Sashe 89
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zazzare ido waje zahra tayi yayin da take kallon Aneelerh, cikin matsanancin tashin hankali da ruɗani, Muryarta na rawa ta furta”Aunty Aneelerh dagaske kike? In bata hadin kai”? Murmushi Aneelerh ta sakar mata hadi da ɗaga mata gira alamar eh, girgiza kai zahra tayi idanuwanta cike tab da ƙwalla tace”wallahi aunty Aneelerh bazan Iyaba, koda kuwa duniya zata mallaka mini don in biya mata buƙatarta bazan ta6a amincewa ba, da in sa6ama Allah na ƙwammace in rasa komai dana mallaka don In biyata kuɗin ta, ina tsoron Allah kuma ina jin tsoron ranar da zan koma gare shi, yanzu idan na mutu kafin in tuba fa”? ta faɗa yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta, kallon da take bin Aneelerh da shi, kallone na mamaki da al’ajabin shawarar da ta bata, har ta fara kokwanton Anya kuwa Aneelerh ce wannan? Ko dai Aljanu sun shige ta ne?
Gyaɗa kai Zahra tayi cikin rauni na murya ta furta “Aunty Aneelerh ki daina wannan maganar kina rikita mini tunanina, idan har ba zaki taimaka mini mu nemi mafita ba bai kamata kina tunzurani akan in aikata zunubi mai girma irin wannan ba, har kin sa nafara kokwanto akanki duk da nasan wacece Auntyna”
Ta6e baki aneelerh tayi haɗi da watsa hannayenta tace” Zahra, we don’t have any other solution besides this, ina ƙara jaddada maki, ki hanzarta zuwa ki biya mata buƙatarta, idan ba haka ba zata kai ƙarar ki kotune sannan ta rufe maku companyn ku, amma idan kika bata hadin kai, kinga zaki ci riba biyu da farko zata yafe maki bashin da take bin ki, na biyu kuma zata yi maku order na kayan amfani daga dubai, wannan fa babbar dama ce agare ki!!!” da sauti mai ƙarfi ta ƙarasa maganar, fuskarta babu annuri, ta yunƙura ta miƙe tsaye, Zahra ta saki baki tana kallon ta da rinannun idanuwanta.
“Ni kinga tafiyata, Idan kin canza ra’ayin ki kina iya zuwa ɗaki ki same Ni, zan taimaka maki da mayukan da zaki gyara mata jikin ki” ta hankaɗe kafaɗa ta juya ta nufi kofar fucewa daga ɗakin.
Kamar sakarya haka zahra tabi bayan Aneelerh da kallo har ta 6ace ma ganinta, hannu biyu ta ɗaura saman kanta, tana faman ambaton kalmar Inna lillahi wa’inna ilaihirraji”un”
Tsantsar tashin hankaline akan fuskarta, wani irin azababben zazza6ine ya lullu6eta, saman floor ta kwanta, idanuwanta na fuskarta ceilling, yau Aunty aneelerh ta bata mamaki, ta karya mata zuciya, duk da har yanzu ta kasa yarda da abunda zuciyarta ke faɗa mata dangane da ita, batasan ya zatayi ba? Don ita har ga Allah bata jin zata amince da shawarar Aneelerh ta ƙwammace ta tattara duk wani abu data mallaka taje ta biyata kuɗinta zaifi mata kwanciyar hankali akan ta sa6a ma Allah, tazo tana danasani mara amfani, babban abunda take jima takaici asarar da zatayi na zuwa gidan Obinna, On friday na satin da suke ciki Za’ayi shagalin birthday na babansu, already sun fidda masu anko, decoration ne da kitso suke buƙatar ayi masu jibi, tasan tarasa wannan damar, Hajiya falmata baza ta bari ta cigaba da yin aiki a companynsu ba muddin bata amince da buƙatarta ba, gashi ita bata da komai, dole ta haƙura tama riga da ta fidda rai, shawarwari ta shiga yankewa da zuciyarta, a karshe ta yanke shawarar Zata yi magana da mahboob watakil ko cikin abokanan sa asamu wanda zai sayi motarta da wayarta, da wannan tunanin baccin wahala ya ɗauke ta, babu ci babu sha tun safe baiwar Allah.
*DAULAR OBIE ESTATE*
Zayn ne kwance saman shimfiɗeɗen gadonsu, daga shi sai short a jikinshi, tun da suka dawo daga office yake ta sharar baccin shi kamar matacce, toilet door din ɗakin aka buɗe Zaid ne Ya fito waist dinshi ɗaure da towel, jikin shi da alamun danshin ruwan wankan da yayo, tun kafin ya ƙarasa gaban gadon ya soma ambaton sunan zayn.
“Bro, get up, I want to have an important talk with you, please,” ya faɗa ayayin da yake ƙokarin zama gefen gadon, hannu yakai yana bubbuga ƙafarshi”pls ka tashi zayn, baccin ya isa haka sai kace mai sleeping sickness, tun da muka dawo daga office kake ta sharar bacci ko dai ka sha ƙwaya ne”? Ya faɗa yana cunkulin kafar zayn da mugunta, dogon tsoki Zayn yaja, yana faman yamutsa fuska ya furta”
“Zain, I don’t want to be stressed, please, let me rest, I’m tired,”
Rai a6ace yai maganar ba tare daya buɗe idanuwanshi ba.
