwa bedroom din nasu.
Koda suka ƙarasa dakin, arude ta furta”Boss babu batool fa”! Ta fadi tana faman zare ido akan gadonsu.

“Calm down ur mind, nasan inda suke, ba sace su akayi ba, abunda ya farune dazu ya tayar masu da hankulansu, shine na rakasu dakin Ummi, nasan yanzu haka sunyi nisa acikin baccinsu” ajiyar zuciya ta sauke, har taji sanyi aranta.

“bayin Allah, nasan daƙyar suka Iya runtsawa, musamman Azeeza tafi kowa tsoro a cikinsu” ta furta hakan tare da kama hanyar closet dinsu, bin bayanta yai da kallo harta 6ace ma ganin shi.

Maganar amininshi ce ta fado mashi aranshi, a ranar daya kira shi video call yana daga kwance saman gado shida Angel dinsa.
Chapter 132 · 0% Book details