Zain na murmushi yace”Haba babyn mommy, you should wake up, you’ve had enough sleep. I know it’s not just work tiredness that made you sleep, because your secretary told me that you’re not doing anything other than gathering girls in your office. Ko nayi ƙarya?” He spoke jokingly, looking at Zayn’s face, tamkar bai ji me yace ba, Ya haɗe fuska babu annuri.
“Dole kayi shiru, tun da baka da abun cewa, adai dinga jin tsoron Allah, taƙamarka kana da kyan fasali shiyasa kake maƙure Ƴan matasan mata a office kana zare masu ido, don kasan dole suyi maka biyayya tunda suna aiki a ƙarƙashin ikon ......” bai ƙarasa maganar ba, sakamakon zaburar da zayn yai ya miƙe tare da damƙar pillow, ya buga mashi akai, Ya janyo wani pillow ya dinga bugunshi ta ko’ina, Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yake fadin”zaid ka takura ma rayuwata, kai ma ka sani wallahi nafi ƙarfin in maƙure ƴa’ƴan mutane a office, Ni bana yima mace dole in ba ita ta nuna tana buƙatana ba, kai ne dai bunsuru da baka Iya gani ka kauda idonka, Ni da aji na matane suke kawo kansu wurina bani nake kiran su ba” ya faɗa yana hararansa”shashasha kawai mai kama da daddy” Ya ƙare maganar Yana haki kamar wanda yasha gudu, idanuwanshi sun kaɗa jawur saboda baccin da bai ishe shi ba.
“Zayn? Ni ne bunsuru? Kuma mai kama da daddy? Kana nufin shima daddyn mu bunsurun ne”? Fuskarshi a ɗaure yayi maganar.
Ɗaga mashi gira zayn yai”ƙarya nayi ne? Babyn daddy, Nifa ba ina nufin bunzuru na dabba ba, No, just ina kwantanta Namiji mai bin mata ne da sunan bunsuru, kasan shima bunsurun haka ɗabi’unsa suke, duk inda yaga mace sai ya bita, shiko namijin da mata suke kawo kansu gare shi bazai yiwu ba a kirashi da bunsuru, sannan Ni bance hada daddy ba, kai kaɗai na ce” a fusace zaid yace”kada ka manta, dani dakai bamu da banbanci ko a murya, idan ina kama da daddy then you look like him too, and you’re a he-goat as well.
gwalo zayn yai mashi”Oho dai, ai kwanan nan zanje ayi mini surgery amaida mun kamannin fuskata irin na mommyna, donni bana son abunda zai haɗa ni da ku” da zolaya yake yi mashi magana, amma shi zaid sai yake ganin kamar baison shi ne, ganin yadda ya haɗe fuska ne yasa zayn saurin cewa” wasa fa nake yi maka, kaima ka sani ni da kai abu ɗayane, na fadi hakanne don in 6ata maka rai kamar yarda ka tada ni daga bacci”
Yamutsa fuska Zaid Yai”naji, yanzu dai mu ajiye wannan gefe, Ya maganar zuwanmu america”? Yai tambayar yana duban fuskar Zayn
“Bamu da isassun kuɗi a account, Ni dai na hakura, ƙwara kaima ka haƙura kawai muyi zaman mu a ƙasar mu ta gado,”
Girgiza kai Zaid yai”bazai yiwuwa ba, zayn bakasan yadda naci burin haɗuwa da Ummi ba, Jiya har mafarkin ta nayi, na kasa gogeta acikin zuciyata”
Ta6e baki zayn yai”faɗamin acikin mafarkin me kuka aikata”
“Bamu aikata komai ba, kawai dai mun hadu a jabi lake mall, har nake tambayarta yaushe ta shigo ƙasar? Kafin ta bani amsa ka katse mini bacci ka tada ni kana fadin lokacin sallar asuba yayi”
Murmushi Zayn ya sakar mashi”kace nayi maka buƙulu, wata’kil da har kiss ta manna maka da hug”
Harara zaid ya jefa mashi atakure yace”ya zamuyi ni dai? Ko dai mu kar6i Atm din daddy daya ce zai bamu”? da sauri zayn ya girgiza kai Yana fadin”No, ba zamu kar6a ba” zaid yace”why? Ni bansan meyasa baka son mu kar6i Atm dinsa ba, maƙudan kuɗi ne fa zayn zasu ishe mu muje duk inda muke so, wai kai kafi son muyita wahalar jiran salary”?
“Eh, ƙwara mu jira salary, akan mu kar6i kudin da ba mu san inda aka same su ba, ka yi amfani da hankalin ka mana, ina daddy yake da arziƙin tara waɗannan millions of dollars din? Abun da baka sani ba, Dana zauna na lissafa dukiyar mommy ko rabin tashi bata kai ba, ita da ta gaji arziƙin kenan, da farko nayi tsammanin ko kuɗinta ne ta bashi ajiya amma daga bisani na zauna nayi nazari sosai na gane cewa kuɗin nan fa bana mommy bane, kuma ba albashin daddy bane suka tara mashi su, Ni tsorona kada mu je mu kar6i kudin sai mun gama sharholiyarmu asiri ya tonu agano daddynmu yana aikata wani abun, duk da ina kyautata mashi zato, amma gaskiya ni zaid ban yarda da kuɗin nan ba, bada guminsa ya tara su ba, akwai dai wani abun a ƙasa”
Damuwace ƙarara akan fuskar zaid sam babu alamun Ya fahimci zancen twin bro dinsa.